← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 196 OF 212

Sashe 196

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ajiye bottle din yayi saman drawer,kafin ya hau saman gadon gaba ɗaya,a dai dai saitin fuskarta yakai tashi fuskar,zuba mata ido yayi yana kallon yadda take ta sambatu
  "Reesh!You know you love me, but why kike wahalar dani"?he said calmly,jin muryarshi yasa ta buɗe idanuwanta,sunyi luhu luhu cike tab da ƙwalla,
   A hankali take kallonshi,yayin da shima yake kallonta,batare da kyaftawar ido ba,tamkar zasu haɗiyi junansu,saboda tsabar so,
   Ganin tana ƙoƙarin sake fashewa da kuka,yasa shi yin saurin toshe mata bakinta,da tafin hannunshi"its ok,u don't ave to cry,tunda gani a kusa dake,"
  Lumshe idanuwanta tayi tare da sake buɗesu akan fuskarshi,zame hannunshi yayi daga kan fuskarta,
"Ya rafayet,Am really sorry,pls don't leave me,i can't survive without you,"
Kalamanta ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya sukeyi ba,
  "why reesh?kin tada mun hankalina,ko bacci bana iyayi just because of you,kin fusata ni sosai,kin sanyani zubar da hawayena,'
  Girgiza mashi kai tayi"Bazan ƙara ba,"
  "Kin yarda cewa inasonki?ba jikinki nakeso ba?kuma kin amince zaki rayu dani a matsayin Mijinki Uban ƴa'ƴanki"?
  Jinjina mashi kai tayi alamar eh,
Kafin tace"na aminta dakai,Na yarda da irin son da kake yi mun,kuma ina namen yafiyarka,akan misunderstanding din da muka samu,ban kyauta maka ba,its all my fault,nice ƙarama koba haka ba,kai ɗan uwana,Yayana kuma Mijina,nice a ƙasa dakai,amma ban duba hakan ba......"
  Bata kai ƙarshen maganar ba,ya dakatar da ita,ta hanyar sanya yatsanshi ɗaya asaman lips ɗinta,
   "Komai ya wuce a wurin,nima ina neman yafiyarki akan laifin da nayi maki,"
  Kallonshi kawai take yi,ba ƙaramin mamaki Sgr ya bata,ta ƙara yarda da irin son da yake yi mata,ya canza mata ba kamar da ba,
  "Nima komai ya wuce A wurina,amma pls,ka fasa tafiya U.s din,idan ma zaka tafi ƙafata ƙafarka,don bazan bari na rasaka ba,"
  Ƙayataccen murmushin gefen fuska Sgr ya sakar mata,gaba ɗaya ya tafi da tunaninta,natsuwa tayi tana kallon kyakkyawan murmushinshi,ƙurawa juna ido sukayi wani irin kallon so suke jefawa junansu,

A wannan yanayin na shauƙi,Marshal Omar ya faɗo bedroom ɗin,Yazo da niyar ya lallashi Sgr akan ya fasa tafiyarshi,tun a palour yaci karo da trolley an ajiyeshi,yana zuwa bakin ƙopar ɗakin,ba zato ba tsammani ya hango romeo da juliet,abun ya bashi mamaki,Yadda ya samesu,manne da juna,sun ƙurawa juna ido,kamar zasu cinye junansu,Ƙayataccen murmushi marshal Omar ya saki,yadda kasan wani zautacce,Su suke yin soyayyar amma yafi su jin daɗinta,a hankali Ya furta Alhamdulillah Ya Allah,Na gode maka daka cikama ɗan uwana burinshi,Nima Ya Allah ka cikamin burina na ganin na mallaki hosana,A matsayin matata,Uwar ƴa'ƴana,Ya Allah ka dawwamar da farin ciki acikin zukatanmu,Ya Allah ka ƙara haɗa kan masoyan nan,ka albarkance da samun zuri'a ɗayyiba,

Bai bari sun ganshi ba,juyawa yayi da sauri yabar part ɗin,A ƙopar palourn Ya tsaya tare da zura hannu cikin aljihun wandonshi,Ya zaro wayarshi,Layin hajiya azeema ya dannawa kira,sae faman sakin murmushi yake yi,kamar wanda Akayiwa Albishir da gidan Aljanna,yafi kowa farin cikin wannan ranar,

A lokacin da kiran Omar ya shiga,Hajiya azeema na kwance bata farka daga baccin asuba É—in data koma ba,ringing É—in wayartane Ya tayar da ita,hannu takai saman side drawer ta É—auki wayar,ganin sunan daya bayyana akan screen É—in wayarna yasa ta cewa"to fa,Omar ne ke kira tunda safe,to Allah yasa muji alkahiri,
  Ta ambaci hakan tare da ɗaga kiran nashi,ta manna wayar a kunnanta,
  Gaisawa suka fara yi kafin tace"Ya Andace ko kuwa har yanzu ba canji"?
  Muryarshi da alamun farin ciki atattare da ita,Yace"Congratulation Mommy azeema,munyi winning,"tunkafin Ya karasa maganar tace"Alhamdulillah Ya Allah,'ta ambaci hakan yayin da take miƙewa zaune,
  "Omar shaƙa mun naji,wlh aƙagare nake,Meya faru,sun shirya,Sehrish ta janye maganar sakin,"
  Dariya omar yayi sosai,jin yadda take ta jero mashi tambayoyi,
  "Aunty ae yanzu haka daga part dinsa nake,Na same su manne da juna,maganar saki ta ƙare,Zama na har abada,"daga haka Omar ya kwashe duk abunda ya faru tundaga daren jiya har zuwa yau da safe daya same su,Ya sanar da ita,
  Saboda tsabar farin ciki,Saukowa tayi daga saman gadon hannunta manne da wayar,Ta shiga yin rawa,tsantsar farin cikine akan fuskarta,
  "Mommy,suna buƙatar wasu abubuwa da zasu ƙara danƙon soyayyarsu,amma kafin nan,Yanzu dai suna buƙatar lafiyayyen breakfast,don jiya ɗan uwana baici komai ba,"
  Murmushi hajiya azeema tasaki kafin tace"in sha Allah,Yanzu zan tafi kitchen don in shirya masu,"
  "Yawwa aunty,mun gode sosai,sai munzo yin godiya nida rafayet,"
  "Haba dai,ae duk yiwa kaine,kada ka wani damu kanka,Amma ya tsakaninka da hosana?Ba tada matsala"?
  Omar yace"Nikaɗai zan iya da hosana,Bata da matsala,"
  Jinjina kai tayi"shikenan omar,duk da haka zan dage damtse wurin ganin na koya mata abubuwan da suka dace,"
  "Thank so much auntynmu,mai son ganin farin cikinmu,"
  Murmushi ta saki"yanzu bari naje na shirya masu breakfast din"
   Daga haka su kayi sallama dashi,Ajiyar zuciya ta sauke fuskarta ɗauke da murmushi ta ajiya wayar sama drawer,

A hanzarce ta nufi hanyar fita daga ɗakin,tana kokarin buɗe ƙopar ɗakin,Amrish ta turo ƙopar,jikinta sanye da jallabiya black colour ta yafa mayafi akanta,
  "Amrish har kin shirya kenan"?
ÆŠaga mata kai tayi"eh mommy,"
  'Meya faru naga fuskarki kamar da alamun damuwa attare da ita,"
  Cike da damuwa amrish tace"ɗazu da zan shiga ɗaki,naci karo da sehrish,fuskarta sharkaf da hawaye,wlh na shiga damu sosai,bansan inda ta dosa ba,har tambayarta nayi ko bata da lafiya,Amma bata tanka mun ba,sai dai kawai naga ta watsa da gudu..."
  Hannu hajiya azeema tasanya tare da shafa gefen fuskarta"Calm down ur mind,A halin Yanzu sehrish tafi ki ƙoshin Lafiya,tana cikin farin ciki,babu abunda ke damunta,don haka kema ki kwantar da hankalinki,"
Ajiyar zuciya amrish ta sauke,haÉ—i da yin murmushi,
  "Muje waje,bari nayiwa wani magana acikinsu sai ya kaiki gidan,"
  Ta ƙarasa yin maganar,tare da yin gaba,Amrish tabi bayanta,
  Suna saukowa Babban Falon,Sai ga kanal Yusif ya fito daga part ɗinsu sai faman sauri yake yi,jikinshi sanye cikin shadda brown colour,wani irin ƙamshine ke fita ajikinshi,
  "Yawwa yusif"hajiya azeema ce ta kwala mashi kira,A hanzarce ya juyo 6angaren da suke,ganin hajiya azeema yasa shi sakin murmushi,da sauri ya tunkari wurinta,yana ƙarasawa ya soma gaisar da ita"Ina kwana Auntynmu,An tashi Lafiya,"
  Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Lafiyalou,Alhamdulilla,Ina zaka je naga kana ta faman zumbula sauri,"
  "Inaso zanje dubo jikin abokina ne,An farmakesu ne wurin aiki da aka turasu,yanzu haka yana asibitin yaya rafayet,acan aka kwantar dashi,
  "Allah sarki,bawan Allah,Allah ya bashi Lafiya,"acewar hajiya azeema,
  Kallon Amrish yayi,ta sunnar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta,
  "Wannan fa,ina zuwa"?
Da sauri tace"Ina kwana yaya yusif,"
  "Lafiya lou,"cike da jin kunyarshi amrish ta amsa mashi,
"Tana so zataje kwaso kayanta ne a gidansu,ni nace ta shirya zanyiwa wani magana yakaita gidan,"
"Ba damuwa,Zan sauketa,in yaso saina wuce asibitin,kafin ta kammala kwasar kayan,sai na dawo na É—auketa,"
Wani irin farin cikine ya lullu6e amrish,
  Godiya hajiya azeema tayi mashi"nagode ssai,Sai kun dawo,"
  Gaba yayi amrish tabi bayanshi,bayan sun fita,Yace ta tsaya ya dauko motarshi,Jim kaɗan sai gashi yayi driving ɗin motar,har zuwa inda take a tsaye,buɗe motar amrish tayi kafin ta shiga daga ciki,yana a diver seat tana a gefen shi,karya kwana yayi,kafin ya fisgi motar da gudun gaske ya fuce dasu,

Lokacin da suka hau titin a tsanake yake yin driving ɗin,har suka isa unguwarsu,adai dai ƙopar gidansu Amrish yayi parking ɗin motar,juyawa ya ɗanyi gefen da take ya saci kallonta,tare da cewa
  "Zan dawo na ɗauke ki,nan da 30 minutes,ina fata bazaki gaji da jirana ba,"
  Murmushi ta ɗan saki tare da kallonshi,suka haɗa idonsu dashi,tayi mamakin irin sanyin kyan dake gareshi,mai matuƙar jan hankali,musamman kwantaccen sajen gefen fuskarshi,
  "Nagode sosai,Ya yusif,sai ka dawo,a gaishe mun da mara lafiyan,"
  Mayar mata da martanin murmushi yayi"ki kulamun da kanki,"
  "Kaima haka,"tana ambaton hakan ta buɗe motar ta fuce,

A buɗe ta samu ƙopar dake jikin gate ɗin gidan,hannu tasa ta tura ƙopar ta shiga daga ciki bakinta ɗauke da sallama,murmushi ta saki lokacin da tayi arba da baba mai gadi,zaune saman tabarma,Ga tray agabanshi mai ɗauke da soyayyun kaji,Ga kayan marmari,Ga kuma lemu acikin cup  hada kankara acikinsa,duniya tayi kyau,
  "Assalamu akaikum,"jin muryarta yasa baba mai gadi yin hanzarin kai idanuwanshi kanta,washe baki ya soma yi,ya miƙe ya nufeta"Allah sarki Amrishi,yau kece da kanki,ashe ba rabon in rigaki zuwa,don yanzun nan nake cewa da zarar na kammala yin karin kumallona,naba furannin can ruwa,Zan shirya inzo har gidanku in duba ki,"
  Zuƙunnawa amrish tayi tare da gaisar dashi,ba ƙaramin daɗi yaji ba,shi kanshi ya lura da irin sauyawar da tayi,don da lokacin bayane ko kallo bai ishe taba,balle har ta gaishe dashi,"
  Bayan sun kammala gaisawa,tace"dama,nazo kwasar kayan sawata ne,"
  "Oh to,bari na ɗauko maki key ɗin,"yakai ƙarshen maganar,tare da juyawa ya nufi cikin ɗakinsa,jim kaɗan ya dawo hannunshi,ruke da key ya miƙa mata,tasa hannu buyi ta kar6a kafin ta wuce cikin gidan,

Komawa baba mai gadi yayi saman tabarmar ya zauna,sae faman washe baki yake yi,duk murnar ganin amrish,A fili yace"Mutanan kirki,gashi har zun canza yarinyar nan,Kai Allah dai ya saka masu da mafificin Alkhairinsa,nima ata dalilin Yaron nan da muka taimaka,Sunyi mun alheri,mahaifinsu ya dunƙulo kuɗi har dubu ɗari shida ya damƙa mun,gashi yanzu inata Cin kaji,"sai faman sambatu yake yi,

Amrish kuwa bayan ta shiga gidan,bedroom É—inta ta shige,ta kwashi kayanta acikin trolley,hada agogon diamond É—in junaid ta haÉ—o don ta mayar mashi da abunshi,a falo ta zauna tana jiran dawowar kanal Yusif,har kitchen ta shiga ta dafa indomie ta zubota acikin plate ta zauna saman Sofa,tana ci tana tunanin Kanal Yusuf,

*Boss Bature*

Bayan tafiyar Amrish da kanal Yusif,juyawa hajiya azeema tayi izuwa kitchen,Anan ta samu abu tare da Mommy da saude suna girke girken breakfast É—in gidan,gaisawa suka fara yi,kafin ta shiga shirya masu lafiyayyen abinci,mutun biyu ta shirya mawa,Na Omar da kuma Na Sgr,Har É—aki taje ta kira hosana don takai mashi abinci,a lokacin suna kwance saman gadonsu,ita da jahad,Hajiya azeema tazo mata da maganar,hada bata shawarar tayi mashi kwalliya,ta sanya kaya masu kyau,dama kamar jira take yi,cike da zumuÉ—i ta sauko daga saman gadon ta faÉ—a toilet don tayi wanka,komawa kitchen hajiya azeema tayi ta É—auki na Sgr da sehrish Ta nufi Uptairs dashi,
Chapter 196 · 0% Book details