← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 212

Sashe 28

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren ƙarfe 10 sun kammala Komai,an gyara kitchen ɗin tamkar ba'a ta6a girki acikinsa ba,tun da wuri Abokanan Abba suka fara zuwa,Hada wasu daga cikin abokan Abusufyan wanda ke zaune a Nigeria,tuni gida ya fara ciki,tun da su sehrish suka tashi daga bacci ko arziƙin yin wanka basu samu damar yi ba,saboda kiransu da ake tayi,duk wanda yazo saiya buƙaci a kira mashi su ya gansu,daga sunje haka za'a dinga yabon kyawunsu ana sanya masu albarka,gashi duk wanda sukaje gaidawa cikin abokanan Abba,sai Yayi masu kyautar makudan kudi,babu wanda yayi masu kyautar ƙasa da naira dubu ɗari biyar,hosana duk tabi ta susuce,sae faman lissafin kuɗaɗen da suka samu takeyi,daga sun dawo cikin ɗaki zata fara fadin Abokin abba mai farin gemu ya bamu kyautar Dubu ɗari takwas,sae wannan abokin nasa mai sanye da kaki da yazo ya bamu kyautar gonaki guda uku,kuma ya haɗa mana da dawakai,Sai kuma wannan mai ƙaton tumbin shine ya bamu kyautar miliyan Uku,Ni miliyan ɗaya,Jahad miliyan ɗaya,sae sehrish itama miliyan daya,bayan shi kuma sae wannan abokin daddyn namu ɗan fari mai kumatu,wanda ya biya mana Umrah,Ashe da rabon zanje in ta6a ka'aba ɗakin Allah,harma in roƙe shi akan ya yaye mun haukan dake damuna,don banson jin anace mun Zararriya,haka ta dinga sambatu har sai da suka fara gajiya da surutun hosana,

Sehrish na cikin toilet tana wanka,amma hankalinta gaba ɗaya ya tafi akan Sgr,kalamanshi na jiya ne suka shiga dawo mata acikin kanta,dole tayi aiki a ƙarkashin shi batasan meyasa yake son ganinta a matsayin ƴar aikinsa ba,
Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo muryar jahad,daga waje tana cewa"Sehrish dan Allah kiyi sauri ki fito,inaso nima nayi wankan,kafin asake kiran mu,"
jin haka yasa tayi saurin kammala wankan ta fito,ɗaure da towel a waist ɗinta,shiga ciki jahad tayi,don tayi wankan itama,duk hosana na zaune gefen gadonsu hannunta ruƙe da biro da memo din Sehrish sae faman lissafin kyaututtukan da suka samu takeyi,"
Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"Aiki ya same ki hosana,kowa na É—okin zuwa yayi wanka amma ke hankalinki na akan kuÉ—in da muka samu,abunda baki sani ba,idan mukayi wanka mu kayi kwalliya,sae mun samu ninkin abunda muka samu a yanzu,"
Juyowa hosana tayi tare da waro ido jin an ambaci kuÉ—i tace"dagaske kike sehrish idan mukayi wanka mukayi kwalliya zamu samu fiye da wannan kuÉ—in da muka samu"?
Jinjina kai sehrish tayi tace"kwarai kuwa,ke dai kawai ki tashi ki fara yin wanka,jahad na fitowa,ki shige ciki,"
Cike da zumuɗi ta miƙe ta koma ta tsaya a kopar shiga toilet ɗin tana kwankwasa ma jahad,
"Ki fito nima in shiga,"
Murmushi sehrish ta saki,dama wayau tayi mata,don taji É—azu suna magana da jahad tana cewa ita ba yanzu zatayi wanka ba,sae da marece,bayan tun yanzu akeso su shirya,don agansu da kyau,
Gaban dressing mirror ta zauna,tana shafa mai ajikinta,sae faman sauri takeyi saboda taje part É—in Sgr,kamar yadda ya umarce ta akan taje da safe ta kai mashi breakfast É—inshi,kuma ta gyara mashi bedroom É—insa,light makeup tayi a fuskarta,saboda wannan wankan safe ne zata É—auka,da anjima Azmee tace za'ayi masu makeover,tamkar brides haka zasu fito,

Bayan ta kammala yin kwalliyar,komawa tayi wurin wardrobe din kayansu ta buɗe tana ƙare masu kallo,dama kullum zata zura kaya ajikinta sai ta tsaya yin ruwan ido wurin za6en kayan da zata sanya,
"Da rana zan sanya shadda lace ɗita,da marece kuma zan ɗauki wankan Swiss lace,yanzu dae bari na sanya wannan Arab gown ɗin,naga sai faman ƙyalli takeyi,in na sanyata ajikina,ba ƙaramin kyau zanyi ba,"ta ƙarasa maganar tare da janyo rigar,golden colour ce,gaba ɗaya jikinta adon stones ne masu ƙyalli da ɗaukar ido,batare da 6ata lokaci ba ta shiga kiciniyar zura rigar ajikinta,daƙyar ta shigeta saboda ta matse ta,gaba ɗaya tabi shape ɗin jikinta,kirjinta ya fito sosai,ga wani uban hips daya bayyana ajikin kayan,dama akwaita da diri sosai,don dai bata cika sanya kayan da zasu bayyana surar jikinta bane,hannun rigar na net ne,dogo ne ya kawo har wrist ɗinta,kana hangen fatar hannunta ta ciki,
siririn mayafin ta ɗauko,ta sanyashi asaman kafaɗarta,wa'iyazubillah,ba ƙaramin wankuwa sehrish tayi ba,juyowa tayi tare da kallon Hosana wadda ta saki baki tana kallonta,tace"Nayi kyau,"
Yadda hosana ta saki baki,tana kallonta ko kyaftawa batayi ba ƙaramin dariya ya bata ba,har saida ta ambaci sunanta,sannan hosana ta iya buɗe baki tace"Wlh kinyi kyau Sehrish sosai,kamar ƴar matan aljanna,"
Dariya Sehrish tayi yayin da ta koma gaban mirror tana kallon kanta,hannu tasa tare da daukar kwalbar turarenta,tabi jikinta ta feshe,sannan ta fuce daga ɗakin,tun da tafito idon kowa ya dawo kanta,abokanan matasan gidan da suka hallara a babban falon,duk saita tsargu,kitchen ta wuce anan ta samu Azmee tana zuzzuba ma saude abinci acikin warmers tana fitarwa waje,wurin baƙi tana kai masu,
Ae tunda azmee tayi arba da ita tashiga zuzuta kyanta,
"Aunty Azmee ni nasan ban kai haka ba,kawai kina hura mun kaine,".

Azmee tace"ae kin zarce duk yadda nake faÉ—i maki,dama shi mai kyau bai gane yana da kyau,sai in ana faÉ—i,"
murmushi kawai ta saki tare da cewa"Aunty azmee ina kayan breakfast É—in babban yaya inaso nakai mashi,"
"Oh kin manta cewa abusufyan ya hanaki"?
"Nasani Aunty azmee,bansan ya zanyi bane,babban yaya jiya yace,baison ki ƙara aiki part ɗinsa,ni kawai yakeso in dinga zuwa inayi mashi aiki,kuma har faɗa mashi nayi akan cewa daddy ya hanani amma yace shi babu ruwanshi,kawai nayi mashi aiki,
Jinjina Kai azmee tayi tare da cewa"TabÉ—ijancan,aikuwa akwai matsala!don wlh Abusufyan yaji wannan maganar bazai yadda ba,kuma ke in banda abunki kin manta wanene abusufyan a wurinki,mahaifinki fa ne,taya zaki tsallake umarninsa kibi na babban yayanku?hakan na nufin cewa yafi iko dake akan mahaifinki?kina ganin cewa abusufyan zaiji daÉ—i idan yaji cewa kin cigaba da yi mashi aiki"?
Jin wannan maganar ta azmee yasa jikinta yin sanyi,sunnar da kanta ƙasa tayi,tuni idonta sun ciko da kwalla,
GyaÉ—a kai azmee tayi tare da cewa"Nasan don baki da yadda zakiyi ne sehrish,zan shirya maki breakfast É—in ki kai mashi,amma karki kuskura ki bari Uncle abusufyan ya gani,kuma koda ya kamaki,kada ki sanya sunana aciki,"
Amsa mata tayi da toh,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta shirya mata warmers da sauran tarkacen abincin acikin kayataccen tray ta bata takai mashi,'
Tunda sehrish ta fito daga kitchen É—in gabanta ke faduwa sai faman waige waige takeyi,tsoranta kar daddynsu ya ganta,cikin sa'a ta haye upstairs batare da taci karo dashi ba,
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin data ƙarasa cikin falonshi,babu kowa aciki,hakan yasa ta tunanin ko bai tashi daga bacci bane,tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinshi,taji muryar namiji a bayanta,
"Ji mana,"a firgice ta juyo don taga wanene,É—an zaro ido tayi tana kallon matashin daya biyota,acan falo ta ganshi tare dasu kanal yousouf da alama abokinsu ne,
Murmushi ya sakar mata tare da cewa"Am sorry na biyo bayanki batare da saninki ba,nagaza jurewa ne shiyasa na yanke shawarar yin hakan,'
muryar sehrish na kerma tace"Am...um..dan Allah ka jira ni awaje,yanzu zan fito,
"Okey,zan tsaya awaje,but pls don't stay long,"
Ya faɗi hakan tare da juyawa zai fita,har ya sakai zai fita daga falon,ya kuma juyowa tare da kallonta har lokacin tana a tsaye yace"Kin tafi da imanina sosai,zan iyayin komai don na mallake ki,"ya ƙarasa maganar tare da fucewa,
Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke aranta tace"Kowanene wannan jarababben,baisan nan part É—in wanene ba,so yake yaja mun masifa,ya wani kwaso kafafunshi ya biyo ni,'
kamar ance ta juya,idanunta suka sauka kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman faffaɗan ƙirjinshi,fuskar nan kwata kwata babu annuri,daga shi sai short fari ajikinsa,

Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba,ƙiris ya rage ta saki tray ɗin hannunta,tuni jikinta ya soma rawa,

  "Zoki wuce ciki,"yayi maganar babu alamun wasa a fuskarshi,jiki na rawa ta nufi bedroom ɗin nasa,matsa mata hanya yayi ta wuce,sannan ya kama hanya azafafe ya fito daga falonsa,anan waje ya samu saurayin nan,tsaye yana jiran fitowar sehrish bawan Allah,ya ɗauki wankan suits,sae faman zabga murmushi yake yi,
..jin an ta6a kafadarshi yasa shi juyowa don yaga wanene,gabansa ne ya faɗi Rasss lokacin da yayi arba da sgr tsaye agabanshi ya ruƙe qugu,tamkar zaki haka ya koma mashi,mugun tsoranshi suke ji,saboda ko magana bata ta6a haɗashi da abokanan ƙannenshi ba,labarinshi kawai suke ji a wurin su Irfan,babu wanda baisan Sgr ba,wato babban yaya,
  Fuskarshi a tamke yace"Wani ganganci ne yasa ka biyota har cikin part ɗina!"?
   Muryarshi na kerma yace"wlh ni ba ita na biyo ba,zuwa nayi kawai don in gaishe ka,dama Jabeer ne yace yakamata muzo mu miƙo gaisuwa wurin babban yayansu,kaji dalilin dayasa na kwaso ƙafata nazo,"
  Wani irin kallo sgr ya wurga mashi,jin ya sharara mashi ƙarya bayan yaji duk abunda yake faɗa ma sehrish,
  Sunnar dakai saurayin yayi yana faman mazurai,tsoranshi karya kai mashi naushi,
   Hannu Sgr yasa tare da ruƙo neck tie ɗinsa yace"menene sunanka"
   Cikin sauri yace"Jazz,"
Sgr yace"Jazz ko?let me warn u,ka tsaya a iya matsayinka,in ba so kake ka kwana a gadon asibiti ba,ka rufe idanunka daga kallon matan mutane,hakan zaisa ka zauna lafiya,'yana kai ƙarshen maganarshi yace"just u can leave....."ae tunkan sgr ya ƙarasa maganar,Sir Jazz ya watsa da gudu jiki na rawa ya sauka downstairs,
  Ajiyar zuciya sgr ya sauke tare da juyawa ya koma ciki,

a ƙopar shiga bedroom ɗin ya tsaya,yana kallon sehrish dake ƙoƙarin gyara mashi gadonshi,har ta ajiye mashi kayan breakfast dinsa,yadda ta rankwafa shape ɗin hips ɗinta ya fito sosai,ba ƙaramin kyau tayi masa ba,sai yanzu ya gane dalilin dayasa wannan saurayin ya biyota,tunda yaga babban kaya dole ya zauce,baisan cewa babban goro sai magogin ƙarfe,
Chapter 28 · 0% Book details