← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 212

Sashe 160

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ya Omar,"firgit ya wurga idanuwanshi akan fuskarta,A lokacin Shima Sgr Ya mayar da hankalinshi akanta,
  Da hannu Yake tambayarta taya akai hakan ta faru"?
  Murmushi ta ɗan saki,kafin ta soma magana a tsanake,
  "Nasan zaiyi wuya ku yarda,Amma tabbas Junaid ne,bai mutu ba,Lokacin da hatsarin motar nan ya faru,Junaid baya acikin motar,"a iya nan ta dakata,dan tasan brain ɗinsu a yanzu bazata Iya ɗaukar dogon bayani ba,
  "Idan muka samu natsuwa zamu fahimtar daku komai,Atare da malamin makarantarmu,Da kuma ƙawata Amrish muka kawo shi,"tayi maganar tana nuna masu Ya mu'allim dake a zaune,
Sai Lokacin Sgr yaja dogon numfashi hadi da sauke nauyayyar Ajiyar Zuciya,runtse idanuwanshi Ya ɗanyi yana tariyo abunda Ya wakana a lokacin da suka je wurin da hatsarin motar ya faru,Tabbas sunyi kuskure da basu kwantar da hankali sun tsananta bincike ba,Shi kanshi Yajima yana ji aranshi cewa Kamar Junaid Yana araye,Koba don haka ba,Yayi mamakin Yadda akai ba'asamu ƙashi ko ɗaya ba na jikinshi,wata irin zufa ce ta wanke mashi fuskarshi,Ganin Yadda ta tsastsafo mashi akan fuskarshi ne Yasa Sehrish ta zame mayafinta,goge mashi zufar fuskarshi tayi,kafin ta mayar da mayafin akanta,
"Alhamdulillah,Junaid bai mutu ba,dama yana raye,Ya salaam!"Omar ne ya ambaci hakan fuskarshi É—auke da wani irin murmushin farin ciki,
Doctor emran ne ya fito daga Medical room É—in da aka kwantar dasu,Fuskarshi É—auke da murmushi,kaitsaye wurinsu Sgr ya nufa yana dariya,Kallo Ya koma Sama,
  "Wonders shall neva end"!Ya ambaci hakan lokacin daya ƙarasa wurinsu,
  "Yau naga abun al'ajabin da banta6a gani ba,Dan Allah ku wayarmun da kaina!wanda ya mutu ne ya dawo ko kuwa ghost dinsa ce"?Yayi tambayar yana kallonsu,a lokacin Sgr ya ɗan buɗe idanuwanshi,Sun canza launi sosai,
  "Nikaina Abun Yayi mugun ɗaure mun kai wlh,Still ina doubting,Am confused Allah,ni dai idan ma mafarki nake yi kada ku tashe ni,Ku barni inta yin shi,"cike da tsantsar farin ciki Omar yayi maganar,hannunshi na dafe da saitin Zuciyarshi,No more tension
  Dafa kafaɗar Sgr Dr emran Yayi da hannunshi yana kallon fuskarshi,
  "Sgr fa kamar suman tsaye yayi,Ku tayani dubawa,"Dariya Sehrish tayi,Da alama farin cikine Ya hanashi yin magana,Ko ƙyafta idanuwanshi baiyi,Ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi ya shiga zurfin tunani sosai,hankalinshi Ya tafi wani wurin daban,

Wayarshi daya jefar ƙasa sai dai Sehrish ta ɗauketa,komawa Sehrish Tayi wurin Oummansu,wuri ta samu ta zauna tana kallon Jahad da ta kifa kanta saman laps ɗin Oummansu,
  Cikin sanyin murya ta Ambaci sunanta"Jahad"
"Na'am"ta amsa mata,batare da ta É—ago da kanta ba,'
  "Inason magana dake,"jin haka yasa ta ɗago da kanta,fuskarta duk a yamutse,idanuwanta sunyi jawur,
  "Sehrish amma dai ba gaskiya bane ko!nasan hakan bazai ta6a zama gaskiya ba,Junaid Ya mutu akan idona,Ni naji kukan shi acikin mota Lokacin da yake ƙonewa,Yau kuma sai gashi ya dawo da ranshi"?tayi tambayar a ruɗe,
  "Just believe it!Junaid bai mutu ba,Yana araye,ba lalle ne ki fahimce ni ba a yanzu,Amma tabbas Junaid muka shigo dashi,"_
  "Bazan ta6a yarda ba Sehrish,Sa dai ko me kama dashi ne kuka ɗauko,Amma Junaid dana sani baya acikin duniyar nan"tana kai ƙarshen maganar ta fashe da kuka tare da mayar da kanta saman laps ɗin Oummansu ta kwanta,Tsananin tausayinta ne Ya kamasu,
  "A yanzu ba lalle ne ta fahimce ki ba,Kada ki wahalar da kanki wurin yi mata bayani,"A cewar abu,da ta raba tsakaninsu,
  Gyaɗa kai Sehrish tayi tare da jingina bayanta jikin seat ɗin da suke,

Har time ɗin sallar Magrib ya shige basu ankara ba,Sae da Abusufyan ya tunasar dasu,daƙyar Ya tattarasu gaba ɗaya suka tafi masallaci,

Ya rage daga Alex dake tsaye a bakin ƙopar ɗakin,Sae Su Sehrish da Oummansu dake zaune saman waiting seat,Hosana dae tuni ta jima da yin nisa a baccinta,Duk wannan budurin da ake ita bata sani ba,anan Cikin asibitin ke akwai masallaci,Na mata dana maza,lokacin da suka tashi Yin sallar suna neman inda zasuyi wata Nurse ce ta yi masu jagora zuwa masallacin mata,Kowa sai da Yayi sallah banda Mommy da Hosana,Basu jima da yin magrib ba aka fara kiraye kirayen Sallar Isha'e,basu Baro masallacin ba sae da suka kammala Sallar Isha'en Sannan suka dawo,Ba ƙaramin natsuwa suka samu ba,

Dawowar su Sehrish da ƴan mintuna,ɗaya daga cikin likitocin dake dubasu Ya fito tare da basu izinin Shiga ciki,Alex ce ta fara Shiga,Oumma tare da su sehrish suka bi bayanta,gefen gadon ta zauna yayin da idanuwanta ke akan Junaid,sun canza mashi kayan jikinshi,Riga suka sanya mashi kamar uniform blue colour iya guiwarshi ta tsaya,hannunshi na sanye da kanula ana yi mashi ƙarin jini,Hancinshi na sanye da robar Oxygen,Sai jan numfashi Yake Yi da ƙarfi da ƙarfi,siraran hawaye ne suka sauko akan fuskarta,ruƙo yatsun hannunshi tayi acikin nata,

Jahad dai ta toge a bakin ƙopar ɗakin tana lekenshi,A tsorace take dashi gani take kamar fatalwarsa ce aka kawo masu,taƙi yarda cewa Shi ne Ya dawo,
  Matsawa Abu tayi zuwa gaban gadon ta samu wuri saman kujerar dake fuskantar gadon ta zauna,Addu'o'i ta soma karantowa tana tottofa mashi akan fuskarshi,hakan baƙaramin daɗi yayi ma Alexandra ba,
  Amrish dae na tsaye ta lullu6e kanta da kallabin lace dinta,hannunta na ruke dana Sehrish,gabanta sae faɗuwa yake yi,tana cikin mawuyacin hali,Duk ta tsani kanta,Gani take yi kamar in suka ji cewa Mahaifiyarta ce tayi ma Junaid haka zasu koreta ne,ko su fara ɗaukar fansa akanta,
  "Ki kwantar da hankalinki,ba abunda zai faru,nasan kina jin tsoro ne shiyasa kika tashi hankalinki,"Sehrish ce tayi maganar cikin sigar lallashi,don ta lura da yanayin da Amrish ɗin ke ciki,
  Ƙasa ƙasa suke magana,a tsakaninsu,
"Ji nake kamar in gudu,kafin kowa yaji labarin ainihin abunda Ya faru da Junaid,ni nasan cewa tawa ta ƙare,Ga kuma Mommy tana can tana nemana ta kashe ni"ta shiga damuwa sosai,batasan yanzu ina zata dosa ba,
'Kina tunanin cewa zamu barki ki tafi ne?duk irin ƙoƙarin da kikayi mana,indai kina fargaba ne akan Family ɗinmu,to ki kwantar da hankalinki,Suna da kyakkyawar Zuciya zasu fahimceki su kuma kar6eki hannu bubbiyu,In ma basu amshe ki ba,ni bazan bari Ki tafi ke kaɗai ba zan bi ki ne,"on a serious note,Sehrish tayi maganar,
Har cikin zuciyarta taji daÉ—in kalaman Sehrish kuma hankalinta ya kwanta,duk da akwai sauran fargaba,

"Assalamu Alaikum"Abusufyan Ne ya shigo fuskarshi ɗauke da Murmushi Hannunshi ruƙe dana Sgr,Omar na abayansu tare da Ya mu'allim,yayin dasu Fawan ke biye dasu,Kowa ka kalla tsantsan farin cikine bayyane akan fuskarshi,tsayawa su kayi agaban gadon cirko cirko suna kallon Junaid,Har lokacin Abbansu na kwance gefen Junaid,tunda akayi mashi allurar bacci bai farka ba,

Sai faman sauke ajiyar zuciya Omar da Sgr suke yi,sun jinjinawa lamarin,ƙaryar da suka shirya ta zama gaskiya,Ga ƙannensu sae murna Suke yi Junaid ya dawo,kidnappers sun sake shi,basu san dawan garin ba,
Da zarar Sgr ya haɗa ido da Omar saisu sakarwa juna murmushi,abun ba'a magana,shigowa ciki doctor Emran Yayi fuskar nan ɗauke da ƙayataccen murmushi,jerawa yayi tare dasu,yadda kasan sun Samu talabijin haka suka ƙurawa Junaid ido suna kallonshi,
Dr emran ne ya soma magana a tsanake,
  "In sha Allah,Zasu samu sauƙi,dama damuwarshi rashin Junaid ne,Yanzu gashi Allah ya dawo mana dashi"yana kai ƙarshen maganar,
  Ya mu'allim ya ɗaura da cewa"Yakamata mu nuna godiyarmu ga Allah subhanahu wata'ala,daya bayyanar mana shi,sannan muyi masu addu'a"
Atare suka É—aga hannayensu sama,Ya mu'allim ya shiga yi masu addu'a suna amsa mashi da Ameen,sun É—auki tsawon Lokaci kafin suka shafa Addu'ar,
  Suna zame hannayensu daga saman fuskokinsu,yatsun hannun Junaid suka fara motsi,Da ƙarfi Mommy ta ambaci sunan"Junaid"fuskarta ɗauke da murmushi,hankalin sauran ya dawo kanshi,
  Mutsu mutsu yaci gaba da yi,Jahad sai leƙenshi take yi daga tsayen da take abakin ƙopar,ita dai har yanzu bata yarda ba,
  Mutsu mutsun yaci gaba da yi,duk sun zuba ido suna kallonshi,la66ansa sae kerma suke yi,Slowly ya soma sambatu tun yanayi ƙasa ƙasa harya fara yi da ƙarfi Sunan Abbansu yake ambato,"Abba!Abba!"cikin fitar hayyaci ya soma kokarin ɗaga hannunshi zai cire Oxygen ɗin da aka sanya mashi,Da sauri Dr emran da Omar suka ƙarasa ta gefenshi tare da rurruƙe hannayenshi,hankalinsu gaba ɗaya ya tashi ganin yadda Junaid ke ta firgita,
  "Abba!Abba"daƙyar sautin ke fitowa daga bakinshi,tunda Ya Mu'allim yaji hakan,Sae ya basu shawarar Su matso da Junaid kusa da Abbansu,tunda akwai interval a tsakaninsu,da alama yana ji aranshi cewa mahaifinshi na a kusa dashi,Shiyasa yake ambaton sunanshi,
  Dubara su kayi a hankali suka janye Junaid zuwa gefen Abbanshi,Abun mamaki suna gyara mashi kwanciyarshi sae gashi yana kokarin lalubar jikin Abbansu,Abun yayi mugun ɗaure masu kai,Sam fa baya acikin hayyacinshi amma yaji aranshi Abbanshi na kusa dashi,daƙyar ya iya ɗaga hannunshi ya ɗaurashi akan fuskar Abbansu yana shafata,kuma wani abun mamaki idanuwanshi arufe suke gam,jikin ne kawai ke motsi,
Chapter 160 · 0% Book details