← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 212

Sashe 107

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Wuri Amani ta samu gefen gadon ta zauna,Amal kuma ta zauna saman plastic chair ɗin dake fuskantar gadon,a ƙasa ta ajiye kwandon hannunta,
a ruÉ—e Amani tace"Hayaam!meya faru dake haka?hatsarin mota kikayi ne"?
  Girgiza mata kai hayaam tayi alamar a'a,kasa buɗe baki tayi,saboda bata da amsar da zata basu ga kukan dake cinta,
    "Hayaam dan Allah ki sanar dani meya faru dake ne,Nayi mamakin ganinki ke kaɗai a asibiti a wannan halin,batare da Laila ba,"
  "Aunty Hayaam,Sannu ya jikin naki"?Amal ce tayi maganar fuskarta da alamun tausayinta,daƙyar ta iya amsa mata,Duk kunya ta rufeta,
   Cikin sanyin murya tace"Aunty Amani nayi danasanin rayuwata gaba ɗaya,Na tsani kaina,Komai ya fita raina,Ban yi tsammanin zaki zo ba,Har na fidda rai da cigaba da rayuwa acikin duniyar nan,Amma ganinku da nayi ba ƙaramin farin ciki nayi ba,"tana magana hawaye na zuba,
  Juyawa Amani tayi tare da kallon Amal tace"Ki jirani a waje,Zan kira ki,inaso muyi magana da hayaam,ki tafi da wayata,ko game ne ki buga,"
  Miƙewa Amal tayi tare da matsawa wurin Amani,ta kar6i wayarta,kafin ta kama hanyar barin ɗakin,
   mayar da hankalinta tayi sosai akan Hayaam tace"ina sauraronki,faɗamun meya faru dake?meyasa kike zaune a asibiti ke kaɗai batare da Laila ba?duk me ya jawo hakan"?a ƙagare Amani take da taji amsoshin tambayarta,
  Hayaam bata 6oye mata komai ba,Tun daga kan Abunda ya faru tsakaninta da haroon har izuwa farfaɗowarta da tayi a gadon asibiti,Hannu tasa tare da ɗaukar wasiƙar da ta cukuikuye agefenta ta miƙa ma Amani ita,kar6a Amani tayi a atsanake ta shiga karanta wasiƙar da Aunty babba ta rubuta mata,wasu irin hawaye ne suka soma shararowa daga kan fuskarta,Saboda tsabar ƙululun baƙin ciki kamar ta haɗiyi zuciya,
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!wannan wani irin rashin Imani da rashin tausayi ne?Anya kuwa laila tana son tagama da duniya lafiya?yanzu duk don saboda neman abun duniya ta tafi ta barki a gadon asibiti rai hannun Allah?Anya matar nan tana da Hankali kuwa?Ya salam"rai a6ace take maganar,abun ya ƙona mata ranta sosai,
  Hayaam tace"bata da imani,wlh duk rashin hankalina,banajin zan iya tafiya in bar Aunty laila a gadon asibiti,Amma haka ta haura ƙafa ta barni,Sai kace ba ciki ɗaya muka fito da ita ba......"kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da yazo mata,
  Itama Amanin kukan takeyi sosai,cikin shessheƙar kuka tace"Ha..hayaam ki faɗamun sunan wanda yayi maki wannan aika aikar,inason nasan Wani mara imanin ne"?
  Daƙyar hayaam ta tsagaita da yin kukan tace"HAROON ne ɗan gidansu Ya Abbas,Mijinki,"
  Saboda tsabar kiɗima a razane Amani ta miƙe tsaye hankalinta a matuƙar tashe take maimaita sunan haroon abakinta,
  Hannu ta aza akai tana faɗin"Nashiga Uku!Hayaam kina nufin haroon shine yayi maki wannan ɗanyen aikin"?ɗaga mata kai hayaam tayi Alamar eh,
   "Wlh bazan ta6a ƙyaleshi ba,Sai na tona mashi asiri wurin Abbas!Fasiƙi kawai mugu,dama ni bai ta6a kwantamun araina ba,Allah kaɗai yasan abunda yake aikatawa"ta ƙarasa maganar tare da komawa gefen gadon ta zauna,
  "Aunty Amani ki ƙyaleshi kawai,kada kice zaki tona mashi asiri,koma me ya faru dani laifina ne,Da ace tun farko na kama mutuncin kaina,da babu namijin da zai nemi aikata fasiƙanci dani,Zan yi haƙuri in rungumi ƙaddarata,Kibarshi kawai,Allah shi zai sakamun,"
  girgiza kai Amani ta shiga yi tare da cewa"Wlh bazan ta6a ƙyaleshi ba,Shikenan yaci bulus kenan?wannan mutumin fa,ba ƙaramin mugu bane,bai kamata a dinga ƙyale irinsu ba,Suna aikata abunda suka ga dama,batare da an yanke masu hukunci ba,Yanzu kika san irin matan da ya lalata ta ƙarfi ta tsiya kamar yadda yayi maki?shiru hayaam tayi tana sauraronta,
  "Dole ya gane kuskurenshi,kuma ni bazanso duk wani abu da zai 6ata sunan family ɗinsu ba,Yana so ya zubda masu mutuncinsu ne a idon duniya,Don haka dole na ɗauki mataki akanshi,"ranta a 6ace tayi maganar,tare da kai hannunta cikin food basket din da suka zo dashi ta zaro plate tare da warmer,Buɗe kular tayi,Soyayyan naman kaza ne acikinta wanda yaji uban kayan haɗi,sae ƙamshi ke tashi,tuni jikin hayaam ya soma rawa sai faman haɗiyar yawu take yi,kamar ta kaima warmer ɗin wawura haka take ji,. 
   Acikin plate Amani ta zuba mata naman tare da miƙa mata,Sannan ta dauko mata ruwa mai sanyi na roba,tare da fresh milk,ta shiga tsiyaya mata su acikin Cup,
   ganin yadda hayaam ke taunar cinyar kazar hada ƙashin duka take haɗawa,yasa Amani cewa"Ki ci a hankali mana,kada kija ma kanki wata matsalar,"kasa natsuwa tayi saboda yunwar da take ji,
  Sosai hayaam taci naman nan,tasha fresh milk ɗin mai sanyin gaske,sai da taci ta ƙoshi,sannan ta samu natsuwa,
  "Itama Laila bazan ƙyaleta ba,nasan cewa zata nemi Abra ne don ta rakata wurin bokan,wama yasani ko har sun tafi,Kuma ina da tabbacin cewar,bazata ta6a sanar ma wani cewa tabarki a asibiti ba,don kada a tuhume ta,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar kafin taci gaba da cewa"muguwar ashe ko ƙannenta da suka fito ciki ɗaya bata iya raga mawa,inajin tsoron tace zata kai Abra wurin fasiƙin Bokannan,don muddin takaita,zaiyi wuya bai nemi ya kusanci ɗaya daga cikinsu ba,"
  Jin wannan maganar yasa hankalin hayaam ya tashi,don ita yanzu tayi nadama,kuma tana jin tsoron halin da Aunty babba zata jefa Abra,kamar yadda tayi mata,

   "Yanzu ya zamuyi mu dakatar da Abra daga zuwa wurin bokan nan"?hayaam ce tayi maganar,
  "Ina ganin idan muka kira Abra muka sanar da ita abunda laila tayi maki na barinki a gadon asibiti,zata fasa bin ta ne,"
  Zama suka yi suna yanke shawarar yadda zasu dakatar da Abra,a ƙarshe suka yanke shawarar kiranta a waya,

*Boss Bature*

*JUNAID*

Tsaye yake a gaban dressing mirror,ya ɗauki wankan pakistan ajikinshi masu kyan gaske farare sun ƙara fito da hasken fatarshi,Fuskar nan har wani kyau ta ƙara,ya gyara sumar kanshi sosai ta kwanta luf a bayan wuyanshi,Slowly ya miƙa hannu gaban mirror ɗin ya ɗauki kwalbar turarenshi,yabi ko ina na jikinshi ya feshe shi,bayan ya mayar da ita,ya ɗauko wrist watch ɗinshi ta diamond da Hajiya azeema ta bashi,Yana ƙoƙari sanyata a hannunshi,Wayar shi ta soma ringing,da sauri ya ƙarasa sanya agogon,tare da tunkarar saman gadonshi inda ya ajiye wayar yakai hannu ya ɗauketa,tare da kollon screen ɗin wayar,Sunan Mommyn su ne ya bayyana akai,tur6une fuska yayi kafin ya ɗaga wayar,cike da shagwa6a ya soma magana"Mommy,ni fushi nake yi dake,"
On the other hand,Alexandra tace"haba romeo É—ina,why are u angry wit me?laifin me na maka da kake fushi dani"
   "Mommy,u forgot about me,tunda na dawo baki kira layina ba,babu wanda ya damu dani,"
  Cikin lallashi tace"Sorry my own son,pls kadaina fushi dani,"
  Bubbuga kafarsa yayi cikin shagwa6e yace"Nidai Mommy indai kina son farin cikina,Ki dawo gida kawai ke da daddy,dasu yaya Fawan,kowa ya dawo gida,nayi missing ɗinku sosai,"
   Alexandra tace"shi ne kawai abunda kakeso,"
  "Eh,adawo gida,acigaba da rainon baby junaid"yanayin yadda yayi maganar ba ƙaramin dariya ya bata ba,yana jiyo muryarta ta cikin wayar tana dariya,
Bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"Calm down ur mind,This week zamu dawo,"
  Fuskarshi ɗauke da farin ciki yace"Mommy pls,Ki tursasa daddy,ko da baya son dawowa,ni dai ku dawo gida kowa da kowa,tare da su yaya fawan,Twins su irfan and sister hafsat,inason ganin kowa a kusa dani,"
  "Don't worry ur self,my romeo kowa zai dawo saboda farin cikinka,"
Ba ƙaramin daɗi yaji ba
  Sun jima suna waya kafin daga bisani,su kayi sallama,ajiyar zuciya ya sauke tare da yin wurgi da wayar saman gadon,kwankwasa ƙopar bedroom ɗinshi akayi,da sauri yace wanene
  "My Romeo,its Me ur juliet,am ready for the outing,"wani irin ƙayataccen murmushi ya saki jin muryar jahad,
   A ƙagare yake daya ga wankan data ɗauka,jiki na rawa ya ƙarasa tare da buɗe mata ƙopar,Gabanshi ne ya faɗi rass,Tun daga kan takalman ƙafarta ya fara kallonta,High heels ne ƙafarta,farare,abun ya bashi mamaki ganin tayi shigar white gown,launin kayanshi daya sanya,tayi rolling veil akanta,lips ɗinta kuwa Red ta sanya masu,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga jikin ko wannansu,

  Ruƙo hannunta junaid yayi tare da janyota cikin bedroom ɗin,lumshe idanuwanshi yayi tamkar maijin bacci,da wata irin kasalalliyar murya,yace"Jahad,You look so beautiful,kayan nan sunyi maki kyau sosai,"
  Hannu tasa tare da shafa side face ɗinshi"Duk kyawuna ae bankai ka ba,kaifa na dabanne,ta ko'ina Allah ya baka,". 
  Aɗan shagwa6a yace"Amma ni bana jin kaina a matsayin cikakken mutun,"
  A ɗan ruɗe tace"Saboda me,'?
Hugging É—inta yayi tare da kai lips É—insa saitin kunnanta sannan yace"Saboda,ban mallake ki ba,sai dake ne zan zama cikakken mutun,'
  Wani irin matashin murmushi jahad ta saki,taji daɗin kalaminsa sosai,
   "Nikaina junaid,bana jin kaina amatsayin cikakkiya,har saina mallake ka,"
  kalaman soyayya suka shiga gayawa junansu,
Duk wannan abunda da suke yi akan idon Haroon wanda ke la6e,ya É—an buÉ—e kopar É—akin ya zuro kanshi yana kallonsu,
  Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Ta kwana gidan sauƙi,"yana faɗin hakan,ya rufo masu ƙopar ɗakin,hannu yasa tare da zaro wayarshi,Contact ya shiga,Tare da rubuta wasu numbobi,ya danna kira,tare da manna wayar asaman kunnanshi,
  Muryar wani kakkauran mutunne yace"Ya haroon,Ya ake ciki ne?ina fata kazo mana da labari me daɗi,"
  ƙasa ƙasa da murya haroon yayi don kada wani ya juyo shi,
   "Ka saurare ni dakyau,Yanzu junaid zasu fita tare da ƴar wurin uncle ɗinmu,Abunda nakeso daku,Karku kuskura ku ta6a lafiyar jikin yarinyar saboda ba akanta zamuyi aiki ba,Junaid kawai nakeso,Ku bi ta kan motarshi da truck,Yadda ko fuskarshi ba'za a gane ba,idan tayi dameji,"
  Fashewa mutun yayi da wata irin Mahaukaciyar dariya,hhhhhhhh kamar zai fasa screen ɗin wayar,Bayan ya tsagaita da yin Dariyar yace"AN GAMA OGA,SAI DAI UWARSHI TA HAIFI WANI,"
Jinjina kai haroon yayi tare da sakin shu'umin murmushin nan nashi yace"ku kasance a ankare,Yanzu zai fito da motarshi,banaso yaron nan ya dawo gidan nan araye,Gawarsa kawai nakeson gani,jaga jaga da jini,"

 

 [3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐
*MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI*💃🏻💃🏻
Chapter 107 · 0% Book details