← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 212

Sashe 108

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sis ko kinsan illar rama ajikin mace in tayi yawa ??? Rama Sam batayi ba mijinki kullum yana iya kokarinshi akanki amma da yawa mutane sai suyi maki kallon kina cikin matsala ne saboda ramar da kikeyi , sannan zaki zquna a abushe bawata mat'aba ajikinki 🤣🤣 wannan yasa nazo maki da maganin kiba mai inganci hajiya yadda zaki ciko sosai ki murje abunki bawai kiba mai yawa ba aa zaki ciko dai kikoma yar dai dai misali ke ba katuwaba ke ba ramamma ba yadda kema zakiji dadin yin kwalliyar da zataja hankalin mijinki agareki😉😉 mmn Yusuf fa ta shirya tsaf domin gwangwaje Ku da zafafan kayanta uwayen gida da Amare👍🏼👍🏼👍🏼👍🏼07069711327

*Boss Bature ✍️*

*HAROON*na kammala yin wayar,ya mayar da ita cikin aljihun wandonshi,da sauri da sauri ya saukko down kaitsaye ya nufi part ɗinsu,Sautin murya yaji ana raira waƙa da sauri yakai idanuwanshi wurin,Hosana ce zaune saman Sofa,ta aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,ta ɗauki wankan jeans da t shirt ajikinta sam bata lura dashi ba,jinjina kai haroon yayi tare da sakin wannan shu'umin murmushin nashi,A ranshi yace"Zan dawo kanku ne,dake da Omar ɗin,tabbas idan na ta6aki tamkar na ta6a zuciyarshi ne,don haka ta wurinki zan biyo mashi,Saina sa ya zubda hawayenshi kamar yadda nima yasa na zubar da nawa,"ya ƙarasa zancen zucin nashi tare da wuce wa part ɗinsa,bedroom ɗinshi ya shige ya fara zarya acikinshi,burinshi kawai yaji Saƙon mutuwar Junaid~

*JUNHAD*

Saukowa sukeyi downstairs hannunsu ruƙe acikin na Juna,
   "Tun ɗazu nake kiran Layin Rishi,Amma bata ɗagawa,I don't know why,nashiga damuwa,"jahad ce tayi maganar,fuskarta da ɗan damuwa,
  Junaid yace"may be tana busy ne,amma ki bari zuwa anjima sai mu jaraba kiranta,may be ta ɗaga wayar,"
  Cikin palour suka saukko,hosana na ganinsu ta miƙe tana sakar masu murmushi,
  Ba ƙaramin burgeta su kayi ba yarfa hannu ta shiga yi tana faɗin"Wow,jahad junaid kunyi kyau kamar sabbin kuɗin da Central bank suka fitar,"gaba ɗaya suka fashe da dariya,
   camera ta shiga,tare da ɗaukarsu hotuna da wayarta,kafin suka wuce tare da barin palourn,komawa hosana tayi saman sofa ɗin tana jiran dawowar Ya Omar,

Wurin motarshi suka nufa,da kanshi ya buÉ—ewa jahad mota,ta shiga,kafin ya zagaya other side É—in,ya buÉ—e ma kanshi motar ya shiga,
juyawa ta É—an yi tare da kallon fuskarshi,Murmushi ta samu akan fuskarshi,
  Cikin sanyin murya tace"Babyna,"
  "Na'am" ya amsa mata tare da wurga idanuwanshi akanta,
  Kashe mashi ido ɗaya tayi kafin tace"Junaid,I love u so much,I can sacrifice my life for u,"
  Ƙayataccen murmushi ya saki,tare da cewa"Me too,",yana ƙoƙarin tashin motar yaji gabanshi yayi wani irin mugun bugu mai sautin gaske ji kake daraaam!har razana sai da yayi,lokaci guda yanayin fuskarshi ya canza,ganin ya kasa tashin motar yasa jahad,cewa"Babyna,Lafiya naga yanayinka ya canza"?
  Ashagwa6e yace"jahad,faduwar gaba nake ji,kamar wani mummunan abu zai faru dani,haka nake ji,"muryarshi a kasalance yayi maganar,
  Cikin sanyin murya tace"In sha Allah babu abunda zai faru da kai babyna,idan har fitar nan da zamuyi bata kwanta maka arai ba,ni inaga kawai mu koma gida..."tunkan ta ƙarasa maganar,yace"a'a,Bazamu fasa ba,na sa rai sosai akan fitar nan,"
  Jinjina kai jahad ta ɗan yi tare da zura hannu cikin ƴar purse ɗinta dake ajiye saman laps ɗinta,Phone ɗinta ta curo tare da buɗeta,adai adai lokacin app ɗin da take amfani dashi na V muslim wurin yin azkhar yayi mata alert na cewa time ɗin yin evening azkhar yayi,
  Juyawa ta ɗanyi tare da kallon junaid,wanda jikinshi duk yayi sanyi,
  "Babyna,yakamata muyi azhkar kafin mu fita daga gidan nan,"
   Ashagwa6e yace"jahad ni ban iyaba,bansan ya zanyi ba,"
  Moving tayi close to him tare da nuna mashi screen ɗin wayarta"kalli ka gani,App ne nake using dashi yana da matuƙar amfani,kuma yana taimaka mun wurin tunasar dani lokuttan yin sallah da kuma yin azhkar,koda ace baka iya ba,zaka iya yi yayin da kake kallo kana karantawa acikin zuciyarka,"
Murmushi ya É—an saki kafin yace"Its ok my juliet,mu fara atare,"
  Nan suka shiga yin azkhar ɗin acikin zuciyarsu,har suka kammala,tukunna
yaja motar da gudu ya nufi hanyar fita daga gate ɗin gidan,a bakin gate ɗin ma sai da jahad ta ƙara tunasar dashi akan yin addu'ar fita daga gida kuma atare suka furta"Bismillah,Tawakkaltu Alallah,wala haula wala ƙuwwata illa billah",

Fitar motarsu keda wuya,Sai ga motarsu Marshal Omar na shigowa cikin gidan,Hatta gifcinsu sai da marshal Omar ya gani,
  "Yalla6ai,kamar motar junaid ce ta wuce yanzun nan"major ne yayi maganar,
Omar dake zaune a back seat na motar yace"I think so,"
  "Amma yalla6ai,kada kace nayi shisshigi,ni dai aganina bai kamata junaid na fita yawo shi kaɗai ba without security guards atare dashi,duk da munsan Allah ke tsare bayinsa,"
shiru Marshal ya É—an yi yana nazarin wani abu kafin yace"Ni kaina na jima ina tunanin hakan,last time har maganar mu kayi da Rafayet,amma daga baya kowa ya share maganar,"
Major yace"gaskiya yakamata aduba,saboda yaron yana da farin jini sosai,kuma kowa yasan irin son da kuke yi mashi,duk wani mai hakon family É—inku zai iya biyowa ta wurinshi ne"_
Jin wannan maganar ta Major,yasa hankalin Omar ya tashi,saboda an sha faɗa masu cewa junaid,Shi ne lagwansu,Duk wani wanda zai kawo masu hari acikin masu son ganin bayansu,dole sai an ƙuntatawa junaid sannan za'a ta6a zuciyoyinsu,

  "Major thank u so much for ur advise,and in sha Allah zanyi wani abu akai,'

Bayan Major yayi parking É—in motar,Ya buÉ—e ya fito tare da zagayawa ya buÉ—ewa Marshal,Saukowa marshal yayi,ya nufi cikin gidan,lokacin da ya shiga babu kowa a main palour É—in,Bedroom É—inshi ya wuce,Shaf shaf ya cire kakin dake ajikinshi,Ya wuce cikin toilet,after some minutes ya fito daga cikin toilet É—in,sanye da short a jikinshi,Agajiye yake ga wani irin bacci da yake ji,Saman gadonshi ya haye,in a short time bacci ya É—auke shi,

A hankali Hosana ta turo ƙopar dakin nashi,tun tana kabbara sallar la'asar ta jiyo shigowar mota cikin gidan,jiki na rawa ta sallame bayan ta gama sallar ta fito,saboda tana da tabbacin cewar Ya Omar ɗinta ne ya dawo,murmushi ta saki ganinshi kwance da gajeran wando ajikinshi,ya baje sai faman sharar bacci yake yi,lalla6awa tayi cikin sanɗa ta haye saman gadon,saman jikinshi ta hau,har zuwa saitin fuskarshi,ta ƙura mashi ido tana kallon kyakkyawar fuskarshi,bata da da burin da ya wuce ta takura mashi arayuwarta,
   "Bari nagani,idan na toshe mashi hancinshi da bakinshi,ta ina zai yi numfashin,"
  Hannu tasa,cike da mugunta,ta toshe mashi hancinshi da bakinshi,ta danne su da tafin hannunta,aikuwa nan take numfashinshi ya soma tattokarewa,A razane ya farka lokaci guda,ya rarumeta batare da ya ankara ba,yayi wurgi da ita,da iya ƙarfinshi na ƙarshe,kai tsaye hosana ta faɗi ƙasan gadon yaraf!kanta ya bugu sosai,fashewa tayi da matsanancin kuka tana fadin"Wayyo Allah na,Ya Omar ka kashe ni wllh,"
  Tunda yaji muryarta,ranshi ya 6aci sosai,saboda ita taja har yayi mata hakan,ko kwanakin baya ta ta6a yi mashi irin hakan har yayi wurgi da ita,miƙewa yayi daga zaune tare da kai idanuwanshi wurin da take yashe a ƙasa tana kuka,
  Da wata irin kasalalliyar murya yace"Why Hosana!why!"?
   Sai faman shessheƙar kuka take yi,tama gaza ɗagowa da kanta,
  Guntun tsoki yaja,kafin ya sauko saman floor ɗin,hannu yasa ya janyota jikinshi ya rungumeta a saman faffaɗan ƙirjinshi,yana ɗan bubbuga bayanta,Cikin lallashi yace"Am so sorry My Hosana,duk laifinki ne,meyasa kike son takuramin ne?
  Cikin shesshekar tace"ya..ya..Omar,nifa wasa nake yi maka fa..."
  "Haka ake yin wasa a garinku?You are trying to kill me,and u are saying that it was a joke!"
   "Ya Omar,nima fa a wani Chinese film ne nagani,Na jakican,shi ne na kwaikwaya,"
  A ruɗe ya ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi yace"Ke!ashe dagaske baki da hankali,saboda kawai kin kalli film kinga anyi haka sai kice nima zaki jaraba akaina?angaya maki cewa abunda ke cikin film dagaske ne?Su idan sunyi sun rayu,to ni idan kika yi mun kashe ni zakiyi,"
  Runtse idanuwanta tayi ganin yadda yake ta surfa mata faɗa,
  Tsagaitawa tayi da yin kukan da take yi"Am sorry Ya Omar bazan ƙara ba,"
  Harara ya ɗan watsa mata"kinfi kowa iya bada haƙuri,idan kikayi laifi kamar matar aure ta gari,"
  Murguɗa mashi baki tayi,lokaci guda ya samu kanshi cikin wani irin yanayi,zuba mata ido yayi yana kallon dress ɗin dake ajikinta,Jeans da t shirt sunyi matuƙar bin shape ɗin jikinta,jin yayi tsit yasa ta ɗan buɗe idanuwanta,ganin ya zuba mata ido ko ƙyaftawa baiyi ba,yasata fara tunanin kome yake kallo ajikinta,Ganin yana kallon ƙirjinta yasa tace"Ya Omar sun ƙara girma ko"?
Waro ido ya É—an yi tare da cewa"Mekenan?"
Hannu tasa tana nuna mashi breasts É—inta,
  "Ya salam,"ya furta hakan tare da ɗan rufe idanuwanshi yace"nifa,basu nake kallo ba,kayan jikinki ne suka burgeni,sunyi maki kyau sosai,"ya ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye yana kallonta,
   "Idan kana jin yunwa in kawo maka abinci"?tayi tambayar tana kallonshi,
   ɗaga mata kai yayi alamar eh,sannan yace"pls,inaso in ɗan kwanta in huta kinga baccin bai ishe ni ba,idan kika kawo mun Lunch ɗin,ki ajiyemun shi saina farka zanci,"
  Amsa mashi tayi da toh,kafin ta miƙe da sauri da sauri ta fuce daga ɗakin,saman gadon ya koma ya kwanta,bakomai bane ya faɗo mashi aranshi ba,fa ce maganar da suka yi da Major dangane da Junaid,hakanan ya dinga jin kamar yayi kuskuren barinshi ya wuce da motarshi,dama ya sani tun a time ɗin yasa security sun bi Bayan Motarshi...........

*Boss Bature*

Ƙarar shigowar Message,da ta ji ne yasa takai hannu tare da ɗaukar wayarta dake ajiye agaban mirror,yayin da take zaune asaman kujerar gabanshi,tana yin makeup,janyo wayar tayi tana karanta message ɗin daya bayyana akan screen ɗin wayar,
   _Abra,inason magana dake,amma bana so kowa ya sani,koda Aunty Laila ce_
  Mamaki ne ya kamata ganin anyi mata saƙo da new number,kowaye wannan,ɗaukar wayar tayi tare da miƙewa tsaye,a lokacin Aunty babba na cikin toilet tana yin wanka,
Chapter 108 · 0% Book details