← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 212

Sashe 78

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wuraren sallar asuba,Jahad ta fito daga ɗakin azmee tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinsu,idonta suka sauka akan sehrish dake kwance a ƙasa,gashin kanta duk ya rufe fuskarta,da ƙarfi ta ambaci Sunanta SEHRISH,da gudun gaske ta ƙarasa tare da zubewa saman guiwowinta agaban sehrish ɗin,
  "Innalallahi'wa'innalairrahiji un,Sehrish!meya faru dake ne!nashiga uku!Aunty Azmee!!!"duk tabi ta ruɗe,musamman data ga jini ya 6ata wandon sehrish ɗin,sai tayi tsammanin kodai taji wani mummunan rauni ne,Jijjiga jikinta tashiga yi tana cigaba da kwalama Azmee kira,
   "Aunty azmee!Hosana!dan Allah kuzo ku dubamin!meya faru da sehrish ne!"
   A ruɗe ta miƙe tare da tunkarar ɗakin azmee,tura ƙopar tayi ta faɗa ciki a hargitse,Adai dai lokacin Azmee ta kammala sallar asuba,juyowa tayi tana kallon jahad ganin hawaye asaman fuskarta yasa ta miƙe da sauri ta tunkareta tana tambayarta
   "Jahad lafiya meya faru ne"
  Muryarta har shaƙewa takeyi wurin ambaton sunan sehrish"Aunty azmee sehrish!bansan meya faru da ita ba,gata can kwance a ƙasa bata motsi,ga jini a jikin wandonta....."tunkan taƙarasa maganar Azmee ta zabura da gudu ta fita daga ɗakin,itama jahad ɗin tabi bayanta da sauri,
  Ƙarasawa azmee tayi wurin da sehrish take akwance,ta zuƙunna tana ƙare ma jikinta kallo,tsananin tausayinta ne ya kamata,Allah kaɗae yasan tun yaushe take kwance a wurin cikin halin ha'ula'e,
   Hannu tasa tare da shafa fuskarta,busassun hawayene asaman fuskarta,la66anta duk sun bushe ƙamas dasu,
É—agowa tayi tare da kallon jahad dake tsaye tana kuka,
   "Ki kwantar da hankalin ki,ina tunanin suma tayi ne sakamakon Ciwon cikin da tayi,Jinin dake ajikinta na al'ada ne,"
  Jin haka yasa jahad ta tsagaita da yin kukan,har hankalinta ya ɗan kwanta duk da akwai sauran damuwa atattare da ita,
  "Aunty azmee duk laifin mu ne ni da hosana,da ace bamu tafi mun barta a ɗaki ita kaɗai ba,da duk hakan bata faru ba,Allah kaɗae yasan tun yaushe take kwance a wurin nan,"
   "ɗaukomin ruwa,in yayyafa mata,"
Da sauri jahad ta nufi fridge dinsu,hannunta har kerma yakeyi wurin yin saurin ta buɗe,bottle water ta ɗauko,sannan ta dawo wurin azmee ta miƙa mata,kar6a tayi ta 6alle murfin ta ɗan kur6i ruwan abakinta sannan ta fesar dashi asaman fuskar sehrish,
  Dogon Numfashi taja,tare da sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,muryarta ƙasa ƙasa tashiga fadin"Cikina zafi,Ciwo yakeyi mun!dan Allah abani magani nasha,kada na mutu,"
  "Jahad dauko mata magani,yana nan ajiye saman drawer ɗina,"juya jahad tayi da gudu ta nufi ɗakin azmee,
    Hannu azmee tasa tare da ɗago da kan sehrish ta azata asaman laps ɗinta,kafa mata ruwan tayi abakinta,a hankali tashiga kwankwaɗar ruwan,dama makoshinta a bushe yake,
   Dawowa jahad tayi hannunta ɗauke da maganin ta miƙa ma Azmee, bayan ta kar6a ta curo mata shi guda biyu ta sanya mata abakinta,tare da ruwan ta haɗiya,
  Bayan ta kammala sha,ta mika ma jahad robar ruwan"ki mayar dashi a fridge,bari na taimakata mu shiga daga ciki,"
   Dakyar ta cuccu6i sehrish,don ma ba wani nauyi ne da ita ba,cikin bedroom ɗin nasu ta shiga da ita,Jahad tabi bayansu,
  Toilet tashiga da ita,jahad sae faman zirga zirga take yi acikin bedroom ɗin nasu,duk wannan budurin da akeyi hosana nacan ɗakin azmee naɗe cikin bargo tana bacci,
   Muryar azmee tajiyo daga cikin toilet ɗin tana yi mata magana"Pad zaki miko mun,tare da pant ɗinta,"_
  Jiki na rawa jahad,ta ƙarasa gaban wardrobe ɗinsu,wurin kayan sehrish ta ɗauko mata pant,sannan ta haɗo mata tare da pads,
   Abakin ƙopar toilet din ta tsaya tare da ɗan knocking kopar,zuro hannu azmee tayi ta kar6i kayan,
  Komawa jahad tayi saman gadonsu,ta zauna tana jiran fitowarsu daga cikin toilet ɗin,
  Within mins,Azmee ta fito daga cikin toilet ɗin,hannunta dafe da sehrish,duk ta rurruketa gudun karta faɗi,Waist dinta na ɗaure da farin towel,sae faman cizon la66anta takeyi,saboda raɗaɗin da take ji har lokacin bata dawo cikin hayyacinta ba,
  Asaman bed ɗinsu Azmee ta kwantar da ita,jahad ta yafa mata bargo asaman jikinta ta lullu6eta,
  "Sannu sehrish,Allah ya baki lafiya," acewar jahad,
   Dama ance ciwon ƴa mace na ƴa mace ne,su da suka son zafin abun gashinan sun taimaka mata,saboda suma sunayi kuma sunsan cewa lalurace,sannan sunsan irin raɗaɗin da takeji ajikinta,dayawa Wasu mazan basu son ya abun yake ba,tunda bayi sukeyi ba,shiyasa har suke ganinshi amatsayin ƙazanta,kuma basu yi ma mata uziri,aduk lokacin da sukayi kuskuren da jini ya bayyana ajikinsu,Wasu mazan nake nufi ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,Haka matan ba,bakowa bace ke taimakon ƴar uwarta ba,acikin irin wannan yanayin na period,
   "Sannu Allah ya baki lafiya,"azmee ce tayi maganar,yayin da idanuwanta ke akan sehrish,wadda ta runtse idanunta tana ta faman ciccije la66anta,
   Bata bar ɗakin nasu ba,har saida bacci ya ɗauki sehrish sannan tayi masu sallama,
  Kwanciya jahad tayi agafenta,suna fuskantar juna,zuba mata ido tayi tana kallonta,cike da so da ƙauna,
   A haka har bacci ya dauketa,

A 6angaren Sgr kuwa,ko sallar asuba bai samu ya halarta ba,Acikin bedroom ɗinshi yayi sallar,komawa yayi saman katafaren gadonshi ya kwanta yayin da blue eyes dinshi ke kallon Ceilling,Kalaman sehrish ne suka shiga dawo mashi acikin zuciyarshi,bakomai ne yafi tsaya mashi aranshi ba fa ce kalmomin nan guda biyu da ta kirashi dasu,MARA TAUSAYI MARA IMANI!sannan kuma tayi comparing ɗinshi da wannan fasiƙin mutumin, yaji raɗaɗin abun sosai acikin zuciyarshi,tayi matuƙar ɗaure mashi kai,Ko a ina tasamu ƙwarin guiwar gaya mashi magana?duk irin yadda take jin shakkarshi?yarinyar da ko cikin idonshi tsoran kallo takeyi,balle har ta ɗaga mashi yatsa,
    Gyara kwanciyarshi yayi,ya koma yana fuskantar right hand ɗinshi,sannu a hankali bacci ya dauke shi batare da ya shirya yin shi ba,
Chapter 78 · 0% Book details