← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 212

Sashe 70

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   "Wow masha Allah,Tabarakallahu Ahsanul khaliƙin!"hajiya azeema ce ta ambaci hakan,jahad kuwa hannunta na ɗauke da Wayar sehrish ta shiga Camera sae video take yi mata,ita ma hosana hannunta na ruqe da wayar hajiya azeema I phone 13,Sun taru sai video suke ɗaukar sehrish,
Ƙoƙarin juyowa tayi da sauri hajiya azeema ta dakatar da ita"Kada ki juyo yanzu,bari na aza maki net ɗin nan asaman kanki zai ƙara maki kyau sosai,Bayan ta kammala sanya mata mayafin sannan tace"Sannu a hankali zaki juyo ba da sauri ba," a natse Sehrish ta soma juyowa a wani slow,Hosana na kallonta ta cikin camera sai faman sakin Murmushi take yi,
  Hajiya azeema tace"Yawwa My photographers ku ɗaukarmun ita da kyau,ta fito sosai acikin Video ɗin,yadda zanji daɗin ɗaurawa a status ɗina,
  Ƙarasa juyowa sehrish tayi,fuskar nan ɗauke da ƙayataccen Murmushi,ita kanta tasan tayi kyau over,Zuciyarta cike fal da farin ciki,kamar wadda akayima albishir da gidan Aljanna,dama hannunta akwai zanen jan lallen da akayi masu na walima,yana nan raɗau a hannunta bai goge ba,ta ruƙe yar purse ɗinta a hannunta,
  Tun daga ƙasa Hosana ta fara ɗaukarta ta cikin camera ɗin har izuwa saman fuskarta,
   "Turn ur back,yadda zasu ji daɗin ɗaukarki da kyau,"acewar Azeema,
  Juyawa sehrish tayi a hankali suka ɗauki bayan,sannan ta sake juyowa,Jahad sae faman zuzuta ta take yi tana cewa"wlh yadda kasan Amaryar Gaske,Sehrish kinyi kyau sosai kamar dollars"
  Dariya hajiya azeema tayi jin abunda jahad tace,
  tace"Wato kuɗi sune suka fi komai kyau kenan?shiyasa ake kwantanta su da mutumin da yayi kyau ko"?tayi maganar tana kallon Jahad dariya sukayi gaba ɗayansu,
  Suna cikin rahar nan wayar hajiya azeema tayi ringing,sunan Abba ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,da sauri hosana ta miƙa mata wayar,hannu tasa ta kar6i wayar bayan ta ɗaga kiran ta kara wayar a kunnanta,
   Tun kafin tayi sallama taji muryar abba yace"Azeema kina ina ne"?
   "Ina a ɗakinsu sehrish ne yanzu haka,na kammala yi mata kwalliya ne harma ta sanya rigar amaren...."
  Katse ta yayi da cewa"Karki kuskura,kice zaki kai yarinyar nan ɗakin Rafayet!". 
   Hankalinta atashe tace"Saboda me Yaya hossein"?tun daga kan muryar Abba ta tabbatar da cewar yana cikin matsananciyar damuwa,
   "Tun farko sai da na faɗa maki cewar wannan auren na sirri ne,kuma na faɗa maki dalilin dayasa ya aureta ba don yana sonta ba fa ce don tayi mashi aiki,.." a ɗan ruɗe hajiya azeema ta dago tana kallon Sehrish,jikinta ne yayi wani irin sanyi har cikin zuciyarta taji babu daɗi,
  Da sauri tace masu"Ina zuwa" tana faɗin hakan ta fuce daga ɗakin,a nan cikin corridor din ta tsaya,Muryarta asanyaye tace"Yanzu yaya kana nufin cewa yarinyar nan bazata tare aɗakin Mijinta ba!"
   "Azeema so nake ki fahimce ni,!ki natsu ki saurare ni,!rafayet wani irin bauɗaɗɗan mutunne mai wuyar sha'ani,Wlh bazai bari yarinyar nan ta zauna a part ɗinsa ba,da sunan amaryarshi,Yanzu haka zancen da nake yi maki,Ya hana uban kowa ya ɗauki hoto tare dashi!gaba ɗaya babu wanda ranshi bai 6aci ba saboda rafayet!"
   Muryar hajiya azeema tamkar zatayi kuka tace"Amma ba'ayi ma yarinyar nan adalci ba!Meyasa tun farko ba'a shawarce ta ba?kafin a ɗaura mata aure dashi!yakamata ace tasan da zancen auren da za'ayi mata da kuma dalilin yin auren!me kuke tunanin zai faru idan har yarinyar nan taji cewar an aurar da ita ne don tayi aiki kawai a ƙarkashinsa"?
  Shiru Abba yayi batare daya ce mata komai ba,
  Jinjina kai kawai hajiya azeema tayi tare da cewa "Shikenan kawai,Zansa ta cire rigar dana sanya mata,Amma dae banji daɗi ba,Kuma in sha Allah rafayet sai yayi danasanin yin hakan da yayi!"tana kai ƙarshen maganarta,tayi rejecting kiran,Tuni idanunta sun cicciko da kwalla,Ranta yayi mugun 6aci,
    "Aunty azeema!"hosana ce ta ambaci sunanta,da sauri takai idanunta ƙopar ɗakin nasu,tsaye take fuskar nan ɗauke da murmushi tace"Munata jiranki,Kince zamu je kai amarya,"
   "Kada ki damu hosana,Yanzu zan shigo ciki,"
  Amsa mata tayi da toh,sannan ta koma cikin ɗakin,Kusan 15 mins hajiya azeema tana tsaye batare da ta motsa ba,sae da zuciyarta ta lafa,sannan ta wuce cikin ɗakin nasu,
    A tsaitsaye ta samesu suna jiran dawowarta,gaba ɗaya duk sai taji ba daɗi,Musamman yadda taga Sehrish sae faman sakin Murmushi takeyi,tsananin tausayinta ne ya kamata,Shin wata irin rayuwa yarinyar zatayi a ƙarƙashin Sgr?mutumin da baisan Soyayya ba,Tabbas zata sha wahala a hannunshi,Domin kuwa zai mayar da ita tamkar baiwarshi ne,su yaya hossein sunyi kuskuren aura mashi ita,da sunan tayi mashi aiki,wannan tamkar ƙasƙanci ne,kuma yarinyar bazata ji daɗi ba,ranta zai 6aci sosai idan ta gano cewar aure akayi mata,auren ma na sirri,tamkar wata mara gata,babu walima babu wani party,babu taron mutane,babu wedding pics,dole abun ya ta6a Zuciyarta,na biyu da sa hannun iyayenta suka aura mata shi da sunan tayi aiki a ƙarƙashinsa ba matsayin matarshi ba,tabbas an gama cutar da ita,

    Mamaki abun ya ba su Jahad ganin hajiya azeema tayi tsaye agabansu,kuma ta ƙurawa sehrish ido tana kallonta,Kamar mai nazarin wani abu,
   Jahad ce ta ambaci sunanta"Aunty azeema,"
  Firgita tayi lokaci guda ta ɗan saki murmushin yaƙe tare da cewa"Am sorry fa,wlh na shafa'a ne,Yanzu mai ya rage mana muyi"?
   Hosana tace"Kai amarya mana,ki faɗa mana a ina zamu kai rishi ɗin,"
   Hajiya azeema tace"Ae wannan shirin drama ne!ba dagaske ba,A nan zakuyi wasan ga wayata ma idan kuna buƙatar yin hotuna,Ni yanzu inaso zan wuce ciki ne,"
  Da sauri Hosana ta kar6i wayar daga hannun hajiya azeeman,sallama tayi masu da sauri ta fuce daga cikin ɗakin,
  "Kamar yanayinta ya canza ko"?jahad ce tayi maganar tana kallon sehrish,
   "Nima na lura da hakan,Hosana wanene ya kira ta a waya nasan kinga sunan daya bayyana akan screen ɗin,Zai iya yiwuwa wani abu aka sanar da ita wanda ya 6ata mata rai,"acewar sehrish,
   Hosana tace"Ni dai naga Sunan Yaya hossein,amma bansan wanene ba,"
  "Sunan Abbansu Junaid ne,Allah yasa dae ba wani abu ya faru ba,"sehrish tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,
  "Kodai naje najiyo mana abunda ke faruwa cikin gidan"?Hosanar tayi tambayar tana kallonsu,
  Jahad tace"A'a,babu ruwanki,tunda ba kiran mu akayi ba,"

Cigaba da É—aukar hotuna sukayi acikin É—akin,Shigowa junaid yayi fuskar nan tashi É—auke da murmushi,Suna ganinshi suka haÉ—a baki wurin cewa"Baby Junaid!"
  Ɗaure fuskarshi yayi tare da ɗan turo bakinshi ashagwa6e yace"Ni ku daina Kirana da sunan baby,In ba haka ba,ran kowa zai 6aci a wurin nan,"ya ƙarasa maganar tare da aza idanunshi kan Sehrish dake tsaye tasha Kwalliya abunta,sakin baki yayi galala yana kallonta,a ruɗe ya ambaci sunanta"Reesh,"
  Murmushi Sehrish ta sakar mashi,tare da yi mashi fari da ido,sannan tace"Na'am,Junaid ya kaga wankan nawa,"?
   daƙyar ya iya cewa"reesh,yanzu kina sane aka ɗaura maki aure da babban yayan mu bayan kinsan da cewar Ina sonki"?
  Gabanta ne ya faɗi rassss!!Ba ita ba hatta su Jahad da hosana a ruɗe suka haɗa baki wurin cewa"Aure kuma,da Babban yayan mu!"
  Shi kanshi junaid ɗin sae da gabanshi ya faɗi,tunani ya shiga yi anya Sehrish tasan da auren kuwa?Yanayin yadda ya ga ta razana ya tabbatar mashi da cewar batasan da zancen auren ba!acikin ranshi yace"meke faruwa ne?Mommy batasan da auren babban yaya ba,kuma itama rishi dasu jahad basu san da auren ba!Abba ya 6oye masu kenan!aikuwa saina tona masu asiri kowa yaji,dama ya 6ata mun raina yau,duk irin amanar dake tsakanina da Abba ya rasa dame zai sakamun sai da wannan,"
  "Junaid dan Allah kayi mana bayani dalla dalla yadda zamu fahimta!"acewar jahad,
   Kallon fuskar sehrish yayi ganin ta zuba mashi ido tana kallonshi,kalmar daya furta masu ce take ta maimaitawa acikin zuciyarta
   "nidai baza aji mutuwar sarki abakina ba,Abba yace kar na faɗama kowa cewa an ɗaura aurensu,"yayi maganar tare da sanya hannu ya toshe bakinshi,
  Hankali atashe suka shiga kallon juna atsakaninsu,
  "Don Allah junaid ka faɗamun auren wa aka ɗaura"? muryarta tamkar zata yi kuka tayi maganar,
   "Sehrish kiyi haƙuri bazan iya sanar dake ba,Amma idan kina son samun ƙarin bayani,kije wurin Uncle ki tambayeshi,
Chapter 70 · 0% Book details