← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 212

Sashe 192

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rai a6ace hosana ta buɗe idanuwanta a ƙule take kallon Jahad,kamar ta shaqota,
  "Oummace tace atasheki,"
Zumburo baki tayi batare data ce komai ba,ta tsani atada ta daga bacci,

Batare da 6ata Lokaci ba,kowannasu yayi alwala,suka zumbula hijabai ajikinsu tare da kabbara sallah,

*Boss Bature*

Bayan dawowarsu daga masallaci,abusufyan tare da dr harris suka nufi É—akinshi,kamar yadda ya nemi yin magana dashi,daga gefen gadon suka zaune suna fuskantar juna,
  "Naji kace kana son magana dani,menene"?
  Murmushi abusufyan ya saki batare dayace komai ba,. 
  Harris yace"Hmmm na ganoka,halan kana son yi mun magana akan zainabu abu ne?Ae gwaggo ta faɗamun cewa zaka mayar da matarka,nace ashe da rabon gaurancin abusufyan ya ƙare......"cike da zolaya yayi maganar,
  Dariya abusufyan yayi"hmmm,ae gwaggo ta sanar dani cewa,kaima zaka angwance da saudatu,wlh naji daɗi sosai yarinyar akwai hankali,"
   "Ni fa da farko nayi tunanin gwaggo zata hanani auranta,kasan basu jituwa ita da saudat,yadda kasan Tom and jerry haka suke acikin gida"harris ne yayi maganar yana dariya,
Abusufyan yace"Allah sarki gwaggo,inata so in tambayeka game da rashin lafiyarta,Ana samun cigaba ko kuwa har yanzu sai a hankali,Duk da naga lafiyalou muke magana da ita....  "
Tunkafin yakai ƙarshen maganarshi Harris yace"Gwaggo fa ta samu lafiya,.
  Cike da mamaki abusufyan yace"Kai haba"?
  "Wlh kuwa,Lafiyarta qalou,garass take kallon kowa,Babu wani ta6in hankali atare da ita,Ae gwaggonku Allah ya bata Lafiya,ita da kanta take faɗamun cewa taji sauƙi,tana cikin hankalinta,"
  Wani irin farin cikine Ya lullu6e Abusufyan,har baisan lokacin daya mike cike da zumuɗi ba,yana kokarin kama hanyar barin dakin don yaje ɗakin gwaggonsu,
  Ruko jallabiyar jikinshi Harris yayi"ina zuwa?ba kace zamuyi magana ba"?
  "Ba zaka gane ba,inaso naganta ne,ka taso mu tafi acan sai muyi maganar atare,"

Fuskar harris É—auke da murmushi ya mike suka fita É—akin a tare,

A ƙopar ɗakin gwaggon katsina suka tsaya,abusufyan ne ya kwankwasa ƙopar dakin,kusan sau uku yana kwankwasawa, kafin suka ji tace"Wanene"
  Har suna haɗa baki wurin cewa"Mune,"

Buɗe ƙopar ɗakin gwaggon katsina tayi,jikinta na sanye da riga da zane na jar atampa,ta kifa ɗaurin ɗan kwali akanta,koda tayi arba da abusufyan sai tasaki murmushi,

   Cike da tsantsar farin ciki Abusufyan yace"Gwaggo wai dagaske kin samu lafiya"?

Kallon Harris tayi"bana ce kada ka sanar dakowa ba"?jin haka yasa abusufyan ya rungumeta yana dariya,
  "Alhamdullillah Ya Allah,I can't hide my happiness gwaggo,"
  Shafa bayanshi tayi"Abusufyan ɗina,kaga yadda Allah ke ikonsa ko?Rana ɗaya kawai na farka batare da haukan nan da nake fama dashi ba,Allah ya yaye mun,"idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,janye jikinshi yayi daga nata,
  Ruƙo hannunta yayi suka shiga daga cikin ɗakin,harris yabi bayansu sai faman sakin murmushi yake yi,saman kujera Harris ya zauna,Abusufyan da gwaggo suka zauna gefen gadon,har lokacin hannunshi na rike dana gwaggo,salati suka fara yiwa Annabi muhammad(S.A.W),kafin daga bisani,Gwaggo tace"Allah yasa inji wani cikinku ya faɗi ma wani cewa naji sauki,Yasin saiyaji ajikinshi,"

Fashewa sukayi da dariya gaba É—ayansu,harris yace"Saboda me bakiso asani mommyna?wannan fa abun farin cikine,"
  Girgiza kai tayi"A'a,banaso na canza daga yadda nake,inajin daɗin barkwancin da nake yi,Ina sanya mutane nishaɗi,Nima kuma ina samun nishaɗi,koda ace zasu sani ba yanzu ba,Ku bari sai bayan an ɗaura auran kowannanku,"
  Abusufyan yace"Duk yadda kikeso haka za'ayi gwaggonmu,babu wanda zaiji wannan maganar,amma fa zan sanarwa abu,don kuwa tana son yin magana dake sosai,"
  Ƙayataccen murmushi gwaggwon katsina ta saki"Shikenan,ka sanar da ita,Don nima inason magana da abu sosai amma bayan ita,banaso kowa ya sani,"
  Bayan sun ɗanyi shiru na wani lokaci,kowa fuskarshi ɗauke da tsantsar farin ciki,

"Gwaggo,dama akwai maganar da nakeson nayi dake,dana yanke shawarar inyi maganar da harris,amma tunda naga kinji sauki zaifi kyau muyi maganar nan atare,"a tsanake yayi maganar,.  .
   Mayar da hankali tayi akanshi"Ina sauraronka,
   "Dama game da gidan nan ne dake a kano nasarawa g.r.a,nayi laifi ban sanar dake ba,tunda na amshi key din a wurin harris,lokacin da muka je kano,neman abu,mun zauna a gidan,Da zamu dawo kuma sai na mallaka ma Malam nura shi,da niyar idan nadawo muka haɗu zamuyi magana inyaso ko siyarmun da gidanne sai ayi,tunda ba mallakina bane,Gadon Harris ne......."
  Tunkan ya kai ƙarshen maganar dr harris yace"Da ace nasan wannan maganar zakayi wlh da ban 6ata Lokacina wurin sauraronta ba,Haba abusufyan menene aciki don kayi kyauta da gidanmu,Mutanan daka ba wannan gidan sunyi mana halaccin da bazamu ta6a mantawa ba,sun taimaki rayuwar ƴa'ƴanmu,kuma sune silar da aka agano inda Zainab take,Ni inaga kamar kanason nuna banbancine atsakanina dakai........"ranshi a6ace yake maganar,

Murmushi kawai abusufyan yayi yayin da yake kallonshi,Ya harzuka sosai,dama saida ranshi ya bashi cewar hakan zata biyo baya,
   "Allah ya huci zuciyarka,ɗan uwana nakaina,Nima badon naso nayi maganar ba,Sai don in sauke nauyin dake akaina,don nasan cewa gidan ba gadona bane,Naka ne,kuma nayi kyauta dashi,batare dana nemi iznin ɗaya daga cikinku ba"
   "Abusufyan kenan,Ni dariya ma ka bani,musamman daka ce inyaso ko kuɗine ayi mashi ka biya,Nace sannu ko"?gwaggoce tayi maganar tana hararanshi,
  Sunnar dakai ƙasa yayi yana dariya,cike da jin kunyarta,
  Ta6e baki ta ɗanyi kafin tace"Akwai takardun gonakina dake a wurin dankama,guda uku,Na Mallaka masu ita,idan mun koma za'a ɗauki takardun nan a damƙa masu a hannu"

Tunda ta soma magana,Abusfyan ke kallonta,Tsabar farin ciki bakinshi yaƙi rufuwa don murna,

Tana kai ƙarshen maganarta,Dr harris yace"Nima kuma,Na ɗauki nauyin karatun ɗansu sadeeq,tun daga secondry har ya kammala Jami'a,a duk inda yakeso koda ba'a nan kasar ba,sannan mahaifiyar yaron,zan bata miliyan biyar,taja jari dasu,"

Daɗi kamar zai kashe abusufyan,baisan lokacin daya rungume gwaggo ba"nagode sosai da irin ƙaunar da kuke nuna mun da kuma jinina,Allah yabar zumunci atsakaninmu daga nan har gidan Aljanna....."sosai abusufyan ya shiga yi masu godiya,duk da sun hanashi,sun jima a ɗakin gwaggon katsina suna fira,har sai da gwaggo ta shigo ta sanar dasu cewa an shirya masu breakfast tukunna,Suka baro ɗakin a tare da gwaggo

*Hafsat*

Tunkafin ta fito daga cikin toilet tajiyo muryoyinsu Khadija da Nafisat suna fira,la6ewa abakin ƙopar toilet ɗin tayi tana sauraronsu,
  "Nifa abunda yafi bani mamaki,Dana ji Ammi tace,Itace wadda Hamma  rafayet zai aura,abun ya girgizani,Nace ashe yana kula mata"?khadija ce tayi maganar,
  Nafisat tace"Ae bake kaɗaiba,nikaina abun ya bani mamaki,Mutumin nan fa lokacin dayazo damaturu,duk kyawun ƴan matan family ɗinmu,ko kallo wannan basu ishe shi ba,balle aje ga magana,Gaskiya yarinyar nan Allah ya bata,Ƴar baiwace ita,jinin nasarace,Wlh da ace nice ita,Yadda yake da farin jinin nan,Sau da ƙafa zanbi shi,ko musu bazan yi mashi ba,"
  Hafsat dake yi masu la6e,sae faman tiƙar dariya take yi,
  "kinga kullum sainaje gaishe shi,ko Allah zaisa mu haɗa ido dashi in samu shiga,Amma ɗan ta halikin nan gaisuwarma daƙyar yake amsa mun,"acewar khadija,cike da takaici tayi maganar,
  Nafisat tace"Yo ba dole yayi rowar muryarshi ba,in yana magana yadda kikasan ana busa sarewa don daɗinta...  "

Surutunne ya ishi hafsat,Hannu tasa ta buÉ—e kopar ta fito,Suna ganinta da sauri suka rufe bakunansu,Gaba É—aya suna xaune saman gadon,sun lankwashe kafafuwasu,Zaman cin tuwo sukayi,
Girgiza kai hafsat tayi"Allah ya shiryeku,Shiyasa dayawa mata suke rasa mijin aure,Saboda Ruwan ido,Yanzu duk kyawun Hamma adam da Osman baiyi maku ba,saboda haÉ—ama ko"?
  Ƙumshe dariya sukayi,batare da Sun tanka mata ba,
    Jin ringing ɗin wayarta ne yasa tayi sauri juyawa ta nufi mirror hannu tasa ta ɗauki wayar,My daddy,Shine sunan daya bayyana akan screen ɗin wayar,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta,
   "Assalamu alaikum,Daddy,"
On the other hand Ishaq yace"Wa'alaiki salam daughter,Ya kike Ya hutu"?
  "Lafiya lau Alhamdullilah,"tayi maganar,a yayin da take zama saman kujerar dake gaban madubin,
   "Shiru baki dawo ba,ko kin manta da aikin ki ne"?
  "A'a daddy Gobe insha Allah xan dawo,naji daɗin zaman gidanne cikin ƴan uwana,"
  "Kada ki damu,yanzu dai goben ki dawo gida,tunda nan bada jimawa ba,zamuzo bikinsu Omar tare,Hada ma Auntynki "
  Murmushi hafsat ta saki"Shikenan zan dawo goben"
  "In kuma kina da wanda kikeso,ki fadamun kinga sai a haɗa auranki danasu Jahad,ayi a wuce wurin,"
    Aɗan shagwa6e tace"Ae bani da saurayi yanzu,nadaina kula kowa "_
Ishaq yace"Zanyiwa daddy magana,Ya sama maki Miji,sai a haÉ—a auranku,"
   Bubbuga ƙafafunta tayi kamar tana agabanshi"ni banason auran haɗi Allah,nafison in auri wanda ke sona nima nakeson shi,"
  "Allah ya baki Miji na gari daughter,I will keep praying for u,"
  "Ameen daddyna nakaina,"
  Shiru suka ɗanyi na wani lokaci,Kafin yace"Ya jikin Mommyn naki"?
  "Da sauƙi,Ae jiya munyi waya da ita,ta kirani da layin ɗaya daga cikin likitocin dake kula da ita,tama faɗamun cikin satin nan za'a sallameta,"
  "Jiki yayi kyau kenan,To Allah ya ƙara mata Lafiya,". 
  "Ameen daddy,mungode ssai,Allah ya saka da alheri,"
  Sun jima suna waya,kafin su kayi sallama,Ta kira Layin Hayaam......'
  Tana fara ringing Hayaam ta ɗaga kiran,bayan sun gaisa Hafsat tace"Aunty hayaam,tunda safe nake ta kiran Layinki tana ta ringing baki ɗaga ba,"

"Na sanya wayar silent ne,dayake naje makaranta ne,"
  "Dama inaso na sanar dake cewa,Mommy na nan zata dawo gida,An kusa sallamarta,"
  Muryar hayaam da alamun farin ciki tattare da ita tace"Alhamdulullah,Amma naji daɗi sosai,nayi farin ciki,Ya mutanan gidan?
  "Suna nan cikin ƙoshin Lafiya,Ae zakuzo bikinsu yaya Omar ko,"_
  Shiru hayaam ta ɗanyi kafin tace"Anya!"
  "Dan Allah aunty hayaam kuzo,Gagarumin biki za'ayi,Kuma hada fa Amal ma,Kodan ita yakamata kuzo,tunda ƴar uwarku ce,"
  "Allah ya bamu ikon zuwan,"
  "Ameen,in sha Allah ma zakuzo,"

Sun jima suna waya kafin daga bisani,Sukayi sallama,
 
*Boss Bature*
Chapter 192 · 0% Book details