← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 212

Sashe 86

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wuraren ƙarfe 6 na marece,wata danƙareriyar mota tayi parking a cikin wani katafaren hotel,a parking space motar ta tsaya,jim kaɗan wata matashiyar budurwa ta fito daga cikin motar,jikinta na sanye da riga bubu ta material,ƙafarta kuwa na sanye cikin high hills,ta coge ɗaurin kallabin nan na rashin ɗa'a,Sae faman taunar cingam takeyi abakinta,
   Hannunta na ruƙe da ƴar purse ɗinta,ta sagala mayafin asaman kafadarta,
....fitowa wani matashi yayi daga gaban motar,daga ganinsa zakasan cewa ba ƙaramin shege bane,kuma tantirin ɗan iska,
  Zagayawa yayi tare da buɗe boot ɗin motar ya ɗauko mata trolley ɗin kayanta,sannan ya kalleta tare da cewa"Babe,Mu shiga ciki ko?in ɗan taka maki"
Murmushi Abrah,ta saki tare da nuna mashi hanya tace"bismillah,"gaba tayi yabi bayanta,suna tafiya yana yi mata sambatu,"Gaskiya zanyi kewarki sosai baby,bansan ya rayuwata zaka kasance ba,idan babu ke,zan zama tamkar maraya,"_
  Abra tace"hmm,dama ka daina yi mun wannan daɗin bakin naka wlh,Don na sanka,mayen mata ne,Allah kaɗai yasan yawan matan da kake mu'amala dasu,Ni bansan ma tanawa bace,"_
   "Subhanallah,Zargina kikeyi ma kenan?babu kyaufa,"
  "Ba zarginka nake yi ba,zahiran na gani ae,"suna magana suna tafiya har suka shiga cikin reception,mutane ne ke ta safa da marwa a wurin,Batare da sun sha wahala ba,ta hango Aunty babba tana tunkarosu,Fuskar nan aɗaure babu annuri,Amma tana hango saurayin da Abra tazo dashi,nan take ta ɗan saki fuskarta,ƙarasowa tayi wurinsu,
  "Sannunku da zuwa ya gajiyar tafiya,"
   Saurayin ya amsa mata"Alhamdulillah,Mun same ku lafiya,"
  "Lafiya lou,"kafin ta mayar da idonta kan abra tace"Wanene wannan kuma?yakamata a gabatar mun dashi,ko da yake bari mu shiga daga ciki,'tayi maganar tana yi masu nuni da hannunta,
  Saurayin yace"kash,bazan samu shiga ciki ba,ina sauri ne zan wuce wurin wani uncle ɗina dake anan,Urgently yake nemana,"
   Aunty babba tace"Amma banji dadi ba,duk irin wannan ɗawainiyar da kayi mana,bazaka shigo daga ciki ba ka huta,ko lemu ne ka ɗan sha,'
  "Kada ki damu Aunty,Idan kuka dawo daga tafiyar zanzo ne sai mu gaisa dakyau,"
   "Aunty wannan shine Bobby ɗin da nake baki labarinshi,Yana da kirki sosai,Saboda yana kyautatamun,"ta ƙarasa maganar,fuskarta dauke da murmushi,
  Aunty babba tace"Ma sha Allah,naji daɗin ganinka sosai,Allah dae ya nuna mana ranar aurenku,Musha biki,'
  Murmushi ya saki yana faman shafa keyarshi da hannunshi,
    "Bari mu shiga daga ciki,Sae munyi waya,"acewar Abra,
   "Okey babe,ki kulamun da kanki,Sae kinga saƙona,"
   Ya ƙarasa maganar tare da juyawa yabar reception din,Aunty babba tayi gaba Abra tabi bayanta,Har izuwa cikin ɗakin da ta kama,
    Suna shiga cikin ɗakin abra ta saki trolley din kayan,ta faɗa saman gadon ta kwanta tana faman sauke ajiyar zuciya,
    Daga gefen gadon Aunty babba ta zauna,tare da kallonta tace"kun sha tafiya,toh ya ku ka baro su mammyn'?
  "Tana can,rai hannun Allah,ae na faɗa maki cewa bata da lafiya,Amma da sauƙi dae,tunda tana ɗan mikewa har ma ta zauna,Matsalar dae babu mai kula da ita,Shima Abie ya tattara yana shi yana shi yabar gidan,yanzu ita kaɗai ce acikin gidan,bansan ya zata ƙare ba,"hankalinta kwance take yin maganar,
  Shiru Aunty babba ta ɗan yi,batare da ta janye idanuwanta daga kan fuskar abra ba,
  "Aunty kinyi shiru,ba kice komai ba?wai nikam Ina Aunty hayaam ne'?nayi tunanin zan ganku atare ne,kuma nayi mamakin ganinki a hotel"
   Harara ta ɗan watsa mata tare da cewa"in ba a hotel ba,a ina kikeson ki ganni ne?Ko bakisan cewa aure na ya mutu ba"?
...ƙumshe dariya Abra tayi,
    "Kiyi mai isarki lokacinki ne ƴar rainin hankali,Muna nan cikin tashin hankali,ke kina can kina holewarki,wato kin samu duniya ko"?
  Turo baki abra tayi tana fadin"matsalar kenan fa,yanzu nasha wahalar tafiya,ko ruwa ban sha ba,Amma zaki fara yi mun faɗa,Allah in naji ban iyawa,sae dai ki neme ni ki rasa,"
   Sakin baki Aunty babba tayi tana kallonta,kafin tace"lallaine wuyanki ya isa yanka,fiye da haka ma zaki iya faɗamun,"
    murguɗa baki abra tayi tare da cewa"na tambaye ki Aunty hayaam amma baki ce komai ba,tana ina,"?
   Ta6e baki Aunty babba tayi kafin tace"Ae hayaam ni kaina bansan inda take ba,kinsanta bata gajiya da yawo,yau kusan kwana uku banganta ba,sae dai ta kirani mu gaisa,Amma ni kona kirata a kashe nake samun wayarta,"
  Saboda rashin tsoran Allah,Aunty babba ta zauna tana shirgawa Abra ƙarya,don tasan cewa muddin Abra taji cewa,hayaam na kwance gadon asibiti ba lafia,baza ta ta6a yarda suyi tafiyar nan da ita ba,Sai ta tsaya tayi jinyarta,kuma in taji cewar ta bar ƴar uwarta a asibiti babu mai kula da ita,to tabbas ranta zai 6aci sosai,"
   "Kai Aunty hayaam,ita ma dae kamar wadda taci ƙafar kare,bata nan bata can,"
  Aunty babba tace"Ni duk ba wannan ba,Kinsan dai dalilin dayasa nace kizo ko"?
  "Eh nasani,"ta bata amsa,
"Yawwa,Jibi nakeso mu shirya mu tafi,lokacin kin huta sosai,"
  Yatsina fuska Abra tayi,tana ɗan gatsina hanci tace"Oh ni,yanzu haka zamu kwasa mu tafi wurin boka har enugu,cikin dajin Allah,Kamar waɗanda basu da mafaɗi,Kuma dae babu tsoran Allah..... "
  Tunkan ta ƙarasa maganar Aunty babba tace"Rufe mun baki,Uwar surutu sai kace aku,Duk ba don ku akeyi ba?don rayuwarku tayi kyau," fuskarta aɗaure tayi maganar,
  Zumbura baki abra tayi,tare da yin ƙasa ƙasa da muryarta tace"mutun yayi sallar dare mana,ya roƙa wurin wanda ya halicce shi sai wani boka can"
  "Me kikace"Aunty babba tayi tambayar tana kallonta,Don tajiyo ƙusƙus ɗin da take yi,
 Abra tace"Ni Bance komai ba,idan ma nayi magana to akan abinci ne,yunwa nake ji,"ta ƙarasa maganar tana shafa stomach ɗinta,
   "Okey,bari nayi mana order,sae muci atare,don nima banci komai ba,"
  
Wuraren ƙarfe 7,Motoci guda biyu suka shigo cikin gidan a jere,a lokacin Jahad da Sehrish suna a kitchen tare da Aunty azmee suna tayata aiki,Azmee na agaban gas cooker,Sehrish da jahad,suna yanke yanken kayan lambu,
  Jin dirar motacin nan yasa Sehrish saurin cewa"Ga babban yaya nan ya ƙaraso gida,"
  Jahad tace"Anya kuwa shi ne?Junaid fa ya sanar dani cewa yau ko gobe zasu dawo,Allah yasa su ne,kada abunda na haɗa mashi ya lalace,"
  Murmushi sehrish ta saki,tana cewa"Mrs romeo,Ae koda bai dawo ba,mu zamu cinye kayan daɗin da kika haɗa mashi,".
  Muryar azmee suka jiyo daga bayansu tana cewa"Nima hadani za'aci daɗin,"
  Dariya su kayi gaba dayansu,
Jahad tace"idan zaki ci Aunty azmee babu damuwa,Amma Allah koda bai dawo yau ba,ƙwara na zuba shi a dustbin da dai inba su rishi suci"
  Harara sehrish ta ɗan watsa mata da yake suna facing ɗin juna na,tace"saboda baƙin hali irin na ɗan adam,'
   "Aunty azmee ina da tambaya dan Allah,"acewar jahad,
  Azmee tace"Allah yasa na sani,"
Murmushi jahad ta yi tare da cewa"Tsakanin babban yaya da Junaid waya fi wani kyau,"
  Har sai da gaban azmee ya faɗi rass,Saboda girman tambayar da tayi mata,jinjina kai tayi na wani lokaci kafin tace"tashin hankali,Kuma ni kike so in amsa maki tambayar,"
  Jahad tace"Eh,saboda nasan kinsan menene kyau,zaki iya fadin wanda yafi kyau acikinsu,"
  Sehrish tuni ta dakata da yankar lettuce ɗin da takeyi,hannunta ruke da wuqa,duk ta qagara taji amsar da azmee zata basu,
  "Ni ko a school,ban ta6a haɗuwa da question mai wuyar Amsawa ba irin wannan,To ae dukkansu kyawawane na bugawa a jarida,Junaid kyau rafayet kyau,"
  Dariya sukayi jin yadda azmee keta nanata maganar,da alama sun caza mata kai,
   "Amma ni a ganina,kamar junaid yafi kyau,saboda shi fuskarshi kullum asake take,Kuma wannan murmushin nashi ba ƙaramin kyau yake ƙara mashi ba,"acewar Sehrish,
Jahad tace"Amma ae bai kai yaya rafayet tsayi ba,duk da shi ma dogone,kuma baida irin surar jikin babban yayan mu,"
  Sehrish tace"Ae da ace shima junaid ɗin zai dinga motsa jiki,in a short time zaki ga ya koma kamar babban yayan mu,ae su maza daga sun fara ɗaga ƙarfe Jikinsu ke buɗewa,"
  Azmee tace"hakane kema kince wani abu anan,Gaskiya dukkansu zan iya cewa babu wanda yafi wani kyau,idan don saboda murmushi zaisa junaid ya ɗare rafayet a kyau,to ae shima rafayet ɗin idan yayi murmushi sai kin kusa zaucewa,kilan bai ta6a yin murmushin bane kun gani,sannan kuma ga surar jiki ta ko'ina dae su duka biyun sai dai ace ma sha Allah..."zugudum sehrish tayi tana sauraron abunda azmee ke cewa,aranta tace"Kutmelesi,Su Aunty azmee har ansan su babban yaya nada kyawun sura,da kyakkyawan murmushi,ba dai kalle mun mijina takeyi ba,"ta ɗan yi maganar hada tamke fuska,can kuma ta fashe da dariya...,
Chapter 86 · 0% Book details