← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 212

Sashe 129

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falo ya koma ya zauna saman sofa,jikinshi duk amace,Ringing É—in wayarshi dayaji yasa shi zura hannu cikin aljihu ya É—auko wayar tare da duba sunan mai kiran nashi,Marshal Omar ne,
  Picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnanshi,
  "Omar me kake yi har yanzu bakayi bacci ba"?
  On the other hand Omar yace"Uncle,Ina ka shiga ne anata nemanka,"?
  Nan Abusufyan yake sanar dashi abunda ya faru dashi akan hanyar dawowarshi gidan,
   "Yanzu na dawo gidanma,Na same su cikin koshin lafiya suna ta bacci,"
  A nan Omar ya kwashe duk abunda Abu ta sanar dasu ya faɗa ma Abusufyan,A zabure ya miƙe tsaye jikinshi na rawa,
  "Pls Uncle,ka kwantar da hankalin ka,Tunda ba abunda ya faru dasu,Abunda ya kamata kawai ku dawo gida yau yau ɗin nan zamanku anan baida amfani,dama saboda ciwon Mahaifiyarsu ne Kuma ta samu lafiya,Yakamata ku dawo gida,Hankalinmu sai ya fi kwanciya,"
..jinjina kai kawai Abusufyan keyi sam ya kasa buÉ—e baki yayi magana,Allah kaÉ—ai yasan raÉ—aÉ—in da yake ji acikin Zuciyarshi,dakyar ya iya buÉ—e baki yace"Shikenan Omar,yanzun nan zamu shirya,'
  "Allah ya dawo daku Lafiya,"
"Ameen"daga haka su kayi Sallama,
Komawa Bedroom É—insu yayi wuraren karfe 6 na asuba,da alama ko sallar asuba basu yi ba,sai sharar bacci sukeyi,
  Zagayawa yayi gefen da Sehrish take a kwance ya zauna tare da zuba mata ido yana kallonta,Yayin da hawaye ke sharara akan fuskarshi,tsananin tausayinta ne ya kamashi,baiji daɗin abunda ya faru ba,ta wani 6angaren kuma yaji sanyi aranshi da Allah ya tsare mashi ita,ga kuma Mahaifiyarsu da ta dawo cikin hayyacinta ta silar abunda ya faru,
  Shessheƙar kukan da Abusufyan keyi ne ya farkar da Sehrish,buɗe idanuwanta tayi masu ɗauke da bacci,Suna haɗa ido dashi tayi hanzarin mikewa daga zaune tana ambaton sunanshi"Daddy!yaushe ka dawo?meya faru kake kuka,"
  "Daughter,Am sorry!am really sorry,duk laifina ne dana tafi nabarki ke kaɗai acikin gidan,"
  "Daddy,bangane akan me kake magana ba?nifa babu abunda ya faru dani,"tayi hakan ne don ta 6oye mashi gudun karya sanya damuwa aranshi,batasan cewa ya riga daya ji ba,
  "Omar ya sanar dani duk abunda ya faru dangane da zuwan sayyadi cikin gidan nan,"
   Mamaki ta shiga yi taya akai Ya Omar yasan abunda ya faru dasu?can kuma ta tuna da lokacin da Oummansu ta nemi yin magana da Abusufyan may be a wurinta yaji komai,
  "Dan Allah Daddy,kada kasa damuwa aran ka tunda ba abunda ya faru dani lafiyata kalau,Sai ma wani abun farin ciki da ya faru,Oummanmu ta dawo cikin hayyacinta,Sanadin zuwan ya sayyadi,Kuma ta lalata mashi idanuwanshi,karkaso kaga yarda ya dinga kururuwa yana ihu," Tayi maganar tana kwatanta mashi irin yarda Ya sayyadi yayi ihun,
  Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba,dama tayi hakan ne don ta sanyaya mashi ranshi,
  ɗaure fuskarta ta ɗan yi ashagwa6e tace"Daddy banga kana farin ciki da abunda na sanar dakai ba"?
  Daƙyar ya ƙaƙaro murmushi akan fuskarshi yace"Ina farin ciki mana,Naji daɗi sosai,kawai dai nadamu ne akan Halin da kika tsinci kanki a lokacin da bana nan,"
  ɗaure fuskarta tayi"Why Daddy,bana ce ka kwantar da hankalin ka ba?komai ya wuce,Yanzu lokacin farin ciki ne,Ga ka, Ga Ni,ga Oummanmu kuma,Bari na tashe ta daga bacci kuyi magana,"ta ƙarasa maganar tare da sanya hannu tana ɗan bubbuga kafadar Oummansu,
  Murmushi kawai Abusufyan ke saki yana kallonta,
  "Oumma!oumma!ki tashi ga Daddynmu nan ya dawo,"
  Kasa tashi abu tayi saboda kunyar Abusufyan da take ji,Ashe tun shigowarshi dakin ta farka,tana jinsu suna magana amma tayi likimo,

"Nasan cewa idonki biyu abu,bakison gani na ko"?Abusufyan ne yayi maganar ayayin da yake leƙen fuskarta,pillow ta sanya tare da rufe fuskarta dashi,
  Murmushi suka saki atare shi da Sehrish,
  "Inason magana dake,ki tashi daga zaune,"cike da jin kunyarshi ta cire pillow ɗin tare da tashi daga zaune suna fuskantar juna,Ta kasa ɗagowa su haɗa ido da Abusufyan,kunyarshi ta rufe ta,kamar tayi rami ta binne kanta,
     
   "ZAINAB"ya ambaci sunanta da wata irin kasalalliyar murya,
   daƙyar ta iya motsa lips ɗinta wurin amsa mashi,
   "Na'am,"
Murmushi ya saki tare da É—aga hannunshi sama yana furta"Alhamdulillah!Alhamdulillah,Almost 3 times yana ambaton hakan,Cike da tsantsar farin ciki,
   Sai faman sauke ajiyar Zuciya take yi,matsawa yayi kusa da ita tare da sanya hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta yana ƙare mata kallo,
  Siraran hawaye ne suka soma Zarya akan fuskarta masu ɗumin gaske,
   "Hawayen menene wannan"?
Cikin Shessheƙar kuka tace"Kayi haƙuri,ka yafe mun,Na gane kuskuren dana yi,Naji jiki Abusufyan,nayi dana sanin butulce maka da nayi,Haƙƙinka ne yake ta bibiyar rayuwata,Ni ce silar duk wani abu daya faru a rayuwarmu nida ƴa'ƴana...."ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka,Hannu tasa ta zame hannayenshi daga saman fuskarta,kafin ta Sauko daga saman gadon ta zuƙunna saman guiwowinta agabanshi,tana ci gaba da yin kukan....
   "Tun da nake arayuwata,ban ta6a ganin mutun mai kyakkyawar Zuciya irin taka ba,duk irin girman laifin dana aikata maka,hakan baisa ka guje ni ba,Sai ma bibiyar rayuwata daka ci gaba dayi duk don kaga Ka taimake ni,Amma na kasa gane hakan,saboda tsabar baƙin kishin da nake dashi na yanke maka hukunci batare dana tsananta bincike ba......"
     Ruƙo hannunta Abusufyan yayi tare da ɗago da fuskarta yace"pls bana son muna tuna abunda ya wuce,Ni komai ya wuce a wurina Abu,tabbas naji zafin abunda kika yi mun Amma wlh banta6a ruƙe ki araina ba,kullum burina inga na taimaki rayuwarki saboda baki da kowa abu,Allah kaɗai gare ki,Sai kuma Ni dana haɗa zuri'a dake,Ba zanso rayuwarki ta wulaƙanta ba,ko ba don haka ba Ke amana ce agare Ni,"

Zuba masu ido Sehrish tayi tana kallonsu fuskarta ɗauke da Murmushi,tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,
  "Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin bayyana maka irin farin cikin da nake ciki ba,Abusufyan Allah kadai ne zai iya biyanka,",addu'oi ta shiga yi mashi yana amsa mata da ameen,Kafin daga bisani Ya nuna mata gefenshi ta miƙe ta zauna,
   "nasan kinyi kewar ƴa'ƴanki sosai,In sha Allah Yau ɗinnan zamu wuce Abuja,Zaki ga Hosana da Jahad,da kuma sauran Family ɗinmu,"

Fira sosai suka shiga yi,Anan ta samu labarin irin wuyar dasu sehrish suka sha bayan 6acewarta,da kuma yadda akai suka haÉ—u da dangin mahaifinsu da shi kanshi Abusufyan din har kawo yanzu da suke bata labarin,Abu tasha kuka sosai tsananin tausayinsu ne yakamata,ta wani 6angaren kuma tayi farin ciki sosai Da Allah ya nuna mata wannan ranar da ranta kuma da Lafiyarta,

Batare da 6ata lokaci ba Suka kammala shirinsu na komawa Abuja,A jere Motocinsu suka fita daga cikin gidan,Motar Abusufyan na atsakiyan motocin security É—in gidan,Kaitsaye hotoro suka wuce domin yin sallama dasu Maman Sadeeq,
  Sunsha kuka sosai,musamman Maman sadeeq da Abu,rungume juna suka yi kamar karsu rabu,babu wanda bai zubda ƙwalla ba acikinsu,kafin su tafi sai da Abusufyan ya damƙa ma Malam Nura key din gidansu dake a nasarawa G.r.a,Ya mallaka masu shi duk da haka sai da ya ƙara masu da zunzurutun kuɗi har miliyan 10,yace ya dauki miliyan bakwai yaba Baban Umari cikon miliyan ukkun,don bai manta da gudunmawar da akace ya bada ba wurin neman abu,anan take ya rubuta ma Malam Nura cheque,Duk da haka bai ƙyalesu ba,Bayan haka kuma yayi masu albishir ɗin cewa tare dasu Za'ayi aikin hajjin bana,Wayyo Allah saboda tsabar farin ciki,kasa bude baki su kayi don suyi mashi godiya,Kuka kawai sukeyi,abun da basu ta6a tsammanin zasu samu a rayuwarsu ba,Yau gashi silar taimakon da sukayi Allah ya ɗaukaka rayuwarsu,
  Sehrish kuwa Dama tayi alƙawarin zata taimaka ma Sadeeq ya gyara keken shi,maimakon kuɗin gyaran keken sai Gashi ya samu kyautar danƙareriyar Motar Abusufyan gaba daya ya mallaka mashi ita,kusan zaucewa Sadeeq yayi saboda tsabar farin ciki,sun jima a wurinsu suna bankwana,kafin daga bisani Sukayi masu Sallama,Anyi rabuwar mutunci sai kuma in Allah ya haɗasu wurin shagalin bikin Ƴa'ƴan abu,

ÆŠaya daga cikin motocin security É—insu suka shiga Gidan baya Abu da Sehrish,Abusufyan yana agaban motar,A jere Motocin suka kama hanyar fita daga unguwar,

Su Maman Sadeeq na tsaye a kopar gida ita da Mlm nura,tare da sadeeq sai bye bye suke yi masu da hannu,yayin da hawaye ke zuba a fuskar kowannansu,

Sehrish sai lekensu takeyi ta glass É—in motar dake a zuge,har sai da suka 6ace ma ganinta tukunna ta hakuri da leken,Rayuwa kenan in akayi hakuri Komai mai wuce ne,

Hannu abu tasa tare da janyo Sehrish ta rungumota ajikinta,a lokacin har motocin sun haura saman titi,Sun miƙi hanyar barin garin da matsakaicin gudu,
Da zarar ta ɗago da idonta ta kalli madubin motar,Fuskar Abusufyan take gani yana sakar mata murmushi,Sunnar da kanta ƙasa tayi tana ƴar dariya,
Sehrish batasan wainar da suke toyawa ba,domin kuwa ta lumshe idanuwanta da alama bacci ya fara É—aukarta,
Sake ɗagowa abu tayi tare da kallon Mirror ɗin,suka ƙara haɗa ido dashi,
Kashe mata ido É—aya Abusufyan yayi,batasan lokacin da ta fashe da dariya ba cike da tsantsar farin ciki,
Shima dariyar yayi,kusan minti 30 bata ƙara dagowa sun haɗa ido ba,saboda baccin da yayi awon gaba da ita,
Wasa wasa shima bacci ya É—auke shi,dama duk basu samu isasshen Bacci ba a adaren Jiya,

Wuraren ƙarfe 2 na rana suka ƙaraso Abuja,Slowly motocinsu suka shararo izuwa cikin gidan,tun da Hosana tajiyo sautin shigowar motoci da gudun gaske ta fito daga cikin falon don taga su wanene,
Chapter 129 · 0% Book details