← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 212

Sashe 113

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Around 12 na dare,Yana zaune gefen gadonshi,message ya shigo wayarshi,da sauri yakai hannunshi ya zarota daga cikin trouser pocket É—insa,buÉ—e message É—in yayi ya soma karanta shi kamar haka,
   _Oga Aiki ya kammalu fa!ka duba whatsapp ɗinka,mun tura maka video zazzafan gaske,nasan yau zakayi kwanan farin ciki_
  Shu'umin murmushin nan nashi ya saki,jiki na rawa ya shiga whatsapp ɗinshi anan ya samu Video ɗin da suka tura mashi,bayan ya kunna Wi-fi ɗin wayarsa,tunkan video ɗin ya ƙarasa yin loading jikinshi keta tsuma harya ƙagara yaga Videon menene,
  Ƙura ido yayi akan screen ɗin wayar,lokacin da video ɗin ya buɗe,motar Junaid ya gani tana ta ci da wuta,ta lomatse ta rakwakkwa6e,Wani irin ihu ya fasa cike da tsantsar farin ciki ya miƙe tsaye yana faɗin"Yess!Yess!!finally Burina ya cika,ko ayanzu na mutu nasan cewa,na gama dasu,na kashe farin cikin da suke taƙama dashi!"
Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da wata irin mahaukaciyar dariya,lokaci guda kuma ya dakata da yin dariyar,jikinshi ya soma kerma sakamakon Muryar junaid da tayi mashi gizau acikin kunnanshi
   _Ya haroon!burinka ya cika ko?ka rabani da rayuwata,laifin me nayi maka?menayi maka dana cancanci wannan ɗanyen hukuncin a wurinka!yanzu shikenan bazan sake ganin ƴan uwana ba?ka rabani da mahaifina kuma kana farin ciki?haƙƙina bazai ta6a barinka ba_
  A tsorace Haroon ya shiga waige waige a cikin ɗakin nashi,ba ƙaramin razana yayi ba,ganin baiga kowa ba,yasa shi sauke ajiyar zuciya,
  ɗago da wayarshi yayi tare da Calling layin waɗanda yasa su kashe mashi junaid,tana fara ringing aka ɗaga kiran,
  Muryarshi asanyaye yace"dagaske ne video ɗin da kuka turomin cewa kun kashe junaid"?
  On the other hand,mutumin yace"ƙwarai kuwa!Yaron nan babu shi yanzu a doron duniyar nan!domin kuwa da truck muka take motarshi,bayan mun tabbatar yana acikin Motar,Amma ita yarinyar bata acikin motar kamar yadda ka bamu umarni,ta tsallaka titi zata siya masu ice cream......"
  Tunkan ya ƙarasa maganar,haroon ya zube saman guiwowinsa,wata irin zufa ce ta shiga tsatstsafo mashi ajikinshi,tuni ta wanke shi sharkaf,
  "Ya Haroon!Kamar baka farin ciki?naji kayi shiru"?
  Kasa buɗe baki haroon yayi,la66ansa sae kerma suke yi,
  "Hello!hello!Oga haroon!kana a kan layi kuwa"?jin shiru bai tanka masu ba yasa suka katse kiran,
  Jikin taƙaura yayi la'asar,gaba ɗaya haroon ya shiga ruɗani,Shin farin ciki yake yi da mutuwar junaid ko kuwa baƙin ciki?Tun yanzu ya fara tsorata da gizan da muryar junaid tayi mashi,
  _Laifin me junaid yayi mun?na kasa yarda cewa ni da kaina na bada umarnin a akashe shi_
  Runtse idanuwanshi yayi sosai,yana tariyo fuskar junaid,mai ɗauke da kyakkyawan murmushi nan nashi,
  Guiwowinsa duk sun sage,ya kasa miƙewa tsaye,yayi fiye da awanni zuƙunne batare daya motsa ba........

*AUNTY BABBA*

Tun bayan da Abra ta gudu daga hotel ɗinnan,Tana fitowa daga wanka,jikinta ɗaure da towel,sam bata kawoma ranta komai ba,duk da tayi mamakin ganin babu kowa,Jinjina kai ta shiga yi tana faɗin"Ko gidan ubanwa taje?bayan na sanar da ita cewa Yanzu zamu tafi,zata dawo ta same ni,"ta ambaci hakan tare da samun wuri gefen gadon ta zauna,tun tana sa ran dawowar abra har ta fara fidda rai,tunawa da abunda ya faru da hayaam a hotel yasa hankalinta ya tashi,tsoranta kar ace itama abra,an samu wani ya ƙurmushe ta ne,hakan yasa tayi firgit ta miƙe tsaye,tare da kai hannu saman bedside drawer ta ɗauki wayarta dake ajiye a samanta,
  Yanke shawarar kiran Abra tayi,tun kafin ta shiga Contacts ɗinta,saƙon abra ya shigo cikin wayar,on the top of screen ɗin wayar,
  Janyo saƙon tayi ta buɗeshi,a tsanake ta soma karanta saƙon
  _Aunty laila sai dai kiyi haƙuri,wlh bazan iya zuwa wurin bokan nan ba!saboda ƙaryar da kika yi mun dangane da hayaam,ashe Aunty hayaam tana kwance rai hannun Allan agadon asibiti,amma kika gudu kika barta saboda kawai tsautsayi ya same ta?ashe dama amfani kike yi damu don ki cimma burinki!baki damu da rayuwarmu ba,Naji tsoro ne saboda nasan cewa nima wata rana in irin hakan ta faru dani zaki gujeni ne,ina mai baki haƙuri Aunty laila,bansan ya rayuwarki zata ƙare ba a Enugu,domin kuwa na kwashe duk wasu kuɗi da muka zo dasu,Na tafi da handbag ɗinki gaba ɗayama,kada ki sha wahalar nemanta Aunty hayaam da aunty Amani ne suka sa nayi hakan a ƙarshe ina maki fatan sa'a_
  Saboda tsabar kiɗima a hautsine ta jefar da wayar ƙasa,Dafe ƙirjinta tayi hankalinta a matuƙar tashe,ta furta"kutumar Uba!Ni Abra zata yiwa iya shege!Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Ya Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani!Ya Allah kasa mafarki ne ba gaske ba,Abra ta yashe ni!ta gama dani!na shiga uku na ni yau! Na gama yawo!
  Tuni Ido ya raina fata,cizon yatsanta ta shiga yi,tana faman yarfa hannunta,Duk tabi ta ruɗe ta rasa inda zata tsoma ranta,
  Zuƙunnawa tayi ta ɗauki wayar da tayi wurgi da ita ƙasa,layin Abra ta kira,unfortunately ta samu wayar akashe!
  "Allahumma Ajirni fil musibati wa'aklifni khairan Minha,Meyasa Abra zatayi mun haka!Nashiga uku ni yau,Wannan wata irin Musiba ce!daga wannan sai wannan?"
  Hawaye ne suka soma saukowa daga saman fuskarta,a susuce ta shiga faɗin"Wlh baku isa ba!baku isa ku hanani zuwa wurin bokan nan ba!Wlh sai naje,Allah ya isa tsakanina Da Amani!Munafuka duk ita ta shirya mun wannan,Ita kuma waccen kingin gardawan bamma san ya akai ta farfaɗo ba,don nasan itace ta sanarwa Amani har suka shiryamin wannan tuggun,Wlh bazan ƙyalesu ba....."Aunty babba fa ta zare sai faman sakin sambatu takeyi,da alama ta fara zarewa,zagaye ɗakin tashiga yi tana safa da marwa,hannunta asaman kanta,
   Yanke shawarar bin bayan Abra tayi,a gaggauce ta buɗe trolley ɗin kayansu,ta ɗauko doguwar riga ta zura ajikinta,Ta yafa mayafi buɗe ƙopar tayi,jiki na rawa,haka ta shiga zagaye hotel ɗin tana neman Abra,har wurin receptionists taje,ta tambayesu ita,hada yi masu kwatancenta anan suka sanar da ita cewa,sunga gifcinta a lokacin da take ƙoƙarin barin reception ɗin,Jin haka yasa Aunty babba ta zabura da gudu ta fuce daga reception ɗin ta miƙi hanyar fita daga hotel ɗin,gudu gudu sauri sauri haka ta fita waje gefen titi tana Neman Abra,
  Hanya ta miƙa tana tafiya tana sambatu,tana ƙoƙarin ta tsallaka titi wata jibgegiyar Mota ƙirar Range rover tayi Awon gaba da ita,Koda mai motar nan yaga aika aikar da yayi jini har asaman glass ɗin motarshi,aikuwa a hanzarce yaja motarshi da gudun gaske ya bata wuta kamar zai tashi sama yabar Wurin!!!
  Aunty babba kuwa sai kwala ihu takeyi tana shure shuren ƙafa asaman titi,
   "Wayyo Allah!nashiga uku!na bani Na lalace!Ya kashe ni!Ya gama dani!"
  Dandazon mutane ne suka taru a kewaye da ita,sun zuba mata ido suna ta kallonta an ransa wanda zai iya taimaka mata,kowa tsoro yake ji kada ace shine yayi silar mutuwarta,Wannan dalilinne yasa aka rasa wanda zai ta6ata,kuma babu wanda yayi tunanin kiran ƴan sanda don yayi reporting akan Incident ɗin,
  Tun tana shure shuren kafarta jini na tsargowa ajikinta,har jikinta ya soma saki alamar rai zai yi Halinsa........

DAMATURU,

Wuraren karfe 1 na dare,Abba na zaune zugudum tsakiyar gadonsu ya zabga uban tagumi,zuciyarshi sai bugawa take yi,kwakkwaran juyi Alexandra tayi karaf idanuwanta suka sauka akan shi,da ya ke akwai hasken bedside lamp dake a kunne,muryarta adisashe tace"Abban Junaid!lafiya har yanzu bakayi bacci ba,"?
Hankalinshi atashe yace"taya zan iya runtsawa?kullum junaid ya saba kirana a waya da daddare kafin ya kwanta yayi bacci,Amma yau shiru wayarshi a kashe,wayar Omar a kashe,na rasa wanda zan samu a gidan in kira shi don ya sanar dani halin da junaid ke ciki,"
Jin wannan maganar yasa hankalin Alexandra ya tashi haiƙam,mikewa zaune tayi cike da mamaki tace"nikaina nayi mamakin rashin kirana da junaid,baiyi ba amma ban kawo komai araina ba har bacci ya dauke ni"
Abba na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,suka ji an ƙwanƙwasa ƙopar ɗakin nasu,
Atare suka haÉ—a baki wurin cewa"Wanene"?
Muryar Twins ce ta amsa masu"Mommy mune,"
Kallon juna sukayi at same time,kafin Abba yace"Ku shigo ciki,"
Tura ƙopar sukayi atare suka shiga kowannansu sai faman hammar bacci yake yi idanuwansu a lumshe saboda baccin da suke ji,
AruÉ—e Alexandra tace"is everything alright twins?me kuke yi har yanzu bakuyi bacci ba"?
Ayaan yace"mommy wlh ba lafiya,mun kasa runtsawa saboda yau junaid kwata kwata bai kira wayarmu ba,Ko text message ɗin da ya saba tura mana yau bamu gani ba,kuma mun bibiyi layinshi a kashe,har ya Omar mun kira muji ko lapia shima a kashe,taya hankalinmu zai kwanta,"yana kai ƙarshen maganarshi jahan ya ɗaura da cewa"Mommy,Daddy Ni da Ayaan mun yanke shawarar komawa gida gobe,dan Bazamu juri rashin junaid a kusa damu ba,"
Tashin hankali,zuba masu ido Sukayi suna kallonsu,kowanne yasha sleeping dress ajikinshi,
"Ku zauna"Abbansu ne yayi maganar tare da nuna masu doguwar sofa É—in dake acikin bedroom É—in,Zama su kayi kowa fuskarshi É—auke da damuwa,
"Mommy!"gabanta ne ya faɗi jin Muryar fawan,da sauri takai idanuwanta bakin ƙopar ɗakin,shigowarshi kenan,idanuwanshi sunyi luhu luhu dasu,ƙarasa shiga ciki yayi daƙyar yake iya ɗaga ƙafarshi saboda bacci,
"Fawan!kaima baka yi bacci ba"?Abbansu ne yayi tambayar,
É—aga mashi kai yayi alamar eh,tare da cewa"Abba,junaid fa?ko wani yayi waya dashi acikin ku?duk yau bai kira ni ba,kamar yadda ya saba,har text yana turamun kullum amma yau shiru,ko ta whatsapp bai turo man ba,da abun na kwanta yanzu na farka still banga sakon shi ba, layinshi ma a switched off,duk na damu wlh,'
Tashin hankali,abun fa ya fara basu tsoro,wasa wasa one by one su Irfan kowa ya shiga shigowa É—akin yana tambayar junaid,dayake family house ne,duka danginsu na 6angaren Mahaifinsu,suna acikin katafaren gidan,wanda ya kasance mallakin kakansu,mijin Ammi,
Aranar dukkansu babu wanda ya runtsa,mafi yawancinsu a zaune suka kwana,don sunci alwashin dawowa gida,tun da asussuba,Abbansu yafi kowa ƙagara daya dawo yaga meke faru ne,Ya ƙwallafa rai akan son ganin junaid,don da ace yana da fiffike da ba abunda zai hanashi tashi sama atsakar daren nan yadawo gida! *Allah sarki*

Kamar yarda su Abba suka kwana a zaune,haka Sgr da Abusufyan suka kwana a zaune,cikin falon gidan,babu wanda ya runtsa acikinsu,haƙika ba ƙaramin so sukeyi wa junaid ba,Rashin kiran da baiyi masu ba a waya yasa duk sun tashi hankalinsu,inaga sunji mutuwarshi?mezai faru?kowa fa yasha jinin jikinshi,

Tunda asussuba Jirginsu Sgr da Armstrong ya É—aga izuwa Abuja,

*Sehrish*
Chapter 113 · 0% Book details