← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 212

Sashe 82

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tariyo abunda ya faru tsakaninsu ya shiga yi cikin ranshi,Yadda ya damƙo wuyan rigarta tare da yin wurgi da ita ta bugi bango,har ta fashe da kuka saboda zafin da taji,da kuma munanan kalaman da ta jefa mashi,da alama nazarin wani abu yake yi,dangane da abunda ya faru jiya atsakaninsu,

Ya jima asaman Sofa ɗin,kafin daga bisani ya koma cikin bedroom ɗinshi,darduma ya dauƙo ya shimfiɗa tare da kabbara salla,Sae da ya fara biyan bashin sallolin da baiyi ba,sannan ya ɗaura da yin nafilfilin daren daya saba yi,bayan ya kammala ya ɗauki qur'ani ya shiga karantawa,nan take yaji natsuwa tazo mashi acikin zuciyarshi,bashi ya kwanta bacci ba,har sae wuraren ƙarfe biyu na dare,sannan ya haye saman gadonshi ya kwanta,bacci 6arawo yayi awon gaba dashi,

Itama Sehrish,sae da tayi sallar daren,kafin ta kwanta bacci,

Abunda ya faru daren jiya da Aunty babba ta zauna zaman jiran Hayaam....

tunda ƙarfe goma ta buga hayaam bata dawo ba,nan hankalinta yayi mugun tashi,fitowa tayi daga bedroom ɗinsu,ta shiga zarya acikin hotel ɗin,ko Allah zaisa taga gifcinta,amma shiru babu ita har receptionists taje ta tambaya ko sunga fitarta suka tabbatar mata da basu ganta ba,ƙarshe da ta gaji da biɗiɗin nemanta,komawa tayi ɗakin nasu zuciyarta a ƙuntace ta kwanta,duk da halin da ta shiga na rashin hayaam,hakan bai hanata yin bacci ba,harda minshari,
  Haroon kuwa tun da ya kammala yi mata wannan aika aikar,ya tattara yabar Hotel ɗin ya gudu gaba ɗaya,don kuwa daƙyar in hayaam zata ƙara moruwa,Ya naƙasata sosai,a saman gadon ya barta a yashe,

Wuraren Sallar asuba,Wayar Aunty babba dake ajiye gefenta ta soma ringing,can cikin bacci ta dinga jin ringing É—in wayar,dama ta kwana da tunanin hayaam zata iya kiran ta in ta buÉ—e wayarta,hakan yasa ta farka da sauri takai hannu ta É—auki wayar,duba screen É—in wayar tayi da 6oyayyiyar lamba aka kirata,cike da mamaki tace"To fa,waye ya kirani a irin wannan lokacin da 6oyayyiyar number?kodai hayaam ce ta kira,bari na É—aga na ji,
   Picking call ɗin tayi ta kara wayar a kunnanta,
  Tun kafin tayi sallama taji ance"Madam,barka da warhaka"
  gabanta ne ya ɗan faɗi rass,amma ta dake tace"yawwa,dan Allah wanene ke magana,"
   "Babu bukatar ki sani,dama na kira ne don in yi aikin lada,Nasan kina ta neman hayaam ido a rufe,to hayaam dae a halin yanzu addu'arki take buƙata,idan kina son sanin inda take,yanzu zan turo maki da message na address ɗin inda take,sae ki hanzarta zuwa don ki kai mata agaji,Allah ya bata lafiya,idan ta samu ciki dan Allah a ajiyemun abuna,inaso" yana faɗin haka,yayi rejecting kiran,"
  Waro ido waje Aunty babba tayi,a hargitse ta saukko daga saman gadon hannunta riƙe da wayar,jikinta har kerma yakeyi,zarya ta shiga yi acikin ɗakin tana jiran shigowar saƙon,
  A fili tace"Allah yasa dae hayaam ba wani taje taba ma kanta ba yayi amfani da ita,Sae da naja mata kunne akan ta daina kula maza,amma da ya ke karya ce gaya nan tana son ja mun bala'e,ina zaman zaman lafiyana,"

Tana cikin wannan zullumin,taji ƙarar shigowar message da sauri ta duba top of the screen ɗin wayar,
  "Vip,Room 34,"shine abunda taga an rubuta acikin message ɗin,kuma babu numbar wanda ya tura,anyi hidden number,
   Sai da tayi zurfin tunani sannan ta gane cewa numbar ɗakin hotel ne aka turo mata,hakan na nufin cewa hayaam tana acikin hotel ɗin,
   Jiki na rawa ta ƙarasa wurin trolley ɗin kayansu dake ajiye,gefen wardrobe,buɗe wa tayi ta dauko mayafi ta lullu6a asaman kanta, 
  Sannan ta tura kopar ɗakin ta fito,tafiya takeyi cike da zullumin abunda zai biyo baya,sae bin ɗakunan dake a wurin takeyi tana bin numbobin jikinsu,cikin sa'a batare da tasha wahala ba tazo kan numbar ɗakin da aka turo mata,sae da ta duba dakyau taga Room 34 ne,Hada key aka ajiye mata ajikin ƙopar,wannan ya tabbatar mata da cewa da gangan aka sanya key ɗin,saboda in tazo ta buɗe ta shiga,
   Gabanta sae faɗuwa yakeyi,a hankali ta sanya hannunta ta ɗan murza key ɗin ɗakin ya buɗe,cike da fargaba ta tura ƙopar ɗakin a wani slow kopar ta soma buɗewa ƙiiiiiii,tun kafin ma ta sanya kafarta acikin ɗakin ta hango pant yashe a saman tiles,Rass taji gabanta ya faɗi,wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,dakyar ta shiga cikin ɗakin,karaf Idanuwanta suka hango mata Bra din hayaam dake sagale ajikin mirror,tun daga nan tasha jinin jikinta,wurga idonta tayi gefen hagunta,Handbag ɗin hayaam ta hango yashe a kasa,da alama wurgi akayi da jakar kayan cikinta suka watse akasa,hada wayarta ma duk screen ɗin ya fashe,
..arazane Aunty babba takai idonta saman gadon,mutunne a kwance an lullu6e shi da bargo,
  A tsananin tsorace ta ƙarasa gaban gadon,sanya hannunta tayi tare da zame bargon a hankali,tana buɗe bargon da sauri ta mayar ta rufe,saboda tashin hankalin da ta gani,hannu ta aza akai ta fasa ihu tana faɗin"Nashiga uku!Wayyo Allah na,Hayaam wani marar imanin ne yayi maki wannan aika aikar!hayaam waye ya yashe ki haka!La'ila ha'illallahu muhammadur rasulillahi!Amma kowaye wannan anyi haihuwar asara,Uwarshi ta haifo mana Bala'e" ta inda take shiga bata nan take fita ba,Muryarta har shaƙewa takeyi saboda tsabar baƙin ciki,tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu,
..a karshe ta fashe da matsanancin kuka,tare da hayewa saman gadon,tana cigaba da sambatu,da alama ta fara zaucewa,
   "mun shiga uku mu yau,Wllh dana san haka zata faru da bamu zauna a hotel ɗin nan ba,ƙaddara ce kawai ta riga fata,Hayaam kowaye wannan ya gama damu,ɗan jarin da muke taƙama dashi ya kwashe komai babu,ya yashe ki,ya karya mana tattalin arziƙin da yayi mana saura,Ya takaita mu don ubanshi,wlh koma wani jarababben ne,Sae Allah ya toni asirinshi,Ni na ta6a ganin jaraba irin wannan,bai bar komai ba,yayi mata wanwar ɗan jakar uban,haihuwar asara haihuwar titi,haihuwar kwararo...."kasa ƙarasa maganar tayi,wani irin ƙululun baƙin cikine ya tokare mata maƙoshinta,nan tashiga yin kakarin amai,ta saukko daga saman gadon agalabaice ta nufi toilet ɗin cikin ɗakin ta shiga,Sosai tayi amai tamkar ƴan hanjin cikinta zasu fito waje,ta jima acikin toilet ɗin kafin ta fito,tana tafiya ƙafafunta na harɗewa,
  Fitowa tayi daga ɗakin ta koma ɗakinsu,Trolley ɗin kayansu ta buɗe,Jallabiya ta ɗaukowa hayaam tare da Mayafi,Sannan ta koma can ɗakin,taci wahala haka ta kinkimi hayaam ta shiga da ita toilet,wani wurin ma ajikinta,baya ta6uwa sae dai anje asibiti duk ya jagule babu kyan gani,hatta la66anta duk sun faffashe hada busasshen jini,nipple ɗinta na right breast kuwa,sai jini yake yi,ƙiris ya rage ya 6alle,haƙika haroon ya cutar da ita,ya zalunce ta,Da mugunta yayi mata hakan,Dama babu Imani aranshi,duk ya faffasa mata skin ɗinta da Nails ɗinshi,saboda baya yanke akaifa,doguwar ƙumba ne dashi,
  Aunty babba tasha kuka,Tuntana kukan fili har ta koma yin kukan zuciya,wanda yafi ciwo,Sai da ta nemi taimako a hotel ɗin,sannan ta samu aka ɗauki hayaam,Suka kaita wani private hospital saidai sam bata sanar dasu haƙiƙanin abunda ya sameta ba don tasan karshe reporting za'ace ayi wurin yansanda ita kuma bata son asirinsu ya tonu har abun ya kai kunnan su Ishaq,tafi son in hayaam din ta farfado ta fadi wanda yayi mata hakan don ta tabbatar ba da karfi aka jata dakin ba don wanda ya kira ta ya sanar da ita halin da take ciki har sunan hayaam din ya ambata hakan kuma na nufin ya santa ne,

 Tunda aka shiga da ita ciki,Likitoci suka taru akanta,Aunty babba na zaune zugudum saman waiting seat,tashin farko sae da suka fara kar6ar kuɗin gadon kusan Naira dubu 50,Sannan za'ayi mata aiki ciki da waje a ƙalla za'a cajesu kuɗi kusan Dubu ɗari biyar,Bayan haka akwai alluran da za'ayi mata ajikinta kuɗinsu ya kai kimanin dubu 20,
  Abun yayi matuƙar girgizata,ita babbar damuwarta,ba halin da hayaam ke ciki ba,Kuɗinsu da suke tattalawa zasu je wurin boka,Har an yashe kusan rabinsu,wasu mutanen dai ba imani aransu,ɗaya daga cikin halin ɗan adam kenan,Duk yadda take da hayaam same parents,Amma harta fara tunanin guduwa ta barta a asibitin saboda gudun kar su talauta ta,Kuma ta yanke shawarar zata yi ma Abra magana tazo su tafi wurin bokan tare da ita,Tunda ita hayaam ta gama lalacewa,babu wani amfanin da zata yi mata,ƙarshe ma taja masu asara,yini tayi a asibitin tana zirga zirga,Yayin da zuciyarta ke saƙa mata,ta gudu tabar asibitin,tun da ta samu ta biya mata kuɗin aikin Can su ƙarata,

Har wuraren ƙarfe Goma na dare,lokacin an kammala yiwa hayaam aikin,Amma bata farfaɗo ba,tsayawa Aunty babba tayi abakin ƙopar shiga ɗakin tana kallon hayaam dake kwance,hancinta na sanye da Oxygen,
  Komawa tayi saman waiting seat din,inda tabar handbag ɗinta,ɗaukar jakar tayi ta buɗe ta,biro ta curo tare da memo,aza takardar tayi saman kujerar sannan ta soma rubutu Kamar haka
  _Hayaam sae dai kiyi haƙuri,Wlh bazan iya cigaba da zama acikin asibitin nan ba,duk laifinki ne,Sai da na gargaɗeki akan karki kuskura ki ƙara kula wani ɗa namiji,amma da yake ke karyace ba'a raba ki da maza,Gashi nan kin jawowa kanki wanda yafi ƙarfinki,Ya gama dake yayi maki kankat,babu abunda yayi saura ajikinki balle har insa ran zakiyi mun amfani,Shiyasa na yanke shawarar zanyi ma Abra magana,zamuje wurin bokan tare da ita,Don bazan bari burina yaƙi cika ba har su Amani suyi nasara,In dana gode ma Allah bake kaɗai bace ƙanwar da nake da ita ba,Wlh dana ji kunya_
  Tana kammala rubuta short note ɗin,Ta ɗauki handbag ɗinta,Sannan ta shiga cikin ɗakin da aka kwantar da hayaam ɗin,A gefenta ta ajiye wasiƙar,Sannan ta curo bandir ɗin kuɗi dubu hamsin ta ajiye mata a gefenta,a hankali ta furta Allah ya baki lafiya hayaam,Idan kuma kin riga mu gidan Gaskiya,Allah ya jiƙanki da rahama,
  Tana kai ƙarshen maganar,da sauri ta juya tabar ɗakin,batare da 6ata lokaci ba,ta gudu tabar asibitin,
  Rayuwa kenan,

*Boss Bature*

   ❤🤍❤
Chapter 82 · 0% Book details