← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 212

Sashe 159

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Saboda halin da Abban junaid ke ciki,Ya mu'allim Ya basu shawarar su ɗauki junaid su koma dashi Can Sgr hospital ɗin,Don A haɗashi da mahaifinshi in yaso sai acigaba da jinyarshi acan asibitin,Sai da suka tsaya Jinin ya ƙare sannan Likita ya sallamesu,Suka ɗauke shi a back seat ɗin motar Ya mu'alim Aka shigar da junaid,Sehrish ta shiga ta ruƙoshi ajikinta,bawan Allah ya zama tamkar lagwanin filita jikin sae kerma Yake yi sam baya acikin hayyacinshi,Mazaunin driver Ya mu'allim Ya shiga,Amrish ta zauna gefenshi,Ya tashi motar,a tsanake yake driving ɗinsu,Amrish sae faman zabga murmushi take yi,burinta Ya cika,junaid zai koma wurin ƴan uwanshi,Sehrish kuwa ba'a magana,Bakinta yaƙi rufuwa,Kamar wadda akayi ma Albishir da gidan Aljanna,Tsabar farin ciki ne kawai,Ta ƙankame junaid ajikinta kamar ta mayar dashi cikin cikinta,Saboda tsabar ƙaunar da take yi ma ɗan uwanta,A ranta tana ayyana irin farin cikin dasu Babban Yaya zasu yi idan suka ga junaid bai mutu ba,

Slowly motarsu ta ƙaraso cikin katafaren asibitin SGR................

*dakwai yiyuwar littafin Abban Sojoji yakai farkon march,Ba kamar yarda nace ba ƙarshen February,Amma idan kuna son ayi maku after 3 years,kuyi mun magana,sai mu katse shi,ra'ayinku nakeson ji,littafin yazo ƙarshe masu tunanin zai kai azumi,Aniyarku tabi ku😂*

*masu son karanta Littafin Abban Sojoji su tuntu6i layina,Message za'a tura mun ta whatsapp banda phone call*

 
 [3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋

𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠

*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*

Members na paid group ɗina Am really Sorry🙏masu cewa ko naje wurin za6e na gaji shiyasa banyi posting ba,Boss ko Voters card bata dashi🤣

Acan cikin asibitin kuwa,Suna cikin matsanancin tashin hankali,Jikin Abba Yayi tsauri sosai sam bai kar6ar treatment din da ake basa,Zuciyarshi tana barazanar bugawa,Kowa yayi zugudum cike da jimami suna jiran Tsammani,Sgr da Omar Sunfi kowa shiga matsananciyar damuwa,Saboda suna ganin sune silar Halin da Abbansu Yake ciki,

Tunda suka fito daga Office ɗin Doctor Emran,a tsaye suke sun jingina bayansu da wall,Sgr Ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,zuciyarshi sai tafarfasa take yi,wani irin bugun zuciya yake ji,Omar kuwa idanuwanshi na kallon Ceiling,tsantsar damuwa ce akan fuskarshi,

Mommy tuni ta jima da kifa kanta saman cinyoyinta,tayi kukan harta gaji tayi shiru,Abu na zaune a gefenta,Yayin da Jahad ta kwantar da kanta saman kafadar Oummansu,idanuwanta a lumshe,Hosana na kwance saman cinyoyin Jahad,ta É—an aza kanta saboda baccin da take ji,

Su fawan kuwa,Duk sun rufe idanuwansu yayin da kwalla ke zuba,Abusufyan dae Ya gaza samun natsuwa Sae faman safa da marya yake Yi a tsakanin Corridor É—in dakin da Abban yake,

Dirar Motarsu Sehrish keda Wuya,Motar Sergeant É—in daya É—aukota daga gida ta faÉ—o asibitin dama Yana biye dasu,A bayan motarsu yai Parking É—in tashi,Fitowa Sergeant É—in Yayi,Sae ga Baba maigadi ya fito daga back seat na motar,Ashe lokacin da suka barshi acan asibitin,Masallaci Yaje don Yayi sallar azhar da bai samu yayi ba yana fitowa motarsu na fita shine sergeant ya taho da shi,

Wayar aljihunsa sai ringing take yi,sam hankalinshi baya a wurin,har sai da Abusufyan ya ambaci sunanshi"Rafayet ka É—aga kiran mana,"
A kasalance Ya sanya hannu ya curo wayar,Abbas ne ke kiranshi,picking call din yayi tare da kara wayar a kunnanshi,akan rashin lafiyar Abbansu suke tattauna,

Kamar daga sama Sehrish ta faÉ—o wurin da suke bakinta É—auke da sallama,jin muryarta yasa Jahad ta É—ago da kanta tana kallonta,kanal Yousouf ma ya É—aura idonshi akanta,Haka Abusufyan da abu ma duk ita suke kallo,Sauran kuwa duk hankalinsu baya a wurinta,abun ya É—aure masu kai ganin tana ta faman sakin Murmushi kamar wata zautacciya,
"Anya Sehrish tana da lafiya kuwa?sai kace batasan halin da muke ciki ba,Sai murmushi take ta saki kamar wata zararra,kodai Hosana batayi wannan haukan ba,"Jahad ce tayi maganar acikin zuciyarta,
  "Sehrish!waya kawo ki?dama bada ke muka zo ba"?Oummansu ce tayi mata tambayar,don ita bata lura ma babu ita ba,
"Daughter,"Abusufyan ya kira sunanta yayin da yake tunkaro wurinda take a tsaye,duk wannan abun dake faruwa Sgr bai ankara da ita ba,Saboda Ya juya bayanshi Yana waya da Abbas,
  A hankali ta soma magana"Bani kaɗai nazo ba"tana kai ƙarshen maganarta ta matsa gefe,Sae ga nurses guda biyu sun shigo da Junaid asaman gadon daukar marasa lafiya suna gunguroshi a wani irin Slow,

Ya mu'allim na a bayansu tare da Amrish da kuma Baba mai gadi,
Zuba ido Abusufyan yayi yana kallon fuskar mara lafiyan da suka ɗauko,Lokaci guda Ya ambaci sunanshi"JUNAID!!!"da tsantsan mamaki akan fuskarshi,Jin sunan Daya Ambata ne Yasa Su fawan suka ɗago da idanuwansu,Ai ko da sukayi Arba da Junaid kwance saman gadon,A wani irin firgice Suka mike suna ambaton Sunanshi Junaid! Junaid!!,Tuni Jahad ta ƙame a tsaye,gaba ɗaya ta rikice Sai faman zazzare idanuwanta take yi akan fuskarshi gani take Yi tamkar Mafarki ne ba gaske ba,Tsabar razanar da tayi ne Yasa ta Yanke jiki ta zube anan wurin,Gaba ɗaya sun miƙe tsaye cirko cirko agaban gadon,Surutun da suke yi ne Ya jawo hankalin Omar kansu,koda Yayi arba da Junaid nan take kirjinshi Yayi wani irin mugun bugu,Waro ido waje yayi yana ƙare mashi kallo a ruɗe ya ambaci sunanshi"JUNAID"!
Adai dai Lokacin Sgr Ya ɗan juyo a sukwane don Yaga meke wakana Yaji sunata ambaton Sunan junaid,baiyi tsammanin wani abu ba,Juyowarshi keda Wuya idanuwanshi Suka sauka direct kan gadon Da junid yake kwance,Saboda tsabar firgitar da yayi baisan Lokacin daya Saki wayar dake hannunshi ba,ta faɗo ƙasa,
Hannu yasa saman idanuwanshi Ya murzasu dakyau don Yaga in dagaske ne,A sukwane Ya kalli Marshal a lokacin shima Omar ya juya a hargitse suka haɗa ido,Just speechless sun gaza magana sai dai nuni da hannu,Sun zama kurmayen Ƙarfi da Yaji,Girgiza kai Sgr ya shiga yi,Alamar bai Yarda ba,
  "I can't believe it,Wannan bazai ta6a yiwuwa ba,Junaid Daya mutu Ya dawo,how can that be possible?Yaron daya ƙone a mota,dama ana mutuwa adawo ne....its just a dream...."acikin ranshi yake wannan Sambatun,Sae faman motsa la66ansa Yake yi amma ya kasa buɗe baki Yayi magana,sunyi matuƙar razana,Sun gigice da ganinshi,Duk da basu Yarda cewa shi bane,Ido kawai suke binshi dashi,

Su kuwa Sauran Matasan Sae murna Suke Yi baby Junaid É—insu Ya dawo,Duk da matsananciyar damuwar da suka Shiga na ganin halin da Junaid É—in yake ciki,Tuni Fawan ya fashe da matsanancin kuka,haka su Irfan sun tasa shi gaba sai kuka sukeyi sun hana nurses É—in su wuce dashi ciki,
Koke koken da suke Yi ne ya farkar da Alex,Dagowa tayi fuskarta sharkaf da hawaye,Ganinsu tsaitsaye cirko cirko Yasa ta miƙe tare da nufarsu tana Tambayar Lafiya,Matsa mata su kayi don ta ganshi dakyau,A sukwane Alex ta zube saman guiwowinta agabanshi Tana kallon fuskarshi,Yatsun hannunta Na kerma ta azasu asaman ramammar fuskarshi,
  Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka tana ambaton Sunan shi"Romeo ɗina ne ya koma haka"?rufe bakinta tayi da tafin hannunta tana cigaba da yin kuka,
  Ganin Suna 6ata Lokaci Yasa nurses ɗin suka nemi alfarmar su basu hanya su wuce dashi ciki,Gungurashi sukayi da sauri Abusufyan tare dasu Kanal Yousouf suka bi bayansu,Ɗakin da aka kwantar Da Abbansu nan suka nuna suna son a shigar dashi,Ko Allah zaisa adace Abba Ya dawo hayyacinshi,shiga ciki Su kayi dashi,anan gefe aka kwantar da Junaid,dandazo likitoci su Kayi acikin ɗakin domin duba Lafiyarshi,gwaje gwaje suka fara yi mashi,Yafi buƙatar blood ajikinshi fiye da Komai,tsabar so da ƙauna har kokawa su Fawan suke yi don a ɗebi jininsu,Kowa so Yake a sanya ma Junaid nashi,One by One aka dinga gwada Jininsu,A ƙarshe aka ɗibi jinin Fawan dana Ayaaan,kusan Leda huɗu za'a ƙara mashi,

Abun sai ya baka mamaki,Gaba ɗaya sun kasa samun natsuwa sae faman sintiri Suke Yi,da taimakon Oummansu Jahad ta farfaɗo da matsanancin Ciwon kai,Still bata Yarda da abunda idanuwanta suka nuna mata ba,Asaman laps ɗin abu ta kwanta,wani irin zazza6i ne ya rufe ta,duk a tunaninta Fatalwarsa ce aka kawo masu,Mommyn Junaid kuwa tana bakin ƙopar ɗakin tsaye ita da Abusufyan,jikinta sae tsuma Yake Yi,ji take kamar ta faɗa ɗakin,

Ya Mu'allim yana a tsaye tare dasu Amrish,ba ƙaramin tausayi suka bashi ba,sam babu kwanciyar hankali atattare dasu,Tunda Allah yasa su kayi arba da Junaid,hankalinsu gabadaya ya koma akanshi,shiyasa basu nemi ƙarin bayani a wurinsu ba,Wuri Sehrish ta nuna masu suka zazzauna,kafin ta wuce izuwa wurinsu Marshal Omar dake a tsaye,Suna bin kowa da ido,Su da suka san Cewa Junaid Ya mutu,Abun ya matukar jijjigasu,
Chapter 159 · 0% Book details