Sashe 72
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bakomai ne ya ƙona mata rai ba,Fa ce abunda kunnuwanta suka jiyo mata,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,komai ya fita aranta,tabbas tana son Sgr sosai har cikin ranta,kuma babu abunda ya canza acikin zuciyarta,tayi farin ciki mara misaltuwa na kasancewarta matarshi,wannan babbar kyauta ce agareta,sae dai kash bataso ya aureta batare da yana sonta ba!Sam bata ta6a ra'ayin hakan ba,tafi son ta auri wanda take so kuma yake sonta,bawai wanda takeso ba,Shi baya sonta,bugu da ƙari kuma ya aureta ne don taci gaba da aiki a ƙarkashinshi na wata uku kacal!
   "Idan ba damuwa inaso ku ɗan bani wuri in shawo kanta,"hajiya azeema ce tayi maganar,
  Abusufyan yace"kina ganin zaki iya shawo kanta kuwa?
 "Ku je kawai,Ni nasan yadda zanyi da ita,ku ɗan bamu wuri,"
 Kama hanya sukayi gaba ɗayansu hadasu jahad suka bata wuri,kamar yadda ta bukaci su fita daga dakin,
 Zuƙunnawa hajiya azeema tayi abakin ƙopar toilet ɗin,Saboda ranta ya bata cewar sehrish tana zuƙunne a ƙasa,ta gane hakan ne ta hanyar sautin kukan nata,
 Cikin lallami ta ambaci sunanta"Sehrish,"
 Cikin shessheƙar kuka tace"Na'am,"
 "Inason magana dake!dan Allah ki bani haɗin kai,kada ki bani kunya,inaso kizo ki buɗe mun ƙopar nan!,"
  Miƙewa sehrish tayi,jikinta sai faman kerma yake yi,daƙyar ta iya sanya hannu ta buɗe kopar toilet ɗin,
 Sauke ajiyar zuciya hajiya azeema tayi tare da mikewa tsaye tana kallonta,fuskar nan tayi suntum da ita,gaja gaja da hawaye,idanun sun kumbura,janbakin da ta shafa duk ya 6ata mata fuskarta,mascara ɗin da aka shafa mata asaman eye lashes ɗinta,duk ya jike sharkaf da hawayenta ya 6ata fuskar da baƙin,kayan jikinta ne kawai basu 6aci ba,
 Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita daga gefen gadon nasu,itama ta zauna suna fuskantar juna,
"Haba amaryar babban yaya,kuka bana ki bane,Farin ciki ya kamata na gani akan fuskarki,"cike da zolaya hajiya azeema tayi mata maganar hada jan kumatunta,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan cikin shesshekar kuka tace"Am...amma..Aunty azeema..meyasa za'ayi mun haka?saboda me za'a ɗaura mun aure tare da babban yayanmu batare da an sanar dani ba?Nasan cewa sun isa dani!Amma yakamata ayi mun adalci,Auren wata uku fa?kawai saboda buƙatar kanshi"?
 Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi cikin sanyin murya tace"Inaso na tambayeki wani abu,amsa ɗaya kawai nakeso ki bani,kuma ki faɗamun gaskiya,'
Dakatawa sehrish tayi da yin kukan tare da mayar da hankalinta kan Aunty azeema tana sauraronta,
  "Inaso ki faɗamun gaskiya,Shin kina son Sgr ko bakya son shi ne"?
 Shiru sehrish tayi yayin da idanunta ke akan yatsun hannunta da ta harɗesu wuri guda tana murzasu,
 "Kinyi shiru baki ban amsa ba"?
ƙasa kasa tayi da muryarta tare da cewa"bazan 6oye maki ba Aunty azeema,ina son Yaya rafayet sosai,fiye da yadda nake son kaina,"
  Murmushi hajiya azeema ta ɗan yi,dama saida ranta ya bata cewar tana sonshi,
 "In har dagaske kina son shi bai kamata kiyi kuka ba don an ɗaura maki aure dashi,"
 "Aunty azeema ba baƙin ciki nake yi ba,bakomai ne ya 6ata mun rai ba fa ce irin auren da akayi mun dashi,Saboda kawai nayi aiki a ƙarƙashinshi,na tsawon wata uku?meyasa za'ayi mun haka?idan aka barni ma zan iya yin aiki a ƙarkashinshi ba sai ansa ya aure ni ba,ba bisa son ranshi ba,tunda ba sona yake yi ba,ni kaɗaice nake ɗawainiya da son shi tun kafin nasan wanene shi,Wahala kawai zansha a hannunshi,Ni ban ta6a son na aureshi ba batare da yana Sona ba,"
 Jinjina kai hajiya azeema tayi tare da cewa"hakane kin faɗi gaskiya,ba'ayi maki adalci ba,Ni kaina bansan dalilin yin auren ba sai daga baya nake ji a wurin Abbanku,Amma kiyi haƙuri dan Allah kada hakan yasa ki bijire ma iyayenki,kiyi masu biyayya in sha Allah zaki ci ribar yin hakan,"
 Batare da musu ba Sehrish tace'Shikenan,in sha Allah zanyi masu biyayya,kamar yadda kika ce,kuma koda baki faɗamun haka ba,Ni bazan yi kuskuren bijire masu ba,"
 Murmushi hajiya azeema tayi tare da sanya hannunta ta shafa gefen fuskar sehrish,
"Good girl,Naji daɗi sosai da kika amince zakiyi masu biyayya,Ni kuma nayi maki alƙwarin cewa atare zamu yaƙi sgr,acikin waɗannan watannin guda uku kacal,Zamu canza mashi ra'ayinshi,don ya gane kuskurenshi,kinsan ance DUK ƘYAN TAKALMI ƘAFA CE KE TAKASHI,So nake ki take mun wannan tsadaddan takalmin da ƙafafun nan naki ya taku sosae,"
Sae lokacin Sehrish ta fashe da dariya,har hakoranta suka bayyana,maganar da hajiya azeema tayi mata ta ƙarshen nan ba ƙaramin dariya ta bata ba,
Cigaba da magana hajiya azeema tayi"domin aikin mu yayi kyau muna buƙatar mu shirya plan A da kuma plan b zuwa c,zamu fara jaraba plan A,idan har akaci nasara akan shi kinga basai mun buƙaci plan B ba,Abunda nakeso dake yanzu shine muna buƙatar satar amsa,kuma ke kaɗae ce zaki iya samo mana wannan satar amsar da muke buƙata a wurinshi,
A tsorace sehrish tace"Ni kuma!"hajiya azeema tace"kwarai kuwa,ba wani abun tashin hankali bane,just akwai bukatar musan me yake so da kuma abunda baya so don mu kiyayesu,Ni dae a iya sanina Sgr mutunne maison abi umarninshi ba'ayi mashi musu,yafi so ayi mashi biyayya abishi sau da ƙafa,sannan mutunne shi mai tsaftar gaske,ya tsani ƙazanta,bayan haka kuma Yana son abinci mai daɗi,shiyasa yake cin girkin azmee saboda tana da tsafta kuma ta iya girki,yakama ki koyi kalar girke girkenta,"
"Ae na fara koyo a wurinta,Kuma na iya waɗansu,amma zanyi mata magana akan ta ƙara koyamun wanda ban iyaba,"
"Yawwa haka nakeson ji,ki dage sosai,Nidae ta 6angarena zan baki gudummuwa sosai,""
Sun jima suna fira atsakinsu tamkar ba uwa da Æ´a ba,har sae da aka fara kiran sallar Magrib,sannan aunty azeema tayi mata sallama,
Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ta samu ƙwarin guiwa sosai a wurin Hajiya azeema kuma taci alwashin zata ɗaura ɗamarar zama da sgr,har na tsawon wata ukun
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 12 na dare,tana a tsaye cikin ɗakinsu,sae faman zagaye zagaye takeyi,tana jiran dawowar Sgr,tun bayan sallar isha'e bai dawo cikin gidan ba,har lokacin wedding gown ɗince a jikinta,ta gyara kwalliyar fuskarta,sannan ta daure gashin kanta da ribbom,
Jahad da hosana sun jima da yin bacci ita kaɗae ta rage batayi bacci ba,zuciyarta cike take da damuwa,sam tagaza samun natsuwa babban abunda takeyi ma fargaba shine taya zata fara tunkarar SGR a matsayin Mijinta?shin zata iya jure zama dashi?tasan cewa dole ta fuskanci ƙalubale dayawa a wurinshi,
Tana cikin wannan zancen zucin taji shigowar motocinsu,ajiyar zuciya ta sauke tare da komawa gefen gadonsu ta zauna tana jiran su ƙarasa shigowa cikin gidan,
Almost 30 mins,sannan ta miƙe tare da buɗe ƙopar ɗakin ta fito waje,babu kowa kai tsaye ta nufi kitchen,batare da 6ata lokaci ba,ta shirya mashi dinner ɗinshi a saman ƙayataccen tray ta ruƙo shi da hannayenta,a hankali take tafiya saboda tsinin takalman dake a ƙafafunta,bata saba tafiya da irinshi ba,babu kowa a main palour ɗin hakan yasa ta wuce upstairs part ɗinsa,
Da sallama abakinta tashiga falon,babu kowa aciki sae dae kamshin turaren nan nashi,kama hanyar zuwa bedroom ɗinshi tayi,a bakin ƙopar ta tsaya tare da yin sallama"Assalamu alaikum"
"Who's there"abunda taji yace kenan,
daƙyar ta iya cewa"Ni ce"
"Okey,Come in"
A hankali ta zura ƙafarta cikin ɗakin nashi,samun shi tayin kwance asaman katafaren gadon nan nashi na mulki,ko takalman ƙafarshi bai cire ba,still shaddar ce ajikinshi,
Ƙarasa shiga ciki tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table,kamar wata mara gaskiya ta juya zata kama hanyar fita daga ɗakin muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"Baki iya gaisuwa bane?"
dakatawa tayi tare da É—an juyo ta saci kallon fuskarshi,A lumshe ta samu idanunshi tamkar maijin bacci,
Muryarta na rawa tace"Ina yini"
Ta6e la66ansa yayi tare da cewa'zonan""
Jiki asanyaye ta tunkareshi,da hannu ya nuna mata gaban gadon nashi,sannan yace"kneel down"
Tattare rigar jikinta tayi,tare da zubewa saman guiwowinta,
"Kukan me kikeyi É—azu?ko don saboda kinji abunda muke tattauna da Abba ne?"
Girgixa kai tayi'a'a ba haka bane,""
"Okey,"
Shiru ya ɗanyi na wani lokacin kafin yaci gaba da magana"Na aureki ne saboda inaso ki cigaba da aiki a ƙarƙashin ikona!Idan har bakya ra'ayin hakan zan iya sakin ki,"Ya ɗan dakata da yin maganar yana jiran jin amsarta,
Â
 Â
 Â
 Â
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة ØØ¨ رومانسية بين Ø³ØØ±ÙŠØ´ ÙˆØ§Ù„Ø¬Ø±Ø§Ø Ø§Ù„Ø¹Ø§Ù… Ø±ÙØ§ÙŠØªðŸ’‹ðŸ’˜â¤ðŸ¤â¤ðŸ’•💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_â¤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana kaitsaye ta layina 08103884440â¤_
Not edited,