← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 212

Sashe 198

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ajiyar zuciya jahad ta sauke,shaf shaf ta É—auko kaya cikin wardrobe ta zura ajikinta,

*Boss Bature*

*Reeshraf*

Sannu a hankali bacci ya É—aukesu,rungume da juna,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi,a Lokacin da Mommy azeema tazo part din nashi,sallama ta fara yi shiru ba'a amsa mata ba,ranta ya bata cewa ko suna a cikin bedroom ne,Shiga cikin palourn tayi babu kowa,kaitsaye ta nufi wurin sofas É—in,A saman table ta sauke masu trayn,yanke shawarar zuwa tadasu tayi,can kuma tayi tunanin yiwa omar magana,Ya kira shi a waya,don ya sanar mashi an kawo masu breakfast,

Sun yi nisa acikin baccinsu,wayar Sgr dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,a hankali ya buɗe idanuwanshi masu ɗauke da bacci don bai ishe shi ba,akan fuskar sehrish ya saukesu,zuba mata ido yayi yana kallonta,sosai ta shige mashi,ta ƙanƙameshi,sai jan numfashi take yi,lumshe idanuwanshi yayi tare dakai hannu ya shafa sumar kanta,kafin ya manna mata kiss asaman forehead ɗinta,
  "I love u.....'ya furta ƙasa ƙasa da muryarshi,har kiran yayi rejecting wani kiran Ya kuma shigowa,Hannu ya miƙa saman drawer ɗin ya ɗauki wayar,tare da duba sunan mai kiran nashi,Omar ne,picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnashi,
  "How are u my own bro,"
Muryarshi a kasalance yace"Am ok,ya kake?
  "Lafiya lou,jiya banji ya kuka ƙare da mutuniyar taka ba,"
Murmushi sgr ya saki,É—ayan hannunshi na acikin sumar sehrish yana wasa da ita yace"nasan duk kai ka shirya wannan,bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin gode maka,
  Omar yace"ae ba komai,duk yiwa kaine,"
  "Tana tare dani,na samu kwanciyar hankali,yanzu haka ma kiran wayarka ne ya tashe ni,"
  Cike da zolaya Omar yace"Ya maganar tafiya U.s ɗin?ɗazu nazo part ɗinka,na samu trolley ɗinka ajiye,"
   "Ka fara ko"?
Dariya omar yayi"Nifa nayi tunanin yanzu haka jirginka ya sauka los angeles,"
   dariya Sgr ya ɗanyi,kafin yace"don't worry ur self,tunda na samu abunda nakeso,Very soon zamu tafi,"
  "Kada na takura maka,naga jiya bakaci abincin kirki ba,Ga break fast nan a palour an ajiye maku,kaida Babynka,"
  Ƙayataccen murmushi sgr ya saki tare da cewa"thank u Omar,"
  "Aunty azeema yakamata kayiwa godiya,duk ita ta shirya wannan,"acewar Omar,
  "Okey,zanje na same ta,"ya ambaci hakan yayin da hannunshi ke asaman wuyan sehrish,yana shafa shi,laushin skin ɗinta ba ƙaramin fusgarshi yake yi ba,
  "Sai anjima,but karka manta,kuyi feeding ɗin juna,hakan yana ƙara danƙon soyayya,"ya ƙarasa maganar muryarshi da alamun dariya yayi rejecting kiran,"yaji daɗin shawarar Omar sosai,don kuwa yana cikin tsarinshi,
  Ajiye wayar yayi saman drawer ɗin,a hankali ya matsar da fuskarshi saitin fuskar sehrish,saitin kunnanta yakai bakinsa,cikin raɗa ya ambaci sunanta"Reesh,can u hear me"?
  Shiru bata  Motsa ba,hannunshi ya sanya yana ɗan shafa bayanta,yaci gaba da ambaton sunanta cikin raɗa,har sai da Sehrish ta fara mutsu mutsu zata farka,tukunna ya janye kanshi daga saitin nata,
Biji biji ta fara ganinshi lokacin da take ƙoƙarin buɗe idanuwanta,ya tasa ta gaba yana kallonta,lips ɗinta duk sun bushe,still akwai jirwayen hawaye akan fuskarta,
   A hankali ta ambaci sunan shi"Ya rafayet,are u with me,"
  Shafa gefen fuskarta yayi"My wife,am sorry nayi disturbing dinki ko?na katse maki bacci"?
  Lumshe idanuwanta ta ɗanyi sun marairaice,
  "I know you're feeling hungry,that's why na tashe ki,"ya ƙarasa maganar,tare da kai hannu ya shafi cikinta,
  A hankali ta furta"Ina jin yunwa sosai,amma nafi buƙatar yin wanka,jikina duk babu daɗi,"yadda take magana tana ɗan yamutsa fuskarta,ba ƙaramin yanayi take jefashi ba,daurewa kawai yake yi,
  Miƙewa sukayi zaune saman gadon ganin tana ƙoƙarin ɗaukar hijab ɗinta yasa shi yin saurin cewa"Ba anan zaki yi ba"?
  Jinjina mashi kai tayi alamar eh,ɗaure fuskarshi ya ɗanyi alamar baiji daɗin maganarba,
  "Why ba zaki yi using da toilet ɗina ba,"?
"Idan kanaso,Sai nayi,"
Ta6a bakinshi ya É—anyi"Sai inaso"?
  Girgiza kai tayi"Am Sorry,"
Ta ambaci hakan tare da saukowa daga saman gadon ta nufi toilet dinshi,ji yake tamkar yabita yayi mata wankan,amma yana jin shakkar ta6ata yanzu gudun kada a koma yar gidan jiya,ta burkice mashi tace Jikinta yake so,

Shiga toilet ɗin sehrish tayi tare da jan ƙopar ta rufe,saukowa sgr yayi daga saman gadon ya dawo bakin ƙopar toilet ɗin,ya jinginar da kanshi,don ya dinga jin motsinta,

Yana jiyo sautinta tana fadin"Assh..wash,"kamar ya faÉ—a toilet É—in ya taimaka mata tayi wankan haka yake ji,

After some muninutes yaji motsinta a bakin ƙopar,komawa yayi gefen gadon ya zauna,yana jiranta,a hankali ta buɗe ƙopar,ta zuro ƙafarta kafin ta ƙarasa fitowa daga ciki,hannunta ruƙe da rigarta,skirt ɗin tajashi har saman ƙirjinta,gashin kanta duk ya rufe mata bayanta da gefen fuskarta,natsuwa yayi yana kallonta batare da ƙiftawa ba,
   Tunda ta ɗago suka haɗa ido dashi,tayi saurin kawar da idonta,wani irin nauyinshi taji,

"Zan jiraki a palour,idan kin kammala shiryawa ki same ni acan,"
  Amsa mashi da toh,kafin Ya miƙe ya fuce daga ɗaikin,zubawa mirror ɗin ido tayi ganin babu glass ajikinshi,bata kawo komai aranta ba,mayukanshi na jiki masu ƙamshi tashiga shafe jikinta dasu,hada turarenshi ta fesa,bayan ta mayar da rigarta,sai da ta fara ɗaukar hijab dinta ta zurata,tukunna ta fito daga ɗakin,A saman Sofa ta same shi,ya jingina bayanshi jikinta,yayin da idanuwanshi ke a lumshe,a tsanake ta samu wuri gefenshi ta zauna,kafin ta ambaci sunanshi cikin sanyin murya"Yaya rafayet,"
  Buɗe idanuwanshi ya ɗanyi a hankali yana kallonta"har kin kammala,"ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
  Yana ƙoƙarin kai hannu yayi serving dinsu tayi saurin rigashi"Zan zuba mana,"wani irin kallon so suke bin juna dashi,zama su kayi gwanin ban shawa'a tana bashi abaki yana bata,atare suka ciyar da junansu,bayan sun kamala cin abinci,ta faɗa mashi cewa zata je ta canza kayan jikinta,tana ƙoƙarin miƙewa ya ruƙo hannunta,tare da janyota ta faɗo saman laps ɗinshi,matsa hancinshi yayi asaman suman kanta"when are u coming back"?yayi tambayar cikin sanyin murya,kafin ta bashi amsa ya kuma cewa"kona minti ɗaya kikayi nesa dani,zanyi missing ɗinki sosai,'gaba ɗaya ya kashe mata jikinta,sae faman sauke ajiyar zuciya take yi,hannayenta duka biyun suna a dafe dashi,
   "Zan dawo da anjima,"
"Promise me,"ya ambaci haka yayin da yake shafa sumar kanta da hannunshi,
  "Nayi maka alƙawari,"jinjina kanshi ya ɗanyi,Okey,zan zuba ido naga zuwanki,idan ma baki zo ba,Ni zanzo,don na baki maganinki"ba don yaso ba,ya saketa,ta mike tare da kai hannu ta ɗauki tray ɗin kayan abincin da suka kammala ci,a hankali take tafiya,yayin da ranta ke bata cewa yana kallonta,

Sai da takai bakin ƙopar,ta ɗan dakata dayin tafiyar,juyawa tayi don ta saci kallonshi,karaf suka haɗa ido dashi,murmushi ta sakar mashi,shima ya mayar mata da martanin murmushi na gefen fuska,dimple ɗinshi ya lotsa,juyawa tayi da sauri ta fuce daga ɗakin,

Tana tafiya tana tunaninshi sai kace ba yansu suka rabu dashi ba,tsananin ƙaunarshi take ji acikin zuciyarta,kitchen ta fara zuwa ta ajiye tray ɗin hannunta,kafin ta koma besdroom ɗinsu,kaitsaye ta faɗa saman gadon,yayin da idanuwanta ke kallon sama,A hankali ta furta"I luv u so much Ya rafayet,Mijina nakaina"

A 6angaren hosana kuwa,Lokacin da taje Kai ma Omar abinci,Cike da zumuɗi ta zabga sallama hannunta ruƙe da tray,sae faman zabga murmushi take yi,kamar wata zautacciya,kamar yadda ta saba shiga ɗakin shi ko sallama babu,a haka ta faɗa ciki sai da tashiga tukunna tayi sallamar daga baya"Assalamu Alaikum"a lokacin yana kwance saman gadonshi,hannunshi ruƙe da wayarshi,ɗagowa yayi tare da kallonta,wani irin kyau yaga tayi mashi,miƙewa yayi daga zaune yana kallonta batare da ƙyaftawar ido ba,gaba ɗaya ta tafi da imaninshi,ganin ya ƙura mata yasa ta ɗan turo baki tare da cewa"Ya omar,wai lafiya kake kallona,"
Ajiyar zuciya ya É—an sauke tare da cewa"hosana,wa yayi maki kwalliya?
"Ni nayi abunda,"
"Amma dai,ni akayiwa kwalliyar ko"?
Murmushi ta É—an saki tare da É—aga mashi gira alamar Eh,
  Ba ƙaramin daɗi yaji ba"Ki kaimun abincin falo,Yanzu zo muci tare ,
  Da sauri ta juya,tana shiga ta sauke tray ɗin a saman table,jiki na rawa ta zura hannunta cikin bra,ta zaro paper din da jahad ta rubuta mata kalaman soyayya,
  Karantawa ta farayi don ta samu ta haddace wasu kafin ya fito,
  "Ya Omar,inasonka so irin wanda uwa keyi ma jaririnta,kaine mutun na farko dana ji ya kwanta mun araina,nakeson kasancewa dashi na har abada,A matsayin mijina uban ya'yana,"tana cikin karantawa Tajiyo mutsu mutsun fitowarshi,A ruɗe ta nannaɗe takardar ta turata acikin bra ɗinta,

Ƙarasowa cikin falon yayi,hannu yasa ya ɗauki tray ɗin data ajiye saman table ɗin,Ya sauke shi saman carpet don suji daɗin cin abincin atare,
Chapter 198 · 0% Book details