← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 212

Sashe 118

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Around 1:30 na rana,
Zaune take asaman Sofa ta zabga Uban tagumi,tunda Daddynsu ya sanar da ita game da tafiyar Sgr Abuja,take jin kanta kamar ba cikakkiyar mutun ba,Bataso tafiyarshi ba,duk da ta yi mamakin tafiyar tashi,kewarshi duk tabi ta lullu6eta,ga kewar gida yau 3 days kenan suna a kano,Yanzu gidan ya rage daga ita sai Oummansu,tun kafin a fara kiran sallah,Maman sadeeq suka koma gidansu,Abusufyan ne ya É—aukesu acikin motarshi,hannu takai tare da É—aukar wayarta dake ajiye agefenta,Contact ta shiga tare da lalubo numbar jahad ta buga mata kira,
  Guntun tsoki taja,jin layin nata a kashe,Layin Junaid ta kira Shima a kashe,hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba,Layin Hosana ta kira,a lokacin sun kammala haɗama Omar breakfast ɗinshi,har ta koma ɗaki ta shiga toilet tayi wanka,tana zaune gaban mirror tana kwalliya jikinta sanye da gown,wayarta dake ajiye saman drawer ta soma ringing,duk a tunaninta ya Omar ɗinta ne,jiki na rawa ta miƙe hada tuntu6e wurin yin saurin ɗaukar wayar,koda taga kira daga Sehrish ne,jiki na rawa tayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanta,
  Tunkafin Sehrish tayi magana,hosana ta ruga ta cewa"Wai yaushe zaku dawo ne?gidan fa ba kowa ni kaɗaice,
   "Hosana wai ina jahad ne?ina kuma junaid?basu dawo daga shan ice cream ɗin bane tun jiya da suka fita?na shiga damuwa saboda rashin samunsu a waya,"
  Hosana tace"Nima bansan inda suka je ba,babu fa kowa gida,daga ni sai Aunty azmee,ya Omar bansan shima ina yaje ba,"
   Hankalin sehrish yayi matuƙar tashi,la66anta na kerma tace"Hosana!yaya Rafayet baizo nan gidan ba"?
  "Eh,baizo ba,ni banga kowa ba,"
Nan take ranta ya bata cewa wani abu ya faru acikin gidan,kuma bada kowa ya faru ba,fa ce Su Junaid da suka fita shan ice cream,saboda rashin dawowarsu cikin gidan
  "Rishi ko breakfast na gaza ci,ina cikin matsananciyar damuwa,"
  Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke tare da cewa"Hosana ki kwantar da hankalinki,Zasu dawo cikin gidan ne,Yanzu zan sanar dake wani abun farin ciki nasan zaki ji daɗi sosai,
   Muryarta aɗan shagwa6e tace"toh faɗamun menene"
   Sehrish ta miƙe tare da nufar ɗakin Oummarsu tana faɗin"Nasan Daddy bai sanar dake ba ko"?
Hosana tace"meke nan"?
Shiga cikin É—akin tayi wayarta manne a kunnanta,
  Video call ta mayar da kiran nasu,bayan ta samu wuri ta zauna gefen Oummansu dake ta bacci hankalinta a kwance,
  "Hosana kalli ki gani,Wacece wannan,"tayi maganar tare da saita Screen ɗin wayar saitin fuskar Oummansu,
  Ƙura ido hosana tayi tana kallon fuskar oummasu,almost 7 mins,a hankali wani kyakkyawan murmushi ya bayyana akan fuskarta,a ruɗe tace"rishi Oumman mu ce ko?
   "Eh itace,naso na sanar dake tun jiya,baki dauki wayan ba kuma bansamu halin sake kiran ba,An samu Oummanmu,Amma bata acikin hayyacinta ta samu ta6in hankali,
  Uban tsalle hosana ta daka,da gudun gaske ta fito daga ɗakinsu,kaitsaye ta nufi kitchen inda ta baro Azmee tana gyare gyare,Cikin rashin sani Hosana taci karo da haroon,ta bangaje shi sosai har wayar dake hannunta ta kubce mata,kaitsaye ta faɗi ƙasa ta daki Tiles Screen ɗin ya fashe,
  Hannu hosana ta aza asaman kanta ta fashe da wani irin matsanancin kuka,tana faɗin"Wayyo Allah wayata!Ka kashe mun wayata,Wlh bazan yafe maka ba,Allah ya isa,"
  Rai a6ace haroon ya ɗaga hannu zai mareta,adai dai lokacin Azmee ta fito daga kitchen ɗin,A ruɗe ta ƙaraso ta damƙi hannunshi,wani mugun kallo daya jefa mata sai da gabanta ya faɗi rass saboda launin idanuwanshi da sukayi jawur dasu,fuskar nan tashi tayi suntum da ita,da sauri azmee ta saki hannunshi,cikin sanyin murya tace"Allah ya huci zuciyarka,"
  Harara ya wurga mata tare da jan dogon tsoki mai sautin gaske,matsawa yayi izuwa inda wayar hosana take a ƙasa,Ya sanya faffaɗan tafin kafarsa mai sanye da takalmi,Ya take wayar ya rugurguzata,hakan ba ƙaramin ƙona ma hosana rai yayi ba,Abun ka ga mai ta6in hankali,Kamar kura ta mamayeshi tare da gartsa mashi cizo asaman damtsen hannunshi,Dama ƴar singlet ce ajikinshi,ƙoƙarin janyeta ya dinga yi amma taƙi cire haƙoranta daga saman fatar hannun,har sai da ta fasa shi,jini ya shiga tsastsafowa a wurin,waro ido waje haroon yayi ganin ta fitar mashi da jini a fatar jikinshi,ƙwaƙƙwarar damƙa yakaima Gashin kanta,Hankalin Azmee ba ƙaramin tashi yayi ba,Ga tsoron shiga huruminshi take yi don tasan halinshi ba imani ya cika ba,Yasha ɗaga hannu zai mareta,
  Wurgi yayi da hosana,gaba ɗaya ta tafi zata faɗi ƙasa,Azmee takai hannu zata ruƙota,
  Tsawa ya daka mata tare da cewa"kika kuskura kika ta6a ta abakin aikin ki cikin gidan nan!uwar shisshigi kawai,ki tsaya a iya matsayinki,"jiki asanyaye azmee ta tsaya tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla,tana ji tana gani haka hosana ta kife ƙasa,fuskarta ta bugu sosai har hancinta ya fashe,
   Haura ƙafa yayi ya wuce Can medical room ɗinsu,saboda yayi dressing raunin da taji mashi,
  "Hosana"Azmee ce ta ambaci sunanta,tare da zuƙunnawa agabanta,tasa hannu ta janyota ajikinta,Lallashinta ta shiga yi,abun ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,Haroon ya 6ata mata rai,
  Cikin shessheƙar kuka tace"Aunty azmee,Kalli yarda ya fasa mun wayata,mutumin can baida imani shi ba jininmu bane,"hannu Azmee tasa tana share mata hawayenta,
   "Kiyi hakuri hosana,Allah shi zai saka maki,"
  Daƙyar azmee ta samu ta lallasheta,har ta rakata ɗakinsu ta kwantar da ita tana ta ajiyar zuciya,cikin lokaci ƙanƙani bacci ya ɗauketa,
  Dawowa falon Azmee tayi wurin da wayar Hosana ta fashe,hannu tasa ta ɗauki wayar tana kallon screen ɗin,Ya dagargaje sosai baka iya ganin komai,

A 6angaren Sehrish kuwa,duk tabi ta ruɗe lokacin da taji sautin kukan hosana,kafin haroon ya taka wayar ta ƙarasa mutuwa gaba ɗaya,zumbur ta mike tana zarya acikin ɗakin,kamar tayi tsuntsuwa ta tafi Abuja haka take ji,ta ƙagara tasan meke faruwa acan ɗinne ... .. '

Tashin hankali!Su marshal na zaune zaman jiran tsammani,sae ga Sgr ya fito daga room ɗin da aka kwantar dashi,Ko riga babu ajikinshi ya yageta ya cireta,ƙirar ƙarfin nan tashi mai matuƙar tsoratarwa gata nan a bayyane,Tsokar jikinshi sai rawa takeyi,miƙewa sukayi gaba ɗayansu suna kallonshi,
  "Rafayet"!Omar ne ya ambaci sunanshi tare da tunkarar shi,damtsen hannunshi ya ruƙo acikin nashi yana sake ambaton sunanshi
  "Omar!I can't believe that junaid has gone,till the day i found out those who planned his death!One by one sai na kashe su da hannuwana,daga nan ne zan yarda cewa Na rasa shi na har abada,wlh in har ban aikata abunda na faɗa ba,Sai na ajiye aiki na"daƙyar yake magana saboda zuciyarshi dake a harzuƙe,jininshi na akan akaifarshi,
  ƙoƙarin kama hanya yake yi yabar wurin Omar ya rurruƙeshi saboda baisan inda zai dosa ba,Likitocin dake kula dashi duk sun kewaye shi sae faman tausarshi sukeyi suna lallashi,Amma ina idanuwanshi sun rufe rufff,baya ji baya gani,
  "Rafayet ka kwantar da hankalinka mana!Duk yarda ka ke jin radadin mutuwar nan nima haka nake ji,nama fika jin raɗaɗi saboda Gani nake yi kamar ni ne silar mutuwarshi,Akan idona Junaid yabar gidan acikin motarshi na gaza dakatar dashi,Har Major sai da ya bani shawara amma banyi saurin ɗaukar mataki ba,Wlh kamar na haɗiyi zuciyata na mutu haka nake ji,"dakatawa ya ɗan yi da yin maganar yayin da suke kallon juna,shi da Sgr idanuwan kowannansu cike tab da Hawaye ba ƙaramin jiki suke ji ba,
  Tausasa muryarshi yayi kafin yaci gaba da cewa"Rafayet!yakamata muyi tunani akan mahaifinmu!mu nemi mafita,domin kuwa ya sanar dani cewa suna akan hanyar dawowa gida yanzu haka,kaima kasan irin yadda yake jin junaid aransa,muddin yaji mutuwarshi tofa zamu rasa shi ne,a yadda shekarunshi suka ja ɗinnan bakomai zai iya jurewa ba,"
  Jikin Sgr ba ƙaramin sanyi yayi ba,bawan Allah duk yabi ya susuce ya rasa kuzarin jikinshi,
   "Omar,yanzu ina ita yarinyar take ne"?yayi tambayar yana kallonshi,
   "Jahad ta zauce yanzu haka an kwantar da ita,ta samu bacci,"
  Jinjina kanshi ya ɗan yi,Shiru sukayi na wani lokaci,kafin Major yace"Yakamata mu nemi mafita,lokaci yana ƙure mana!"

Doctor Emran ne ya basu shawarar su shiga É—aya daga cikin resting rooms na asibitin,yadda zasu ji daÉ—in tsara yadda zasu tunkari Abbansu,
Chapter 118 · 0% Book details