← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 212

Sashe 71

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Jiki na rawa sehrish ta kama hanyar fita da sauri Hosana tabi bayanta,suka fita atare,
    Matsawa yayi kusa da jahad,tare da ruƙo hannayenta yace"Jahad!Albishirinki"?
"Goro,"ta bashi amsa fuskarta É—auke da murmushi,
"Fari ko Ja"? Wurga ido ta É—an yi sama kafin tace"Fari,"
    "Uncle ya bani aurenki,"jin wannan maganar yasa hankalin jahad ya tashi,lokaci guda ta ɗaure fuskarta,tare da fisge hannunta daga cikin nashi,
   Gabansa ne ya faɗi,ganin yadda ta canza mashi lokaci guda tsoranshi kada ace jahad ba son shi take yi ba,
  "Jahad baki sona?bakison ki aure ni ko"?
  Shiru jahad tayi tana ƙare mashi kallo daga ƙasa har sama,
   Tuni idanunshi sun cicciko da kwalla,fargabarshi wata amsa jahad zata bashi,in har bata amince ba shikenan zai rasa damar da yake da ita,na mayar da gurbin rishi ɗinsa daya rasa,
   Motsi ta soma yi da la66anta daƙyar ta iya cewa"Junaid!dagaske kake mun ko wasa?tell me the truth pls,i know u are just teasing me,'
    Girgiza kai yayi tare da cewa"Am serious jahad,Bazan 6oye maki ba,da farko sehrish nake so sosai,in har ba zaki manta ba,lokacin dana ɗauko ki a school matsayin sehrish,idan zaki iya tunawa sunanta nake ambata a matsayin ke,nayi tunanin itace shiya sanya na sanar dake abunda ke acikin zuciyata,Amma yau batare da sani na ba,A masallaci naji sanarwar ɗaurin Auren Sehrish da babban yayan mu,har sai da na kusa zaucewa ƙarshe a masallacin na yanke jiki na fa....."
  A razane jahad ta katse shi da cewa"Wai dagaske an ɗaura auren Sehrish!kuma da babban yayan mu!?
   ɗaga mata kai yayi alamar eh,kafin ya ɗaura da cewa"Ni kaina bansan da zancen auren nasu ba sae a masallaci dana ji ana sanarwar,abun ba ƙaramin ta6a zuciyata yayi ba,na shaqu sosai da sehrish,
  Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba,jin zancen auren Sehrish da Sgr,ta rasa gane a wane yanayi take ciki,farin ciki ko kuwa akasin hakan!babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda aka 6oye masu ba'a sanar dasu ba,Ko meyasa?Yanzu shikenan an ɗaura auren rishi ɗinsu?ta zama married woman?
   Runtse idanuwanta tayi tare da sanya hannu ɗaya ta dafe gefen goshinta,a hankali ta furta"Ya salaam,"
   "Jahad,inason naji amsar tambayar da nayi maki"?muryarshi a kasalance yayi maganar,don ya qagara yaji amsar da zata bashi,
   A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskar junaid,tana kallonshi tace"junaid Daddy da kanshi ya baka aure na?kuma ya tabbatar maka da cewar bada wasa yake maka ba"?
   Bubbuga ƙafafunshi yayi saboda hasalar da yayi,a ƙule yace"eh mana,shi da kanshi ya mallaka mun ke agaban kowa da kowa,yaji tausayina ne saboda halin dana shiga,"
.....fuskarta aɗaure tace"Meyasa daddy zai yi mun haka?nace mashi ina sonka ne?kuma ya rasa ma wazai ba aure na sai kai?junaid kayi mun ƙanƙanta!Ni bazan iya zaman aure dakai ba,nafison namijin daya mallaki hankalinshi ba shagwa6a66e ba sangartacce irinka...."tun kafin takai ƙarshen maganarta,hawaye suka fara wanke mashi fuskarshi,cikin shessheƙar kuka yace"au haka ma zaki ce jahad?shikenan babu komai,"da sauri junaid ya juya tare da nufar kopar ɗakin nasu gwanin ban tausayi,
  Yana ƙoƙarin kai hannu ya buɗe ƙopar,da gudu jahad ta faɗa bayanshi tare da rungumoshi sosai tana dariya,wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya junaid ya sauke,kwantar da kanta tayi asaman bayanshi,magana ta soma yi mashi anatse"junaid,ko da yake yanzu na canza maka suna,Ka tashi daga junaid ka koma Babyn jahad,Ina fata hakan yayi maka,"
  Tafin hannayenshi ya sanya tare da share hawayenshi,wani irin sanyi ne ya ratsa cikin zuciyarshi,Calmly ya ambaci sunanta"Jahad,Kin amince da aure na?a yadda nake?zaki iya haƙuri dani?ki zauna dani amatsayin Mijin ki uban ƴa'ƴanki kuma"?
  Lumshe idanunta tayi yayin da hancinta ke shinshinar ƙamshin turaren jikinshi,
   "I accept ur love junaid,I love u so much,nayi farin ciki sosai da daddy ya baka aurena,a ashirye nake dana baka kulawar daya dace junaid,"
  Saboda tsabar farin ciki bakin junaid yaƙi rufuwa,hannunta ya ruƙo tare da zagayo da ita,ta dawo gabanshi suna facing ɗin junansu,zuba ma juna ido sukayi na wani lokaci,batare da sun sha Wahala ba,Sun amince ma junansu kowa ya samu abunda zuciyarshi ke muradi,janyota yayi ta faɗa asaman ƙirjinshi,zagayo da hannayenshi yayi ta bayanta,sosai ya rungumeta,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi,lokaci guda suka kamu da tsananin son kasancewa da junansu,
 

*Boss Bature*

  ❤🤍❤
 

"Rafayet!Ka 6ata mun rai!ka ƙuntatamun!Amma kai ko ajikin ka?meyasa zakayi mun haka"?Abbansu ne yayi maganar a yayin da yake tsaye acikin bedroom ɗin Sgr,Idanuwanshi sun cika tab da hawaye,
  "Abba,don me zaka tashi hankalin ka akan auren nan!You know the reason why I married her,Saboda inaso taci gaba dayin aiki a ƙarƙashina,ni ban shirya yin rayuwar aure ba,Babu wannan a tsari na," yana magana huci na fita a bakinshi,saboda tsabar 6acin ran da ya ke ciki,ji yake gaba ɗaya sun takura rayuwarshi,ba don komai ba sai don saboda sun nemi Alfarmar ya taimaka yayi koda hoto ɗaya ne shi da Sehrish don su ajiye na tarihi,
  Gyaɗa kai Abbansu yayi tare da cewa"A haka kakeso kai ayi maka biyayya,bayan Ni ban isa na sanya ka abu kayi mun ba,narasa gane kai wani irin mutunne!ka ce yarinya bazata zauna a part ɗinka ba!kuma ba zaka ɗauki hoto ba atare da ita,nasan meyasa kayi hakan!saboda kada hotonku ya shiga duniya a dinga nunata a matsayin matarka!saboda kai a wurinka wannan ƙasƙancine aganta a matsayin matarka,saboda ka fi ƙarfin ta ko"?
  Yayi maganar ranshi a 6ace,Sgr kuwa ko ajikinshi,yana daga tsaye agaban dressing mirror ɗinshi ya juya ma Abbansu baya,har lokacin bai canza kayan jikinshi ba,babu wanda baizo yayi mashi magana ba akan ya amince da buƙatar mahaifinsu amma yaƙi yarda,hatta Ishaq da Abbas sunyi sunyi har sun gaji sun ƙyale shi,haka Marshal Omar sunyi barambaram dashi,saboda ya 6ata masu rai,
  "Zan tafi na bar maka ɗakin ka,Amma inaso na ƙara tunasar dakai cewa Abusufyan ya baka tsawon wata ɗaya kacal akan ka canza ra'ayinka game da auren yarjejeniyar nan,Zaka iya soke shi in har kana so acikin ƴan kwanakin nan,Amma idan har ka bari wata ɗaya ya wuce baka canza ra'ayin ka ba,duk abunda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa ka kuka da kanka!kuma babu ruwana Na zame hannu na aciki,
  A fusace Sgr ya juyo tare da kallon Abban nasu yace"bazan ta6a canza ra'ayi na ba akan hakan!Idan ma yana tunanin hakan to ya daina!Bana buƙatar wani time nayin tunani!wata uku na cika zan sallame ta ne!
  Abba na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,ta wutsiyar idonshi ya hango mutun atsaye,a ɗan firgice ya juya don yaga wanene,
  Sehrish ce atsaye tana kallonsu,gaba ɗaya jikinta ya gama mutuwa,domin kuwa taji duk abunda suka ce kaf acikin kunnanta,Jikinta har kerma yakeyi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gangarowa akan fuskarta,
  Jin shessheƙar kukanta yasa Sgr Juyawa tare dakai idanunshi wurin da take tsaye a ƙopar ɗakin nashi,tun daga ƙasa har sama yabita da kallo,
  A hankali Abbansu ya ambaci sunanta"Sehrish!"
  Juyawa tayi da gudun gaske tabar ƙopar ɗakin nashi,gaba ɗaya tabar part ɗin nashi,saukkowa tayi downstairs,Su fawan ne tsaitsaye acikin babban falon,koda suka ji shessheƙar kukanta sae hankalinsu ya koma akanta,kowa ya shiga tambayarta lafiya,
  Bata tsaya sauraronsu ba,da gudu ta wuce bedroom ɗinsu,tana shiga ciki ta samu junaid da jahad azaune gefen gadonsu suna shan soyayya,jin shigowarta yasa suka mike tsaye hankali atashe suka shiga tambayarta Lafiya,
  Bata basu amsa ba,kai tsaye ta nufi toilet ta buɗe ƙopar ta shige ciki,da ƙarfi ta datse ƙopar,sannan ta tsugunna ƙasa tana kuka tamkar ranta zai fita,

Gaba ɗaya Jahad da Junaid suka nufi ƙopar,Suna kwankwasawa suna kiran sunanta"Sehrish!Sehrish!dan Allah Rishi ki buɗe mana kopa!
  Turo kopar ɗakin nasu akayi,Abusufyan ne tare da hajiya azeema suka shigo ciki hankalinsu atashe,basu jima da shigowa ba,sai ga Abbansu junaid,dama tunda yaga ta watsa aguje tana kuka ya biyo bayanta,
  A bakin kopar shiga toilet ɗin suka tsaitsaya cirko cirko
   "Dama nasan abunda zai biyo baya kenan!"acewar hajiya azeema,
  Abusufyan yace"Ni bansan waya faɗa mata ba,Naso ace ni na fara sanar da ita,"
  Fuskar Abba a yamutse yace"wlh bansan da ita ba!Yanzun nan fa naganta a ɗakin Rafayet,muna cikin magana dashi akan zancen auren nasu,kawai naji shessheƙar kukanta,ashe duk taji abunda muka ce,"
   Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,musamman Abusufyan har cikin zuciyarshi ya ke jin kukan nata,
   Ƙoƙarin lallashinta suka shiga yi amma ina,Sehrish taƙi sauraron kowa kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita,tana jin muryoyinsu a waje sai faman yi mata magiya sukeyi akan ta buɗe masu ƙopar,
   Junaid duk yabi ya ruɗe sam baisan cewa abun zai ta6a zuciyarta ba har haka,Ita kanta jahad ba ƙaramin tausayin Sehrish taji ba,kowa sai da yasha jinin jikinshi,babban abunda suke ji ma tsoro kada ta illata kanta,
Chapter 71 · 0% Book details