← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 212

Sashe 173

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan sau uku Marshal Omar yana kwaÉ—a sallama amma shiru bai amsa mashi ba,sam hankalinshi baya atare dashi,
  "Rafayet"Ya ambaci sunanshi Yana shigowa cikin ɗakin,Firgit yayi tare da ɗago blue eyes ɗinsa,tamkar na wanda yasha Giya,fuskarshi tayi sharkaf da zufa,
  Zama gefenshi Omar yayi"bro lafiyarka kuwa?Zaman me kake yi,Muna ta jiranka,Time ɗin sallah yayi fa"
  Daƙyar ya iya buɗe baki yace"Omar,lokacin da zaka shigo kaga Uncle"?
  Jinjina kai omar yayi alamar eh,
"Ashe ba mafarki bane"Ya ambaci hakan acikin zuciyarshi,
  "What's wrong with u?ko wani abu ya shiga tsakaninka dashi ne"?
  girgiza kai yayi"bakomai,bari na shirya mu tafi,"yunƙurawa yayi tare da miƙewa tsaye,Daƙyar yake jan ƙafarshi,Direct ya nufi Closet ɗinshi,after some minute Ya dawo jikinshi sanye da Jallabiya,Omar ya tadda a tsaye hannunshi ruƙe da paper ɗin daya keta,Kallonshi yayi"Wannan fa?naga an yayyagata"
  Yatsina fuska yayi tare da cewa"Bakomai,mu tafi,"a jere suka fita,Shiru kawai Omar yayi amma tabbas yana ji aranshi cewa wani abu ya faru dashi,Jikinshi duk yayi sanyi,downstairs suka sauko anan suka haɗu da sauran matasan gidan suka ɗunguma izuwa masallaci,

A 6angaren Sehrish kuwa,Tunda ta gudo daga part É—insa,Bedroom É—in Aunty azmee ta wuce,tana shiga ta samu amrish a tsaye saman darduma ta kabbara sallah,lalla6awa tayi cikin sanÉ—a ta shige toilet,don ta tsarkake jikinta,ta fito É—aure da towel ta nufi wadrobe,Da yake duk ta kwaso kayanta,Doguwar riga ta zura ajikinta orange colour,mara nauyi Æ´ar ta shan iska,saman dardumar ta hau,A gefen Amrish ta kabbara sallah,bayan sun kammala Sallar,ko addu'a bata samu tayi ba,Saboda yanayin da take ciki,kasala duk ta baibayeta,Saman gadonsu ta koma ta haye,ta janyo bargo ta lullu6e har kanta,duk amrish na kallonta,ta fara sanya mata ido,in dare yayi ta É—au wanka,ta fuce daga É—akin,tsakar dare ta dawo ko wurin asuba,Ta shiga toilet,Wani irin bacci ne ya É—auketa mai daÉ—in gaske,hada minshari,

Bayan Amrish ta kammala Yin addu'ar da take yi,Komawa tayi gefen sehrish ta kwanta tana fuskantar ceilling,da alama tayi zurfin cikin tunani,

Tun wuraren ƙarfe 7 na safe,Mommy tare da Oumma suka shiga kitchen domin shirya breakfast ɗin gidan,basu jima da fara ƴan soye soye ba,Saude ta shigo kitchen ɗin tare da hajiya azeema,domin su tayasu aiki,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,Suna aiki suna fira,
  "Naji kuna ta fira banji kuna zancen gagarumin bikin da muke dashi ba,"Hajiya azeema ce tayi maganar,.
mommy tace "Wai har mutun nawa za'a É—aura ma aure ne?donni abbansu bai sanar dani ba,Amma yace mun in shirya tarbar surukai na,"
  Aunty azeema tace"Ni kaina bansan mutun nawa za'a shafa fatihar tasu ba,Amma ina da tabbacin cewa hada abusufyan acikinsu,"da gangan tayi maganar,cike da zolaya tana satar kallon Abu,
Wata irin kunyace ta rufe ta,har ta kasa tanka mata,
  "Ga kuma saude,Amaryar harrisun gwaggo,Kai gaskiya masha Allah zamu sha bikin da ba'a ta6a yin irinshi ba"abunka ga fulani ga kunya,da gudu saude ta fuce daga kitchen ɗin,
  Gaba ɗaya suka fashe da dariya,
"Tunda saude ta gudu bari in dawo kan Zainabu abu,tauraruwar dake haskaka zuciyar abusufyan,Gaskiya abu ki gode ma Allah,Abusfyan ba ƙaramin Sonki yake yi ba,Ae dole ma yaso ki,Tashin farko kika haifa mashi triplet kyawawan gaske,"
Murmushi kawai abu ke saki,da alama taji daÉ—in maganar Aunty azeema,
   Mayar da idanuwanta tayi kan mommy,
  "Auntynmu,Kinsan nifa bana 6oye 6oye,nasan su Ya hossein basu sanar dake ba,"
  Fuskar mommy ɗauke da murmushi tae"mekenan?
  "Nima fa bani da tabbaci nadaiji ƙishin ƙishin wai cikin ƴan ukunta za'a haɗa aurensu da biyu daga cikin zaratan samarin wurinki,Amma fa bansan wanne daga cikinsu ba,"da biyu Azeema tayi maganar don taga reaction ɗinta,
Shiru Alex ta ɗanyi jimmm batare da tace komai ba,har na tsawon mintuna,azeema ta kafe ta da ido,don tasan halinta,a lokacin baya tasha faɗin cewa Ƴa'ƴanta bazasu auri baƙar fata ba,ita kanta abu ta lura da sauyawar da tayi tunda akayi mata maganar,
  Lokaci guda,murmushi ya bayyana akan fuskarta,a tsanake ta soma magana"Zanfi kowa farin ciki,idan Zainab da abusufyan suka zama surukaina,Saboda na yaba da irin tarbiyar ƴa'ƴansu,suna da hankali sosai,ga girmama na gaba dasu,"
  Wani irin farin ciki ne ya lullu6e Aunty azeema,dama ita fargabarta karta basu matsala,
Abu kuwa taji daÉ—i sosai da irin yabon da Mommy tayi ma Æ´a'Æ´anta,
  Cigaba da magana mommy tayi"Dama fa junaid ya sanar dani tun kwanakin baya,duk da na ɗanji nauyi wlh,Ya nuna yana son aure,mukuma a ƙa'ida Yaro kamar junaid ko soyayya bai isa ya fara ba,nayi tsammanin sai ya kai shekera Talatin koda biyar haka kafin ya fara zancen aure,Amma sai gashi tun yana 19 years aure yake so......"da sauri aunty azeema tace"Wannan ae ba wani abu bane,Ya hossein fa,tun yana 20years yayi aurenshi na farko,duk dashi A lokacin ya mallaki komai na rayuwa,Shi kuma junaid sakamakon tauye mashi haƙkinshi da Azeemi tayi,baisamu damar yin karatu ba,Balle aje ga maganar aiki,Amma bai kamata mu damu akan wannan ba,Still junaid yana da sauran damar da zai gyara rayuwarshi,zai cigaba da zuwa makaranta,Sannan za'a sama mashi aikin yi,tunda alhmdllh Allah ya hore mana,"
  Murmushi mommy ta saki,Taji daɗin maganar azeema sosai,daga haka suka cigaba da yin firarsu suna aiki,cikin lokaci ƙanƙani suka kammala Girke girken nasu,a lokacin saude ta dawo kitchen ɗin,Atare da Oumma suka soma ɗaukar food stuffs ɗin suna kaiwa saman d-table,

Bayan sun kammala jerawa,Saude tabi É—akunansu tana tashinsu,Don su hallara a fara É—a'amin,

Turo ƙopar ɗakin ammi tayi,Zaune tasame ta gefen gadon hannunta ruke da ƙur'ani tana karanta,Idanuwanta na sanye da glass fari,
  Zuƙunnawa tayi cike da girmamawa ta gaishe da ita"Ammi ina kwana,kun tashi lafiya,Ya gajiyar tafiya,"
Murmushi ammi ta sakar mata"Lafiya lou,Gajiya tabi jiki,"
  Saude tace"An kammala shirya breakfast Anan zan kawo maki,".
  "A'a,nafison nafito naci atare da jikokina,"murmushi saude ta saki kafin ta miƙe tare da juyawa zata bar ɗakin,. 
  "Ji mana,"ammi ce ta katse mata hanzarinta,"juyowa tayi tana kallonta,.  . 
  "Amm..ince ko kinyi ma su Nafisa da khadija magana"?tana magana akan ƴan matan da suka zo dasu jiya
  "Ae daga ɗakinsu nake,Na same su suna shiryawa,"
  Jinjina kai tayi"Masha Allah,zaki iya tafiya,"
  Buɗe kopar tayi ta fuce izuwa ɗaki na gaba,

Jahad na kwance,since yesterday night bata runtsa ba,tashiga damuwa sosai akan junaid,hankalinta yaƙi kwanciya,tunda ya nuna baisanta ba,duk ta rasa natsuwarta,ita kaɗai Ce kwance saman gadon,Hosana na acikin toilet,

Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,Muryarta adisashe tace"Wanene"?
  Muryar Hafsat ta juyo daga waje,
  "Nice,"
saukowa tayi daga saman gadon taƙarasa tare da buɗe mata ƙopar,
  "Aunty hafsat"Tsaye take jikinta sanye da riga da wando,ta yafa mayafi akanta,
  "Jahad ce ko sehrish,"tayi tambayar ne don bata ganeta ba,
  "Jahad ce,Kin tashi lafiya?Ya gajiyar tafiya"?
  "Lafiyalou Alhamdullih"ta amsa mata tare da shugowa daga cikin ɗakin,
Gefen gadonsu ta zauna,kafin tace"Jahad inason magana dake,"jin haka yasa jahad ta koma gefenta ta zauna,ina sauraronki Aunty hafsat,
  Calmy ta soma magana"Game da abunda Mommyna tayi maku,Ina nema mata yafiya a wurinku,dan Nasan haƙƙinku ne ke bibiyarta,Jahad tana cikin mawuyacin hali,Yanzu haka maganar da nake yi maki,ƙafarta ta ru6e ta lalace,A sakamakon wani mai mota daya bugeta A enugu,Ni bansan ma meya kaita can ba"idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,
  Hankali tashe jahad Tasoma ambaton'Innalallahi wa'inna ilaihirra'jin!"
  "Wlh jahad,ta zama abun tausayi,A gefen bishiya take kwana,dare da rana tana zaune a wurin,Kona abinci bata dashi sai in ansamu na Allah ya bata sadaqa,tukunna take samun abunda zata sama cikinta,"
  Jahad sarkin tausayi tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,

Hosana dake a la6e cikin toilet tana sauraronsu,Sai 6a66aka dariya takeyi hada dafe cikinta,Don bala'e ko kuskure bakinta batayi ba,yayi dama dama da kumfa,Hannunta ruƙe da brush,
  "Allah sarki aunty hafsat,wlh na tausaya mata baiwar Allah,Ni indan tani ce,Tuntuni na yafe mata,Amma meyasa ba ataimaka mata ba"?
   "Jahad bamusan komai game da tafiyarta enugu ba,wayarta ma ba'a samu,Ashe tun lokacin da mai motar ya bugeta,Anan ta rasa wayarta,Shiyasa bamusan halin da take ciki ba,Amma yanzu nayiwa daddy magana,Yanzu haka tana kwance gadon asibiti acan enugun,saboda lalacewar da ƙafar tayi baza a iya ɗaukota kaitsaye ba zuwa abuja,Dole acan za'a fara yi mata aiki,Za'a cire ƙafarne....."
  Tunkan hafsat takai ƙarshen maganarta,Hosana dake ƙumshe dariya acikin toilet,ta tuntsire da wata irin mahaukaciyar dariya,
"Waye acikin toilet?Naji kamar sautin dariya"
  Da sauri jahad tace"Bakowa aunty hafsat,Allah Ya bata lafiya,in sha Allah zata ji sauƙi,zamu tayata da addu'a,"
Hannu tasa tana share hawayen fuskarta,Kalaman jahad sun sanyaya mata zuciyarta,
  'Nagode sosai jahad,Yanzu saura hosana inaso na nema mata yafiyarta,"
  Jahad na ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,hosana dake acikin toilet ta ɗaga murya tare da cewa"Wlh na yafe mata,tunda an gutsire kafar,Allah ya kyauta gaba,"
   Da sauri jahad ta daka mata tsawa"Hosana ya ishe ki haka,Wai meyasa baki iya magana ba,"
  Hafsat kuwa murya asanyaye tace"Nagode hosana,Ni banga laifinta ba,Ai ita taja ma kanta,"tana kai ƙarshen maganar,ta nufi hanyar fita daga dakin,bayan fitarta,hosana ta futo daga cikin toilet,bakinta washe,
Harara Jahad ta jefe mata"Wawuya kawai sullu6iya,Yanzu abunda kika faÉ—a ma Aunty hafsat ya dace"?
  Murguɗa mata baki Hosana tayi"Anje an faɗa,Allah shi ƙara in ma da ƙarin Ya ƙara,Uban dayasa ta kulle mu acikin store kamar wasu dabbobi,Wlh ni daɗi naji,wai agefen bishiya take kwana,har na hango ƙoƙwan bararta....."fashewa ta kuma yi da dariya hada dafe ciki,jahad dai bata tanka mata ba,ido kawai tabi ta dashi,cike da takaici,
Guntun tsoki taja"Ya omar dai baiyi dacen mata ba,"
   Harara hosana ta watsa mata kafin tace"eh ɗin ina ruwanki?A haka ya gani yana so,ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu,Ni da ya Omar mutu ka raba takalmin kaza,"
    Girgiza kai kawai Tayi batare da ta kuma tanka mata ba,Komawa tayi gefen gadon ta zauna,
 
*Junaid Romeo*

Har cikin É—aki,Mommy ta shigo mashi da breakfast É—inshi,Jiya atare dashi suka kwana,dama tunda ya fara jinya a tsakiyarsu suke sanyashi,Yanzu kuma ya fara jin sauki,Ya fara tunanin komawa bedroom É—inshi,
Chapter 173 · 0% Book details