Sashe 63
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,bugun ƙopar tashiga yi amma arufe take,sun datse ƙopar tun jiya da daddare da zasu kwanta,tana cikin bugun ƙopar ɗakin nasu sai ga Azmee ta shigo corridor ɗin ɗakin nasu,da alama daga kitchen take,ganin hafsat a ƙopar ɗakinsu sehrish tana ta faman yi masu magiya akan su buɗe mata ƙopar,yasa azmee yin hanzarin ƙarasawa kusa da ita tana tambayar ko lafiya,tun kafin ma hafsat ta bata amsa ta jiyo sautin kukansu Jahad acikin ɗakin,kuka fa bana wasa ba,hankali atashe azmee tace"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Meke faruwa ne!meyasa su ke kuka"?  Fuskar hafsat ɗauke da damuwa tace"Wlh bansani ba,zuwana kenan najiyo sautin kukansu hada ma buge buge da alama faɗa suke atsakaninsu,Ni tsorona ma kada su lahanta junansu,'  A ruɗe Azmee ta shiga bugun ƙopar tana kwala masu kira"Jahad!Sehrish!hosana!wai bazaku daina ba!Me kukeyi haka!kuzo ku buɗe ƙopar nan tun kafin ranku ya 6aci," duk wannan kwakwazon da azmee keyi a banza domin kuwa babu mai sauraronta,hasalima basu son tana yi ba saboda basu a hayyacinsu,  "Hafsat!kije ki sanar da Daddynsu ko wani daga cikin yayyensu game da abunda ke faruwa,su taimaka suzo ko ƙopar ce a 6alle,tun kafin yaran nan su halaka kansu,"acewar Azmee wadda hankalinta ya gama tashi,  Da gudun gaske hafsat ta fita daga corridor ɗin ɗakin,A main palour ta samu Mommynsu junaid tare da Abbansu da kuma Hajiya Azeema suna tattaunawa,wurinsu ta tunkara tana faman yarfa hannu idonta cike tab da kwalla,  Tun kafin tayi magana suna ganinta suka miƙe tsaye suna tambayar ko lafiya,  Muryarta na kerma tace"Su jahad ne,suke faɗa acikin ɗakinsu,gashi can suna ƙoƙarin halaka kansu,munyi munyi su buɗe ƙopar sunƙi buɗewa sae dai sautin kukansu kawai da muke ji,"  Tun kafin ma ta karasa maganar,Jiki na rawa suka nufi ɗakin nasu,hajiya azeema hada tuntu6e saboda tsabar sauri,a ƙopar dakin nasu suka tsaya,bubbuga ƙopar ɗakin Abbansu ya shiga yi a tsawace yake ambaton sunayensu,amma shiru babu wadda ta amsa masa,sae dai sautin kukan nan da suke ji na tashin hankali,   "Ina ganin bari na kira mahaifinsu wata'ƙil idan yayi masu magana sun ji maganar shi,'Abba ne yayi maganar tare da zura hannu cikin aljihun wandonshi ya ɗauko wayarshi,yatsun hannunshi har kerma sukeyi wurin lalubo number Abusufyan,ya danna mashi kira ta soma ringing,  Hajiya Azeema da Alexandra duk sun bi sun ruɗe,  "Ni babban tashin hankalina ma kada yaran nan su illata kansu,Wlh abun ya tsoratar dani sosai ya tayar mun da hankalina,"Hajiya azeema ce tayi maganar,fuskarta tamkar zata fashe da kuka,  Hafsat kuwa tana acikin main palour ɗin,Sae faman kuka takeyi,kwatsamm taji takun takalmi,da sauri takai idanunta wurin MARSHAL OMAR ne ke saukowa daga upstairs da gudun gaske ta tunkare shi tana fadin"Ya Omar,gasu jahad can suna faɗa acikin ɗakinsu,kuma sun kulle ƙopa,anyi anyi su buɗe sun ƙi su buɗe....."  Jin wannan maganar yasa hankalin Omar mugun tashi,da sauri ya nufi bedroom ɗin nasu,lokaci guda kowa na gidan labarin abunda ke faruwa yaje musu,hatta su Junaid dake ɗakunansu suna bacci sae da suka tashi,su fawan twins,dasu Irfan,hada Dr hariis da gwaggon katsina,da Ammi,dukkansu kowa fa amma banda Sgr dake a bedroom ɗinshi,  A ƙopar ɗakin nasu sukayi cirko cirko,Abusufyan yafi kowa shiga damuwa bawan Allah,kamar ya zauce haka yake bugun ƙopar ɗakin nasu yana roƙonsu akan su daina kokoyin da sukeyi suzo su buɗe mashi ƙopa amma shiru babu wanda ya tanka mashi,Haka Marshal Omar ma,Tamkar zai 6alle ƙopar haka ya dinga bugun ƙopar ɗakin nasu,amma duk abanza,Junaid kuwa tuni ya fashe da kuka,yadda kasan wani ƙaramin yaro,  Cikin shessheƙar kuka Gwaggon katsina tace"nashiga uku..Wayyo Allah na,wlh nasan duk sharrin Ya sayyadine bazai barsu hakanan ba,yanzu haka shine ya shiga tsakaninsu,Ya Allah kayi mana maganin wannan baƙin shaiɗanin....'kuka takeyi hada majina,   Lokaci guda sukaji shiru tsit cikin bedroom ɗin nasu babu wani gunjin kuka,hakan ya tabbatar masu da cewar wani mummunan abunne ya faru dasu,nan fa kowa ya shiga kallon kallo,yayin da zuciyoyinsu keta bugawa da karfi,   Jiki asanyaye Abusufyan ya zame ƙasa,tare da aza hannayenshi saman kanshi,yayin da bakinsa ke furta kalmar"Innalillahi wa'Inna ilaihirraji'un,'  "Abba,ina ganin kawai a 6alle ƙopar," acewar kanal yousouf, Omar yace"Nima abunda nake tunani kenan,amma ƙopar fa ta cije sosai,na buga na buga amman ko motsi batayi,duk irin ƙarfin da nake dashi,"  Cikin shesshekar kuka junaid yace"Bari naje na ɗauko zarto sai a datse kubar,"   Ya ambaci hakan tare da watsawa da gudu ya nufi weapons Room ɗinsu (ɗakin ajiye makamansu,"A rufe ya samu ɗakin,sam ya manta cewar key ɗin yana a wurin babban yayansu,sae da yayi arba da ƙopar a rufe sannan yasha kwana ya dawo da gudu ya haye upstairs ɗin,  Faɗawa part ɗin SGR yayi,a rikice ya shiga bedroom ɗinshi,a lokacin Sgr na kwance saman shimfiɗeɗen gadonshi yana bacci,  Junaid baibi takanshi ba saboda a ruɗe yake,side drawer ɗinsa ya tunkara,ya shiga bubbuɗeta yana neman key ɗin,duk inda ya duba babu key ɗin,saman gadon ya hau,yana kiran sunanshi"Babban yaya!Babban yaya!pls wake up!babban yaya ka tashi dan Allah,'  Cikin bacci rafayet yaji muryar junaid dake ta faman kiran sunanshi,a hankali ya buɗe idanunshi kai tsaye suka sauka kan fuskar junaid,ganin hawaye jaga jaga a fuskar junaid yasa Sgr yin hanzarin miƙewa daga zaune,hankalinshi aɗan tashe yake kallon junaid,da wata irin kasalalliyar murya ya ambaci sunanshi"Junaid!what are u crying for?meya faru ne?.   "Babban yaya,key nake nema na weapon's room,inaso in ɗauko saw ne,za'a 6alle ƙopar ɗakinsu Sehrish"  Cike da mamaki Sgr yace"For what reason?wani abu ya samu door ɗin da za'a 6alleta"?  Ganin bai fahimci inda zancen nashi ya dosa ba,yasa shi yi mashi bayanin abunda ke faruwa,   Saukowa Sgr yayi daga saman gadon nashi,junaid na biye da bayanshi suka fito daga part ɗin nasa,da sauri da sauri suke saukowa down stairs,   Lokacin da suka shigo Corridor(doguwar hanyar) da ɗakunnansu sehrish suke a jere,Hankalin Sgr ya ɗan tashi musamman daya ga dandazon matasan gidan,ga kuma su Abbansu kowa atsaye cirko cirko,fuskokinsu sun nuna alamun damuwa atattare dasu,'  Abbansu na ganinshi yayi saurin ruƙe hannunshi yana fadin"Yawwa rafayet,nasan zaku iya kai da Omar,dan Allah ku haɗu ku 6alle ƙopar nan,ko mun samu muga meke faruwa aciki,'  A hanzarce kowa ya dare ya basu wuri,da iya ƙarfinsu Na ƙarshe suka daddage suka kaima ƙopar wani irin kwakkwaran bugu ji kake daraamm!nan take Sakatar ciki ta zame da kanta,ƙopar ta buɗe,gaba daya suka afka ciki,  Ba ƙaramin girgiza sukayi ba,gaba dayansu musamman Abusufyan,abunda suka gani yayi matuƙar tayar masu da hankali,Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un!!!wannan shine abunda suke ambato a bakunansu,  Sun tarwatsa komai na bedroom ɗin nasu,ɗigon jini jinin da suka gani shi yafi komai tayar masu da hankali, Jahad ce kwance ƙasan gadon saman tiles,damtsen hannunta duk sawun cizo ne,wurin duk ya farfashe,hatta saman kumatunta cizon ne,daga can saman gadon kuwa hosana ce,baje hannunta dafe da kanta ta toshe kunnuwanta sae faman mutsu mutsu takeyi da ƙafafuwanta,alamar idonta biyu,Sehrish kuwa basu san ina ta lula ba,  Zubewa Abusufyan yayi agaban Jahad dake kwance,hannu yasa yana jijjigata yana ambaton sunanta saboda ya gane itace,hawaye sae faman sintiri sukeyi akan fuskarshi,   Jikin kowa yayi sanyi,zukunnawa Abbansu yayi agaban Abusufyan din yana kallon jahad dake kwance,Sawun haƙoran dake asaman fatar jahad ya tabbatar mashi da cewar faɗa ne ya 6arke a tsakaninsu har sukayi kokoyin nan,   "Ina tunanin suma tayi ne,wani ya ɗauko mun ruwa dan Allah,"Abbansu ne yayi maganar,da sauri fawan ya fuce daga dakin,ya nufi babban falo don ya ɗauko masu ruwan da za'a yayyafa mata, ....a hankali Sgr yake bin ɗakin nasu da kallo,sunyi mashi kaca kaca,damben daga saman gadon nasu ya fara,Hatta bargon lullu6arsu duk sun jefo shi ƙasa,zagayawa yayi ta dayan gefen gadon,6angaren hannun hagu,tunkan ya ƙarasa ya hango ƙafafun mutun,hakan ya tabbatar mashi da cewar cikon ta ukunsu ce,ta wuntsila ta baya,lokacin daya ƙarasa wurin a kwance ya samu Sehrish,gefen bakinta ya ɗan fashe,ga kuma sawun haƙora asaman ƙirjinta,da kuma damtsen hannunta,zuƙunnawa yayi agabanta yana ƙare mata kallo,  "Rafayet!wacece anan?ko cikon ƴar ukun tasu ce"?Ishaq ne yayi maganar ganin rafayet ɗin zuƙunne a wurin,  "Itace," ya bashi amsa atakaice,da sauri Abusufyan ya miƙe tare da sauran suka nufo wurin don suga a wani hali take ciki,  Tun kafin su ƙaraso Sgr yayi saurin kai hannunshi gaban rigarta yaja rigar ya lullu6e mata ƙirjinta daya fito sosai,  Fashewa da kuka gwaggon katsina tayi tana fadin"Wayyo Allah ƴa'ƴan Abusufyan ɗina!ni nasan cewa ba yin kanku bane,Wlh sai Allah ya saka maku,Bayin Allah sunji jiki,kowanene yayi masu wannan ɗanyen aikin,jibi yadda aka ciccije masu fata,Yanzu haka ya sayyadine yazo masu da suffar kura yayi masu wannan aika... aikan,' Harris ne ya katseta da cewa"pls gwaggo kibarmu muji da abunda ke damunmu idan ma kina magana ƙara masu zafin ciwon kikeyi,  Jin haka yasa tayi saurin rufe bakinta,tana cigaba da matsar kwalla a idonta,   "Abun ya ɗaure mun kai!garin yaya haka ya faru?gaba daya kowannansu sawun cizo ne a fatar jikinsu",Abbansu junaid ne yayi maganar,a yayin da suke tsaye gaban sehrish,Sgr kuma na a zuƙunne,   Hafsat ce ta basu amsa da cewa"lokacin da nazo ƙopar dakinsu,naji sautin Kukansu acikin ɗakin da kuma sautin bugu kamar suna dambe a tsakaninsu,ina tunanin cewa faɗa sukeyi a tsakaninsu,'  Jinjina kai marshal Omar yayi tare da cewa"Tabbas sunyi sa insa a tsakaninsu ne har abun yakai ga fada,Kuma wannan cizon dake asaman fatar jikinsu,ba kowa bace tayi masu shi ba fa ce HOSANA!saboda nima ta ta6a cizo na a kwanakin baya,da ranta ya 6aci a asibiti,ta cije ni kuma ba ƙaramin zafi naji ba a lokacin,"  Abba yace"No wonder!in kuka lura babu sawun cizo a fatar jikinta,indai itace kwance asaman gadonsu,ku kalli jikinta dakyau,kuma bata jigata ba,kamar yarda ƴan uwan nata suka jigata,"   Suna cikin maganar nan,Fawan ya shigo hannunshi ɗauke da robar ruwan daya dauko masu a fridge,da sauri kanal yousouf ya kar6i bottle water din,ya 6alle murfin,tare da tarbo ruwan a tafin hannunsa na dama,ya watsa shi a fuskar jahad,Nan take taja dogon numfashi tana ambaton sunan Allah abakinta,ajiyar zuciya suka shiga saukewa,da sauri Abusufyan ya dawo wurinta,tare da zukunnawa agabanta,ya ɗago da ita ajikinshi yana ambaton