← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 212

Sashe 43

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda ta watsa a gujen nan,É—akin hayaam ta faÉ—a,jikinta sae faman rawa yakeyi,zagaye tashiga yi a É—akin tana tunanin hanyar da zata bi ta gudu daga cikin gidan tun kafin ishaq ya waiwayeta,tsoranta karya bata takardar saki,don bata shirya yin zawarci ba,hannu ta aza aka tana fadin"Nashiga uku ni laila,na jama kaina masifa da bala'e,Ina zan tsoma raina inji daÉ—i,"tana cikin zancen zucin nan,hafsat ta shigo É—akin,kamar jira takeyi nan ta shiga balbaleta da faÉ—a ta inda take shiga bata nan take fita ba,
"Don ubanki ki faɗa mun taya akai yaran nan suka rayu!nasan kinsan komai munafuka algunguma!"hafsat na ƙokarin buɗe baki,Aunty babba takai mata naushi a kumatunta,har sai da le6enta ya ɗan fashe,idonta jawur ta ɗago tare da kallon Mommyn nata idanunta cike taf da hawaye tace"Mommy!ni kika buga saboda zunubin da bani na aikata ba?
A faÉ—ace Aunty babba tace"Zanci ubanki ko ki rufe mun baki,wlh hafsat kin cuce ni!Allah ya isa tsakanina dake!ae kinsan da zaman yaran nan acikin gidan nan, shiyasa don munafunci kika sanyo nikabi uban meyasa baki sanar dani ba tuntuni don inyi takaina!Kece kika tseratar dasu daga hannun baba alamu,in ba haka ba taya akai har suka kawo kansu cikin gidan nan"!?
Girgiza kai hafsat ta shiga yi yayin da idanunta ke fitar da wasu irin hawaye masu ɗumi,cikin shessheƙar kuka tace"banta6a dana sanin kasancewarki mahaifiyata ba sai yau!Kin jefani acikin masifa kin kuma zo kina neman ƙala mun sharrin cewa ni na tseratar dasu daga hannunshi,wlh Mommy bakiyi ba!duk wasu magayen ɗabi'u da halayen dana ɗauko naki ne,baki ta6a cemun nayi badai dai ba,baki bani tarbiya mai kyau ba,kullum gur6atamun tunani na kikeyi,saboda kar in dauko halayyar mahaifina,Ni banta6a ganin uwa irinki ba,Yanzu gashi nan daga ni harke wa gari ya waya?kuma inaso ki sani mommy,Ni bansan komai agame dasu hosana ba,bansan ya akai suka dawo hannun Ya Omar ba,Na faɗa maki hakan ne ba don ina jin tsoranki ba,sai don kisan cewar Bani na aikata hakan ba,Allah ne Ya Kamaki,ba yadda banyi ba don ki kyale yaran nan karki salwantar da rayuwarsu kika ki,kuma ni ce da hannuna na goge hotunan da hayaam ta tura maki a wayarki,saboda nafi son ki tako da ƙafafunki don ki gir6i abunda kika shuka......"
..saboda tsabar tsuma jikinta har kerma yakeyi,shaƙo wuyan rigar hafsat tayi da ƙarfin gaske,gadan gadan kasheta zatayi,kiciniyar kwace wa hafsat tashiga yi,suna cikin wannan halin,Amani da hayaam suka faɗo cikin ɗakin da gudun gaske sukayi kansu,daƙyar suka kwaci hafsat daga hannun Aunty babba,dafe maƙoshinta tayi tana faman yarfa hannu tana ambaton"ruwa!ruwa'
Da sauri hayaam ta fita waje,sai gata ta dawo da bottle water a hannunta mai sanyi,miƙa ma Hafsat ruwan tayi,jiki na rawa ta cire marfin robar tare da yin wurgi dashi,ta kafa robar abakinta tana kwankwaɗar ruwan,hayaam ce ta zauna a wurinta,tana lallashinta,
Rai amatuƙar 6ace tashiga fadin"ae da kun barni na kasheta don ubanta,wlh hafsat baƙin cikinki bazai ta6a kashe ni ba,Muguwa kawai,nafi kowa dana sanin haihuwarki,Ni ina kokwanton cewar Anya ba'a asibiti akayimun musanyarki ba,"
Fashewa da dariya Amani tayi tana tafa hannayenta,
Nan take Aunty babba ta É—aure fuska,tana jifarta da harara,
Tsagaitawa tayi daga yin dariyar da takeyi masu sannan tace"Wannan abun daya faru nafi kowa farin cikinsa,tamkar na zuba ruwa a ƙasa na sha,"
"Amani baki da hankaline?kinsan me kike faÉ—i kuwa?wannan abun fa ya shafi kowannanmu,bai kamata ki dinga yi mana dariya ba,"Acewar Aunty babba,
wurga mata harara amani tayi tare da cewa"yadai shafe ku!karki kuskura ki ƙara mentioning ɗina aciki,domin kuwa bansan anyi ba,lokacin da kuka tsara muguntarku kuka cutar dasu,kunyi shawara dani ne?Kuma ae har shawara saida na baki akan ki daina azabtar da yaran amma kika ƙi ji ke ga shugabar azzalumai,wlh baku da imani zuciyarku ta bushe,kwakwalwarku a toshe take,tamkar ana zuba maku dussa acikin kawunanku saboda ɗabi'unku sak irin na kafuran farko ne,....."
Waro ido waje Aunty babba tayi tare da faÉ—in"Ni kike faÉ—ama wannan maganar!"
Amani tace"Kwarai kuwa dake nake,Muguwa macuciya kuma Azzaluma,zuciyarku ta ƙeƙashe Zalunci kawai kuka sa agaba,daku da uwarku Mammy,tsohuwar banza me shegen son kuɗin tsiya,wlh kunji haushin rayuwarku,shegen kwaɗayin abun duniya,ga baƙar zuciya,ga dogon burin tsiya ko tsoran mutuwa bakwayi..."
Tunkan amani ta ƙarasa maganar Aunty babba ta kwashe ta da tagwayen maruka,ji kake tasss tatasss!'kafin Aunty babba ta janye hannunta daga kan kuncin Amani,itama ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe ta kikkifa mata maruka a jere kusan uku ji kake fass tasss taaasss!
dafe kumatu aunty babba tayi yayin da idanunta sukayi jawur,tunda take arayuwarta ba'a ta6a yi mata irin marin da Amani tayi mata ba,hasalima Amani shakkarta take ji,amma sai gashi yau ta cire yatsunta guda biyar cuf,ta kikkifa mata maruka,
Koda ganin haka,sae hayaam ta miƙe tare da ɗaga hannu zata sharara ma Amani mari,aikuwa hafsat ta yunkura tare da miƙewa ta damƙo hannun hayaam tana faɗin"baki da hankaline?matar da ta iya ɗaga hannu ta mari mommy har sau uku,itace zaki mara?kina tunanin cewa zaki iya rama mata ne," dariya Amani tayi tare da cewa"ki barta inga ƙarshen rashin kunya,wlh dai dai nake da kowane shege acikin ku,Bana jin tsoranku a yanzu,tun ranar da Amal ta sanar dani komai game da ukubar da kukeyi mata tun daga ranar na ɗaura ɗamarar yin yaƙi daku,"
Hankali tashe hayaam da aunty babba suka kalli juna jin ta ambaci sunan Amal,
Hafsat ce tace"Amal na wurinki ne"!?
Jinjina kai amani tayi tare da cewa"Amal tana wurina!itace yarinyar dana zo da ita cikin gidan nan,kun so ku kashe mun ƙanwata,Amma Allah bai baku nasara akanta ba,Amal ta tako da ƙafafunta ta kawo kanta har cikin garin nan,"
Shiru duk sukayi suna sauraronta,
"Haƙƙin Amal kaɗai ya isa ya jefa rayuwarku cikin masifa,laifin me Amal tayi maku da har kuka wulaƙantar da rayuwarta?yarinya ƴar ƙanƙanuwa amma kukayi mata taron dangi wurin azabtar da ita,saboda tsabar mugunta irin taku,ƙiri ƙiri kuka hanani ganin Amal,ku ka yi mun ƙaryar cewar Amal ta 6ace ba'a ganta ba,mugaye kawai ashe gidan makwabtanmu kuke kaita kuna rufeta,duk in nazo har in bar garin,tana can arufe kamar akuya,ko abinci ma baku bata,wai ku wasu irin mutanene?wace irin zuciya gare ku...?
Kasa ƙarasa maganar Amani tayi saboda kukan daya ciyota,nan take ta fashe da wani irin matsanancin kuka,ba ita kaɗae bama hatta hafsat sai da ta zubar mata da kwalla,baƙin ciki kamar ta binne kanta,abun kunyar da mommynta ta aikata ba ƙaramin illa yayi ma zuciyarta ba,
Hayaam kuwa sae faman mazurai takeyi ita da aunty babba sunyi wuƙi wuƙi,basu da abun cewa,dama ance rana dubu ta 6arawo,rana ɗaya ta me kaya,
"Wlh kaɗan kuka fara gani!haƙƙin Amal da kuma haƙƙin waɗannan bayin Allahn da kuka cutar bazai ta6a barinku ku zauna lafiya ba,in har ba zaku canza waɗannan munanan ɗabi'un naku ba,mugunta da kwaɗayin abun duniya,dogon buri,rayuwar ƙarya,duk ku kadae gashi har yau Allah bai ta6a baku nasara ba,mutumin da bai ta6a sa Allah alamurransa ba taya zaiga dai dai"?
Tsoki Aunty babba ta buga tare da nuna mata hanyar fita daga É—akin tace"zo ki fuce ki bamu wuri tun kafin ranki ya 6aci a wurin nan!shashasha kawai kina tunanin cewa kalamanki zasu iya tankwarani ne?duk duniya ba ayi mutumin da zai zauna yanayi mun nasiha ba,wlh ba ayi shi ba,"
Girgiza kai amani tayi tare da juyawa a fusace tabar É—akin tana faÉ—in"Jiki magayi,"

Komawa Aunty babba tayi yaraf ta zauna gefen gadon tana faman cizon yatsa,miƙewa hafsat tayi tare da fucewa daga ɗakin,
Fitar ta keda wuya,Hayaam ta dawo gefen aunty babba ta zauna tana faÉ—in"Yanzu menene mafita"?
..fuskarta a hargitse tace"mafita ta wuce mu gudu salin alin batare da sanin kowa ba,"
"Saboda me zamu gudu?hakan na nufin cewa sun ci nasara akanmu kenan"?
"Hayaam ba zaki gane ba,ina tsoran in sake yin arba da hosana ne,bata da hankali,zata ci gaba da tona mun asirine a bainar jama'a"
"Amma Aunty laila,taya akai yaran suka zauna a wurinki har hakan ya faru?meyasa baki kashesu ba tun lokacin"?
Guntun tsoki taja tare da kawar da kanta gefe cike da takaici tace"sai yanzu nake danasanin barinsu araye,meyasa ban kashesu ba tun lokacin da suke a wurina ba?wancan shashashan mutumin dana bama aikin zubar mun dasu a daji bansan ya akai yayi sakacin da har suka ku6uta daga hannunshi ba,kuma tun ranar dana bashi su nake ta jaraba kiran wayarshi akashe kullum har na gaji na daina kira,duk shi ya kwafsamin wlh,yanzu yawo acikin gidan nan ma ya haramta agareni,Allah yaso Hafsat ta siya niqabi a kasuwa,zan kar6e shine in sanya a fuskata saboda gudun kar waccen mai ta6in hankalin cikin sun ta ganni.....'
Shiru suka É—anyi na wani lokaci,zurfin tunani ta shiga yi kwatsam ta tuna da maganar nan da hajjaju ta ta6a sanar da ita kwanakin baya can da suka wuce lokacin su hosana na a gidan,
"Idan kin toshe waÉ—annan hanyoyin,ita kuma waccen É—ayar hanyar da ta riga isa inda baki so fa ya zakiyi da ita'
Jinjina kai Aunty babba tayi tare da faɗin"Allah ya isa tsakanina da hajjaju,sarai tasan komai game da rayuwar yaran nan amma taƙi sanar dani,babu yadda banyi da ita ba,amma taƙiya saboda tsabar baƙin hali irin nata,da tun farko ta sanar dani cewa ƴan ukune yaran akwai ɗaya dake aiki a gidan da tuni nasan abunyi,

wannan masifar har ina"?
Chapter 43 · 0% Book details