Sashe 148
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana cikin tafiyar nan kwatsam taji ta taka wani abu a ƙafarta,da sauri ta ɗan ɗaga ƙafarta tare da kai idanuwanta kan abun,Wrist watch ce da alama yarda ta akayi a ƙasa,Zuƙunnawa tayi agaban agogon sai faman ƙyalli take yi da alama ta Diamond ce,
Hannu tasa ta ɗauki agogon tana jujjuyata,Aranta tana ayyana farashin agogon,Daga gani ba ƙaramin diamond bane,Don tunda ake siya mata Diamond ba'a ta6a siya mata mai ƙyalli kalar wannan ba,Agogon ta haɗu sosai,Tayi mata kyau,
 Murmushi ta saki tare cewa"Yanzu haka cikin baƙin jiya ne da suka shigo cikin gidan nan da daddare aka samu wani ya yarda ita ƙasa wanda baisan muhimmancin kuɗinshi ba,Ko kuma wanda bada guminshi aka siya agogon ba,"
Jin takun takalmin Mommynta Yasa tayi saurin,zura agogon acikin aljihun jeans É—in jikinta
"Wlh bazan bari mommy taga wannan danƙareriyar agogon ba,Don ta burgeni da ita Zanyi Hotunan Birthday ɗina,Inyaso daga baya sai a mayarwa mai agogon kayanshi,"
 Ta ƙarasa zancen zucin tare da miƙewa ta wuce dining,Kujera taja ta zauna tana jiran ƙarasowar breakfast ɗinta,
 Shigowa area ɗin Hajiya Sarat tayi hannunta ruƙe da faffaɗan tray mai ɗauke da kayan kalacinsu,Saman table ɗin ta ajiye tray ɗin,
 Murmushi Amrish ta saki tare da yi mata sannu"
 "Yawwa Daughter,"ta amsa mata a yayin da take ɗaukar plate,warmer ta buɗe mai ɗauke da Chips ta soma zuba mata,bayan ta gama ta haɗa mata da kakkauran Tea,tare da slide bread wanda aka jerashi da wainar kwai,"
Nan fa suka hau cin abincin atare suna fira,abunda basu ta6a yi ba ita da amrish,
Wuraren ƙarfe 9,Sehrish ta farka daga bacci tana ta faman yin hamma wata irin matsiyaciyar Yunwa ce ta addabe ta,Saukowa tayi daga saman gadon babu kowa a ɗakin,duk sun fita yin breakfast,ita kaɗai ta rage,
Toilet ta shiga,shaf shaf tayi wanka after some minutes ta fito ɗaure da towel,gaban mirror ta zauna tana shafa mayukan jikinta,sai da ta kammala mulke ko'ina,Sannan ta ɗauki powder zata shafa,Kamar ance ta ɗago ta kalli mirror,kwatsam ba zato ba tsammani taga madubin ya koma mata tamkar tv,manya manyan bishiyoyi ta gani acikin daji ga wasu gwaggon burai gandara gandara masu uban gashi ajikinsu,Sae miƙo mata hannu suke yi ta cikin madubin suna kiran Sunanta"Sehrish kizo,Sehrish kizo"shi ne abunda suke faɗi
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,Idanuwanta suka firfito waje tamkar ƙwayar idonta zata faɗo ƙasa sai kuma taga madubin ya koma lafiya lau,jikinta na kerma ta miƙe ta bar gaban madubin,Da sauri da sauri ta buɗe wadrobe ta ɗauko jallabiya ta zura ajikinta,Mayafin ma a hannu ta ruƙe shi,ko takalmi bata sanya a ƙafarta ba,Gudu gudu sauri sauri ta fito daga cikin ɗakin,
Lokacin da ta ƙaraso dining area din gaba ɗaya ta samu kowa zaune suna cin breakfast ɗinsu,tun daga kan Daddynsu Abusufyan,Oummansu da kuma su Hosana da Jahad,Ga Abba kuma tare da Mommynsu Alex,sai su twins da fawan kanal yousouf dasu Jabeer,Ganin Azmee tayi atsaye tana yin serving ɗinsu,Nan fa ta ƙara shan jinin jikinta,
Jiki asanyaye ta ƙarasa dining ɗin,hankalin kowa ya dawo kanta,
Fuskarta É—auke da murmushi ta soma gaisar dasu"Abba ina kwana"
"Lafiya lou Æ´an matan Abusufyan"murmushi ta É—an saki tare da kallon Mommy"ina kwana mommy an tashi lafiya,
 "Lapiya lou Daughter,"
Komawa tayi kan Daddynsu"Ina kwana daddy kun tashi lafiya,"
Fuskarshi É—auke da murmushi Ya amsa mata"lafiya lou daughter,An sha bacci ko"?
 Dariya sehrish ta ɗan yi tare da kallon Oummansu ta gaisar da ita,Sai da tabi kowa ta gaisar dashi,tana ƙoƙarin zama Abusufyan yace'baki ga Aunty Azmee bane?naga kamar baki gaisar da ita ba,"
 Jimm ta ɗanyi kafin ta wurga eye balls ɗinta kan fuskar Azmee dake tsaye,murmushi ta samu akan fuskarta,
Ba don taso ba hakanan ta daure ta gaisar da ita"ina kwana Aunty Azmee,"
"Lafiya lou Sehrish,Yanzun nan nake shirin zuwa na taso ki sai gashi ma kin fito"
 Baki asake Abu da sehrish ke kallonta,Ta ƙware wurin iya kisisina da munafurci,
 Banza sehrish tayi,batare da ta tanka mata ba,
 Zagayowa Azmee tayi wurinta tare da kai hannu ta ɗauki plate,Warmer ta buɗe mai ɗauke da farfesun Ƴan cikin shanu,Ta zuba ma Sehrish ta tura mata shi agabanta,
 Zuƙunnawa tayi daidai saitin kunnan sehrish cikin raɗa tace"Nasan zaki ji daɗin shan farfesun nan,"
 Tana kai ƙarshen maganar ta miƙe daga tsaye,kallon Oummansu tayi da ido tayi mata alamar ta kwantar da hankalinta,
Ajiyar zuciya ta ɗan sauke tare da zura yatsun hannunta cikin plate ɗin,A tsanake ta soma shan farfesun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,
Sai da ta nutsa cikin shan farfesun ta dinga jin motsin wani abu a hannunta,duk in takai hannu zata ɗebo ƴan cikin sai taji suna kufce mata daga hannunta kamar abu mai rai,hakan yasa takai idanuwanta cikin plate ɗin,Tsutsotsi ta gani suna yawo acikin plate ɗin manya manya,A wani irin firgice Sehrish tayi wurgi da plate ɗin ta fasa Uwar ƙara,Nan take ta shiga kwarara Amai,
Gaba ɗaya hankalin Kowannansu Ya tashi haiƙam,Mikewa tsaye su kayi suna kallonta,kowa na tambayar Lafiya,Da ƙarfi take ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Wayyo Allah na,Na bani na lalace Daddy,Oumma ku taimake ni,Naci tsutsotsi acikin cikina,
Tana magana amai na zuba daga bakinta,duk ya 6ata gaban rigarta jaga jaga,duk tabi ta gigice ta rikice,Watsa wa tayi da gudun gaske tana kuka ta nufi bedroom É—insu,A guje Suka bi bayanta
Toilet ta faɗa cikin fitar hayyaci ta nufi basin,Cigaba da kwarara aman tayi har saida takai ga babu abunda ke fitowa bakinta sai ɗigon jini ta ƙarar da koma da taci ko ruwa babu a cikinta,
 Soso ta ɗauko tare da detergent ta zazzaga shi abakinta,Adai dai lokacin suka ƙaraso ƙopar toilet ɗin,sunyi ƙoƙarin su tura ƙopar amma ƙopar ta datse sakamakon Bugata da sehrish tayi bayan ta shiga,Ƙwanƙwasa ƙopar suka shiga yi kowa na ambaton sunanta,
 'Sehrish!kizo ki buɗe mana ƙopa,kada ki Lahanta kanki fa,"muryar Oummansu ce keyi mata magana,tamkar zata fashe da kuka
Abusufyan ma murya na kerma yace"Wai baza ki buɗe mana ƙopa ba?meyake damunki ne?Dan Allah Daughter ki fito kiyi mana bayani,"
Kwata kwata Sehrish bata jinsu domin kuwa ta jima da makancewa,Ta fita hayyacinta,abunda ta gani a plate É—inta keta dawo mata cikin kanta,
 Tura soson tayi abakinta,Ta dinga gurzar bakin,har saida Le6enta suka faffashe jini ya soma zuba ta ko'ina abakinta,daga waje suka dinga jin Azababben kukan da Sehrish ke yi,na tashin hankali,
 Da gudun gaske Abusufyan yabar ɗakin kaitsaye ya nufi upstairs don ya sanar da Sgr,Suzo su 6alle ƙopar kada ta kashe kanta,
Lokacin da ya shiga Part dinshi ko sallama babu,faÉ—awa kawai yayi gudu gudu sauri sauri ya shiga bedroom É—inshi,Sai faman haki yake yi,A kwance ya sameshi yana bacci jikinshi sanye da jallabiya,
 Tun kafin ma Ya ƙarasa wurin gadon ya shiga ƙwala mashi kira"Rafayet!Rafayet!!"
 Farkawa Sgr yayi lokaci guda ya wurga idanuwanshi masu ɗauke da bacci kan Abusufyan dake ta kwala mashi kira,
 "Uncle lafiya"?
"Ina fa lafiya!Ga sehrish can zata kashe kanta acikin toilet,bamu san meke damunta ba,sai ihu take tana kuka,Munyi munyi mu buɗe ƙopar ta datse ta,"
 Tunkafin Ma Abusufyan yakai ƙarshen maganarshi,Sgr ya sauko daga saman gadon,da wani irin sauri ya fito daga part ɗin,gudu gudu sauri sauri Ya nufi bedroom ɗinsu,Abusufyan kuwa bai baro Upstairs ɗin ba sai da ya wuce ɗakin Omar ya taso shi daga baccin don abun kowa ta shafa,
Lokacin da Sgr ya ƙaraso ɗakin abun ya tashi hankalinshi sosai,Tunda ya shigo corridor ɗin ɗakin Ya fara jin sautin kukan da sehrish keyi,Tamkar ana zare ranta daga jikinta,
 A sukwane ya faɗa cikin ɗakin,Ganinshi yasa suka matsa mashi daga wurin ƙopar,A zafafe ya daddage ya bangaji ƙopar da ƙafaɗarshi,Nan take ƙopar ta buɗe,Faɗawa cikin toilet ɗin yayi a lokacin Harta yanke jiki ta faɗi ƙasa,jinin da ya gani jaga jaga ajikin basin ɗin ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,inda take kwance kasa ga soso nan a gefenta ga kuma ledar detergent ɗin da ta fasa,Bakinta yayi jaga jaga da jini fatar le6enta ta munana duk rauni,
 Jikinshi Yayi mugun sanyi,yaso ace tun lokacin da ta fara haukan suka sanar dashi,slowly ya zuƙunna agabanta,tare da kai hannu ya tallabo kanta,da hannu ɗaya,Ɗayan hannun kuma zura shi yayi cikin bakinta Ya buɗe shi,runtse idanuwanshi yayi yayin da zuciyarshi ke ta faman tafarfasa,harshenta gaba ɗaya ya faffashe,detergent ɗin yayi mata illa sosai,duk ya sale fatar harshen nata,Yaji raɗaɗin abun har cikin zuciyarshi,miƙewa yayi azafafe ya juya yana kallonsu dayake duk sun shigo cikin toilet ɗin,Oummansu sai kuka takeyi,Haka su Jahad da Hosana ma,
 "Tun yaushe ta fara wannan abun?meyasa ba'a sanar dashi ba!"a ruɗe yayi maganar
 "Rafayet yanzu duk ba lokacin wannan bane dan Allah ka taimaka,kada mu rasata,"Abbansu Yayi maganar fuskarshi duk a hargitse
Juyawa yayi tare da sanya duka hannayenshi ya É—aukota tare da É—aurata saman kafadarshi,Ya fuce da ita daga É—akin,A hanzarce Ya haura da ita Upstairs part É—inshi,A saman gadonshi ya kwantar da ita,da sauri ya kuma saukowa down bayan ya É—auki key Ya nufi medical Room É—insu,da kanshi Ya shiga duba Sehrish koda ta farfaÉ—o tana koke koke Allurar bacci yayi mata,
kowa ya shiga damuwa,abincin ma duk sun ƙoshi dashi,A ƙarshe saman Sofa kowa ya zauna cike da jimamin halin da Sehrish ta shiga,Abun ya ta6a masu zuciyarsu sosai,
Har lokacin abu bata daina kuka ba,Haka Jahad da Hosana ma
 "Dan Allah ku kwantar da hankalinku,In sha Allah Sehrish zata samu lafiya,"acewar Kanal yousouf,
 "Kusan kashe kanta tayi fa,Omo ta zuba abakinta ta wanke da soso,Ni bansan meke damunta ba,Sae faman ambaton tsutsa takeyi ni banga komai ba a plate ɗin abincinta,"Abusufyan ne yayi maganar idanunshi cike tab da kwalla,
"Dole akwai wani abun dake damunta,ni tsorona ma kada ta Zauce"
Abba da Mommy sai kwantar musu da hankali suke yi,
Â
Hannun Abu sae kerma ya ke yi,acan ƙasan zuciyarta kuwa,tunanin yarda zata fallasa Azmee take yi don tasan cewa itace Silar Halin da Sehrish ke ciki,tayi jinkiri ne saboda bata jima da zuwa gidan ba,ba lallai bane su yarda da maganarta ba,