← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 212

Sashe 104

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bayan komawarsu hannun kishiyar babata,Sai hankalin mu ya dawo kan tunanin a ina zamu ga uwar yaran nan,Nemanta muka bazama yi acikin unguwar nan ruwa A jallo,duk wasu gidajen masu unguwanni na kewayen mu mun cigita haka ma ofishin yan sanda,tsawon lokaci ana nemanta bamu same ta ba,Hankalinmu ya tashi,Saboda sanin cewa Yarinyar nan bata da kowa,Gashi tabar gida a wani yanayi na ta6in hankali,Ga ƴa'ƴanta dake buƙatarta,hakan yasa bamu yi kasa a gwiwa ba ni da baban umari muka kai cigiya awani gidan Redio amman shiru kake ji ba Abu babu dalilinta Allah kaɗai yasan ina ta nufa don kasan garin kano da faɗi,aƙarshe muka fara zullumin anya Abu na'a garin nan ma kuwa,hakan yasa muka hana idonmu bacci wurin rokon ubangijin sammai da kassai da ya bayyana mana ita cikin aminci ya kareta aduk inda take,tsawon lokaci muna ta rokon Allah ba tare da gajiyawa ba,Ana haka kwatsam wata rana muka samu labarin bayyanar Abu ta hanyar Sanarwa a gidajen radio dana talabijin cewa Ana neman danginta,tare da adireshin asibitin da aka kwantar da ita sakamakon motar wani bawan Allah da ta bugeta a saman titi tana gararanbarta shine ya kaita asibiti ya kuma bada ayi cigiyar danginta,koda sanarwar nan ta isar mana jiki na rawa,Ni da Maman sadeeq tare da yaron nan ɗan wurin makwabcinmu muka kwasa muka tafi asibitin,ba ƙaramin daɗi muka ji ba da muka samu abu zuciyoyinmu suka cika da farinciki,duk da babu hankali atattare da ita,A lokacin likitan dake kula da ita ya buƙaci akawo wani makusancinta,wata'ƙil adace ta dawo cikin hayyacinta idan tayi ido biyu da ƴa'ƴanta da take yawan ambaton sunansu,jin haka yasa na yanke shawarar zuwa katsina domin in taho da yaran nan,ko Allah zaisa adace abu ta dawo cikin hayyacinta,alokacin nayi kokarin kiran lambar tsohuwa don in sanar da ita game da zuwa na don a shirya ma yaran amman a kashe,hakan baisa nayi tunanin wani abu ba,don dama mafi yawancin lokutta wayar tata na kasancewa a rufe sai anyi sa'a ake samu,ahanzarce na shirya zuwa katsina,Sai dai kash!wani mummunan labari ya riskeni a lokacin da naje unguwar da suke,Na rasuwar ita mariƙiyarsu Kishiyar babata tsohuwa,Sannan kuma naji cewa an liƙa masu ƙazafin maita,wai sune suka kashe ta saboda an ga kumfa a bakinta kamar taci guba,Hankalina yayi mugun tashi saboda ina da tabbacin cewar yaran abu bazasu ta6a aikata hakan ba,Ni shaida ne akan yaran,nayi baƙin ciki sosai kamar zan haɗiyi zuciya in mutu lokacin da Makwabcinsu ya rakani police station ɗin da aka kulle yaran,ƴan sandan da muka samu a wannan lokacin sun tabbatar mana da cewa,a nan police station ɗin aka kawo case ɗinsu,sai dai daga baya sun bar hannunsu sakamakon ciwon ɗaya daga cikinsu daya tashi aka kaisu asibiti Anan ne wani babban Jami'en Soja ya kashe Case ɗin gaba ɗaya,Shine silar barinsu asibitin,kamar zanyi hauka alokacin,Saboda tsabar takaici,na nace akan dole ƴan sandan nan su haɗani da mutumin daya kar6i yaran,Amma suka sanar dani cewa su kansu basu san wanene ba,Saboda basu bane asalin waɗanda case ɗin ya mutu ahannunsu ba,waɗancan anyi masu canjin wurin aiki,A ƙarshe dana takura masu na dinga zarya a police station ɗin akan su faɗamun waye wannan jami'en sai su kayi mun barazanar idan na ƙara zuwa zasu ɗaure ni,Tun daga wannan lokacin,jiki a mace nadawo kano alokacin aka sallami Abu bayan likitan dake kula da ita ya bada shawarar amaida ita asibitin masu ta6in hankali amman muka dawo nan gidana da ita da tunanin yi mata addu'oi don alokacin ina ganin kaman harda sihiri atare da ita,haka na dukufa yi mata addu'oi ba dare ba rana amman sauki dai sai wurin Allah,yadda taga rana haka take ganin dare sam bata bacci,sai sambatun Babanta da ya'yanta,in takaice maku dai Abu buge buge ta fara tana kokarin guduwa,Babu yarda muka iya muna ji muna gani haka muka dauki Abu muka kaita Asibitin mahaukata......"daƙyar ya ƙarasa maganar saboda kukan daya zo mashi,yana kai ƙarshen maganar ya fashe da kuka,tuni hawaye sun wanke fuskokinsu gaba ɗaya,Musamman Sehrish sosai take kuka,
  Muryar Abusufyan na kerma yace"Ya..yanzu...a wani psychiatric ne aka kaita,"
  Maman sadeeq ce ta bashi amsa da cewa"Tana a Dawanau Psychiatric Hospital,ko watan daya gabata sai da muka je gano ta,baiwar Allah tana cikin halin ha'ula'e,gwanin ban tausayi,duk in muka je kai mata ziyara,haka zamu sameta tana ta kuka tana sambatun Ya kashe mata mahaifinta,Ƴa'ƴanta Suna ina,akawo mata ƴa'ƴanta,kada ya kashe mata su,"
Jin wannan maganar yasa Sehrish ta ƙara sautin kukan nata sosae,
  "Inason ganinta yanzu,"Abusufyan ne yayi maganar tare da miƙewa jikinshi na rawa yace"dan Allah idan ba damuwa,Ku taimaka ku jagorance mu izuwa asibitin,"
  Miƙewa suka yi gaba ɗayansu,Baban Sadeeq yace"nafi kowa farin cikin wannan ranar,duk da ina da uzuri a makaranta,Zan iya dakatar da komai,dan In raka ku muje a tare,"
  Ɗaga hannu Abusufyan yayi sama yana godiya ga Allah,Ita kanta Sehrish tsantsar farin cikine ya rufe ta,
  Atare suka fito daga cikin gidan,a ƙopar gidan suka tsaya,Abusufyan ya ɗauko wayarshi tare da dannawa Sgr kira,Bayan ya amsa kiran anan yake sanar dashi cewa Zasu wuce Dawanau Psychiatric Hospital,Sgr yace su haɗu acan,"

A back seat na motar Baban Sadeeq tare da Maman Sadeeq suka shiga suka zauna,Yayin da Abusufyan ya shiga mazaunin driver,Sehrish na a gefenshi,ganin yadda hannunshi ke ta kerma wurin ƙoƙarin tashin motar yasa tace"Daddy,Anya zaka iya driving ɗin nan"?
  A ruɗe yace"Daughter,ki ganni kawai,ba zaki gane halin da nake ciki ba,Am so eager to see her,Kamar nayi fiffike,"
Murmushi ta ɗan yi,Ita kanta ji take da ace tana da fiffike da ta tashi sama don ta ƙarasa asibitin da wuri,

da gudun gaske ya fisgi motar kamar zasu tashi sama,cikin ƙankanin lokaci suka ƙarasa asibitin,

*DAWANAU PSYCHIATRIC HOSPITAL*

A dai dai lokacin da Abusufyan yake ƙoƙarin shigar da motarsu cikin asibitin,Sai ga Motocin Sgr da jiniya mai sautin gaske,sun shararowa a jere,Jibga jibgan sojoji ne a saman motocin bana wasa ba,ko shugaban ƙasa albarka,tuni mutane suka dare aka bar masu hanyar su kaɗae,
A daidai bakin gate din aka tsaida jiniyar,kafin motocin suka shiga cikin Asibitin, Motar Abusufyan ce ta fara shiga sannan nasu suka rufa masa baya,wasu daga cikin sojojin dake a motar ƙarshe ne suka diddiro suka ƙame a bakin gate din shiga sai faman mazurai suke yi kowannansu hannunshi na riƙe da ƙatuwar bindiga gwanin ban tsoro,parking ɗin motocin su kayi,buɗe motar Abusufyan yayi tare da fitowa daga ciki,ya zagaya ya buɗema Su Baban Sadeeq motar suka fito,Sannan itama Sehrish ta fito,tana ƙarewa asibitin kallo,tun kafin ma su shiga ciki,ta fara ayyana yadda zata samu mahaifiyarsu,duk da tana cikin damuwar halin da zasu same ta,

Fitowa Armstrong yayi daga cikin Motarsu,ya zagaya tare da bude mashi,A hankali ya zuro ƙafarshi daga cikin motar,Kafin ya ƙarasa saukowa daga cikinta Masha Allah,Open shirt ce sanye a jikinshi white colour,rigar ta bayyana Ƙirar faffaɗan ƙirjin nan nashi,Cos bai sanya button ko ɗaya ba,a buɗe yabarta sai farar vest,Dogon wandon jikinshi black colour ne,Wankan black & white ya ɗauka,ƙafarshi na sanye cikin oxfords shoes,daga saman sumar kanshi kuma ya sanya facing cap black,Eyes ɗinshi na manne da Sunglasses,Wa'iyazubillah Ya haɗu iya haɗuwa,kamar a buga a jarida,
Duk da yanayin da suke ciki hakan baisa sun ƙi kallon wankan nashi ba,Musamman Babban sadeeq da kuma Maman sadeeq,tare da sauran jama'ar dake zarya a cikin asibitin,Yayi matuƙar jan hankalinsu,Ita kanta Sehrish sai da ta girgiza da irin wankan da ya ɗauka,

Kama hanyar shiga ciki su kayi,Baban sadeeq ne agaba shi da Maman sadeeq,Abusufyan da Sehrish na abayansu,yayin da Sgr tare da Armstrong suke a biye dasu,sai wasu daga cikin security,mutum biyu dake ruƙe da jibga jibgan bindigogi,suna take mashi baya,a bakin OPD suka ƙame,yayin da Sgr da Armstrong wanda ƙugunshi ke manne da bindigu pistol guda biyu suka shiga ciki,batare da sunsha wahala ba saboda su Maman Sadeeq sun san asibitin,suka nufi wurin da nurses suke,wato nurses station,Anan suka taras da Nurses ɗin dake Duty,koda nurses ɗin nan sukayi arba dasu,gaba ɗaya hankalinsu ya koma akan Sgr,kallon ƙurulla suka shiga binshi dashi,
Gyaran murya Abusufyan yayi masu hankalinsu ya koma akanshi,A natse ya soma magana"Sannunku da aiki,"
  Atare suka haɗa baki wurin amsa mashi"Yawwa yalla6ai,munayi maku barka da zuwa,"
   gabatar masu da kanshi yayi tare dasu Sehrish kafin yace"akwai patient ɗinmu dake anan asibitin,munzo dubata ne,'
  ɗaya daga cikinsu ce,ta kai hannu gaban drawer chest ɗin dake a jikin table ɗin gabansu,tana ƙoƙarin zaro roster ɗinsu,tace"Zan iya sanin sunan mara lafiyan naku,"
Abusufyan yace"Sunanta Zainab ibrahim buzuwa,"yayi maganar tare da kallon baban Sadeeq,don yaji idan ya faÉ—a dai dai,jinjina mashi kai yayi alamar eh,
  A saman table ɗin gabansu ta ajiye patients roster ɗin,tana dudduba sunan marasa lafiyan,
  "Last week,an canza ma wasu daga cikinsu wurin zama,bansan ko kuna da masaniya akan hakan ba,"acewar nurse ɗin
  Kallon juna sukayi hankalinsu aɗan tashe fargabarsu kar ace,an ɗauke abu daga asibitin,
  "Yawwa,itace Zainabu ibrahim buzu ko"?
Har suna haÉ—a baki wurin cewa "eh,itace,
Murmushi Nurse ɗin tayi tare da cewa"Zainab tana a female ward B,"kallon abokiyar aikinta dake a gefenta tayi tare da cewa"kiyi masu jagora izuwa ɗakin da Zainab buzuwa take,"Amsa mata tayi da toh,sannan ta fito tare da nufar wani corridor,gaba ɗaya suka bi bayanta,kowa da abunda yake saƙawa aranshi,jikin Sehrish dana Abusufyan sae kerma yake yi,duk sun sha jinin jikinsu,

Tun kafin su ƙarasa ward ɗin,mahaukatan dake a killace suka fara kwala masu kira,
  "Yalla6ai,yalla6ai,"Sehrish ba ƙaramin tsoro taji ba,gasu nan gwanin ban tausayi,sae faman zuru hannuwansu suke yi daga cikin bars ɗin,
  "Baiwar Allah!"wata mahaukaciya ce ta kwala ma Sehrish kira,tana nuna ta da hannu,a firgice Sehrish ta juya tana kallonta,Washe mata haƙora tayi tana kashe mata ido ɗaya tace"ki ce wa mijinki ya dinga sanya Niƙabi a fuskarshi,in ba haka ba wlh za'ayi maki kwacenshi,Don mu nan da kike ganin mu ba cikakken hankali ne damu ba,"
Chapter 104 · 0% Book details