← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 212

Sashe 168

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waro ido waje Amrish tayi,idanuwanta sunyi jawur dasu,a fujajan ta watsa da gudu ta nufi Glass cups ɗin da suka faffashe a wurin,ta ɗauko ta daddage zata Caka shi a ƙahon zuciyarta da sauri Kanal Yusuf yayi hanzarin damƙar hannunta,ƙoƙarin kwacewa tadinga yi don ta Caka ma kanta,Amma ya hana hakan,Fisge glass ɗin yayi tare da jefar dashi ƙasa,Ya ruko kafaɗunta ya jinjigata"baki da hankali ne?Saboda me zaki kashe kanki?saboda Iyayenki sun kasance Gur6atattu!Laifinki ne?ko kin manta da ayar da Allah subhanahu wata Allah ke cewa"Yana fitar da mai rai daga matacce kuma yana fitar da matacce daga mai rai,kuma yana rayar da ƙasa a bayan mutuwarta,Kuma haka ake fitar daku,acikin suratul rum Ayata 20,Bayan ita akwai surar da tayi magana makamancin wannan acikin suratul Ahli'emran Aya ta 28,don haka ki kwantar da hankalinki,Ki rungumi ƙaddararki,Bakanki farau ba,Sau nawa cikakken malami ke haihuwar 6arawo ko kasurgumin dan fashi?Ba yadda Allah bai ikonshi,kuma bawai don baya sonku ba face don Ya jaraba imaninku,Sannan Laifin da iyayenki suka aikata bazai ta6a shafarki ba,ki gode ma Allah da baki ɗauko irin ɗabi'unsu ba,Ke tsarkakkiyace,Allah ya tsarkake ki daga faɗawa halaka.......'jikinta ba ƙaramin Sanyi yayi ba,Kalaman kanal Yusuf ba ƙaramin sanyaya mata zuciyarta su kayi ba,Har taji ta haƙura da kashe kanta da tace zata yi,Jiki asanyaye ta juya ta koma wurin Sehrish,rungumeta Sehrish tayi ajikinta,gaba ɗaya suka fashe da kuka maicin rai,dole Amrish taji ba daɗi,very heart touching ace iyayenka su dukansu gur6atattune kuma 6atattu,dayawa mutane zasu dinga yi maka wani mummunan kallo,Ya Allah kasa mu dace,

"Nasan bazaku ta6a yafe mun ba,Ku yanke mun duk hukuncin da ya dace dani,wlh zan kar6eshi hannu bibbiyu,Amma dan Allah ina neman wata alfarma É—aya agare ku,"Azmee ce tayi maganar,yayin da kwalla ke cigaba da zubowa akan fuskarta,

Kasa kunne su kayi suna sauraronta,
"Dan Allah,Kada ku ta6a Haroon,Duk hukuncin da zaku yi mashi,Ni kuyi mun saboda ba laifin shi bane,tursasa mashi akayi,Bayan tafiyarku asibiti,Na same shi acikin mawuyacin hali ɗakin da kuka kwantar dashi,Na kwanceshi sannan na fitar dashi daga cikin gidan nan,Saboda gudun kada ku kashe shi nasan bazaku ƙyaleshi ba"

"Azmee kin bani mamaki,Kin karya mana zuciyoyinmu,Bakisan irin raɗaɗin da kika sanya mana acikin Zuciyoyinmu ba,Why Azmee?Duk don saboda daukar fansa Yasa kika shiga jikinmu!Ina iliminki ya tafi ne?Ke fa musulmace,bakiyi imani da ƙaddara bane?Meyasa Laifin wani zai shafe mu ?ballantana ma Ba wani abu akayi maku ba,Komai ya faru da family dinku laifinku ne,Saboda kun kashe ne shiyasa aka kashe naku,Da baku ta6a kowa ba,babu wanda zai ta6a naku,Kuskure ɗayane na kashe mijinki da akayi wanda shima don ya taka sahun 6arawo ne,Tsautsayine ya rutsa dashi....."daƙyar yake magana,sauke ajiyar zuciya yayi kafin yaci gaba da cewa"Almost 20 years Azmee kina tare damu ashe ba don Allah bane,Wlh tausayinki nake ji,Kin 6ata wayonki,kuma kinyi asarar Rayuwarki,Yanzu komai da kikayi ya tashi abanza,hatta ibadar da kikeyi itama ta tashi abanza,Idan yanzu kika faɗi kika mutu me zaki ce ma Allah?ya ƙarasa maganar yana kallonta,Sosai Azmee ta fashe da kuka kamar ranta zai fita
"Da ace kinyi hakuri,kin rungumi ƙaddara,Yaya kike tunanin Rayuwarki zata kasance?yadda kowa ke sonki,Kina da farin jini sosai,Ko abokanaina in suka zo gidan nan har santin girkinki suke yi,Kowa yabonki yake yi,Why Azmee?Kin ɗauki alhakin mutane dayawa,Kin cuce mu kin yaudare mu,kin kuma zalunce mu,Amma inaso ki sani,Wlh duk kanki kikayi mawa!"abun ya ƙona mashi rai sosai,
"Ni wlh da tun farko kin sanar dani cewa kina sona,a yadda na yaba da kyawun halayanki a wannan lokacin,Da ba abunda zai hana in aure ki!"
ÆŠagowa tayi da idanuwanta waÉ—anda su kayi jawur dasu,tana kallon Abba dake magana,
Rai a6ace Mommy tace"Ni bansan me kuke jira da ita ba,Banason ganin matar nan,Rayuwarta bata da amfani,ta mutu kowa ya huta,"

Gaba daya sun fusata,ganin suna ƙokarin zame belt ɗin wandonsu don su jibgeta,Abba yayi saurin dakatar dasu"Innallaha ma'assabirin!Kubarta da Allah Shiyasan yarda zaiyi da ita,ban amince ɗaya daga cikinku Ya ta6a lafiyar jikinta ba,Azmee bata kashe mun kowa ba,Iya cuta dai ta cutar damu,Ina neman alfarma a wurinku,daku miƙata wurin hukuma su yanke mata hukuncin daya dace da ita,Sannan kuma Ina umartarku da ku hanzarta Ruguza ƙungiyarsu,Da duk wani wanda ke cikinta,Kamar yarda kakanku salahudeen yayi,haka nakeso kuma Kuyi,Kada ku raga masu,banaso daya daga cikinsu Yasha,gawawwakinsu kawai nakeson Gani,"Yana kai ƙarshen maganar,Ya juya tare da barin wurin Ya koma bedroom ɗinshi,Idanuwanshi cike tab da kwalla,a ƙopar ɗakin ya tsaya yayin da idonshi ke akan Junaid dake kwance saman gadonshi Yana ta sharar bacci abunshi,Har cikin ranshi baiso Azmee Ta kasance haka ba,Koma miye ita taja ma kanta,Ya Allah kakare mu daga aikata Aikin dana Sani,

Bayan tafiyar Abba,Ya Mu'allim Yace"Shawarar da zan baku shine,Kuyi amfani da Azmee wurin kama sauran masu aikata laifin,saboda tasan komai,Tasan inda ƙungiyarsu take Inyaso daga bisani Sai a miƙata ga hukuma,zamu tayaku da Addu'a akan Allah ya baku nasara,"

Sosai sukayi ma Ya mu'allim Godiya,domin kuwa ya basu shawara mai kyau kuma Ya taimakesu,batare da 6ata Lokaci ba,suka tasa ƙeyar Azmee zuwa Ɗakin horonsu,Tambayoyi suka shiga jero mata,tana amsa masu,In tayi kuskuren yi masu taurin kai kuwa,zazzafan Mari take sha,Anan suka samu bayanin inda Ya sayyadi Yake,Ashe baya ƙasar tun Lokacin da abu ta kashe mashi idanuwanshi,Suka fiddashi ƙasar waje,Don a duba lafiyarshi,Da wayar Azmee sukayi amfani wurin gano Duk wani mugun abu da suke aikatawa,A ranar suka shirya tsaf cikin kakin Sojojinsu gaba dayansu domin fara yaƙar ƙungiyarsu,Manya manyan makamai suka ɗauka,Sai da Abba ya fara sanya masu Albarka,Yayi masu addu'a,Mommy ma tayi masu tare da sauran Mutanan gidan Kafin Su kayi masu sallama,A tare da Azmee suka tafi Asaman Helicopter kusan guda shida Ya ɗaga dasu,

Kasa samun natsuwa su Sehrish su kayi,kowa zullumin yake yi game da tafiyarsu Babban Yaya,wurine mai matukar haɗarin gaske acikin wani ƙurmamin daji,inda suka kafa ƙungiyarsu ta matsafa,kodai su kashe ko akashe su,Allah kaɗai yasan wanda zaiyi nasara,

Abu kamar wasa har goma sha ɗayan dare basu dawo ba,babu wani labari dangane dasu,Wayoyinsu kuma duk in aka kira bata shiga,Hakan Ya ƙara tayar masu da hankalinsu,shi kanshi Abba sai daga baya ya fara danasanin turasu,Mommy kuwa tuni ta fara zubda kwalla,tsoranta kada ta rasa Ƴa'ƴanta,

A 6angaren su Sehrish kuwa,Babu wanda ya runtsa acikinsu,kwana su kayi saman darduma sunayin sallah akan Allah ya basu nasara ya kuma dawo dasu Lafiya,abu kamar wasa Tsawon kwana biyu kenan su Sgr basu dawo ba,lamarin ya fara tsoratar dasu,Gashi ba'a samun Layinsu balle asan awani hali suke Ciki,

Sai adaren Rana ta biyu ne,Allah yayi suka dawo,Sunyi nasara sai dai sunyi babban rashi na mutun ɗaya acikinsu,Irfan Allah yayi mashi rasuwa,sunji mutuwar nan kamar kamar me,tare da gawarshi suka dawo,wasu daga cikinsu kuma sun raunata sosai,Dan Fawan Allah ne yayi zai rayu,Twins kuwa sun jigata sosai,kowa Yaji ajikinshi,Nasarorin da suka samu sune sun ruguza Ƙungiyar matsafan,sun lalata masu komai,Sun kuma kashe mutanan cikinta gaba ɗayansu,don sunyi masu zuwan bazata,kuma sunci sa'a adai dai lokacin suna kan yin meeting ne,kowa Ya hallara,Hada shugaban nasu Ghali,Da taimakon Azmee suka kashe shi,Yanzu mutun ɗaya ya rage masu su kamashi Wato Ya Sayyadi,

A washe garin ranar akayi jana'izar Irfan,Abba Yafi kowa jin mutuwar nan,Abubuwa sunyi mashi yawa,Ga Junaid dake kwance yana jinya,Ga kuma fawan shima Yana ƙarkashin kulawar likitoci,

Bayan kammala Jana'izar Ifran,Batare da 6ata Lokaci ba,Sgr Ya tura Armstrong tare da wasu daga cikin sojojinshi,Suka hau jirgi zuwa ƙasar Malaysia,Don bala'e har asibitin da aka kwantar da Ya sayyadi suka Cafko shi,idanuwanshi Na manne da uban bandegi,da Alama aiki akayi mashi a wurin,Cikin jirgi suka sanyoshi,Sannan Suka dawo dashi Nigeria,har cikin gidan suka taso ƙeyarshi gaba,a garden ɗin gidan Sgr ya sanyasu suka Kwantar mashi dashi,kafin ya yanke mashi hukunci,Sai da Ya fara kiran Abusufyan tare dasu Jahad,da oummansu gaba ɗayansu suka hallara a garden ɗin,
Abusufyan yace"dama saida na faɗa maka,Wannan ranar zata zo,kuma gata Allah ya nuna mun da raina da lafiyata,Gani ga kuma Yaran daka zalunta,Ga kuma mahaifiyarsu,Kaji haushin rayuwarka Sayyad,A yau ƙarshenka yazo,tun a gidan duniya zaka fara ɗanɗani raɗaɗin azaba,kafin ka koma Ga Allah," gaba ɗaya yabi ya ruɗe,jikinshi sai kerma Yake yi,daga yayi ƙoƙarin buɗe baki zai basu haƙuri,Sai Sgr ya Kai mashi naushi a kuncinshi,duk saida Ya zubar mashi da haƙoran bakinshi,Jini jaga jaga A bakinshi,
"Mugu azzalumi,Ni Ko kaɗan banji tausayinka ba,Allah yaji ƙanka don nasan cewa taka ta ƙare,Allah ya ƙara nauyin ƙasa,"Abuce tayi maganar,
Jahad da sehrish basu ce komai ba,Hosana dai ce Ta tofa mashi Miyau Asaman fuskarshi,bayan sun gama gaya mashi magana,Sgr Yaba sehrish umarnin ta kawo mashi tafasasshen Mai,

Jiki na rawa ta juya ta koma cikin gidan,Oummansu dasu Jahad suka bi bayanta,Bada jimawa ba ta dawo hannunta ɗauke da ƙaramar tukunya,Tafasasshen mai ne aciki sai tartsatsi yake yi,
Umarni yaba Su armstrong,Su cire wandon jikinshi,Ganin haka yasa Sehrish ta ajiye man,ta watsa da gudu ta koma cikin gida gabanta na faÉ—uwa,
Bayan sun cire wandonshi,suka yi mashi zirr,sojoji guda biyu suka tale ƙafafunshi,Abun nan da yake takama dashi yana yi ma mutane iskanci dashi,Sgr ya ɗauki tafasasshen man nan ya kwarara mashi agabanshi gaba ɗaya,
Wa'iyazubillahi!Wata irin kururuwa Ya sayyadi yayi,lokacin da gabanshi ke ƙonewa,wani irin raɗaɗin azaba Ya dinga ji,Gaba ɗaya ya zauce ya gigice Ya fita hayyacinshi,

Umarni Ya basu Su ɗauke shi su kaishi can cikin ƙurmin daji,ko namun dawa sun samu abinci,A ƙarshe dae Ya sayyadi A cikin daji rayuwarshi ta ƙare,gawarshi A wulaƙance A ƙasƙance abun ba kyan gani,

Ita kuma Azmee Tare da Saratu,Jami'an ƴan sanda ne suka tafi dasu,Bayan an tattara hujjoji,Suka miƙasu Court domin Yin shari'a,A ƙarshe Aka yanke masu hukuncin zama gidan Yari,A ɗakin duhu na tsawon shekara 20,Sehrish tasha kuka,Saboda har lokacin tana son Azmee,Lokacin da aka kammala shari'ar za'a tafi dasu gidan Yari,Daƙyar aka rabasu,Sun rungume juna sosai suna kuka,ita da Sehrish,ita kam Amrish kin zuwa tayi wurin Mommynta balle ma ta rungumetan dama dakyar ta biyo su kotun,kowa baiji daɗin halin da Azmee ta jefa kanta ba,ba lalle ne lokacin da zasu fito ɗakin duhu ba,su dawo da idanuwansu ba,zaiyi wuya in basu makance ba,idan ma sun rayu kenan,'
Chapter 168 · 0% Book details