Sashe 106
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da Aunty babba tabarta a asibitin nan magashiyan rai hannun Allah,Sai yau ta dawo cikin Hayyacinta,duk ta bushe ta dishe ta ƙanjame,jikinta duk faci,kamar wadda tayi hatsarin Mota,Komai nata ya ƙare,tayi mamakin ganinta a asibiti kuma babu kowa atare da ita,daƙyar ta iya miƙewa zaune,jikinta sae kerma yake yi,lokaci ɗaya ta shiga tariyo abunda Haroon yayi mata,fashewa tayi da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,duk taji ta tsani kanta kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu,cikin shessheƙar kuka take faɗin"Meyasa na farka ban mutu ba?me yayi mun saura acikin duniyar nan,Natsani kaina,Natsani komai ban sha'awar cigaba da zama acikinta!bazan ta6a yafe mashi ba,mugu azzalumi ya cutar da rayuwata,hannu tasa ta yaye farin yadin da aka rufeta da shi,riga ce ƴar dai dai guiwa aka sanya mata blue colour kamar uniform,yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin ƙoƙarin ɗage rigar don taga menene a wurin,don tana jin kanta kamar ba dai dai ba,
 Slowly ta tattare rigar,ta dage ta,koda tayi arba da gabanta,A rikice ta mayar da rigar ta rufe tare da fashewa da wani kukan mai cin rai,
 Tana cikin kukan nan,Dr ya shigo tare da Nurse abayanshi,
  Lallashinta suka shiga yi har suka samu ta lafa,Sannan Dr ɗin ya soma magana a tsanake,
 "Baiwar Allah,Ya jikin naki"?_
Cikin shessheƙar kuka tace"da sauƙi,dan Allah ku faɗamun wanene ya kawo ni asibitin nan,yaushe aka kawoni,"tana magana hawaye na wanko fuskarta,
 "ƴar uwarki ce,ta kawoki asibitin nan,Tun last week,Sai dai tun ranar da ta kawoki,Ta gudu tabarki anan bamu ƙara jin ɗuriyarta ba,Mun nemeta sosai ba mu same ta ba,A ƙarshe sai muka samu wannan wasiƙar a gefen gadon ki,bamu karanta abunda ke ciki ba,"ya ƙarasa maganar tare da miƙa mata wasiƙar,
Tunkan ta kar6a gabanta ya shiga faɗuwa rasss!rass!buɗe paper ɗin tayi ta soma karanta abunda ke cikinta,tun da ta fara karantawa tafin hannunta ɗaya ke rufe da bakinta,hawaye sai shararowa sukeyi daga cikin idanuwanta,ƙiris ya rage zuciyarta ta buga saboda tsabar takaici,Ba ta ta6a tsammanin cewa Aunty laila zata iya guduwa tabarta a asibitin ba,Taji ciwon kalmar nan da ta kirata,Wato karya wadda ba'a rabata da maza,ta yanke mata hukunci batare da tasan ainihin abunda ya faru da ita ba,"
Dunƙule takardar tayi ta cukuikuyeta a hannunta,sai faman matsar kwalla take yi,wasu nabin wasu,
"Lokacin sallamar ki bai yi ba,Amma ya zama dole muyi discharge ɗinki saboda kuɗin gado da aka biya sun ƙare,Sannan akwai wasu bayanai masu mahimmanci game da lafiyarki,da muke so mu samu wani makusancinki mu sanar dashi,Gashi baki da kowa,Bayan wannan akwai alluran da kike buƙata da kuma magunguna domin bunƙasa lafiyar jikinki,Ko kina da wani wanda zai iya taimaka maki"?
 Kuka sosai hayaam take yi,tunani ta shiga yi wa zata kira yanzu don ya taimake ta?Waye take dashi wanda zaiji tausayinta,A iya saninta bata da kowa,in ma akwai babu wanda zai agaza mata saboda sanin Mugun halinta,Shiyasa a koda yaushe akeso mutun ya kasance yana aikata abun kirki a rayuwarshi,ba ka son awani hali zaka tsinci kanka ba a nan gaba ba,duk wani abu da kake taƙama dashi,Walau kyau ko dukiya ko mulki,wata rana Allah zai iya kwace abunshi,Hayaam tayi dana sanin rayuwarta gaba ɗaya,abun ya tsaya mata arai,Wai har ƴar uwarta wadda suka fito ciki ɗaya,Zata iya guduwa tabarta a gadon asibiti rai hannun Allah,ta rayu kota Mutu wannan badamuwarta bace,Wannan wace irin rayuwace?ɗan uwa na gudun ɗan uwanshi,koda yake ɗa ma ya kashe ubansa,Sau nawa akayi?
"Baiwar Allah,kin yi shiru ba kice komai ba"?Dr É—inne ya katse mata zancen zucin da takeyi,
 Cikin shessheƙar kuka tace"Dan Allah,ku taimaka mun da waya,inaso na kira ƴar uwata ne,"_
Hannu Dr ɗin yasa a aljihun wandonshi ya zaro wayar shi,Infinix ya miƙa mata,jiki na rawa ta kar6i wayar,sai da ta ruƙeta a hannunta ta shiga tunanin wa zata kira,Bakowa ya faɗo mata aranta ba,Fa ce AMANI,duk da tana jin fargabar kada Amani,ta balbale ta da faɗa sakamakon irin wulaƙancin da sukayi masu,daƙyar ta iya danna numbobin wayar Amani,da yake ta haddace numbarta a kanta,Danna mata kira tayi,nan take ya shiga,gabanta sai faɗuwa yake yi,almost 3 times Amani bata ɗaga ba,
A lokacin tana a kitchen tana shirya lunch,tajiyo muryar Amaal tana kwala mata kira,fitowa tayi daga cikin kitchen É—in ta tunkarota tana tambayar wanene ke kiranta a waya,
Amal dake saukkowa downstairs,tace"New number ce,bansan wanene ba,ta ƙarasa maganar tare da miƙa mata wayar,zuba ma numbar ido tayi tana kallonta,a ƙa'ida bata cika ɗaukar bakuwar number ba,amma tunawa da yadda Amal tazo hannunta,ta hanyar kira da bakuwar number,yasa tayi tunanin ɗaga kiran kada ace wani abu mai mahimmanci ne,Sanya wayar tayi a kunnanta bayan ta amsa kiran,sallama tayi"Assalamu alaikum,"
 On the other hand Hayaam na jin an ɗaga kiran,jiki na rawa ta kara wayar a kunnanta,cikin shessheƙar kuka ta ambaci sunanta"Aunty Amani,"
 Cike da mamaki Amani tace"To fa,kamar muryar Hayaam nake ji,"
Murya na kerma tace"Ni ce,"shiru amani ta É—an yi kafin tace"Lafiya kika kirani?fuskarta a É—aure tayi tambayar kamar tana agabanta,
 Cike da fargaba hayaam tace"Aunty Amani ina gadon asibiti,nayi fiye da sati a kwance,babu wani a kusa dani,"
  Murmushi Amani ta saki tare da cewa"Sai akai yaya kenan?menene amfanin kira na?ina Laila ne?inasu Abrah?
 Jiki asanyaye Hayaam tace"Duk basu atare dani,Aunty laila itace ta kawoni asibitin,Amma ta gudu ta barni ni kaɗai,gashi ina cikin mawuyacin hali,kamar zan mutu,"
 tana kai ƙarshen maganar Amani tace"Oh Allah sarki,Allah ya baki lafiya,"
 "Dan Allah Aunty Amani ki taimaka mun,Nasan kina da kyakkyawar zuciya,"
 Fashewa Amani tayi da dariya mai sautin gaske,hada yin shewa kafin tace"Sai yau kika san inada kyakkyawar zuciya?Kin manta irin rashin mutuncin da kuka shuka mana?Ashe akwai rana irin wannan da zaki nemi taimako a wurina?bakiyi tunanin hakan ba?Saboda tsabar rashin kunya a haka kike tunanin cewa zan taimake ki,Koda yake dama ae ba kunya gare ku ba,"guntun tsoki taja mtswww kafin ta ɗaura da cewa"Karki kuskura ki ƙara kiran layina da sunan taimako,don da in taimaki Mugaye masu kafirar zuciya irin taku,wlh ƙwara na tattara duk wani abu dana mallaka,na kaishi gidan marayu,ko Allah ya bani Lada,Amma taimakon irinku,bakomai zai janyomun ba,fa ce Zunubi!"tana kai ƙarshen maganarta,tun kan taji me Hayaam zata ce mata,Nan take ta katse kiran,
 "Aunty Amani meyasa zakiyi mata haka"?Acewar Amal,wadda tuni tausayin hayaam ya kama,
 Harara Amani ta watsa mata tare da cewa"Oh harkin manta irin Muguntar da su kayi mana kenan!waɗannan mutanen da baƙin cikinsu mahaifiyar mu ta mutu,Sannan sune su kayi silar Da mahaifinmu ya Zauce,yake rayuwa tamkar mahaukaci,Bayan wannan Sune suka wulaƙantar da rayuwarki suka mayar dake tamkar dabba a haka kike tunanin zan iya taimakonsu!"?
  Cikin sanyin murya Amal tace"Aunty Amani be kamata kina tuna abunda ya faru ba,wannan su da Allah,Tunda har hayaam ta kira a waya tana neman taimakonki,Yakamata ki agaza mata,koba komai ita ƴar uwarmu ce,bai kamata mu juya mata baya a irin wannan halin na neman taimako ba,Wata'kil ya zamto silar shiriyarta,dama kuma shine abunda muke fata,duk wani wanda ke aikata badai dai ba,ya gane kuskurenshi ya koma ga Allah..."sosai Amal ta shiga tausar Amani,har ta ɗan fara saukowa,
Tunda Amani ta katse mata kira,ta fashe da wani irin matsanancin kukan,mai cin rai,Hada majina,miƙa ma Dr ɗin wayarshi tayi batare da ta iya furta mashi komai ba,Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,shi da nurse ɗin dake atsaye suna kallonta,duk ta fita hayyacinta,
 "Am sorry sister,dukkan tsanani yana tare da sauƙi,Ki ci gaba da addu'a in sha Allah,Zaki samu wanda zai taimake ki,"ɗagowa hayaam tayi da idanuwanta waɗanda sukayi jawur tana kallon nurse ɗin da tayi maganar,cikin shessheƙar kuka tace"Allah bazai ta6a yafe mun zunubin da na aikata mashi ba,Sakayyace ke bibiyata,haƙiƙa Nayi danasanin zuwana wannan duniyar,"tana magana hawaye na zuba akan fuskarta,
 Nurse ɗin tace"Ki gode ma Allah da kika kasance araye har wannan lokacin da kika gane kuskuren da kika aikata,baki mutu kina mai aikata shi ba,Yanzu dama ce agare ki,da zaki tuba ki koma ga Allah,"
 Tana kai ƙarshen maganarta,Tabi bayan Dr ɗin suka fuce daga ɗakin,
Sosai hayaam ke yin kuka har kanta ya fara ciwo,Ga uwar yunwa dake cinta,kamar tayi hauka,zama tayi zugudum tana tunanin inda zata dosa idan likita ya sallameta,bata da kowa babu wurin wanda zata je,gashi bata da ko sisi balle ta doshi gida,ko da tana da kudin inama zata iya zaman mota zuwa maiduguri a wannan halin,saboda raunin dake a jikinta,Batajin zata iya taka ƙafafunta ma har taje wani wuri,uban tagumi ta zabga,tare da rufe fuskarta,tana cigaba da shessheƙar kukan,
Almost 30 mins bata motsa ba,tana cikin wannan halin,Ta jiyo sautin takalma,Kamar ana shigowa É—akin da take ciki,
  "HAYAAM!"kai tsaye kiran ya shigar mata har cikin dodon kunnanta,a firgice ta ɗago don taga wanene,har sai da gabanta ya faɗi,Abunda batayi tsammani ba,Hannu tasa tana murza idanuwanta,don ta tabbatar da abunda su ke gane mata,
 Amani ce atsaye bakin ƙopar,jikinsu na sanye da jallabiya,sunyi rolling veils a kansu,Hannun Amani na ruƙe da Hand bag ɗinta,Amal kuma na ruƙe da Basket mai ɗauke da food stuffs,da suka zo mata dashi,
  Sakin baki hayaam tayi tana kallonsu cike da tsananin mamakin ganinsu,Lokaci guda kuma tasake fashewa da wani kukan na farin cikin ganinsu,
 Ƙarasa shiga cikin ɗakin sukayi,abayansu kuwa Dr Osman ne a biye dasu,likitan dake kula da ita,
  Ashe bayan fitarshi daga ɗakin Hayaam,ya wuce Office ɗinshi,bada jimawa ba,sae ga kiran Sabuwar numbar a wayarshi,Daya ɗaga kiran,suka gaisa da Amani,ta buƙaci ya bata address ɗin asibitin,Ba ƙaramin farin ciki likitan yayi ba,Saboda ya gane cewa ƴar uwar mara lafiyannan ce,Bayan ya tura mata address ɗin asibitin,After some minutes Motarsu Amani ta shigo asibitin,da kanta tayi driving ɗinsu a motarta,Bayan sun ƙaraso ta kira layin doctor ɗin,Da kanshi yazo inda suke,sannan ya jagorance su izuwa Room ɗin da aka kwantar da Hayaam,