← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 212

Sashe 109

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Arab gown ce ajikinta,pink colour abunka ga fara tass,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin nasu,ta miƙi hanya kamar zata fita daga corridor ɗin,Sai da ta bada tazara sosai,Sannan ta dannama numbar kira,tana fara ringing aka ɗaga,
  Tun kafin tayi sallama,taji muryar hayaam tace"ABRAH"!tun daga kan yadda ta kira sunanta yasa gabanta ya faɗi rass,
   "Aunty hayaam kece"?
Bata amsa mata ba,sae ma fashewa da tayi da kuka mai sautin gaske,hakan ya ƙara ɗagawa Abra hankali,a ruɗe ta shiga faɗin"Aunty hayaam meya faru dake ne?meyasa kike kuka?dan Allah kiyi mun bayani,"

On the other hand,Hayaam ta miƙa ma Amani wayar tare da cewa"kiyi mata bayani,"
  Gyaran murya Amani tayi tare da ambaton sunan Abra,
  Duk sunbi sun ɗaga mata hankali,muryarta har kerma takeyi wurin cewa"Dan Allah kuyi mun bayani,kun sanyani acikin duhu,"
  "Abrah!ki natsu ki saurareni,"jinjina kai abra ta shiga yi tana fadin"ina sauraranki Aunty Amani,meya faru ne naji Aunty hayaam tana kuka,
  Amani bata 6oye mata komai ba,game da abunda ya faru da hayaam da kuma guduwar Aunty babba daga asibitin,da kuma wasikar da ta bar mata,wasu irin zafafan hawaye ne suka soma gangarowa akan fuskar Abra,hankalinta a matuƙar tashe tace"Nashiga uku!kenan nima wata rana idan ƙaddara ta same ni,Aunty laila zata iya guduwa ta barni?
  Amani tace"ƙwarai kuwa!saboda bata da Imani kuma bata da tausayi,karki so kiga yadda na samu hayaam a asibitin nan a wulakance,kamar wadda tayi hatsarin mota amma a haka laila tabarta,saboda bata da amfanin da zata yi mata,To kema muddin kika kuskura kika bita wurin bokan nan rayuwarki ta faɗa halaka,Kuma wlh da zarar amfaninki ya ƙare a wurinta shikenan kin zama Waste product!Zata yi watsi dake ne,"jin wannan maganar yasa Abra ta fashe da matsanancin kuka,wani irin tsoro ne ya kamata,don Aunty babba ta zama abun tsoro a wurinta,ta girgiza da jin rashin imaninta,
Da gangan Amani ta dinga tunzura abra don ta tsoratar da ita akan karta goyi bayan Aunty babba suje wurin bokannan,
  "Abra!ina ƙara jan kunnanki,karki kuskura ki bi ta,Kiji tsoron Allah,ki tuna cewa wata rana zaki koma gare shi,kada kiyi silar da za'a cutar da rayuwar wasu,Aunty laila bata da Imani,tanaso ta jefa rayuwarku cikin haɗari ne,kuma tana yin amfani da ku ne don ta cimma burinta,kuma da zarar amfanin ku ya ƙare a wurinta,zata yi watsi daku ne,ta kama gabanta,Ga hayaam nan dai yanzu ta gane kuskuren da tayi,tana mai dana sanin abunda ta aikata,"
  Amani nakai ƙarshen maganarta,ta miƙa ma hayaam wayan"kiyi mata magana,"
  Kar6ar wayar hayaam tayi tare da karata a kunnanta,Kukan da Abra keyi har cikin zuciyarta,dama tasan dole taji raɗaɗin acikin zuciyarta,ɗan uwa ba wasa ba,
  Cikin Sanyin murya tace"Abra,baki ga yadda na koma ba,bani da wani abu daya rage na ƴa mace a jikina,komai ya lalace,Yanzu ma bana jin kaina amatsayin mace,"
  Wani sabon kukan Abra ta ƙara fashewa dashi,cikin shessheƙa tace"Aunty hayaam wlh bazan bi ta ba,sai dai taje ita kaɗai,Ashe ba son mu take yi ba,bata ɗauke mu abakin komai ba,Amfani kawai take yi damu don ta cimma burinta,Ni wlh bansani ba Aunty hayaam,harfa tambayarta nayi ina kike amma tace mun wai batasan inda kika tafi ba,kinacan kina yawon gantali,Ashe kina gadon asibiti rai hannun Allah,yanzu haka fa da nake yin maganar nan,tun jiya muka iso Enugu da ita,Yanzu haka ma shirin zuwa wurin bokan muke yi,
  Hayaam tace"Abra,ki natsu ki saurare ni,kada ki bari tasan da shirinki naƙin binta wurin boka,saboda bata da imani tana iya kasheki,in kika 6ata mata rai,Abunda nake so dake shi ne,Duk wani kuɗi dake a wurinta,ki tattarasu gaba ɗaya ki sanyo su acikin jakarki,muguwar rabi da kwata na kuɗin dake a hannunta nawa ne,amma saboda tsabar rashin Imani ta kwashe hada nawa ta gudu dasu,"
  Jinjina kai Abra tayi yayin da take share hawayenta,
  "Aunty hayaam,yanzu tana acikin toilet,bari nayi sauri na tattara kayana,in biyo mota in dawo nan,"
  Hayaam tace"Yawwa,kiyi sauri kada fa kiyi kuskuren da zai sa ta gane cewa guduwa zakiyi ki barta,". 
  "In sha Allah bazan bari ba,"
.daga haka su kayi sallama,

Ajiyar zuciya hayaam ta sauke tare da kallon Amani dake zaune gefen gadon,tace"Har hankalina ya kwanta,So nake Aunty laila ta É—anÉ—ani kuÉ—arta,taji irin raÉ—aÉ—in dana ji acikin zuciyata,
  Murmushi Amani tasaki,tare da cewa"Nafi ki jin daɗi Hayaam,A shirye nake dana taimaka muku wurin ganin kun gyara rayuwarku,"acikin ranta kuma tace"Ita kuma waccen bijimar,Sai nasa ta tsani kanta,duk wani makusancinta saina kwace shi ya dawo a ƙarkashin ikona,So nake ta gane kuskuran da ta aikata arayuwarta,"

A 6angaren abra kuwa,tun bayan da suka kammala yin wayar,jiki na rawa ta koma Room ɗin nasu,A hankali ta tura ƙopar ta fara leƙawa ciki,don taga ko ta fito daga wankan,Ajiyar zuciya ta sauke,ganin bata fito ba,da sauri ta faɗa cikin ɗakin,Jikinta sai kerma yake yi,asaman bedside drawer,ta samu jakar Aunty babba,hannu tasa ta ɗauki handbag ɗin,tare da zagayawa ta Other side ɗin ta ɗauko ƴar purse ɗinta,saboda tsabar sauri jin Aunty babba na motsi kamar zata fito daga cikin toilet ɗin,aikuwa a gigice ta buɗe ƙopar ɗakin ta fuce,da gudun gaske,mutanen dake kai komo a cikin hotel ɗin sai kallonta sukaye,wasu kallon burgewa suke yi mata saboda rigar jikinta,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,gashi bata sanya mayafi akanta ba,ƙafafunta ko takalma babu,

Hankalinta bai kwanta ba,har sai da ta fito daga cikin hotel ɗin,gudu gudu sauri sauri ta miƙi hanya tana tafiya tana waiwayon bayanta kada ace Aunty laila ta biyota,Masu motoci sai parking sukeyi agabanta suna yi mata tayin shiga motarsu,amma taƙi sauraron kowa saboda gudun kada wani ya cutar da rayuwarta,kamar yadda aka yiwa Hayaam,baiwar Allah ta tsorata sosai,gashi babu wanda ta sani a garin,haka bata san ko ina ba,ba ƙaramin galabaita tayi ba,

    *Koya Abra zata ƙare?Shin ina Aunty Babba dake a cikin toilet tana wanka?Batasan an yashe ta ba*

*Boss Bature*

   ❤🤍❤

Kano state

Wuraren ƙarfe 6 na marece,Slowly motocin Sgr suka shiga cikin unguwar batare da jiniya ba,saboda patient ɗinsu da suka ɗaukko,a back seat na motar Abusufyan suka kwantar da ita,Abusufyan shi ne ke driving ɗin motar,fuskarnan tashi a washe,kamar wanda aka yima Albishiri da Gidan Aljanna,Sehrish na agefenshi sae faman sakin murmushi take yi tana waiwayawa,bakinta yaƙi rufuwa,a ƙagare take dasu ƙarasa gidan,ko ta samu ta kira sauran ƴan uwa ta sanar dasu cewa An samo Oummansu,

Bayan motar su Abusufyan Motar dake É—auke da Baban Sadeeq ce,tare da Maman Sadeeq,É—aya daga cikin motocin Sgr ne,wanda wani soja ke driving É—insu,
Mamaki yaƙi barinsu,musamman Maman sadeeq,abun ya ɗaure mata kai har tagaza rufe bakinta,
Kasa kasa tace "Baban Sadeeq kaga wani iko na Ubangiji"?
  Murmushi Baban sadeeq yayi tare da kallonta yace"dama ae naji ma ina sanar dake cewa,Allah yana tare dasu,kuma shi zai kula da abunshi,Yau nasan kin shaida maganata,"
Murmushi ta saki tunawa da wannan kalami na Baban sadeeq,a duk lokacin da ta rufe shi da faɗa kan cewa sunƙi ɗaukar mataki akan Ya sayyadi,yana ta cutar da bayin Allah,an zuba mashi,sai babban sadeeq yace mata"Bazan iya tunkarar mutumin nan ba,Mutumin da kana ja mashi ayar ƙur'ani yana fassara maka?taya zan iya tunkararshi?in dai akan yara ne Allah yana tare dasu,Kuma shi zai kula da abunshi,"
  "Amma gaskiya Baban sadeeq,nayi matuƙar mamaki,har yanzu fa ji nake yi kamar mafarki nakeyi wlh,wai yanzu waɗannan danginsu rishi ne?bayin Allah,wlh na tayasu murna sosai,"
  Baban sadeeq yace"Ni ji nake kamar nafi kowa farin cikin wannan ranar wlh,Alƙawarin dana ɗaukarwa kaina,Ya cika yau ga abu ga Ƴa'ƴanta,ga kuma danginsu,Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala,"

A bayan motarsu dasu Baban sadeeq suka,Motar dake biye da tasu,nurse ce É—aya tare da Dr,An zo dasu ne don a nuna masu gidan,Saboda sune zasu ci gaba da zuwa suna duba lafiyarta,security guards sun sanya motocinsu a tsakiya,gaba da baya duk motocin Soldiers É—inne,Sgr baisamu ya biyo bayansu ba,Sun wuce Hotel shi da Armstrong,

A parking space suka tsayar da motocin nasu,fitowa Abusufyan yayi tare da zagayawa ya buÉ—e gidan baya,Hannu yasa ya kinkimo abu,tare da azata asaman kafaÉ—arshi,gaba É—aya suka kama hanyar shiga cikin falon gidan,tun kafin su shiga ciki sehrish ta fara ganin canji alamun kamar anyi gyara acikin gidan,shi kanshi Abusufyan yayi noticing hakan,

Main palour ɗin suka shiga,Nan fa suka sha mamakin ganin an canza Sofa set ɗin falon izuwa sababbi,Hatta ƙasan falon wani jigunannan carpet ne aka shimfiɗa ya mamaye ko'ina,ga wani irin sanyi na A.c dake ratsa ko'ina cikinshi,Abun ya ɗaure masu kai,
   "Abba kodai munyi mistake ne"?Sehrish ce tayi maganar,
  "Ba kuskure mu kayi ba sehrish,ni kaina nayi mamaki,daga gani aikin Sgr ne,Shi ya sanya aka gyara gidan,dama ina ta fargabar awani wuri zamu aje Oummanku"yayi maganar,a yayin da suke tunkarar Bedroom ɗin abu,ciki ya shiga da ita,nan ma an sanya A.c ɗin,daga gani duka gidan aka gyara,hatta furniture ɗin duk an canzasu,Naira tayi aiki daga safe zuwa maraice gidan ya koma tamkar na amarya,amaryar ma yar masu fada aji,a hankali ya kwantar da ita saman gadon,wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana ƙare mata kallo cikin zuciyarshi kam hamdala yake tayi,
  Sehrish dake tsaye tana kallon fuskar Oumman tasu,sae faman sakin murmushi takeyi,ji take kamar ta faɗa jikinta ta rungumeta sosai,'
  Sehrish ki zauna gefenta,bari na fita wurinsu Baban sadeeq,mun barsu a palour,"yayi maganar tare da miƙewa ya fuce daga ɗakin,
  Wuri Sehrish ta samu daga gefen gadon ta zauna,tana kallonta,
  "Allah ya baki lafiya Oummanmu,Nasan zakiyi farin ciki sosai,idan kika ga yadda ƴan ukunki suka koma,Ashe da rabon mukai wannan lokacin araye,mu dukkanmu"?hawaye ne suka soma saukowa daga saman fuskarta,kwantar da kanta tayi daga gefen Oumman,ta sanya hannunta tare da ruƙo nata,

Lokacin da Abusufyan ya koma palourn,A zaune ya samu Malam Nura tare da Maman sadeeq saman 3 seater,Nurse É—in kuwa tana zaune saman 2 seater ita da Doctor,
Chapter 109 · 0% Book details