← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 212

Sashe 10

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

 Lokacin da sehrish ta shiga main palour din nasu,anan ta samu matasan gidan duk tsaitsaye akan junaid,dake kwance saman doguwar sofa ɗin da Abbansu ya kwantar dashi,a lokacin har sun yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo,bakinsa sai faman kerma yake yi kuma har lokacin bai daina faɗin "Rishi guda uku"ba,
  Abusufyan yace"bawan Allah,nidai naji an saki ƙara ashe wai junaid ne,bansan time ɗin daya shigo ba,lokacin ina bacci ne,ae da ban bari hakan ya faru ba,da tun lokacin na fahimtar dashi,ashe har yanzu junaid na nan da wannan firgitar tashi,ae nayi tunanin ya daina,'
  Shafa gefen fuskarshi abba yayi a yayin da yake zaune daga gefen daman kujerar yace"Ya tsorata ne sosai,ae ni kaina banyi tsammanin zaije ɗakin nata bane,naso ace saida na fara yi mashi albishir sannan yaje wurinsu,'
  Jahan dake tsaye yace"Aikin ayaan ne,shine ya tura shi ɗakin nata,'ya ƙarasa maganar yana hararar ayaan dake tsaye yana dariya,
  Duk Alexandra na tsaye tana sauraronsu,sam batasan inda zancen nasu ya dosa ba,
  Koda sehrish ta ƙaraso,zuba mata ido Alexandra tayi tana kallonta,gaban sehrish ne ya faɗi lokacin da tayi arba da ita,har sai da ta ambaci Innalillahi acikin zuciyarta,ba komae ya firgitar da ita ba face ganin fuskar sgr a fuskar matar,kuma batasan da ita acikin gidan ba, sai dai lokaci guda taji aranta kaman ta ta6a ganin hoton matar,
  Cike da mamaki Alexandra tace"wacece wannan kuma"?tayi maganar tare da yin nuni da sehrish wadda tuni ta koma bayan abusufyan ta tsaya,
  Jahan ne ya bata amsa da cewa"Ƴan ukun uncle abusufyan ne,'.
  "Abusufyan kuma?dama ya ta6a aure ne?
  "Eh,ya ta6a aure batare da sanin kowa ba,sai daga baya abun ya bayyana cewar ƴa'ƴansa ne,kuma ƴan ukune kamanninsu iri ɗaya sak,abunda yasa kika ga junaid ya ruɗe kenan,baisan cewa su uku bane,ɗaya ya sani acikinsu,muma sai jiya Allah yasa mukasan da zamansu muka san cewa ƴa'ƴanshi ne,Nasan abba zai sanar dake komai,'
  Jinjina kai Alexandra tayi tare da ɗan ta6e bakinta,yayin da ta janye idanunta daga kan sehrish ta mayar dasu kan junaid dake ta faman sambatu,
  "Abba pls ku fahimtar dani mana!meyasa nake ganin Sehrish guda uku?ko na samu ta6in hankali ne,'
  "Junaid u should calm down ur mind,in baka natsu ba taya zamu fahimtar dakai,"acewar abbansu,
  Jin hannun mutun acikin nata yasata yin saurin juyawa,sai lokacin ta lura dashi sam bata ga fitowarshi ba,
  "Mommy,"ya ambaci sunanta cikin sanyin murya,cike da farin ciki tace"Fawan!ka farka daga baccin kenan"?tayi maganar ayayin da take janyo shi jikinta,sosai ta rungume shi,
  "Mommy tun yaushe kika zo ba'a sanar mun ba?sae dai na fito na ganki unexpected"
  "Tun jiya nazo fawan,muna tare da junaid acan gidana muka kwana tare dashi sai yau da safe muka dawo atare,da fatan na sameka cikin ƙoshin lapiya,'
  "Alhamdulillah mommy munyi missing ɗinki sosai da sosai,'
  "Nima nayi missing ɗinku fawan,'magana suka cigaba dayi atsakaninsu,
  Duk wannan abun dake faruwa alexandra bata tanka ma abusufyan ba,shima kuma bai tanka mata ba,tun lokacin daya shigo falon yayi arba da ita,yaga ta kawar da kanta gefe tun daga lokacin shima ya share ta,dama bata shiri dashi,tun lokacin da Abba ya aurota,ya ta6a zama agidan,yanayin yadda take wahalar da yayanshi ne yasa yayi mata rashin kunyar da ta haddasa gaba atsakaninsu,saboda shi bakinshi bai rufuwa muddin yaga tana gaya ma Yayanshi hossein magana saiya mayar mata da martani mai zafi,wannan dalilin ne yasa Abba yace ya tattara ya koma wurin ammi don bazai iya jurar zama dashi ba,kullum haɗa mashi Bomb yakeyi acikin gida,shiyasa abusufyan bai zauna agidan yayan nashi ba,kuma ammi bata kawo shi gidan ba lokacin daya addabeta da rashin jin maganarshi,kawai ta yanke shawarar kai shi gidan hajiya Ameenatu,
   Kowa daya fito tun daga kan su irfan jabeer,khaleed da kanal yousouf babu wanda baiyi farin cikin zuwan mommynsu junaid ba,daya bayan ɗaya saida tayi hugging ɗinsu ajikinta,kanal yousouf ne kawai ta manna ma kiss a gefen fuskarshi,ji suke tamkar mahaifiyarsu ce Maryam ta dawo gidan,Allah sarki Allah ya jiƙan rai,tun daga yanayin yadda alexandra ta kar6esu hannu bibbiyu tana rungumarsu ransu ya basu cewar ta shiryu yanzu,da alama babu wannan girman kan nata da kuma Zafin ran nan,
   Sehrish dae duk jikinta yayi sanyi tun daga kan irin kallon da taga Mommynsu junaid nayi mata,ranta ya bata cewar akwai matsala,sam fuskarta babu yabo babu fallasa lokacin da Jahan ke sanar da ita cewar ɗiyar uncle ɗinsu ce,
  Abbansu na ƙoƙarin fahimtar da junaid,suka jiyo muryar sgr yana tambayar"Meya faru ne!"yayi maganar ne ayayin da yake saukowa daga saman stairs ɗin,jikinshi na sanye da shirt fara ta ɗame jikinshi sai kuma dogon wando jeans,ba ƙaramin kyau yayi ba,
Gaba daya suka juyo suna kallonshi,Marshal Omar na biye dashi abayanshi,atare suka sauko,
  Wani irin farin ciki ne ya lullu6e alexandra lokacin da tayi arba da first born dinta wato Surgeon General Rafayet,gaba ɗaya tagaza rufe bakinta saboda ba ƙaramin so take mashi ba,tana matuƙar alfahari dashi,
  Sehrish kuwa tunda taji muryarshi taji gabanta ya faɗi rass,tabbas tayi kewarshi sosai,jiya abubuwan da suka faru ne suka hana takai mashi dinner ɗinshi,tasan cewa daƙyar ne idan yaci wani abu ajiyan nan,
  Aranta tace"bansani ba ko yana farin ciki da kasancewata ƴar uwarshi,ɗiyar ƙanin Mahaifinshi,ko yaya yaji aranshi"?
   Jahan ne ya sanar dasu abunda ya faru da junaid,
  ƙarasawa Sgr yayi wurin Mommyn tasu,ita tafara manna mashi kiss a gefe da gefen fuskarshi sannan shima yayi mata kamar yadda tayi mashi,daga bisani kuma suka rungume junansu,
Abun ba ƙaramin burge sehrish yayi ba,har sai da ta ɗan saki murmushi kaɗan a fuskarta,
  "Am really glad to see u mom,"ya furta hakan ayayin da suka raba jikinsu daga na juna,
  Shafa gefen fuskarshi tayi tare da cewa"Yanzu ka kyauta mun?tun yaushe rabon dana sanya ka a idanuna Alex?ka daina zuwa wurina,kusan 1 year kenan baka tako ƙafarka kazo ba,'
  Ganin hawaye sun cicciko a idanunta yasashi yin saurin ruko hannayenta tare da cewa"pls mom just forget about the past,nasan ban kyauta ba,amma kullum kina araina,kuma ina kiranki awaya muna gaisawa....'
  Abbansu ne ya katse firar tasu da cewa"Ashe ba daɗi,Rama mun yayi Nima,ƙiri ƙiri kin rabani da aurena kinsa anata yi mun kallon Tazuru,'
  Dariya sukayi gaba ɗayansu,banda sehrish dake tsaye jugum tana sauraronsu,
  Matsawa Omar yayi cike da zolaya yace"Oh Mommy abun ƴar wariyar launin fata ce ko?atare da bro ɗina muka fito,amma ko kulani bakiyi ba...'yayi maganar yana ɗan ɗaure fuskarshi,
  murmushi alexandra tayi tare da komawa wurin marshal,ta manna mashi kiss agefen fuskarshi sannan ta dafa shoulders ɗinshi tare da cewa"Omar ni bazan iya cewa komai ba,so nake nafara huce haushina akanshi kafin nadawo kanka,dama kaine mai ɗan son zumuncin,duk lokacin da kuka samu hutun aiki kana janyo shi kuzo wurina,amma yanzu duk kun juya mun baya,ni nasan duk shirin Abbanku ne yasan cewa dole nayi kewarku....'
  Omar yace"no ba haka bane mommy,rayuwarce sai a slow,bamu manta dake ba,kuma kamar yadda rafayet ya fadi,muna kiran ki fa awaya kullum mu tambayi lpyrki,da ace kin ƙara 1 week baki zo nigeria ba,da kin ganmu munzo,ba don ma aiyuka da sukayi mana yawa ba,ae da mun rigaki zuwa....'
  Ba ƙaramin daɗin kalaman Omar taji ba,yasan duk wata hanya da zaibi don ya kare kansu a wurinta,ba kamar SGR ba,shi kai tsaye kawai yake maganarshi ba wata kwana kwana,'
  Sai da suka samu natsuwa sosai,sannan suka tattara hankalinsu kan junaid,
   "Ina sehrish take ne"?Abbansu ne ya ambaci sunanta,saboda yaga gifcinta a wurin,
  Da sauri ta amsa mashi da cewa"Gani nan Abba,"tayi maganar tare da fitowa daga tsayen da take abayan daddynsu,
   Haɗa ido sukayi da Sgr,da sauri ta kawar da idonta,zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi,daƙyar ta iya ƙarasawa wurin abban nasu ta gaishe shi,
  Bayan ya amsa mata yace"ki fahimtar da junaid,ina tunanin in yaji daga bakinki zaifi yadda cewa ku ƴan uku ne,'
   Murmushi sehrish ta ɗan yi tana kallon fuskar junaid wanda ke kwance saman kujerar duk yabi ya rikita kanshi,tunda tayi magana yasan cewa itace saboda yaji muryarta,
   Cikin sanyin murya ta soma magana,
  "Junaid ka manta kwanaki na ta6a sanar dakai cewa Ina da ƴan uwa?waɗanda nake kira da wayarka?
"Amma ai kince mun baki da wasu Æ´an uwa lokacin da muka yi maki magana akansu ni da aunty azmee,"yayi maganar yana faman hura hanci,
  "Junaid a lokacin bana cikin hayyacina bansan ya akai na manta dasu ba,amma yanzu nadawo hayyacina kuma Zan iya tuna komai a game dasu,idan baka yadda dani ba,bari na tuna maka,ko ka tuna Yarinyar daka ɗauko a school cikin motarka?tun lokacin saida nayi ƙoƙarin fahimtar dakai cewar bani bace,ni ina a makaranta ka barni,shine dalilin da yasa nasha wahala aranar,'
  Jin wannan maganar ta sehrish yasa junaid miƙewa daga zaune,bakomai ne ya faɗo mashi aranshi ba face,yadda jahad ta kasa sakewa dashi,kuma launin gashin kanta baƙi ne ba irin na sehrish ba,hatta muryarsu ma akwai ɗan bambanci,haba no wonder shi dae ya jima yana tunanin cewa al'jana ya ɗauko a motarshi ashe ashe mutunce,indae dagaske ne xancen sehrish hakan na nufin cewa ƴar uwartace ya ɗauko a motarshi?to kodai sune yaran da Ya Omar ɗinsu yasa su gyarama gidan uncle ɗinsu zai kawosu suyi rayuwa aciki......'bai ƙarasa zancen zucin nashi ba,Muryar Omar ta katse Hanzarin shi"Junaid!maganar da take faɗa maka dagaske ne!they're triplet,kuma ƴa'ƴan uncle abusufyan ne,dukanmu bamu son da haka ba sai jiya Allah ya bayyana mana komai,'
  Yana kai ƙarshen maganar tashi ya juya tare da kallon fawan yace"Kaje ka kira mun su hosana da jahad suzo ya gansu da idanunshi don ya shaida cewar mutane ne ba aljanu ba,'
  Cike da zumuɗi fawan ya wuce bedroom ɗin sehrish a lokacin har jahad ta kammala shirya kanta cikin riga da skirt na sehrish,ba ƙaramin kyau tayi ba,
  Kwankwasa ƙopar fawan yayi kafin ya turo tare da cewa"Ya omar nason ganinku yanzu,'jin haka yasa sukayi saurin kimtsawa,duk suka yafa gyala a kansu,
  Atare da fawan suka shigo cikin main palour ɗin,
   Jerawa sukayi kusa da sehrish duk sun sha jinin jikinsu tsoransu kar ace wani abun ne kuma ya taso,
  zuba masu ido junaid yayi yana kallonsu,idan ya kalli jahad sai ya kalli hosana,
  A ƙarshe ya tsaida idanunshi kan jahad,ta hanyar gashin girarta ya gane cewa itace ya ɗauko a motarshi,har suka sha Love,
  Dafe kanshi yayi tare da cewa"OMG!Abba kenan reesh ƴar uwata ce,jini na,ɗiyar uncle ɗinmu abusufyan!taya hakan ya faru?kuma dama rishi ƴan uku ne su ba ita kaɗae bace!idan har dagaske ne meyasa basu taso atare damu ba!!!!!!!_
Karaf maganganun da junaid ke faÉ—i suka dira a kunnan Hayaam,wadda fitowarta kenan,yunwa ta korota daga bedroom É—inta ta gaza jurewa shine ta lalla6a ta fito don ta shiga kitchen,
  Gabanta ne yayi wani irin bugu ji kake rasss!rarasss!hankali amatuƙar tashe ta ɗago da idanunta ta sauke su akan Mutanen dake tsaitsaye acikin falon,waro ido waje tayi ganin Sehrish dasu jahad,anan ta tuna abunda azmee ta faɗa mata jiya na cewa ƴan uku ne su,kuma kamanninsu iri ɗaya sak,a fili ta ambaci"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!Ya Allah ka rabani da mugun Ji da kuma mugun gani!nashiga uku Ni yau Hayaam,bari dae na ƙara kasa kunne naji uban da suke tattaunawa,ya Allah kasa korar shaggun za'ayi daga gidan,
Chapter 10 · 0% Book details