← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 212

Sashe 133

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da aka fara kiran sallar Asuba,azmee ta farka,har sai da ta tsorata da taga mutum kwance a gadonta,Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta gane cewa ashe Sehrish ce,
Hannu tasa tare da dan bubbugata"Sehrish!Sehrish!"
Daƙyar Sehrish ta amsa mata"Na'am,"
"Lokacin sallah yayi,ki tashi kiyi sallah,"
"Toh"ta amsa mata batare da tayi yunkurin tashi ba,saukowa daga saman gadon Azmee tayi ta nufi toilet,
Har Azmee ta kammala salla Sehrish bata motsa ba,bacci ne mai nauyi yake É—awainiya da ita,
Buɗe ɗakin Azmee tayi ta fuce tabar sehrish aciki,Sai da ta fara zuwa ɗakinsu Jahad ta kwankwasa masu ƙopa,taji alamun sun tashi,Sannan ta wuce kitchen,
Tunda wuri ta fara shirye shiryen É—aura girki,
Sehrish kuwa sai da ta mula tasha iska kafin ta miƙe zaune,a hankali ta sauko daga saman gadon ta wuce toilet,bada jimawa ba tafito tana faman Yarfe hannunta,har lokacin akwai kasala atattare da ita,

BuÉ—e wardrobe É—in Aunty Azmee tayi tana neman Hijabin da zata sanya tayi sallah,a gida na farko Cikin jerin hijabanta Sehrish takai hannu ta janyo wata maroon colour,Abayar ta gogu sosai ga ninkin da akayi mata,
Tana kammala janyo hijabin,Ba zato ba tsammani taji sautin faɗowar wani abu ƙasa kamar ƙarfe ƙarfe haka sautin ya bada,wurga eyeballs ɗinta tayi ƙasan tiles ɗin don taga menene,ƙura ido tayi tana kallon Diamond ring ɗin da ya faɗo ƙasa,A sukwane Sehrish ta tsugunna saman guiwowonta,tare da sanya hannunta ta ɗaukko zoben,Stone ɗin jikinshi sai faman ƙyalli yake yi,
Kamar ta ta6a ganin zoben a hannun wani,zurfin tunani ta shiga yi tana ƙoƙarin gano inda ta ta6a ganin Zoben ko kuma hannun wanda ta ta6a gani,
Lokaci guda kanta ya É—auki Caji,Almost 15 mins bata motsa ba,Jujjuya zoben take yi tana kallonshi,ta kasa tunawa amma tabbas ta ta6a ganinshi,
Matso da zoben tayi saitin idanuwanta,Harafin da ke ajikin Dutsen Zoben ta ƙura wa ido,Harafin *J* ne,Duk yadda Sehrish taso ta gano a ina tasan zoben Sam ta kasa,miƙewa tayi hannunta ruke dashi,
"Kodai in tambayi Aunty Azmee nawa ne farashinsa,Yayi mun kyau sosai,"ta ƙarasa maganar tare da tura zoben cikin wadrobe ɗin wurin da take tunanin tanan ciki ya faɗo,
Darduma ta ɗauko ta shimfiɗa a ƙasa,A tsanake ta kabbara Sallah,Bayan ta kammala ta zauna saman dardumar tana Addu'a,
Hannayenta ta É—aga sama"Ya Allah kaine gatan mu!Da kai kadai muka dogara!Ya Allah kana ganin halin da muke ciki,Ya Allah ka kawo mana É—auki!
"Ya Allah kaji ƙan Junaid,ka gafarta mashi kurakurenshi,Ya Allah Kasa can yafi mashi nan,Allah ka tonu asirin wadanda suka kashe shi....."sosai ta shiga yi ma junaid addu'a,bayan ta kammala sallar ta naɗe sallayar tare da hijabin da ta cire ta mayar dasu inda ta daukkosu ta ajiyesu,

Bude kopar tayi ta fuce daga cikin É—akin,
ÆŠakinsu ta koma,da sallama abakinta ta shiga cikin É—akin,
"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikum Salam,"muryar Oummansu ce ta Amsa mata,
Murmushi ta saki tana kallonsu,gaba É—aya suna zaune saman gadon sun zagaye juna da alama fira suke yi,
Ƙarasawa cikin ɗakin tayi tare da samun wuri saman gadon ta zauna itama,
"Oumma ina kwana,kin tashi lafiya,"murmushi abu ta sakar mata tare da cewa"lafiya qalou rishi,ina fata kin tashi cikin ƙoshin Lafiya"
"Alhamdulillah Oumma,"
Hosana tace"Yawwa rishi ƙwara da kika zo wlh,wai Oumma taƙi yarda cewa Ya Omar Saurayina ne shi zan aura,"
Dariya Sehrish tayi tare da cewa"Amma baki da kunya Allah,Oumman kike faÉ—ama cewa kina da saurayi,"?
Zumbura baki hosana tayi a ɗan shagwa6e tace"ai ƙwara ni,saurayi gare ni,ke da ma kike da au. "bata ƙarasa maganar ba,Sehrish ta buge mata baki,"shashasha karki kuskura ki faɗa wlh ranki zai 6aci ne,'
A harzuƙe tace"Wlh sai an faɗa,"
Jahad tace"ki fada É—in,Ni kuma in faÉ—awa ya Omar cewa baki respecting É—inmu,"
Tsuke baki Hosana tayi tana gatsina masu hanci,
Ita dai Oummansu sai bin su takeyi da kallo,gwanin ban sha'awa,
"Oumma,Jiya kinsha farfesun Aunty Azmee ko?ya kika ji É—anÉ—anon girkinta,"Sehrish ce tayi maganar don ta kawar ma Hosana zancen da takeyi na son tona mata asiri,
"Yayi daÉ—i sosai,É—anÉ—anon girkin na musamman ne,Amma sai dai bansan wacece Azmeen ba,saboda banga fuskarta ba jiya da kyau,kodai itama Auntyn ku ce"?tayi maganar tana kallon fuskar Sehrish,
Girgiza mata kai tayi alamar a'a,
"Ba Auntyn mu bace,Amma kuma matsayin Auntynmu take,ta jima tana aiki acikin gidan nan,tana da mutunci sosai,zan haÉ—a ki da ita ku gaisa kuma kiyi Mata godiya,saboda ta bani kyakkyawar kulawa lokacin da nake cikin mawuyacin hali,"
Fuskar Abu É—auke da murmushi tace"Allah sarki,har naji ta kwantamin arai na,na kosa na ganta ma,"
"Ae yanzu haka tana aiki a kitchen,bari muje mu tayata aiki idan muka haÉ—u wurin yin Breakfast zaki ganta ne,Sai ku gaisa,"
Abu tace"To shikenan,Yanzu kuje ku tayata aiki ke da Hosana,Jahad ta zauna a wurina tunda bata da ƙoshin Lafiya,"
Maƙe kafaɗa Hosana tayi"Ni bazanje wani kitchen ba,Ae ni ba ƴar aiki bace,"
Dariya su kayi gaba ɗayansu,sehrish tace"Sha zamanki,Ni kaɗai na isa na tayata aikin har mu kammala,"ta ƙarasa maganar a yayin da take ƙoƙarin sauka daga saman gadon.

Fitowa tayi daga cikin É—akin ta nufi kitchen,azmee ta samu acikin kitchen tana aikace aikacenta,
"Assalamu Alaikum,"sehrish ce tayi sallamar a yayin da take shiga daga cikin kitchen É—in,
Juyowa azmee tayi fuskarta asake tace"Mutanen kano,An tashi lafiya'?
  "Lafiya lou Aunty azmee,Nayi missing ɗinki sosai,"
  Azmee tace"i missed u too,jiya naso mu haɗu dake,In tayaki murnar ganin Oummanku,Amma bansamu halin yin hakan ba,"
  "Nima jiya naso nazo ɗakinki mu gaisa Amma gajiya ta hana,"acewar Sehrish,
  "Ae na ganki da asuba,kinso ki tsoratar dani Allah,sam Ni banyi tsammanin akwai mutun a kwance  gefena ba,Ashe ke ce,"
  Dariya Sehrish ta ɗanyi kafin tace"Oh,aunty Azmee ashe kema kina da tsoro kamar ni,"
   "Ni ba mutun bace"ta ɗanyi maganar tana hararar sehrish
   Murmushi kawai tayi batare da tace komai ba
  Takowa azmee tayi izuwa kusa da ita,hannunta ta ruƙo cikinta
  "Sehrish,kinji abunda ya faru ko"?
Cikin sanyin murya tace"Eh,jahad ta sanar dani komai,dangane da garkuwar da akayi dasu,nasha kuka sosai na gode wa Allah,Fatana shine Allah ya bayyanar da Junaid,"tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla,
   "Wlh aunty azmee na karaya sosai,jikina yayi mugun yin sanyi,Allah sarki Junaid,bawan Allah,Yaso ni sosai,Ya bani kyakkyawar kulawa,"
   Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi,
"Sehrish akwai abunda na manta ban sanar dake ba,koda yake junaid ne Ya hana in faÉ—a maki tun lokacin bayaa yanzu tunda baya nan inaso na sanar dake,"
   "Menene aunty azmee"tayi maganar yayin da take kallonta,
   'A lokacin baya,farko farkon zuwanki gidan nan,Zaki iya tuna ranar da kikayi Ciwon ciki mai tsanani?har kika sanar dani cewa Aljani ne yazo maki a daren ranar"?
.shiru sehrish ta ɗanyi tana ƙoƙarin tunawa da ranar,Can tace"Na tuna,"
  Ajiyar zuciya azmee ta sauke kafin ta ɗaura da cewa"JUNAID NE ba Aljani ba!Sehrish shi ne ya taimake ki a wannan ranar,Ya sanar dani komai,kuma tun a lokacin yake ta ɗawainiya da sonki acikin zuciyarshi,"
  Fashewa sehrish tayi da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,Cikin shessheƙar kuka tace"Dama junaid ne aunty azmee,Wayyo Allah na,Meyasa tuntuni baki sanar dani ba?meyasa aunty azmee!
  Hawaye ne ke shararowa akan fuskar Azmee,
  "Shiya ce karna faɗa maki Sehrish,saboda yana tsoron kiji haushinshi,Saboda ya gane cewa ke maca ce,After that,Sehrish junaid Shi ne ya siya maki wannan wayar taki ta farko,Tecno Camon 18,Wayarshi sabuwa ya mallaka maki ita,Bayan haka kuma Shi ne Silar da aka sanyaki Makarantar Boko,da kuɗinshi kuma,Wanda babban yayansu ya bashi don yayi Celebrating birthday ɗinshi,Amma ya fasa yin murnar ranar haihuwarshi Duk don saboda Ke!Na faɗa maki ne saboda in sauke nauyin dake akaina,"
Gaba ɗaya jikin Sehrish ya gama mutuwa,Kasa motsawa tayi daga tsayen da take,Ta ƙame kamar gunki,yayin da hawaye ke ta wanke mata fuskarta,masu ɗumi wasu nabin wasu,kamar wadda aka zarewa lakar jikinta,Ta rasa duk wani ƙarfi na jikinta,Abun da Ciwo acan ƙasan Zuciya,raɗaɗinshi yafi na zafin wuta,

Hannu tasa tare da dafe saitin Zuciyarta,ji take tamkar zata 6allo daga ƙirjinta,

Dafa shoulders ɗinta Azmee tayi tare da cewa"Sehrish!meya faru naga duk kin Canza?ban faɗa maki hakan ba don na tashi hankalinki,Na Sauke nauyin dake akaina ne,Junaid addu'armu yake buƙata Allah ya bayyanar dashi,Ni sai ma nake ji araina kamar bazai dawo ba,"
  Sai lokacin Sehrish taja dogon numfashi,daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta tana tafiya,Ta fuce daga cikin kitchen ɗin,Har lokacin babu kowa a falon duk basu fito ba,kewar junaid duk ta baibayeta,tsananin sonshi ne ya kamata,komai ya fita ranta a yanzu junaid kawai take son gani a yanzu,Gashi ya tafi ya barta,Tafiya ta har ABADA,

  Garden ɗin gidan ta shiga,slowly take tafiya saman korayen Ciyayin dake aƙasan wurin,bakomai take tunawa ba,Fa ce irin rayuwar da sukayi da junaid,musamman ranar da suka fara haɗuwa a garden,Ranar da yazo zai bayyana mata kanshi amatsayin mutun na farko daya gane cewa ita maca ce,harya sanya hannu yana cire mata gashin bakinta,da kuma ranar da suka shirya zasu haɗu dashi a garden har yayi ta zaman jiranta bata fito ba,har dare Yayi akayi ta nemanshi acikin gida,
  Duk duniya bata da masoyi daya wuce junaid,kifa kanta tayi asaman table ɗin gabanta,Sosai ta fashe da kuka mai cin rai,taso ace tuntuni junaid ya bayyana mata soyayyarshi da babu abunda zai hana ta aure shi,
...tashin sense......

Mu haɗu on monday✍️

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*💃🏻💃🏻💃🏻

*takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji✋🏻✋🏻✋🏻

Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,💃🏻💃🏻
*Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Chapter 133 · 0% Book details