Sashe 165
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Azmee cikakkiyar bafullatana Ce ƴar jihar Gombe state,asali garinsu daga ruga ya fara kafin a hankali ya zama gari,A tsakanin family ɗinsu da family ɗin Salahuddeen basu Shiri,faɗansu tun kaka da kakanni ne,Dama tsakanin family ɗin soja da family ɗin Masu tada ƙayar baya a kasa basa jituwa,faɗan nasu ya fara tun daga kan kakanninsu,Kaka wanda sunan kakansu ne kuma dashi ake yi masu inkiya amatsayin sunan family ɗinsu,Kaka Mugun mutunne wanda ya gagari kowa hakan yasa al'ummar dake kewaye dashi Ke tsananin tsoronshi,Matsafin gaskene a wurinshi duk suka gado wani tsaface tsafacen da suke Yi,Sun kasance wasu irin mutane marasa buri a rayuwarsu,Mugunta kawai sukasa a gaba,Kuma abunda zai baka mamaki Suna da ilumin addinin musulunci,Da yawansu Mahaddatan Alqur'ani ne,Suna Yin iliminne ba don komai ba,Sai don su kawar da idanun mutane daga kansu,Don Tafiyar da rayuwarsu batare da jama'a sun zargesu ba,Kuma suna yin amfani dashi wurin Gudanar da sihirinsu,Dama ance in mutun ya 6ace ya 6ace kenan,Sae wani iko na Ubangiji,Sun tsunduma tsulundum wurin aikata shirka,Zubda jinin al'umma da kuma Yin amfani da Mutane wurin yin tsaface tsafacensu,A zamanin kaka,Salahudeen shi ne Ya kawo ƙarshen tawagarsu ta matsafa,Sunyi nasara akansu wurin ruguza ƙungiyarsu,Tundaga wannan lokacin Suka zama abokanan gaba,Salahuddeen Ya kafa dokar duk inda akaga ɗaya daga cikinsu yana yawo nan take A yanke mashi hukuncin kisa,Suma haka su kaka suka sanarwa jama'arsu da zarar sunga Jinin Salahudeen Su kashe shi,Kisan wulakanci,ya kasance suna farautar junansu,A lokacin da su salahudeen sukayi nasara akansu,Saida suka ƙarar da rabi da kwata na jama'arsu,Kuma a wannan lokacin suka kashe Kaka har lahira,sunyi tunanin sun gama dasu ashe akwai sauran runa akaba,Kaka ya mutu yabar ƴa'ƴanshi,Wanda bayan mutuwarshi,su kuma suka tada ƙungiyar,suka cigaba da aikata munanan laifuka acikin ƙasa,Nan fa su salahudeen suka bazama neman inda suke shirya maƙarƙashiyarsu,Babban danshi ne ya amshi mukamin mahaifinsu kaka,Sunanshi Ubaid Hatsabibine harya fi Ubanshi kaka,Su biyu kaka Ya haifa dashi da ƙaninshi Wanda suke Kira Uba,Dukkansu Mugayene Basu da Imani ko misƙala zarratin,Shan jini ya zama ruwan dare a wannan lokacin,cire sassan jikin ƴa'ƴan mutane abun ba'a magana,Sai dai kawai a tsinci gangar jikin mutun an cire wasu Organs na jikinshi,Abun Ya tashi hankalin Al'umma,Zama baiga su salahudeen ba,Nan fa suka Bazama neman waɗannan hatsabiban guda biyu,Ubaid da Uba,Yadda kasan aljanu haka suke,Baka ta6a ganinsu cikin jama'a,Sai Lokacin Sallah,Ubaid ma Shike jan Sallah a babban masallacin Yankinsu,Babban limaminsu ne,kuma babban Malamin addini ne,Baka ta6a gane halinshi inba gani kayi ya aikata agabanka ba,Fuska biyu ne shi,A fuska musa azuci fir'auna,a yadda mutane suka sanshi,Mutumin kirki ne,Mai tausayi ga son jama'a,Yafi kowa Iya kiran sunan Allah,Idan Ya hau mumbari zaiyi wa'azi sai ka sha mamakin yarda yake kuka Yana kira ga mutane su Koma ga Allah,shu'umin mutunne mai wuyar sha'ani,Ƴa'ƴanshi Biyu Gali shi ne babban ɗanshi,Sai mai bi mashi mace ce Wadda suke kira da Saratu,Ƙanin mahaifinsu Uba shima Ƴa'ƴanshi Biyu,Babbar ƴarshi itace Azmee,Mai bi mata kuma Namiji ne,Wanda suke kira da Sayyad wato Ya sayyadi,
tundaga kan Iyayensu maza har matan Mugayen mutanene,Mushirikai,Tun daga kan kakanninsu ne abun Ya fara,Sai wanda Allah yaso acikin zuri'arsu yake zama na gari,kamar Azmee duk acikin Æ´a'Æ´ansu itace bata É—auko mugun hali ba irin na sauran,Hasalima batasan me iyayensu ke aikatawa ba,Mace ce mai tsananin son addini,Kamilar gaske,Tun tana da shekara goma sha Biyar a duniya ta haddace alqur'ani mai girma,Saratu kuwa Æ´ar wurin wan mahaifinsu jakkace,bata gane komai sai Iya mugunta,
Ana haka Azmee ta fara soyayya da wani bawan Allah,Wanda Ya ta6a taimakonta,akan hanyar dawowarta daga islamiyyar dare,Wasu ƴan iska suka biyota suna ƙoƙarin yi mata fyaɗe,A wannan lokacin wani matashin saurayi ƙakƙarfan gaske ya riƙesu sun kewayeta,Haɗa kawunansu yayi ya dinga bugu sai da yayi haɗa masu jini da majina,Sannan Yace ta sanya hijabinta suje ya rakata gidansu,A ƙopar gidansu yayi sallama da ita,Tunda ta koma gida ta kasa runtsawa saboda tunanin bawan Allahn nan daya taimaketa,tun adaren ranar ta kamu da tsananin sonshi,so bana wasa ba,
Saboda shi kullum sai taje islamiyar dare,tunda ta gane cewa hanyar dawowarshi ce,duk in suka haɗu saiya rakata har gidansu sai ya tsaya yaga shigarta kafin shima ya wuce gidansu,Soyayya mai ƙarfi ce ta shiga tsakaninsu,sam batasan asalinshi ba,Abu ɗaya kawai tasani akanshi yana da kyakkyawar Zuciya,
Tun tana 6oye ma Iyayenta soyayyarta dashi har suka fara lura da yadda Azmee ke yawan ambaton sunanshi Jabeer,ko bacci take yi sai ta dinga sambatu tana ambaton sunanshi,Sa6anin da in tana bacci karatun haddar da aka basu ne zaka ji tana biyawa a bakinta,
Da iyayensu maza suka gane cewa tana son wani bare ba danginsu ba,Sai suka gargaɗeta akan ta rabu dashi,In ba haka ba zata ja mashi ne,su sunfi son suyi mata auran zumunci dama kuma Family ɗin kaka basu auren bare,Yasu yasu ne,ita kuma ta tsani Wanda suke son su haɗa ta dashi,Ɗan wurin Ubaid ne yayan mahaifinta,Wato Ghali mugun mutunne kuma Arne ne shi,Sunan yana musulmi ne ko sallah baya yi,a lokacin taƙi jin maganarsu ta kangare,Aikuwa mahaifinta Uba yasa aka ɗauko mashi Jabeer,A wani kogon dutsi suka Rufe shi,Anan suke gana mashi azaba,duk don su raba ta dashi,kwana biyu da azmee bata sanya shi a idanuwanta,Ko abinci tadaina ci a ƙarshe ciwon zuciya yakusa kamata,ganin dagaske takeson Jabeer kuma zata Iya Kashe kanta akanshi gashi kuma Uba yafi Sonta cikin ƴa'ƴanshi,Sae ya yanke shawarar zai aura mata jabeer,ashe da wata mummunan manufa Ya amince zai aura mata shi,Saboda yayi bincike akanshi ya gano cewa Jinin Maƙiyansu ne,mutanan da suke hari,shi kanshi Jabeer ɗin baisan wanene shi ba,Yawo kawai yake yi acikin garinsu tun yana ƙarami ba'asan danginshi ba,Amma su dayake Shu'umaine da suka bi diddigi saida suka gano ainihin wanene shi............
Cikin lokaci ƙanƙani aka ɗaura auren Azmee da Jabeer,Aranar Hamma Gali kamar Ya haɗiyi zuciya Ya mutu,Ya tsaneshi kamar mutuwarshi,Saboda Shi ke son Azmee,duk da ba son Allah da Annabi yake yi mata ba,Yasha yin kokarin Keta haddinta amma Allah bai bashi iko ba,
Bayan sun É—aura auren Azmee da jabeer,Mahaifinta da kanshi Ya basu kyautar gidan da zasu zauna,Saboda Jabeer baida komai,Talaka ne shi gaba da baya,
A ranar da aka kai Azmee gidan Jabeer wani mummunan abu ya faru,lokacin da kowa yabar gidan Amarya Ya kasance su biyu ne acikin gidan,Bayan sunyi al'wala sun gabatar da sallah,jabeer ya ɗauketa zuwa saman gadonsu,sai da yafara karanta addu'ar saduwa da iyali kafin suka soma biyan buƙatar junansu,Ita dai a wannan lokacin tasan da jabeer suka kwanta,Amma a washe garin Ranar da ta farka cikin mawuyacin hali,Hamma gali ta gani kwance saman gadonta babu kaya ajikinshi,ta fasa wata irin gigitacciyar kara ta soma ƙoƙarin mayar da kayan jikinta,Da gudu ta shige bandaki tana kuka,Bata fito daga toilet ɗin ba har saida taji Muryar Jabeer yana ambaton sunanta,
Sannan ta fito tana kuka,A gefen gadonsu ta same shi zaune,Hawaye wasu na bin wasu akan fuskarshi,Jikinshi sai kerma yake yi,Zuƙunnawa tayi agabanshi tana kuka,
Cikin shessheƙar kuka take tambayar meya faru dasu a daren jiya?ina ya tafi yabarta har Hamma Gali ya shigo cikin ɗakinsu,ta rikice ta rasa gane waye ya kusanceta a cikinsu,A lokacin Jabeer Ya amsa mata da cewa shine ya kusance ta,Bata yarda da kalamanshi ba,Hakan yasa ta soma tambayarshi Idan har dagaske shi ya kusanceta meyasa da ta farka da safe bata ganshi ba,Sai dai Hamma Gali ta gani kwance Saman gadonsu,Sannan meyasa yake kuka?"ganin halin da ta shiga ne yasa bai sanar da ita ainihin abunda ya faru ba,Shi dai A iya saninshi a daren jiya bashi kaɗai ya kusanceta ba,An gusar mashi da hankalinshi,Ya mike a wani irin yanayi yabar ɗakin bai ƙara sanin inda kanshi yake ba,A wannan lokacinne Gali ya shiga ya ƙarasa aikin,shi kanshi kokwanto Yake yi Anya Shine ya kawar da budurcinta ko kuwa Gali ne?kamar yarda tace Gali ta gani kwance saman gadonsu,Allah kaɗai yasan Ƙuncin da jabeer yaji acikin Zuciyarshi,Iya cuta dai an cutar dasu,Hakanan ya daure Ya rungumi matarshi suka ci gaba da rayuwa da ita,
Ana haka,Azmee ta fara ganin sauyi atattare da jabeer,Ya canza mata sosai,kwata kwata babu kwanciyar hankali atare dashi,Ko magana baisan yi,abinci ma baya ci,idan dare Yayi baya bacci sai dai ta farka ta same shi saman darduma Yana sallah yana kuka,Duk in ta tambayeshi meke damunshi sai yace mata,tayi ma mahaifinta magana,Yadaina yi mashi abunda baiso,Ta rasa gane me jabeer ke nufi,ita dai a iya saninta Mahaifinta mutumin kirki ne,babban malamine shi,ko maiyasa jabeer ke ƙorafi akanshi,duk yarda taso ya sanar da ita,ainihin abunda Iyayenta keyi mashi amma Yaƙi sanar da ita,tun tana tambayarshi har ta gaji ta ƙyaleshi,
Wata É—aya da yin auransu,Azmee ta fara laulayin samun ciki,A lokacinne suka shiga ruÉ—ani ita da jabeer,Ga ciki Ya bayyana ajikinta,Amma basu da tabbacin Cikin Shi ne kona Hamma Gali,A wannan time É—in Jabeer Ya bata kyakkyawar kulawa,ya rage nuna damuwarshi,don kawai farin cikinta,
Ranar da Azmee bazata ta6a mantawa ba,Shine ranar da cikinta Ya shiga wata Tara ta fara nakuda,Dayake ƙa'idar family ɗin kaka in mace zata haihu,a gida suke kar6ar haihuwarta,
Cikin É—akin mahaifiyarsu Dije aka shigar da ita saman gadon karfe,Su biyu ne akanta zasu kar6i haihuwarta,Hada matar wan mahaifinsu Ubaid,mahaifiyarsu Gali,Inno bata da mutunci matar nan,Halinta sak Æ´a'Æ´anta suka biyo,Duk acikin gidan suke,Dayake babban gidane na iyali,zumuÉ—inta akan jaririn da za'a haifa ne saboda gali ya sanar da ita cewa É—anshi ne,