← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 212

Sashe 115

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A 6angaren Abusufyan kuwa,lokacin daya shiga yayi arba Da abu a zaune dirshan saman gadon tana faman zazzare idanuwanta,ba ƙaramin daɗi yaji ba,ƙarasa shiga ciki yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,
   Murmushi ya sakar mata tare da miƙa mata hannunshi,zuba ma tafin hannunshi ido tayi tana kallonshi,ta gane fuskarshi a matsayin wanda ya taimaketa,ta fito daga hannun masu fararen kayan nan,
   "Ina ƴa'ƴana suke"?muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
   "Kada ki damu,ƴa'ƴanki suna atare dani zan kaiki wurinsu,kina so ko"?
  ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
  "A ƙarshe dai duk yawace yawacen naki,gashi kin dawo wurina abu,saboda ƙaddararki tana atare dani,kamar yadda kika zama ƙaddarata nima,Ashe da rabon zan sake ganin wannan kyakkyawar fuskartaki"?calmly yayi maganar,tsantsar sonta ne da ƙaunarta ke addabarshi,ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinshi,
  "Abu na,Faɗamun har yanzu kina sona kamar yadda nima nakeson ki,"
  Wuƙi wuƙi tayi mashi da ido tana kallonshi,sam batasan inda zacen nashi ya dosa ba,
   "Kaine ka kashe mun babana ko?kuma ka rabani da ƴa'ƴana ko?Zaka kashe munsu ko"?
girgiza kai Abusufyan yayi tare da cewa"ni bani bane na kashe maki mahaifinki ba abu,Nifa ne Abusufyan É—inki,uban Æ´a'Æ´anki,ba zaki iya tunawa ba ko kaÉ—an,"
  Kallon dayaga tana binshi dashi ne ya tabbatar mashi da cewar a harzuke take,jira take yayi yunƙurin matsawa kusa da ita,Yasha bugu,
  Dariya ya ɗan yi tare dacewa"kwantar da hankalinki,

⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫
*_MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_*

*DOMIN. DAWO DA MARTABAN NONONKI*

Shin ko kinsan nono yanada matukar muhimmanci a wajan mai gida ,? Shin ko kinsan babu abunda namiji yafiso yafi daukar hankalinahi kamar cikar k'irji , ? To nono shine babban Martaban mace a wajan mijinta , don babu namijin da zaiso mace mai yakunannen nono kamar silifas ,wannan yasa Nazo maku da sahihi kuma ingantaccen maganin nono Wanda bashida wata matsala hadin gargajiya ne , acikin lokaci kalilan zakisha mamakin yadda nononki zai ciko sosai Wanda wannan cikowar ita zata bashi damar da zai tashi sosai ta yadda kema zaki Shiga cikin jerin mata masu aji agaban mazajensu ........kedai hanzarta ki nemi mmn Yusuf mai kayan mata yar mutan sokoto zaki samu ingantattun kayan mata masu tafiyar da hankalin maigida.......don neman Karin bayani 07069711327 ......
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Am sorry🙏

Babu abunda zan yi maki,a haka ma daÉ—i nake ji,kina kallona ina kallonki,"murguÉ—a mashi baki tayi tare da kawar da idanuwanta gefe guda,

Wuraren ƙarfe 8 na safe,nurse ɗin dake kula da abu ta ƙaraso,taimaka mata tayi wurin yin wanka a toilet ta gyara mata jikinta,da gashin kanta ko'ina ta wanke mata shi,lokaci guda Abu ta fito fess da ita,ƴar doguwar rigar material ta sanya mata,ita kanta abun sai murna takeyi da aka gyara mata gashin kanta da jikinta,taji daɗin jikinta sosai,Sehrish ce ta shirya masu breakfast gaba dayansu suka hallara a falo suka zauna suna ci,banda abu dake zaune a bedroom ɗinta tare da nurse ɗin,saboda ita kaɗai zata iya da ita,dama sune masu kula dasu a gidan mahaukatan,Sun san duk wasu dabaru da zasu bi wurin tafiyar dasu batare da sunsha wahala ba,a baki ta dinga bata abincin kalacinta tana ci,saboda bata iya ci da hannunta ba,Zubarwa takeyi a ƙasa,kamar ƙaramar yarinya haka take yin wasa da abincin,Bayan nurse ɗin ta kammala kimtsata,Dr yazo ya duba ta,bayan tafiyarshi ne ta samu bacci,

*SGR*

Da gudun gaske motarsu ta shararo izuwa cikin gidan yadda kasan zasu tashi sama,gudu bana wasa ba,Sam ya kasa samun natsuwa acikin zuciyarshi,jikinshi sai tsuma yake yi a ƙagare yake dasu ƙarasa cikin gidan,Armstrong nazaune agefenshi sai faman tausarshi yake yi ganin yadda ya tashi hankalinshi,slowly sojan daya ɗaukkosu from Airport ya rage gudun motar lokacin da ya ƙaraso wurin da zai yi parking ɗinta,saboda tsabar sauri,tun kafin a buɗe mashi ƙopa yasa ƙafarshi azafafe ya harba ƙopar,gudu gudu sauri dauri ya nufi cikin main palour ɗinsu,wayaam babu kowa tsit kake ji,A hanzarce ya haura upstairs direct ya wuce bedroom ɗin junaid,a buɗe ya samu ƙopar ɗakin hannu yasa ya tura tare da shigewa ciki,gabanshi ne ya faɗi rasss ganin babu junaid,saboda yasan cewa junaid bai zuwa ko'ina tunda sanyin safiya,adai irin wannan lokacin zaka same shi kwance saman gadonshi rungume da pillow,
  Muryarshi tamkar zata fasa maƙoshinshi haka ya shiga ƙwala mashi kira"JUNAID!JUNAID!!JUNAID!!!"a gaggauce ya nufi toilet ɗinshi yasa hannu ya tura,nan ma yaga wayaam babu kowa,jiki asanyaye ya fito daga ɗakin junaid ya wuce bedroom ɗin Marshal Omar,tura ƙopar yayi ya shiga daga ciki,babu kowa a falonsa,bedroom ɗinshi ya nufa nan ma babu kowa,tashin hankali!
  Wani irin wahallallan yawu ya haɗiya,fitowa yayi daga part ɗin Omar ya nufo downstairs,gudu gudu sauri sauri haka yake taka staircases ɗin,yana a second to the last step,yaji shigowar message a wayarshi,dakatawa yayi tare da sanya hannu cikin trouser pocket ɗinsa,duba screen ɗin wayar yayi,bayan ya sanya finger ɗinsa ya buɗe saƙon,a tsanake ya soma karantawa
  _Gm Sir,ina fata ban takura maka ba,Marshal yana kwance a gadon asibitin mu yanzu haka_
  Message from doctor Emran,Hankalinshi yayi mugun tashi,a ruɗe ya furta"Omar?kwance a gadon asibiti?
  Da sauri ya nufi hanyar fita daga falon,fitarshi keda wuya,Hosana ta fito daga bedroom ɗinsu,tasha kuka kamar ranta zai fita,saboda an barta ita kaɗai,babu Jahad babu Sehrish babu Junaid,bugu da ƙari kuma babu Ya Omar,tun ɗazu take ta zaryar zuwa ɗakin shi,don taga ko ya dawo amma babu shi,palour ta dawo ta zauna saman sofa,hawaye wasu na bin wasu,fuskar ta jiƙe sharkaf,

"Hosana"!jin muryar Azmee yasa ta miƙe tare da juyowa tana kallonta,sanye take cikin doguwar jallabiya,tayi rolling mayafi akanta,
   Tunkararta hosana tayi cikin shessheƙar kuka tace"A...aunty azmee har yanzu basu dawo ba,ni kaɗai aka bari,gidan duk babu daɗi,"
   Janyota Azmee tayi tare da rungumeta ajikinta,tana ɗan lallashinta,
  "Don't worry ur self,wipe ur tears,in sha Allah nasan nan bada jimawa ba,Ya Omar ɗinki zai dawo cikin gidan nan,Just calm down ur mind,"ta ƙarasa maganar tare da ɗago hosana daga jikinta,
   "Aunty azmee,shiru fa since yesterday night,kuma har kiran layinshi nayi wayarshi a kashe,Ni shikenan kowa ya tafi ya barni,dama ba so na akeyi ba,"tana magana hawaye na sharara akan fuskarta,ɗan murmushi Azmee tayi tare da kai hannunta saman fuskar hosana,taja kumatunta tare da cewa"Haba Babyn Omar,shalelen Abusufyan,kinfi kowa sanin yadda ya Omar ɗinki ke tsananin sonki,Ina da tabbacin cewa duk inda yake a yanzu,tunaninki yake yi,ya hosanata ta ke?me take yi a yanzu?tana kewata kuwa?
   Murmushi hosana ta saki har hankalinta ya ɗan kwanta jin abunda Azmee tace,
  "Aunty azmee kin tabbata cewa ya Omar yana tunani na yanzu haka"?
  ɗaga mata kai azmee tayi alamar eh,kafin tace"Kina aransa mana,yanzu abunda za'ayi,me zai hana mu shiga kitchen atare mu haɗa mashi lafiyayyen breakfast,da zarar ya dawo gida kinga sai ki kai mashi,Zaiji daɗi sosai,"
  Cike da zumuɗi hosana tace"Mu tafi kitchen ɗin,Hada chocolate zamu haɗa mashi,nasan zaiji daɗinshi sosai"
  Ruƙo hannunta Azmee tayi atare suka wuce cikin kitchen,Suna aiki suna fira,gwanin ban sha'awa,

  *SGR HOSPITAL*
Chapter 115 · 0% Book details