← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 212

Sashe 177

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗaya bayan ɗayan Matasan gidan suka fara fitowa domin halartar Sallar Asuba,kamar yadda suka saba tafiya atare,Lokacin da Marshal Ya sauko down,Suna haɗa ido da Abusufyan da Abba sai da gabanshi ya faɗi,tunkafin wani daga cikinsu yayi yunƙurin yi mashi magana da sauri yace"Lokaci yana ƙurewa,"

Babu wanda ya lura babu Sgr sai Abba da Abusufyan,gudun kada lokacin sallah ya wuce su ne yasa basu tambayeshi ba,sun bari sai sun dawo daga masallacin,

Tunda ta farka take jin zuciyarta babu daɗi,gabanta sai faɗuwa yake yi,wurga idanuwanta tayi kan Hosana da Jahad ta samu kowannansu cikin ƙoshin Lafiya,hannu tasa tana ɗan bubbuga ƙafafunsu,
  "Hosana!Jahad!ku tashi lokacin salla yayi,"jahad ce ta fara farkawa,saukowa tayi daga saman gadon ta wuce cikin toilet,
  "Hosana ki tashi mana kullum saikin bani wahala,"tayi maganar tana ɗan bubbuga ƙafarta,
  Daƙyar ta samu hosana ta farka,miƙewa tayi zaune tana hamma tare da yin Miƙa,
  "Oumma wlh nayi wani mummunan mafarki acikin bacci na,"
  Kallonta abu tayi"wani irin mafarki,"
  "Oumma,rishi ɗinmu na gani acikin wani ƙurmun daji,tana ta tsala gudu kamar zata tashi sama,Ga zaki yana ta bin ta,Sai kuka take yi tana ta ambaton sunanki dana Daddy don ku taimaketa amma babu wanda yaje wurinta har sai da zakin nan Yaji mata ciwo......"tana kai ƙarshen maganar ta fashe da matsanancin kuka,abun ya ƙona mata rai,

Shiru abu tayi,yayin da idanuwanta ke kallon fuskar Hosana dake kuka,
  Fitowa Jahad tayi daga cikin toilet,
  "Meya sameta take kuka"?Tayi tambayar tana kallon Oummansu,
  Ajiyar zuciya abu ta ɗan sauke tare da cewa"wai mafarki tayi da Sehrish acikin daji tana ta gudu,Zaki ya biyo ta har ya ji mata rauni,Shine take kuka"abu nakai ƙarshen maganarta,
Jahad taja dogon tsoki mai sauti"Amma hosana ban ta6a ganin Hamago irinki ba,kawai daga yin mafarki sai ki fara yiwa mutane kuka Angaya maki mafarki gaskiyane,Ko yau kika fara yin mafarki ne"?
  Cikin shessheƙar tace"Wlh in nayi mafarki yana zama gaskiya,kin manta 6eran gidansu Maman sadeeq daya saci daddawar gidanmu yakaita raminshi dake a zauren gidansu,Bani nayi mafarki ba har na tona mashi asiri,Muka yi mashi bugun tsiya har ƙafarshi ta 6alle....."
  Basu san lokacin da suka fashe da dariya ba,gaba ɗayansu Jahad hada dafe cikinta,ɗaure fuska hosana tayi don ita dagaske tayi maganar ba don suyi mata dariya ba,Saukowa abu tayi daga saman gadon ta nufi toilet tana ta faman tiƙar dariya Sai da takai bakin ƙopar tukunna ta tsagaita da yin dariya ta shige ciki,
  Cike da zolaya Jahad tace"Da alama nan gaba malamar duba zaki koma Hosana,tunda harkin fara yin mafarki Yana zama gaskiya,dama akwai mafarkan da nakeso nima a fassara mun"
  Harara hosana Ta wurga mata,rai a6ace ta sauko daga saman gadon,Sleeping dress ne ajikinta riga da wando,Ganin ta nufi hanyar fita daga ɗakin yasa Jahad yin saurin dakatar da ita"Ke ina zuwa!Salla fa aka tasheki kiyi"
  A ƙule tace"Ina ruwanki,ni zanje in ga rishi ɗinmu ne,"
  "Kinsan Allah karki fita,zoki wuce kije kiyi sallah "
. ko sauraronta batayi ba,Ta buɗe ƙopar ɗakin ta fuce tana ƙunƙuni

Ɗakin Azmee ta shiga,ko sallama babu,Amrish ta samu agaban wardrobe tana lalubo abayar da zatayi sallah,jin an turo ƙopar ɗakin yasa ta juyo don taga wanene,duk a tunaninta Sehrish ce,
   "Kin dawo kenan"
Turo baki hosana tayi"Ina rishi É—inmu take?ita nake son gani,"sai da tayi magana sannan ta gane wacece
"Nima bansan inda taje ba,tun da na farka ban sanyata a idanuwana ba,"
  Guntun tsoki hosana taja,duk a tunnaninta,Amrish ƙarya take yi mata,
  Toilet Ta buɗe ta shiga tana neman Sehrish,Jim kaɗan ta fito daga toilet ɗin,Duk amrish na kallonta,Har ƙarƙashin gado ta leƙa bata ganta ba,a ƙarshe Tayi ƙwafa tare da bude ɗakin ta fuce,bedroom ɗinsu ta koma,A lokacin har Abu da Jahad sun kammala Sallah,toilet ta shiga shaf shaf ta ɗauro alwala,
Ta fito ta É—auko hijabi a wardrobe ta jera dasu,

Bayan an kammala Sallar Asuban,suna dawowa gidan,Abusufyan bai nufi ko ina ba sai upstairs,tsabar sauri kamar zaiyi tuntu6e ya faÉ—i,Abba na biye da bayanshi,Omar ma yabi bayansu,kowannansu na sanye cikin jallabiya,

Yana shiga bedroom ɗinshi,Yaga wayaam babu kowa,yayi tunanin yana acikin toilet,wuri Ya samu gefen gadonshi Ya zauna yana jiran fitowarshi daga cikin toilet ɗin,Don ayita ta ƙare kowa ma ya huta,
A tsaye Abba ya tsaya Omar na agefenshi,Gabanshi sai faÉ—uwa yake yi,Sgr ya tafi ya barshi da zullumi,duk yabi yasha jinin jikinshi,
  "Omar me ya hana Rafayet zuwa masallaci"?Abusufyan ne ya jefo mashi tambayar,
  A ruɗe ya soma ƙoƙarin yin magana,En ena ta hana shi"am...um...'
  Cike da mamaki Abusufyan ke kallonshi don a iya saninshi Omar baya en inar magana,Amma sai gashi yau daga ƴar tambaya duk yabi ya dabarbace,
  Wurga idanuwanshi yayi kan Abbansu dake a gefenshi,Suna haɗa ido Omar yayi saurin sunnar da kanshi kasa,Dama ance Labarin zuciya a tambayi fuska,Tuni Abbansu Yayi hasashen wani abu acikin ranshi,kuma ga dukkan alamu Sgr baya acikin toilet ɗinshi,
  "Abusufyan"!ya ambaci sunanshi,
"Na'am yaya,"
"Ina tunanin bayan fitarmu masallaci Rafayet ya fita yin sallah shima,mu ƙara haƙuri mujira dawowarshi,"
  Girgiza kai Abusufyan yayi"ba inda zanje,ina nan ina jiran dawowarshi "
  "shikenan,Omar inason magana dakai," ya ƙarasa maganar tare da ruƙo hannun Omar,Suka fito falonshi,

  "Omar ka faɗa mun gaskiyar abunda ya faru,Ina SGR ya tafi"?cike da tuhuma yake kallonshi,
  A ruɗe Omar yace"Bansan Komai ba Abba,bani da masaniya akanshi,"
  "Hmmmm Omar kenan,Nifa mahaifinka ne,Har akwai abunda zaka iya 6oye mun?fuskarka kawai na kalla raina ya bani cewa wani abu ya faru kuma kana da masaniya akanshi,Shiyasa har kake in ina,"shuru Omar yayi batare daya ce komai ba,
  "Zuciyata har ta karaya,Dan Allah Omar ka faɗamun meya faru?Ina Sgr ya tafi tunda Asuba,"?ganin yadda Ya shiga damuwa sosai,Yasa Omar Ya soma bayyana mashi abunda Ya faru,tun daga kan zuwan da Sgr yayi bedroom ɗinshi,bai 6oye mashi komai ba kaf ya sanar dashi,
  "Innalillahi'wa' Inna ilahirraji'un!"

jiri ne ya soma ɗibarshi,Yayi tangal tangal zai faɗi,da sauri Omar ya ruƙoshi tare da taimaka mashi Ya zauna saman Sofa,Hankalinshi yayi mugun tashi,
  "Nashiga uku Omar,Ashe rafayet bai da hankali!Dama saboda ya aikata mata hakan Ya nemi da mu ƙara mashi lokaci....wlh in har ya kuskure yarinyar nan ta rasa ranta,shima sai na kashe shi,
  "Abba pls,ka rage muryarka,bansan ya zanyi ba,idan Uncle yaji wannan maganar,shiyasa tun jiya nayi ƙoƙarin in dakatar daku akan kubi komai asannu amma kuka ƙi saurarena...."tun kafin yakai ƙarshen maganarshi Abba ya katse mashi hanzarinshi da cewa"Amma Omar rafayet bai kyauta ma kanshi ba,Yayi tunanin idan yayi mata hakan zai zame mashi mafita,Gashi yanzu ya ƙara jefa kanshi cikin tashin hankali,Bansan wani irin bauɗaɗɗen mutun bane shi,Nikaina da nake mahaifinshi Yafi ƙarfina...."Idanuwanshi cike tab da kwalla yayi maganar,
  "Abba,kayi haƙuri da abunda zance,bai kamata kuna ganin laifin Rafayet ba,Irin rayuwar da aka saba mashi da itane,komai yake so shi yake samu,tunfarko kuskuren da aka tabka shine barinshi da kayi Uncle donald ya tafi dashi U.s,tun kafin ya mallaki hankalinshi,Kasan wanene Donald,Yayan Mommy ne,tarbiyar ɗan uwana kwata kwata ba irin tanan bace,ya taso ba a musulmi ba,kuma an damƙashi hannun wanda ba musulmi ba kuma bature,taya rayuwarshi bazata kasance haka ba?Abba kayi tunani,da ace kai da kanka kaba shi tarbiya ya taso a wurinka,Ya kake tunanin zai kasance? ......'ya ɗan dakata da yin maganar yana kallon Abbansu,wanda tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,tsananin tausayinshi ne ya kamashi,
"Omar ka faɗi gaskiya,Laifina ne wlh,nayi danasani yafi a ƙirga,duk in na tuna cewa Sgr ba a hannuna ya taso ba,Na cutar da rayuwarshi banyi mashi adalci ba,banbari Ya taso a hannuna ba,a lokacin so ya rufe mun idanuna bani da burin daya wuce in faranta ma Alex rai,komai tace tana so gudun kada ranta ya 6aci yi mata shi nake yi,inaji ina gani Sgr ya taso ba'a musulmi ba,kullum in zaku tafi masallaci batare dashi ba,Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata,Donald yazo ya ƙwallafa rai akanshi,Alex tace in bar mashi shi ya tafi dashi can,wlh Omar bada son raina ba,Allah na gani inason Rafayet sosai,na amince ne don tayi mun alƙawarin zata ƙara haihuwa dani,kuma hada ƙarin don bana son ina ganinshi a matsayin wanda ba musulmi ba,shiyasa kawai na yanke shawarar Ƙwara yayi nesa dani,in banda ma rashin hankali irin nawa na ɗauki ƙaramin yaro naba wanda ban haɗa komai dashi ba,ƙanwarshi kawai nake aure,shi ba musulmi ba,Yanayin rayuwarsu da al'adarsu ba irin tamu ba,yanzu da ace rafayet ya mutu a wannan yanayin me zance ma Allah?Akan amanar daya bani!,ya makomarshi zata kasance Ya mutu a matsayin wanda ba musulmi ba,wlh na cuci rayuwarshi........'kasa ƙarasa maganar yayi saboda kukan daya ciyoshi,Tafin hannunshi yasa Ya rufe fuskarshi,shi kanshi Omar hawayen ne sharkaf akan fuskarshi,gefen Abba ya koma Ya zauna,tare da janyoshi jikinshi,Yana lallashinshi,
  "Ba don Allah yasa a wannan lokacin nayi tunanin haɗaka dashi ba,Har ka bisu U.s,kuma cikin sa'a ata dalilinka Ya musulunta,da bansan Ya rayuwarshi zata kasance ba,duk cikin ƴa'ƴana Rafayet ne ban yiwa adalci ba,Ya Allah ka yafe mun...."
  Lallashinshi Omar ya soma yi"Abba kayi haƙuri dan Allah,kadaina zubar da hawayenka,Yakamata muyi ƙoƙari wurin ganin mun nemo inda ya tafi da ita,bamusan a wani Hali suke ciki ba,naji takaici da ban taimaka mashi ba a lokacin da yazo wurina cikin mawuyacin hali,na rufe ido na kore shi da duk hakan bata faru ba,yasan cewa ni kaɗai zan iya fahimtarshi shiyasa yazo wurina,Sam baya acikin hayyacinshi amma haka yazo,Ni kuma maimakon in jashi ajikina in taimakeshin saina yi mashi tsawa nace ya fita ya bani wuri,

Duk wannan maganganun da suke yi akan kunnan Abusufyan dake tsaye abayan sofa ɗin da suke zaune,Kaf yaji abunda suke tattaunawa tun daga farko har ƙarshe,jikinshi yayi mugun sanyi,Hankalinshi Yayi matuƙar tashi,Har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi,
Chapter 177 · 0% Book details