← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 212

Sashe 144

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo takun tafiyar mutun yana tunkaro ɗakin,Ba shakka Azmee ce,A tsananin tsorace Sehrish ta katse kiran,gashi wayar akwai password,babu yarda za'ae ta goge kiran da akayin,dole idan aka shiga Call log agane cewa An ɗaga kiran da akayi,
A matukar firgice Sehrish ta tura wayar acikin drawer ɗin,Duk tabi ta ruɗe ta rasa inda zata dosa,A ƙarshe ta faɗa toilet ta rufe,tana faman sauke ajiyar zuciya,jijiyoyin wuyanta duk sun fito saboda tsabar tsoro,Tayi danasanin ɗaga kiran wayar Azmee da tayi,

A hankali Azmee ta turo ƙopar ɗakin ta shigo,Jikinta sanye da baƙaƙen kaya,Jallabiya ce tare da mayafinta,kamar wadda taje anguwa,zama tayi daga gefen gadon,tare da kai Hannu jikin drawer ɗin ta ɗauko wayarta,dannata ta shiga yi,kafin ta danna call,

Sehrish dake la6e acikin toilet ɗin da alama mutumin da ya kira Sehrish ta ɗaga shi Azmee ta kira,Addu'a sehrish tashiga yi hannunta na kerma ido ya raina fata,tuni zufa ta wanke mata fuskarta,Ga fitsari daya matse,ta kasa tsugunnawa tayi futsarin gudun kada azmee taji ƙarar fitarshi,
  Ba ƙaramin haushi Sehrish taji ba lokacin da Azmee ta soma Magana Cikin harshen fulatanci,taso ace da yaren hausa tayi maganar don ta samu taji abunda zata ce,yanzu ta ƙara ƙarfafa zarginta akan Azmee,

*Boss Bature*

Around 10pm

Jami'an da Sgr ya sanya su tsare grave ɗin Junaid,sunyi 6adda kama yadda kasan ba Sojoji ba,kowannansu na sanye da Kaya namu na hausawa,riga da wando na yadi,ɗaya daga cikinsu yana zaune saman dogon benci yayin da ɗayan ke zuƙunne agaban bencin gefenshi kayan Shoe shiner ne,Yana goge ma na saman bencin Takalminshi,dayake akwai hasken street light,Bakomai suke jira ba fa ce wannan mai zuwa yana yin zarya a ƙabarin nasa,bisa Command ɗin da Sgr ya basu nasu sanya ido akanshi idan ya ƙaraso,Su sanar dashi yana so yaga ko wanene,Suna zaman jiran zuwanshi,Aikuwa cikin sa'a ƙarfe goma na bugawa,kamar yadda ya saba zuwa,Sai motar nan ƙirar Venza ta shararo da gudu izuwa titin,tunkan ya ƙaraso ɗaya daga cikin sojojin wanda ke zaune saman Bencin yace"Gashi nan!yakamata mu sanar da Sgr,tun kafin ya kufce mana"
  Wanda ke goge mashi takalmin yace"sai munyi taka tsantsan if not zai gudu ne,"

Koda ya ƙaraso wurin ƙabarin slowly yayi parking ɗin Motar a gefen titin batare daya fito ba,

A hankali Sergeant ɗinnan dake zaune saman bencin ya ɗauko wayarshi tamkar yana dannata,message ya turawa Sgr,bayan ya kammala tura saƙon Ya mayar da wayar cikin trouser ɗinshi,

Buɗe murfin motar yayi tare da saukowa daga cikinta,kamar yadda ya saba zuwa haka yau ma yazo,Ya sanya face mask a fuskarshi yayin da idanuwanshi ke sanye da glass baƙi,Jikinshi na sanye da Crazy jeans tare da T-Shirt purple,tafiya ya soma yi har izuwa gefen bishiyar nan inda aka kewaye ƙabarin Junaid,tsayawa yayi kamar mai neman wani abu,hada ruƙe qugu,kusan minti 5 kafin ya soma zagaye bishiyar yana jinjina kanshi,

Miƙewa ɗaya daga cikin Sojojin nan yayi,A hankali ya nufe shi batare daya ankara ba,koda matashin nan Ya lura da cewa wani na tunkaroshi,Aikuwa da gudun gaske yabar wurin bishiyar,Sojojin nan suka bishi a guje,duk yabi ya rude ko motarshi bai tsaya ɗauka ba,a rikice ya faɗa saman titin yana gudun ceton rai kamar zai tashi sama,da gudu suma suka bi bayanshi don karya kufce masu,yana gudu yana waiwayen bayanshi,Unfortunately Yana ƙoƙarin karya kwana,Adai dai Lokacin Motarsu Sgr ta shawo kwanar,Kwatsam ya faɗama motarsu ta bugeshi sosai,ya saki wata irin razananniyar ƙara tare da zamewa ya faɗi wanwar ƙasa,Ƙarasowa Sojojin suka yi suna faman sauke ajiyar zuciya,Ta kwana gidan sauƙi,

Fitowa Sgr yayi daga cikin motar,Armstrong ma ya fito,Atare sojojin suka sara mashi,Kafin ɗaya daga cikinsu ya nuna saurayin dake a kwance ƙasa yana bullayi"Sir,Wannan shi ne wannan matashin dake zarya a ƙabarin ƙaninka,rashin gaskiya yasa yana ganinmu ya zabura zai gudu",

Zuba mashi ido Sgr yayi yana bin shi da kallon ƙurulla,tun kafin ma Ya cire mashi face mask ɗin fuskarshi,Ya shaida shi,zuƙunnawa yayi saman guiwarshi ɗaya,tare da kai hannu Ya zame face mask ɗin saurayin tare da cire glass ɗin fuskarshi Yayi throwing dinshi saman titin,runtse idanuwanshi yayi jikinshi sae kerma yake yi,

A hankali Ya furta sunanshi"HAROON" kamar bashi ba,Ya rame,yayi baƙi,jin muryar Sgr yasa haroon ware manyan idanuwanshi masu kama dana mujiya,koda yayi tozali Da Sgr a hargitse Ya tashi daga zaune yana kallonshi yayin da yake faman zazzare ido,wata irin zufa ce ta soma tsastsafo mashi agefen fuskarshi,. 
  "Dama kaine"?cike da mamaki Sgr yayi tambayar,
  Shiru Haroon yayi bai tanka mashi ba,
  "Me kake yi a wurin grave ɗin Junaid"
  Daƙyar ya iya furta"ƙabarin junaid kuma?yayi maganar tamkar baisan akan me suke magana ba,
  ɗagowa Sgr yayi tare da kallon sojojin dake tsaye suna ta faman haki"Zaku iya komawa bakin aikinku,"juyawa su kayi da sauri suka bar wurin,
  "U will explain it don ubanka,I have been suspecting you for a while,Zuba maka ido nayi kawai inga ƙarshen gudun ruwanka,abunda ka aikata ne yasa ka gaza samun natsuwa acikin ranka That's why kazo kana zarya akan ƙabarinsa"?

Waro ido haroon yayi amatuƙar tsorace Yayi yunƙurin miƙewa ya gudu,damƙar ƙafarshi Sgr yayi hakan yasa ya gaza motsawa,
  "Amstrong,ɗaukarmun shi ka sanyamun shi acikin mota,"

Gadan gadan Amstrong ya tunkareshi,Yadda kasan ƙaramin Yaro haka ya ca6eshi asaman kafaɗarshi,Ya turashi cikin motar Sgr,Front seat suka shiga,Sgr da Amstrong Tada Motar yayi da gudun gaske ya fisgeta,
"Wai ina zaku kaini ne?Motata fa?kun barta a wurin"shiru su kayi mashi babu wanda ya tanka mashi,
  "Wlh kada kuce zaku ta6ani,Rafayet ku sauke ni in kama gabana!Ni bansan akan me kuke magana ba"Sai faman sambatu yake yi,zufa duk ta wanke jikinshi"
  Har Lokacin basu tanka mashi ba,ƙoƙarin buɗe motar yayi donya buɗe,amma yaji ƙopar adatse ta ko'ina babu hanyar da zai gudu,

Da gudun gaske motarsu ta shigo cikin gidan A lokacin Sehrish na la6e cikin toilet ɗin Azmee,Har cikin kunnanta tajiyo sautin Shigowar Motar Sgr,kamar ta fasa ihu haka take ji ga Azmee taƙi yin bacci bare ta lalla6a ta gudu,Sae dannar wayarta take yi,Yadda kasan tasan da zaman wani acikin ɗakin,

Window ta hango acikin toilet ɗin,Da gudu ta nufe ta,so take ta leƙa window ɗin don taga idan shi ne ya dawo dagaske,net ne ajikin tagar,kuma tagar tayi nesa,Tsawon sehrish bazai kai ta leƙa tagar ba,Lalla6awa tayi cikin sanɗa ta ɗauko bokiti,Ta kifa shi ajikin bangon,Sannan ta daddage ta haye saman bokitin cike da tsoran karya fashe bokitin,

Ƙura idanuwanta tayi tana leƙan wajen gidan daƙyar take hangen wurin da motar Sgr take,fitowa yayi daga cikin motar tare da zagayawa ya Shaƙo wuyan rigar haroon ya wurgo shi waje,gaba ɗaya ya kife ƙasa a susuce,Gabanta ne ya faɗi rass!lokacin da taga Ya damƙo rigar haroon,Tabbas ranta na bata cewar Sun kamoshi ne a matsayin me laifi!tsoranta kada Sgr yayi kuskuren raunata shi,wata'ƙil Sunji kalamanshi ne dayake cewa zai kashe Farin cikin mutanen gidan Shiyasa suke tuhumarshi,kamar ta bur6a tagar ta fito haka take ji,

Ɗaukarshi Sgr yayi asaman kafadarshi Ya wuce dashi cikin gidan Amstrong na biye da bayanshi,ɗakin horon nan nasu Ya shiga tare dashi,ɗakinda idan aka rufe ƙoparshi ko ihun mutun ba'aji,

Sauke shi yayi yana tangal tangal Zai faɗi ƙasa,Nuna mashi ɗaya daga cikin kujeru biyu dake kallon juna yace"Ave a seat,magana nakeso nayi dakai,"
  "Nifa bansan komai ba!meyasa ka shigo dani wurin nan"?
Wani irin kallo da Sgr ya wurga mashi yasa shi lalla6awa ya zauna,jikinshi nata kerma,kai cike da iskanci ga shegen tsoro

Zama Sgr yayi suna fuskantar juna yayin da Amstrong ke atsaye yana kallonsu,

  Sai faman mazurai haroon keyi,irin na marasa gaskiyar nan,
  "Meyasa ka aikata hakan"?girgixa kai ya shiga"Ni wlh ban aikata komai ba,Nifa bansan komai ba,bansan akan me kake magana ba"
  Tsabar takaici ne yasa sgr ware yatsunshi Biyar ya kwasa mashi mari asaman fuskarshi,nan take le6enshi ya fashe,hannu yasa ya dafe kuncinshi saboda zafin daya ji,

"Ka faÉ—amun meyasa ka kashe junaid"?
    "Rafayet ba zaka ta6a jin komai ba,a abakina"Duk da halin da yake ciki hakan baihana shi gaya magana ba,
..rai amatuƙar 6ace,Sgr Ya damƙi kwalar rigashi da iya ƙarfinshi na ƙarshe ya daddaɗao da haroon a zafafe ya tunkari faskeken Madubin dake a aɗakin,Gaba ɗaya ya rotsa kanshi acikin glass ɗin,Wata irin gigitacciyar ƙara Haroon ya fasa yana fadin"Nashiga uku!Rafayet ka kashe ni!Na bani Na Lalace!!!.."kafin Haroon yayi wani yunƙurin kwace kanshi tuni Sgr ya ƙara Tarwatsa kanshi Acikin glass ɗin madubin,Nan take jini Ya soma tsastsafowa Asaman kanshi,Ya hada mashi Jini da Majina,Fitsari ya saki a wando ya shiga zubowa Zirrrrr yana kawarara Yaji bala'e,
  Naushin cikinshi sgr ya shiga yi gaba ɗaya,Duk In ya naushe shi sai Jini ya fito ta bakinshi,Ganin yana ƙoƙarin kashe shi yasa Amstrong Yin saurin dakatar dashi Ta hanyar ruƙo damtsen hannunshi"Allah ya huci zuci zuciyarka,Bai kamata ya mutu a yanzu ba,Still bamu samu bayanan da muke son samu a wurinshi ba,"
Ranshi amatuƙar 6ace yake magana"Kabarni in kashe wannan mugun mutumin Mara imani da tausayi!In har ban kashe shi ba,bazan samu kwanciyar hankali ba,Bazan cigaba da jure ganinshi yana yawo araye ba,
  Haroon dai tuni ya fita hayyacinshi sai faman ambaton Innallahi wa'inna ilaihirraji'un yake yi acikin bakinsa kamar wani musulmin ƙwarai,Jini duk ya wanke mashi fuskarsh,
  Daƙyar Amstrong ya samu ya shawo kanshi,Ya haƙura da zancen kashe haroon,Zuƙunnawa yayi agabanshi Yana kallonshi,Idanuwanshi tuni sun jima da juyewa,Yayi bleeding sosai,
  "Sir!ya rasa jini sosai,Yakamata Abashi Emergency treatment,don ya dawo cikin Hayyacinshi,idan yaso sai mu tuhu me shi daga Baya,
   Hannu Sgr yasa tare da kinkimar haroon ya wuce dashi medical Room ɗinsu,Ba don yaso ba haka ya shiga duba shi,Uban bandage ne akan goshinshi,duk ya cire mashi pieces na gilashin daya Sossoke shi,biji biji yake kallonsu
Chapter 144 · 0% Book details