← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 212

Sashe 17

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankali a matuƙar tashe Sehrish ta zazzare idanunta tana kallon fuskarshi,gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,ganin ya fara motsa idanunshi yasa ta soma kiciniyar miƙewa daga saman jikinsa,sae dai kash bata samu wannan damar ba domin kuwa Sgr harya ware kyawawan idanuwanshi,biji-biji ya dinga ganinta acikin idanunshi,ita kuwa tuni jikinta ya shiga kerma,a hankali yakai hannunshi tare da ɗan Murza idanunshi,kafin ya ƙara ware su da kyau akanta,gaba ɗaya duk tabi ta rikice tuni zufa ta fara tsattsafo mata,ganin cewa dagaske dae ita yake kallo yasa ta ambaton nashiga uku,a hanzarce ta bar jikinshi ta sauka daga saman gadon,la66anta na rawa tace"dan Allah kayi haƙuri babban yaya,wlh ba yin kaina bane,na kawo maka fruits ne kuma banyi niyyar na tashe ka ba,tuntu6e nayi da ƙafarka na faɗo saman jikinka.....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda wani irin kallo da taga yana jifarta da shi,sunnar da kai ƙasa tayi tana faman wasa da yatsun hannunta dake ta faman kerma,
  "Kneel down," ya furta da wata irin kasalalliyar murya ta wanda bacci bai ishe shi ba,
   cikin sauri Sehrish ta zube saman guiwowinta agaban gadon nashi,
"Ur Hands up and close ur eyes," yayi maganar yana yi mata nuni da hannunshi,
  Jiki na rawa ta ɗaga hannayenta sama tare da kulle idanunta,sosai ta rufe su,tana matsar kwalla,
  "Kada kiyi attempting buɗe idanunki,ko sauke hannayenki if not kinsan mai zai biyo baya,'
  Muryarta na kerma tace"bazan buɗe ba,'
"Gud," ya furta hakan a yayin da yake cire blanket ɗin dake rufe da jikinsa,a hankali ya sauko daga saman gadon,tsayawa yayi yana rage kayan jikinsa,sae da ya rage daga shi sae short,sannan ya wuce cikin toilet ya rufe ƙopar,
   Saboda tsabar tsoro batama san cewa Sgr ya shiga toilet ba,sae faman shessheƙar kuka takeyi,after some minutes ya fito daga cikin toilet ɗin nasa,jikinshi sanye da bathrobe white colour,gaban dressing mirror ɗinshi ya zauna,ya shiga shafe jikinshi da mai,bayan ya kammala ya feshe ko'ina tass da tsadaddun tururrukan jikinshi,nan take ƙamshin ya gauraye ko'ina na cikin bedroom ɗin,ya jima agaban mirror ɗin kafin ya yunƙura tare da miƙewa ya nufi can cikin bedroom ɗin wurin Closet ɗinshi,
  Almost 30mins Sehrish tayi zuƙunne saman guiwowinta jikinta na kerma,
  dawowa yayi jikinshi sanye da nigh dress masu kyan gaske,
   Wuri ya samu ya zauna daga gefen gadon yana fuskantarta,a hankali ya miƙa hannunshi tare da buɗe side drawer ya ɗauko wannan hoton da Uncle ɗinsu Abusufyan ya ta6a basu lokacin da suna ƴan shekara sha a duniya,zuba ma hoton ido yayi yana ƙare mashi kallo,kafin ya ɗago da idanunshi ya azasu akan fuskar sehrish yana kallonta,da alama nazarin wani abu yake yi a fuskarta da kuma fuskar ƙaramar yarinyar dake acikin hoton hannunsa,so yake ya gano wacece yarinyar dake acikin hoton nan,ƴar ƙaramar yarinya wata zararriya da ita,gashin kanta duk ya tarwatse ya yamutse yayi datti babu gyara,kayan jikinta duk sun fita hayyacinsu sun yage,ga ƙafafunta ko takalma babu,fuskarta kuwa duk tayi jaga jaga da majina,hoton yayi confusing ɗinshi,kokwanto ya shiga yi anya itace a cikin hoton?kodai ɗaya daga cikin ƴan uwanta ne,
    "Open ur eyes,"
Jin muryarshi yasa tayi saurin buɗe idanunta wanda ke fitar da kwalla,muryarta na rawa tace"babban yaya dan Allah kayi haƙuri bazan ƙara ba,"tayi maganar tana faman shassheƙar kuka,
  Miƙa mata hoton hannunshi yayi tare da cewa"Who is she"?
  hannunta na kerma ta kar6i hoton daya miƙa mata,Ƙura ido tayi tana kallon hoton,nan take tashiga tambayar kanta ina Sgr ya samu hoton ɗaya daga cikinsu?ita kanta bazata iya tuna waya ɗauki hoton ba,kuma haka zalika bazata iya tantance wacece acikin hoton ba,saboda abun yayi confusing ɗinta,Kamar ita kamar kuma hossana,saboda gashin kan daya harmutse kamar na Mahaukaciya,tasan cewa hosana ce kawai keda irin wannan hargitsastsen gashin,
  "Ina sauraranki,"ya furta hakan a yayin da yakai hannunshi tare da ɗaukar cup of cofeen da takawo mashi,ya shiga kur6ar shi anatse,
  Cikin en ena tace"Wannan kamar hosana ce,bazan iya tantance wacece ba,'
  ɗaure fuskarshi yayi tare da cewa"Oh ba zaki iya tantance wacece acikin hoton ba?what does that mean"
  Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Inaji hosana ce,wannan itace gashin kanta yake a haka,"
  Hannu Sgr yasa tare da kar6e hoton ya ajiye shi a gefen shi,'
  Tsuru tsuru tayi da idanunta,cike da tsoran kar ace ta ƙara wani laifin,
  "I want u to tell me..,wannan bastard ɗin menene ma sunan shi?
  "Ya sayyadi," ta bashi amsa,
"akwai wasu mahimman bayanai da nakeso naji daga gare ki,hope zaki natsu kiban amsa," jinjina kai tayi tare da cewa"in sha Allah,"
  "Awani area kuka zauna a kano?"
"A hotoro ne" ta bashi amsa,
Jinjina kai yayi tare da ajiye cup É—in dake hannunshi,then ya É—auki banana yana 6areta a hankali yace"zaki iya tuna address É—in gidanku kenan"?
  "Eh,"
"Okey,' ya É—anyi shiru bayan yakai ayabar abakinsa ya É—an gutsireta acikin bakinshi,kafin ya kuma cewa"a labarin da sister É—inki ta bayar,ta faÉ—i cewa shi wannan mutumin ya ta6a nemanku,a cikinku akwai wadda ya ta6ayin raping"?
Daram!!!taji gabanta ya faÉ—i,girgiza kai tashiga yi muryarta har tana harÉ—ewa wurin saurin cewa"babu...bai ta6a samun nasarar yin hakan ba,yadai ta6a yunkurin hakan,"

Shiru Sgr ya É—anyi sae lokacin ya É—an É—ago da idanunshi ya kalli fuskarta,gaba daya duk tabi ta rikice jikinta sae faman kerma yakeyi,yanayinta kuma kamar akwai wani abu data 6oye masa,
  "Tell me the truth!kinsan bana son ƙarya,even if u hide it to me i will find out soon,so its better ki sanar dani,before naji a wurin wani!!"
  Hawaye taji sun wanke mata fuskarta,ji take kamar ta tashi ta watsa da gudu,saboda ta tsani taji ana zancen Ya sayyadi,
  ɗagowa tayi da idanunta waɗanda suka rune suka canza launi,kai tsaye suka sauka acikin nashi,cikin shessheƙar kuka tace"bazan maka ƙarya ba,yaso yayi hakan amma Allah bai bashi dama ba,'
  "In har dagaske ne abunda kika faɗa,to meyasa kike kuka"?
  "Saboda banason ana mun maganar shi,hakan yana tunamin rayuwar da mukayi a baya,"
  kawar da idanunshi yayi daga kan fuskarta,sannan yace"Its okey,u can wipe ur tears,amma ba hakan yana nufin za'a daina maki maganar shi bane!dole ta hanyarku ne zamu samu dukkan bayanan da mukeso,before muci nasarar kama shi,'
  Hannu tasa tana share hawayenta tace"Allah ya bani ikon Amsawa,"
  "U can leave,"ya bata umarnin tafiya,
  Tashi tayi jikinta asanyaye ta juya tana nufar hanyar fita daga bedroom ɗin nashi,gaba ɗaya duk jikinta yayi mugun sanyi,wata irin kasala ta lullu6eta,har ta kusa fita daga bedroom ɗin nashi ta ɗan tsaya tare da juyowa a hankali don tayi ma ɗakinshi kallon karshe tunda daga yau bazata ƙara zuwa sashen shi ba,da sunan yi mashi aiki,

Juyowarta keda wuya,idanunta suka shiga acikin nashi,har saida gabanta ya faÉ—i,kasa tafiya tayi kallonshi kawai takeyi,a yayin da shima yake kallonta,
Kusan 8 mins sannan taji muryarshi acikin kunnanta yace"Lafiya"?
  girgiza kai tayi alamar ba komai,kafin tasa kai ta fuce daga bedroom ɗin nashi,

Saukowa downstair tayi,hawaye nata faman zarya a fuskarta,sai da ta goge tears ɗin sannan ta wuce  bedroom ɗinsu, a hankali ta tura door ɗin ɗakin ta shiga,Samun Jahad tayi zaune daga gefen gadon ta zabga tagumi,yayin da hosana ke ta faman sharar bacci,
  Bayan ta rufe masu ƙopar ɗakin ta koma daga gefen jahad ta zauna tare da ambaton sunanta"Jahad,"
  A razane ta ɗago tana kallon Sehrish,sam bataji shigowarta ba,
  "Mekike tunani ne"?
Murmushi jahad ta É—anyi tare da cewa"Ashe kin fita,na farka ban ganki ba,acikin É—akin,'
Sehrish tace"Naje part É—in babban yayanmu ne,'
"Wannan mai blue eyes É—in"? Jahad ta tambaya yayin da take kallonta,
"Eh,Sunan shi RAFAYET,amma suna kiranshi da BABBAN YAYA,"
  "Shine babbansu kenan"?acewar jahad,
  "A'a bashi bane babbansu gaba ɗaya ba,Akwai wanda suka girme shi sosai,Sunan ne ya dace dashi shiyasa suke kiranshi da haka,"
  Jahad tace"kamar bazaiyi sauƙin kai ba,na lura ko magana baisan yi,ni in inama kallonshi tsoro yake bani,araina har cewa nake yi wai shima nan ɗan uwanmu ne,ƙwayar idonshi daban koda yake ga Ayaan nan shima idanunshi ash ne,mommynsu ma nata kalar na babban yaya ne,amma Mommynsu fa kamar bata son ganinmu nake gani ko kin lura da haka"?
  Sehrish tace"eh hakane,amma kada kisa ma ranki wannan,idan kika lura abun kamar a jininsu yake ita da babban yaya,in ka biye ta yanayinsu toh bazakayi rayuwa asake ba,duk zaka takure kanka ne,kayi tunanin cewa kamar sun tsani mutane basa son ganinsu bayan ba haka bane,kawai basu cika son magana ba,ko kallon mutane basa son yi,'
  Cike da mamaki jahad tace"tofa su kuma haka suke?shiyasa junaid shima baison ganina,har yau fa junaid ko son haɗa ido baiyi dani,in kuwa muka haɗa ido dashi har hararata yake yi ya kuma murguɗa mun baki,Wlh bana jin daɗin abunda yake yi mun,sai inga kamar ya tsane ni ne,abun ba ƙaramin damuna yake yi ba,gashi inason nasamu kusanci sosai dashi,kamar yadda naga kuna shiri a tsakaninki dashi,bansan meyasa ni yake mun haka ba,'
  Tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,
  Sehrish tace"kai junaid ɗin keyi maki hakan?to ae duk gidan nan babu kamar shi,indai wurin son mutane ne,yafi kowa faran faran da mutane kullum cikin fara'a yake,Junaid fa ko yau kuka fara haɗuwa dashi zai nuna tamkar kun ta6a haɗuwa a baya,kuma yadda zai saki jiki da mutun zaisa kayi tunanin kamar kun share shekaru kuna atare,"
  Sosai Sehrish ta shiga kora mata bayani agame da junaid,
  Abun ba ƙaramin ɗaure ma jahad kai yayi ba,cike da mamaki tace"To Amma meyasa ni yake mun haka"?
  Murmushi sehrish tayi tare da cewa"dole akwai dalili,amma ki barni dashi in sha Allah zan tambaye shi inji,"
  gyaɗa kai jahad tayi tare da cewa"Shikenan,dan Allah duk yadda kikayi dashi ki sanar mun,"
  sun jima suna fira atsakaninsu kafin bacci yayi awon gaba dasu,ƴan ukun Abusufyan,
Chapter 17 · 0% Book details