← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 212

Sashe 46

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ƙarasowa hafsat tayi ƙopar bedroom ɗin nasu,jikinta sanye da dogon hijabi,hannu tasa ta ɗan bubbuga ƙopar ɗakin,shiru ba'a buɗe ba,ƙara bugawa tayi,bugun ya isa cikin kunnan sehrish,cikin bacci tace"Wanene"?
Hafsat tace"Ni ce,"
"Kece wa"? Sehrish ta tambaya a yayin da ta miƙe tare da tunkarar ƙopar ta buɗe,Tun daga ƙasa har sama sehrish ke bin ta da kallo don batasan wacece ita ba,amma tabbas ta ta6a ganin fuskarta,kuma jiya taga gifcinta acikin gidan,ga kuma kamannin fuskar Yaya ishaq a fuskarta,
  ƴan kame kame hafsat ta shiga yi,muryarta na inda inda tace"am...um..jahad.." katse ta sehrish tayi da cewa"ba ita bace,Ni sunana sehrish,jahad tana ciki tana bacci,"
  "In ba damuwa inason ganinta,"
Matsa mata hanya sehrish tayi,ta shiga cikin ɗakin nasu,rufe ƙopar sehrish tayi sannan ta koma ciki itama,sae faman kallon kallo suke ita da hafsat,duk tabi ta kama kanta,kana ganin fuskarta zaka fahimci cewar bata da gaskiya,
  Wuri ta samu gefen gadonsu ta zauna,idanunta na akan su jahad da hosana dake ta sharar bacci,
  Muryarta a sanyaye tace"in ba damuwa,dan Allah ki tashe su daga baccin inason yin wata magana dasu mai mahimmanci,"
  Batare da musu ba,Sehrish tace toh,sannan ta haye saman gadon tana ambatan sunayensu,gami da bubbuga ƙafafuwansu"jahad!hosana!ku tashi ana son ganinku,"
  cikin bacci hosana ta buga tsoki tana fadin"dan Allah a ƙyale ni,kar a takuramin,"
  Jahad kuwa tuni ta farka,tana faman mutsustsuka idanuwanta,wurga idanunta tayi kan sehrish tace"Wai lafiya"?
  "Wannan ce ke son magana daku,"tayi maganar tana nuna hafsat dake zaune,
  Juyawa jahad tayi tana kallonta,cike da mamaki ta ambaci sunanta"Aunty hafsat!" sunnar dakai ƙasa hafsat tayi,fuskarta dauke da matsananciyar damuwa,daƙyar ta iya amsa mata"Na'am jahad,"tashi zaune jahad tayi,suna fuskantar juna ta sake ambatar sunanta"Aunty hafsat,"
  "Kinsanta ne"? Sehrish ce tayi tambayar,jahad tace"Niko na santa,itace ɗiyar wannan matar da nake faɗa maki wadda ta azabtar da rayuwarmu,kuma wannan itace ta ɗauke mu acikin motarta,ni da Hosana ta kai mu hannun wannan mugun mutumin wanda ya kai mu daji har yayi ƙoƙarin cutar da Hosana,"
  Jin wannan maganar yasa ran sehrish ya 6aci,harara ta wurga ma hafsat tare da nuna mata hanyar fita daga ɗakin tace"Dan Allah malama tashi ki fita ki bamu wuri!bamu son ganinki!mugaye kawai Azzalumai,kun cutar da rayuwar ƴan uwana,saboda son zuciya irin naku,basuyi maku laifin komai ba,Amma kuka tsangwamesu,saboda kunga basu da gata,Insha Allah sai kunga sakayyar da Allah zaiyi masu,kuma sai kun ɗanɗana irin uƙubar da kukayi masu,"
  Hawaye ne suka shiga zarya a fuskar hafsat,dama saida ranta ya bata cewar dakyar ne su yafe mata,
  Janye idanunta tayi daga kan sehrish ta mayar dasu kan Jahad,cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah ku yafe mun Jahad,nasan mun cutar daku,amma inaso ku sani bada son raina ba,na kaiku wurin wannan mutumin,Mommy ce ta sanar dani cewa Gidan marayu za'a kaiku,shiyasa har na ɗauke ku,kuma nayi hakan ne saboda tsoran karta halakar daku acikin gidan nan don ba yadda banyi ba akan ta kyale ku amman ta kiya,shiyasa ma na amince da akaiku gidan marayun ashe zubar daku tasa ayi,'
  "Ba zamu ta6a yarda da kalamanki ba,saboda tun farko baki nuna kina son mu zauna acikin gidan ba,ke da mommynki,shiyasa kuka haɗa baki ke da ita,kika fara yaudararmu kina nuna kamar kina son mu ashe,so kuke ku fitar damu daga cikin gidan,saboda rashin Imani Aunty hafsat kika damƙa mu a hannun wannan mutumin,to bari kiji Ya Omar ya kashe shi har lahira!!
  Gabanta ne ya faɗi rassss!hankalinta yayi mugun tashi,a kiɗime tace"Ya kashe shi!"
  Jahad tace"kwarai kuwa Ya Omar shi ne ya kama shi da hannun shi acikin gidan gonarsa,lokacin da yake ƙoƙarin keta haddin hosana,aikuwa ya fasa mashi kai,anan wurin ya zama gawa,'
    Tana kai ƙarshen maganarta sehrish ta ɗaura da cewar"tun yanzu kwara kusan inda dare yayi maku!don wlh Ya Omar bazai sassauta maku ba!muddin yaji cewar kune kukayi silar da har wannan mutumin ya ɗauki su jahad ya kaisu daji,sannan ku fara tunanin irin hukuncin da kuma zaku fuskanta a wurinshi!"
  Wani irin wahalallan yawu hafsat ta haɗiya,tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta,ba don komai ba sai don jin cewa An kashe mutumin nan!tun da har Omar zai iya kashe rai akan su hosana,tabbas ba ƙaramin so yake masu ba,kuma akansu zai iya hukunta kowa,yanzu su menene sakamakonsu?
  "Baku da wata mafita,shawara nake baku tun kafin hosana tayi maku tonan asiri,kwara kusan abunyi,don tace saita sanar ma Daddy da Ya Omar abunda kukayi mana!" jahad ce tayi maganar,
  Gaba ɗaya duk sun bi sun tsoratar da ita,la66anta har kerma suke wurin rokonsu tana cewa"Dan Allah ku yafe mun,wlh nayi dana sanin duk wani abu da mu kayi maku,har ga Allah ni bada sanina ba,mommy ce ta shirya duk wannan,Allah shine shaidata,bazan yi maku ƙarya ba,"sosai hafsat ke kuka,
Ruko hannun jahad tayi acikin nata tana fadin"jahad nasan kina da sauƙin kai,dan Allah ki yafe mun,wlh nayi nadamar abunda mu kayi maku ni da mommyna,nasan naƙi ku da farko amma daga baya naso ku sosai,kuma nayi kukan rashinku atare dani,lokacin da nagane cewa Mommy ba gidan marayu tasa akaiku ba,har faɗa sai da mu kayi da ita,ko isasshen bacci bana samu a lokacin saboda tunanin wani hali kuke ciki......"ƙarasa maganar tayi tare da sanya hannu tana share hawayen dake zuba a kan fuskarta,
  Shiru su kayi da alama jikinsu ya ɗanyi sanyi,Sehrish tace"Jahad,idan kinyi niyya ki yafe mata,'jinjina kai jahad tayi tare da cewa"Ni dama ban ruƙe ki araina ba Aunty hafsat,na yafe maki Allah ya yafe mana gaba ɗaya,"
  Amsawa tayi da "Amin,sannan tace"Hosana fa?dan Allah ku tashe ta inaso in nemi yafiyarta,"
  Hannu Sehrish takai tare da bubbuga ƙafarta,farkawa hosana tayi,idanunta sunyi suntum saboda bacci,
  "Hosana ki tashi,ga Aunty hafsat nan tana son magana dake,"jin an ambaci sunan Aunty hafsat yasa ta wartsakewa ta miƙe daga zaune,koda idanunta su kayi arba da fuskar hafsat,nan take ta murtuke fuska rai a6ace tace"Ni bana son ganinta,na tsaneta kamar yadda suka tsane mu ita da Mommynta,Aunty hafsat muguwace bata tsoron Allah,itace takai mu wurin wannan mummunan mutumin wanda yakusa kashe ....."katse ta jahad tayi da cewa"pls hosana just forget about the past,forgive her pls,Aunty hafsat tayi nadama,kuma bada son ranta ba ta kaimu wurin mutumin nan ba,Mommynta ce ta shirya wannan,"
  Maƙe kafaɗa hosana tayi alamar bata yarda ba,harara ta wurga ma hafsat ɗin tana murguɗa mata baki tace"Allah saina faɗama Ya Omar da daddy,ko kukan jini zatayi sai dai tayi,amma saina faɗa,saboda rashin Imani kamar wasu dabbobi haka kuka rufe mu acikin store babu abinci ga ƙishin ruwa,ko iska babu,amma ko ajikin ku mu rayu ko mu mutu wannan ba matsalarku bace,zafi kamar zai kashe mu,adaren ranar da muka kwana a store,ba don jahad tayi mun fifita ba da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya don rashin imani ku kuna can kuna shan A.c,wlh saina faɗama daddy....."fashewa hosana tayi da kuka,hada bubbuga ƙafarta,daga gani abun ba ƙaramin ciwo yake yi mata ba,ya tsaya mata arai,
  Gaba ɗaya jikinsu yayi wani irin sanyi,musamman hafsat,duk yadda taso ta shawo kanta amma abun yaci tura,hosana ta rantse ta maya akan cewar saita faɗa ma Ya Omar,hatta jahad sai da taso ta lallasheta,amma ina ƙarshe sai ta dinga ƙoƙarin bugun jahad din,
  Ganin haka yasa sehrish kallon hafsat tare da cewa"dan Allah kiyi haƙuri ki tafi kawai,hosana batasan ganinki,idan tana kallonki haukanta zai iya tashi,"
    Jiki asanyaye Hafsat ta mike,tana tafiya tana waiwayonsu yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,a haka har ta isa ƙopar ɗakin ta buɗe ta fuce da gudu tana kuka,
  Hannu Sehrish tasa tare da janyo hosana ta rungumeta sosai ajikinta tana lallashinta,da ƙyar ta samu hosana tayi shiru,sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,komawa su kayi suka kwanta kowa da abunda yake saƙawa aranshi,

*Aunty Babba*
Chapter 46 · 0% Book details