← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 212

Sashe 54

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   Gaban jahad ne ya faɗi rass!!jin sautin kukan Junaid,rarrafowa tayi ta dawo gefen gadon tare da ɗan leƙawa don ta tabbatar ma kanta abunda kunnuwanta ke ji,Zaro ido waje tayi cike da mamaki take kallonshi,yadda kasan wani jinjiri ya 6are baki sai kuka yake yi,da ƙarfi ta ambaci sunanshi"JUNAID"dakatawa yayi daga yin kukan da yakeyi jin an ambaci sunanshi,wurga idanunshi yayi akan jahad,yayi mata wuri wuri da ido yana kallonta,
  Muryarta na rawa tace"juj..junaid!dama kai Ne?me kake yi acikin ɗakin mu?
cikin shessheƙar kuka yace"Nifa Zuwa kawai nayi don in taya ku kwana,"
...zuba mashi ido kawai tayi tana  kallon fuskarshi don abun ya fi ƙarfinta,
  Daga cikin toilet ta jiyo Muryar Sehrish tana ce wa"Jahad wai dagaske junaid ne?Naji kin ambaci sunanshi"?
  A ƙule jahad tace"Bansani ba,ku fito ku gane ma idonku,kunaji ina kukan neman taimako amma duk kuka watsa a guje kuka barni,yanzu da wani mugun abunne ba junaid ba,da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya,"
  buɗe ƙopar sehrish tayi tare da fitowa daga cikin toilet ɗin,hosana ma ta buɗe wardrobe ɗin tare da fitowa daga ciki,suka tunkari inda junaid yake kwance yana faman sauke ajiyar zuciya,sae faman lumshe ido yakeyi,saboda baccin dake a idanunshi,
  "Junaid!" sehrish ce ta kira sunanshi,ware idanunshi yayi akanta yana kallonta,
.."junaid me kake yi a ɗakin mu?waya kawo ka?anya baka fara shan ƙwaya ba"
  Harara ya wurga mata tare da murguɗa mata baki yace"bansani ba,duk kun bi kun takura rayuwata,hakanan kawai ina baccina kun tashe ni,laifi ne in na kwana aɗakinku,ni ba ɗan uwanku bane"? Sakin baki sukayi suna kallonshi,hosana tace"wlh saina faɗa ma Daddy da Ya Omar,ince ka shigo ɗakinmu ka kwanta mana asaman gadonmu,ƙato dakai,"tana kai ƙarshen maganarta,junaid yace"idan kin tashi ki faɗama Kaka ƙarewar daddyn,mai kan kurciya kawai" wannan maganar ba ƙaramin fusata hosana tayi ba,jikinta har rawa yakeyi wurin dauko pillow daga saman gadonsu,ta buga mashi asaman fuskarshi,koda ganin hakan,sehrish ma ta ɗauko pillow ta shiga taya hosana,jahad tace"wlh nima bazan ƙyale ka ba,junaid saboda ka bani tsoro,kuma babu kyau ma tsoratar da musulmi,"tasa hannu ta ɗauko pillow itama,nan fa suka tasa junaid kamar sun samu jaki,suka dingi jibgarshi da pillows,tun yana yi masu magiyar su daina har ya sake fashe masu da kuka yana bubbuga ƙafafunshi,suna cikin bugun nan nashi,suka ji tsit junaid ya daina motsi,cikin sauri Jahad ta kalli jikin pillown hannunta,Ɗigon jini ta gani,ɗagowa tayi da nufin ta nuna ma su Sehrish aikuwa karaf idonta ya sauka akan pillown dake hannun sehrish da hosana,duk ɗigon jini ne ajikin pillown hannunsu,Tashin Hankali!
  Gaba ɗayansu ba ƙaramin kiɗima suka yi ba,ƴan hanjin cikinsu suka kaɗa,zagaye shi su kayi a zuƙunne suna kallon fuskarshi,
  Fashewa hosana tayi da kuka tana faɗin"Wlh babu ruwa na!bani na kashe junaid ba!"maganar da tayi ba ƙaramin tsoratar dasu tayi ba,tuni ido ya raina fata,daga wasa!?
  Jijjigashi suka shiga yi atare suna ambaton sunanshi"Junaid!junaid!!!ka tashi!dan Allah junaid ka tashi!!Wayyo Allah munshiga ukun mu!!dan Allah baby junaid ka tashi," ko motsi wannan junaid baiyi ba,matsawa sehrish tayi tare da kanga kunnanta asaman hancinshi don taji in yana numfashi,ɗufff taji babu numfashi da sauri ta sanya tafin hannunta asaman kirjinshi saitin zuciyarshi nan ma taji zuciyar tashi tadaina bugawa,a wani irin sukwane ta ɗago da idanunta waɗanda sukayi luhu luhu cike tab da hawaye tana kallonsu Jahad da hosana,jiki a mace tace"ZUCIYAR JUNAID BATA BUGAWA HAKAN NA NUFIN MUNYI SILAR MUTUWAR JUNAID"!!!
  Girgiza kai jahad ta shiga yi tana cewa"Junaid bai mutu ba,dan Allah ki daina faɗan hakan,kada ya tabbata dagaske,"tayi maganar a yayin da take kai hannu tana tatta6a fuskarshi"junaid!junaid!ka tashi dan Allah ka tashi junaid,"
   Ganin yaƙi motsi yasa suka fidda rai da cewar junaid zai tashi,kifa kai sukayi su duka ukun suna shessheƙar kuka,ɗan ɗagowa jahad tayi tare da kai idonta kan fuskarshi,Abun mamaki sae ga murmushi ya bayyana akan fuskarshi,dimples ɗinsa guda biyu sun lotsa,Wani irin ihun farin ciki ta saki tana fadin"Bai mutu ba!junaid wasa yake yi mana,gayanan yana murmushi,'jin haka yasa su sehrish saurin ɗagowa da kawunansu suna kallonshi,sae faman wangale baki yakeyi yana dariya,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,
  "Junaid"sehrish ce ta ambaci sunanshi,a hankali ya buɗe manyan idanunshi yana kallonsu one by one,sai faman 6a66aka dariya yakeyi,
  Har suna haɗa baki wurin cewa"Kai junaid!meyasa zakayi mana haka?wlh ka tsoratar damu sosai,"
  "Wanda yasa kuka bugeni,ko tausayina bakuji,kun wani taru akaina kuna jibgata kamar kunsamu jaki amale,shiyasa nima na rama da gangan na ɗauke numfashina don kuyi tsammanin kona mutu"yayi maganar yana murguɗa masu baki,Ajiyar zuciya suka shiga saukewa,
  "Junaid dan Allah kayi haƙuri,bazan ƙara bugunka ba,kada ka faɗama kowa,"acewar hosana,
  Harara ya jefa mata tare da ƙara tamke fuskarshi,
  Cikin sanyin murya jahad tace"junaid baka da lafiya ne?mun ga jini ajikin pillow lokacin da muke bugunka,kuma da alama daga hancinka muka gogo shi,"
  Shiru ya ɗan yi yana kallonta kafin yace"Lafiyata ƙalau Ni,nose bleeding ne ba wani abu ba dama ina yawan yinshi,yafi zuwa mun da daddare,shiyasa baku ta6a gani ba"
  "Amma ka faɗama Abba ko wani game da nose bleeding din"? Girgiza kai yayi alamar a'a,da alama baison maganar,don haka yace"pls nidai mubar wannan zancen,kusan yadda za kuyi dani don Allah bazan iya komawa bedroom ɗina ba,tsoro ma nakeji,"yayi maganar ashagwa6e,
  Jiki asanyaye jahad ta kalli su sehrish tace"kuje ku kwanta,bari ni na rakashi ɗakin nashi," mikewa su kayi atare da ita da hosana suka koma kan gadon suka kwanta,tare da jan bargo suka lullu6e,
    Miƙewa daga zaune junaid yayi yana cewa"Allah sai dai ki goyani,don na riga dana faɗa maki cewa ƙafafuna ciwo suke yi mun bazan iya taka stairs ba,"
  Murmushi jahad tayi tare da cewa"shikenan,zan goya ka amma ka bari sai munje wurin benen tukunna in goya ka," amsa mata yayi da toh,sannan ya mike tare da ruƙo hannunta cikin nashi yace"Tashi muje,"mikewa tayi suka fita atare,suna tafiya tana satar kallon gefen fuskarshi kamar wani zautacce sai faman sakin murmushi yake yi,hakanan ta dinga jin gabanta na faɗuwa,lamarinsa ba ƙaramin mamaki yake bata ba,kokonto ta shiga yi anya wannan ɗigon jinin da suka gani na ha6o ne? Yanayin yadda abun ya afku tamkar ba jinin ha6o bane,tabbas akwai dae wani abu dake damunshi wanda baison kowa ya sani,
Tana cikin zancen zucin nata taji yace"Mun ƙaraso wurin stairs ɗin,yanzu ki goyani,ki kaini har bedroom ɗina,kuma ki kwantar dani,"
  Amsa mashi tayi da toh,sannan ta zuƙunna,ya daddage ya haye saman bayanta,tare da kwantar da kanshi luff kamar wani jinjiri,zagayo da hannayenshi yayi ta saman stomach ɗinta,hakan ba ƙaramin yanayi ya jefa ta ba,ji tayi tamkar bazata iya miƙewa tsaye ba,saitin kunnanta taji daddaɗar muryar nan tashi mai haɗe da shagwa6a"jahad ki tashi mu tafi,bacci nake ji,"
  Daƙyar ta iya mikewa tsaye goye dashi abayanta,hannu tasa ta tallaboshi sosai,sannan ta haye saman benen,tana tafiya tana tangal tangal har ta ƙaraso ɗakin nashi,hannu tasa ta ɗan tura ƙopar sannan ta shige ciki,Talal suka samu kwance yana ta sharar bacci,ƙarasawa tayi tare da sauke junaid saman gadon,ya gyara kwanciyarshi,bargo taja ta rufe mashi body ɗinsa zuwa neck ɗinsa,tana ƙoƙarin juyawa tabar wurin,taji ya ruƙo hannunta cikin nashi,jimmm tayi tana jiran jin me zaice mata,
  "Jahad"ya ambaci sunanta da wata irin murya ta mai jin bacci,
  "Na'am,"ta amsa mashi kiran a yayin da take juyowa" murmushi ya sakar mata tare da sanya yatsan hannunshi acikin dimple ɗin fuskarshi yace"Kiss me pls," bakomai ya faɗo mata aranta ba,face abunda ya ta6a faruwa atsakaninsu,cikin motarshi,daga zuwa manna mashi kiss a side face ɗinsa,bakinta ya goce izuwa cikin bakinsa,a ranar zauce mata yayi,
  Maƙe masa kafaɗa tayi alamar bazatayi mashi kiss ɗin ba,bubbuga ƙafarshi ya shiga yi yana yi mata shagwa6a,hakan ba ƙaramin burgeta yayi ba,saboda wani irin kyau da yake bayyana akan fuskarshi aduk lokacin da yake shagwa6a,tamkar tayi hugging ɗinshi ajikinta haka ta dinga ji,
   "Baza kiyi mun ba ko"?yayi maganar.yayin da idanunshi ke ƙoƙarin lumshewa,
   "Shikenan,zanyi maka,amma ka rufe idanunka," da sauri ya rufe su yana jiran jin la66anta asaman fuskarshi,tsayawa tayi asaman kanshi,tana karanto addu'o'i tana tattofa mashi akan fuskarshi,daga ƙarshe ta haɗe yatsun hannunta guda biyu na hannun damanta,a hankali ta aza yatsun nata asaman la66ansa,sannan ta furta sautin kiss ɗin da bakinta,wani irin farinciki ne ya lullu6e junaid,duk a tunaninshi bakinta ne ta aza asaman nashi,baisan cewa wayau tayi mashi ba,tasa yatsun hannunta amatsayin la66anta,
rufe mashi fuskarshi tayi da bargon,sannan ta kama hanyar fita daga bedroom É—in,
   "I Love u so much jahad," muryar junaid ce ta katse mata hanzarinta,dakatawa tayi tare da ɗan juyawa tana kallonshi,yana acikin bargon ya furta mata wannan kalmar,
   "Kina sona jahad"?
Wani irin ƙayataccen murmushi ne ya sauka akan fuskarta,bata bashi amsar tambayarba,cikin sauri ta fuce daga ɗakin nashi,ta koma bedroom ɗinsu ta kwanta zuciyarta cike fal da farin ciki,ta ji daɗin kalmar da junaid ya furta mata,duk da bata da tabbacin cewar ko dagaske yake yi mata," da wannan tunanin bacci ya ɗauketa,

  *Boss Bature*

    🤍❤🤍
Washe Gari,
Chapter 54 · 0% Book details