Sashe 152
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan wasu mintuna Sgr ya fito É—auke da Sehrish saman kafaÉ—arshi ya É—aura mata towel,zaunar da ita yayi saman front chair ta gaban madubinshi,
 Saitin kunnanta ya duƙo a hankali yace"in shafa maki ne ko zaki iya shafawa,"?da sauri ta ɗaga mashi kai Alamar eh,
 "Okey,"ya miƙe tare da juyawa ya shige toilet ɗin don ya samu yayi wankan shima,Tana jin ya rufe ƙopa ta buɗe idanuwanta,Sae faman zabga uban murmushi takeyi,bata ta6a tunanin Sgr zai iya caring ɗin mace ba irin Yarda yayi mata a yau,Ko jinjira albarka,bakomai yafi burgeta ba fa ce Yarda yake ɗaukarta asaman kafadarshi,daɗi take ji sosai,Ajiyar zuciya ta ɗan sauke tare da kai hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin body oils ɗinshi ta soma shafawa ajikinta,Bayan ta kammala ta feshe ko'ina da turarenshi ita ma yau ta ɗanɗana turaren Babban Yaya,Zasu yi ƙamshi iri ɗaya,
Miƙewa tayi daga saman kujerar ta nufi gadon tana ƙoƙarin ta gyara mashi,zanin gadon ta cire ta musanya da wani sabon da ta ɗauko ta jera pillows ɗin,Tana cikin gyaran nan tajiyo alamun motsin ƙopa tasan shine zai fito,A hanzarce ta haye saman gadon ta zauna tare da jingina bayanta ta kuma rufe idanuwanta saboda kunyarshi da take ji,Ya gama gane mata jiki saƙo da lungu,"
Sako fararen ƙafafunshi yayi masu sanye da slippers,A saman ƙaramin carpet ɗin dake bakin ƙopar toilet ya cire slippers ɗin,towel ya ɗaura asaman waist ɗinshi,Slowly ya ɗago da blue eyes ɗin shi yana kallon Sehrish,takawa yayi izuwa gaban dressing mirror ɗin ya tsaya don ya gyara jikinshi,satar kallonshi Sehrish ta dinga yi ta wutsiyar idonta,ba ƙaramin kyau yayi mata ba,ya saki kwantacciyar sumar kanshi ta baya,natsuwa tayi tana kallonshi,Ashe Sgr ya gane tana satar kallonshi,
Da gangan ya sanya hannunshi asaman ƙugunshi ya warware towel ɗin jikinshi,Aikuwa a ruɗe Sehrish ta kifa kanta saman pillow Jiki na kerma,duk a tunaninta babu short ajikinshi,Ƙayataccen murmushi Sgr ya saki,Shi kanshi baisan ya kubce mashi ba,razanar da tayi ne yaso bashi dariya,
É—ago da kanta tayi daga jikin pillow É—in don ta saci kallonshi,karaf suka haÉ—a ido dashi,wani irin kallo taga yanayi mata,murmushi ta saki tare da mayar da fuskarta jikin pillow É—in ta rufe,
Suna cikin wannan Yanayin na shauƙi Hosana ta kwala Sallama da ƙarfi,da sauri Sehrish taja bargon ta lullu6e kanta gaba ɗaya,Wucewa can cikin ɗakin yayi wurin closet ɗinshi,Jallabiya Ya zura ajikinshi kafin ya dawo ya zauna daga gefen gadon,
Jin Anyi shiru ba'a bata izinin shiga ba yasa tace"In shigo"?tayi tambayar tana leƙa kanta cikin ɗakin
 "Come in"ya bata permission din shiga,a tare da Jahad suka zo ɗakin tana la6e abayan Hosana,dama tun kafin su Shigo taja kunnan Hosana akan karta kuskura ta faɗa masu ɗaki batare da an basu izinin shiga ba,don tasan halinta,ɗan kaine da ita,
A tsanake suka shigo cikin ɗakin hannunsu ruƙe dana juna,
 "Yaya Rafayet ina kwana,kun tashi lafiya?Ya mai jiki"?
 "Alhamdulillah"bayan ya amsa masu ya miƙe tare da kallon Jahad a lokacin Hosana ta koma bakin gadon tana kallon Sehrish dake kudundune cikin bargo kamar mai bacci,
 "Ki ɗauko mata kayan da zata sanya ajikinta,"
 "Toh"ta ambaci hakan tare da juyawa ta nufi kopar fita daga ɗakin,fitowa palour yayi tare da samun wuri saman Sofa ya zauna,
"Rishi ya jiki?kinji sauƙi"?a hankali Sehrish ta ɗan zame bargon data lullu6e fuskarta dashi,kamar wadda ta tashi daga bacci haka tashiga mutsustsuka idanuwanta,kallon Hosana tayi daƙyar ta iya buɗe baki tace"da sauki,"
"Allah ya baki lafiya rishi,jiya fa ko bacci banyi ba saboda tunaninki...."murmushi kawai Sehrish tayi mata don tasan cewa ƙaryane,ba ƙaramin abu bane zai hana hosana yin bacci ba,
 Cigaba da magana Hosana tayi"nasha kuka Allah,Oumma tayi tayi dani akan in kwanta inyi bacci,Naƙiya nace nidai bazan iya bacci ba,har sai kin samu sauƙi,"ta ƙarasa maganar,hada ɗan kwa6e fuska,
 Murmushi Sehrish taci gaba da yi tana kallonta,
 Dawowa Jahad tayi hannunta ruƙe da rigar da ta ɗauko ma Sehrish,turkey gown mara nauyi red colour mai maɗaurin igiya daga tsakiyarta,atare da mayafinta ta ɗaurosu asaman hannunta,Shigowa palourn ta yi da sallama abakinta,Amsa mata sallamar yayi kafin ta wuce bedroom ɗin,
Anan ta samu Hosana tana ta shirga mata ƙarya,da alama ba ƙaramin nishaɗi take sanyata ba,agaban gadon ta tsaya tare da kallon hosana"ki sauka down Oumma na kiranki zaku ci abinci ne An kammala shirya breakfast,"jin haka yasa Hosana ta juya da gudu ta fita daga bedroom ɗin,dama wayau Jahad tayi mata don tabar ɗakin ko Sehrish ta samu ta shirya,ta lura babu kaya ajikinta,
"Ya jikin naki My own sis,"fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa mata da ƙyar"Am feeling better now,"
"Allah ya ƙaro lafiya,Ga wannan Ya rafayet ne yace in kawo maki,"tayi maganar tana miƙa mata kayan,yunkurawa tayi tare da miƙewa daga zaune takai hannu ta kar6i kayan,kafin ta sauko daga saman gadon,ɗaure da ɗan towel ɗinta,
"Bari na jiraki a palour,"da sauri Sehrish ta dakatar da ita"A'a,zan shiga daga cikin ɗakin na sanya kayan,Idan na kammala sai mu fita tare,"ba ƙaramar wahala take shaba idan zatayi magana,kamar ana tsaga bakinta haka take jin raɗaɗin,juya baya jahad tayi tana ƙarewa Bedroom ɗin kallo,a can ƙasan zuciyar kuwa tsabar farin ciki ne,Saboda ta gano wani abu game da Babban Yayansu,Da alama Ya fara faɗawa tarkon rishi ɗinsu,ashe da Rabon mafarkinta ya zama gaskiya,Wato na ganin Sehrish da ƙaton ciki ga kuma kwaɗayin Son Ganin Ƴa'ƴansu da take yi,lokaci guda kuma Yanayinta Ya canza,matsananciyar damuwa ta bayyana akan fuskarta,Bakomai Yasa ta shiga wannan Halin ba,Fa ce Masoyinta da ta tuna,tayi babban rashi wanda har ƙarshen rayuwarta bazata ta6a manta raɗaɗin rasa shi da tayi ba,a duk lokacin da suke waya dashi haka zai addabeta da tambaya wai Idan sunyi Aure A daren farko me zasuyi,duk in ta tuna wannan tambayar ta Junaid sai Murmushi Ya bayyana akan fuskarta,wasu siraran Hawayene suka soma saukowa saman cheeks ɗinta,
"Jahad,na shirya zamu iya tafiya,"jin muryar Sehrish yasa tayi saurin goge hawayenta,sannan ta juya tana kallonta,Ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba,kamar wanda zata gasar kyau,Hannunta na a ruqe da wayarta da ta ɗauko,
 "Masha Allah"tayi maganar tare da ruƙo hannun Sehrish tana murmushin dole,
Atare suka shigo cikin palourn,har zasu fita ta É—an dakata tare da juyawa ta kalli Sgr dake zaune saman sofa,ya jinginar da bayanshi,yayin da ya lumshe idanuwanshi tamkar wanda Bacci bai ishe shi ba,
 Sakin hannun Jahad tayi"ina zuwa,"
Fita daga wajen palourn Jahad tayi tana jiran dawowarta,
  A hankali ta ƙarasa wurin sofan dayake zaune ta tsaya,Cikin sanyin murya ta soma magana"bansan da wasu kalmomi zanyi amfani dasu ba wurin yi maka godiya,saboda irin kyakkyawar kulawar daka bani,Thank You So much Ya Rafayet"tunda ta soma magana,Ya natsu yana sauraronta,daɗin voice ɗinta yake ji kamar kamar me ba kaman da take maganar a hankali,
 "Never mind,"yayi maganar batare da ya buɗe idanuwanshi ba,Juyawa Sehrish tayi da sauri ta nufi hanyar fita falon,Sai da ya tabbatar tabar wurin tukunna ya ɗan buɗe idanuwanshi tare da waigawa yana kallon bayanta,har sai da ta fuce daga falon,
A 6angarensu Hayaam da Abra waɗanda tun jiya suka bar Abuja,Abun da ya faru lokacin da suka isa unguwarsu,wuraren marece tunkafin Su shiga gidansu suka lura da yadda mutane ke kallonsu,tun daga nan suka sha jinin jikinsu,Har nunasu akeyi da hannu ana cewa gasu can sune ƴa'ƴanta,Sun dawo daga yawon biɗiɗin nasu,Wlh anyi asarar Rayuwa,wasu kuma na cewa,Ae laifin uwar tasu ne da bata basu tarbiya ba ita ta lalatasu,Lokacin da suka ƙarasa ƙopar gidansu,A buɗe suka samu gidan,Da sallama suka shiga sunyi tunanin za'a amsa masu amma sai suka ji shiru,gidan babu kowa,komai na gidan babu,An kwashe komai,hatta butoci da bokatai babu,Har kan fanfonsu an 6alleshi,
Nan fa hankalinsu yayi mugun tashi,Tun a tsakar gidan Abra ta saki trolley É—in hannunta,da gudun gaske suka shiga cikin É—akunan suna kwalawa Mammynsu kira,Mammy! Mammy!!gabansu ne ya faÉ—i ganin É—akin mammynsu babu komai wayam hatta katifarta,yanke shawarar zuwa makwabtansu Suka yi donsu tambayi Ina mammynsu taje ne,
Suna zuwa zauren gidan suka fara jiyo hayaniyar mutane,kasa kunne suka yi suna sauraran Surutun mutanen da sukayi masu dandazo a ƙopar gidan,
"Kuna ina la'anannu!waɗanda basu son ciwon kansu ba,Ku fito muci ubanku inba haka ba Mu ƙona gidan da fetur,kun tafi kun barmu da bala'e acikin unguwa,Yau sai mun fanshe haushinmu akanku,Jinin ku ya halatta"
 Jin wannan yasa tsoro ya kamasu,da gudu suka Koma cikin gidan,A ɗaki suka datse ƙopa,Hankalinsu Yayi mugun tashi,Sun rasa gane zunubin da suka aikata har mutane ke neman bugunsu,Suna Cikin wannan halin ne suka ji anyi masu Sallama,muryar Limamin Unguwarsu ce,ƙin fitowa su kayi har saida suka ji yace"Kada kuji tsoron komai,ku fito inason magana daku ne,Naba mutanen anguwar haƙuri Sun tafi,"jin wannan maganar yasa suka buɗe ƙopar ɗakin suka fito,Bayin Allah kowacce jikinta sai kerma Yakeyi,hawaye sharkaf akan fuskarsu,