← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 212

Sashe 137

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

High heels ta sanya a ƙafarta launin rigar jikinta,ƙarasawa tayi tare da buɗe ƙopar ɗakin ta fito,tun kafin ta ƙarasa fitowa daga cikin corridor ɗin ta soma jin sautin ƙarar Cokula,alamar abinci suke ci,

Kamar karta fito haka ta dinga ji,batasan taya zata nufi part É—inshi ba,ga mutane a dining area kuma dole ne in zata gifta sai sun ganta har ma su nemi jin ba'asin rashin fitowarta cin abincin,

Daƙyar ta ɗaure,ta nufi dining ɗin kaitsaye,tun kafin ta isa sautin takalmanta yaja hankalinsu,gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta
  "Daugher!dama idonki biyu?amma shi ne baki fito kin ci abinci ba"?Abusufyan ne yayi maganar,
  "Ni nayi tunanin ma ko bacci takeyi shiyasa banyi magana ba,"acewar Abba,wanda ya tasa plate ɗin abinci agabanshi sam ya kasa cin abinci,har yanzu kewar junaid ke ɗawainiya dashi,
  "Ina kwananku,"ta gaisar dasu cikin girmamawa atare suka amsa mata,
  Duka matasan gidan nan suka hallara,dogon table ɗin mai mazaunin mutun 12,anan Abbansu yake tare da Mommynsu,Fawan,Irfan, Jabeer,Khaleed,sai kanal Yousouf tare dasu Talal,Najeeb da twins,

ÆŠayan table É—in kuma mai mazaunin mutun 6,Oummansu ce tare da Abusufyan sai su Jahad da Hosana,idan ka kalli fuskokin matasan gidan sai sun baka tausayi,don kuwa kamar anyi masu dole don suci abinci,musamman fawan jujjuya cokalin hannunshi kawai yake yi,har yau ya hana kanshi jin daÉ—i duk don saboda Junaid,

"Samu wuri ki zauna mana"Mommynsu Junaid ce tayi mata magana ganin ta tsaya atsaye kiƙam,
  Sunkuyar da kanta ƙasa tayi,tana wasa da yatsun hannunta sam taƙi motsawa,
  "Ki zauna mana baki ji ana magana ba"Abusufyan ne ya tunasar da ita,
  Tafiya ta soma yi zata zagaya ta zauna,
  "Ina azmee take ne?naga yau tunda ta jera abinci,bata fito tayi serving ɗinmu ba kamar yadda ta saba,kodai bata lafiya ne"Abba ne yayi maganar cike da son jin ƙarin bayani daga wurinsu
Abusufyan yace"Nima tun É—azu na lura bata a wurin nan,yakamata a dubo ta aji ko lafiya,"
"Bari naje na kirata,"Ko sauraron amsarsu batayi ba,dama so take ta gudu daga Dining area É—in,
  Gudu gudu sauri sauri ta nufi corridor ɗin ɗakinsu,a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya tare da sanya hannu ta kwankwasa ƙopar,kusan sau uku tana buga ƙopar,ana ƙarshe ne tajiyo muryar azmee daga cikin ɗakin tana tambayar wanene,
  "Sehrish ce Aunty azmee,su daddy ne ke nemanki,Sun ji shiru shi ne suka ce a kirawo ki,"
  "Okey,gani nan zuwa,bana jin daɗi ne,"
  Tsayawa sehrish tayi a bakin ƙopar ɗakin har saida azmee ta fito jikinta sanye da hijabi,
  "Aunty azmee ya jikin naki"?
Daƙyar ta iya buɗe baki"da sauki,ciwon kai ne,kuma nasha magani,"
  "Allah ya ƙaro sauki Aunty azmee,"ta ƙarasa maganar tare da ruko hannun azmee cikin nata,suka kama hanyar zuwa dining ɗin atare,

Lokacin da suka ƙaraso dining area ɗin,hankalin kowa ya dawo kansu,
"Oumma ga Aunty azmee nan,kallatta ki gani,itace muke baki labarinta jiya mai girka mana abinci"a wani slow abu ta wurga eyeballs ɗinta akan fuskar Azmee,karaf idanuwansu suka shiga cikin na juna,Zumbur abu ta miƙe tsaye tana kallonta,kallon kamar nasanki,Itama Azmeen kallon Sani take yi mata,
  Ganin sun ƙurawa juna ido,babu mai magana acikinsu,yasa Abusufyan tanka masu"Ko kunsan juna ne"?
  Girgiza kai abu tayi"a'a gani nake yi kamar na santa ne,tayi mun kama da wata dana ta6a sani arayuwata,Amma bazan iya tunawa ba,
  "Aunty azmee kefa?kinsan Oumma ne"?Sehrish ce tayi mata tambayar,girgiza kai azmeen tayi"A'a nima dai kallon sani nake yi mata,kamar na ta6a sanin wata mai irin fuskarta,amma dai ba ita bace ba,sunyi kama ne"
  Murmushi sehrish ta ɗan saki tare da cewa,"tunda baku san juna ba,bari na gabatar da kowannanku,"
  "Aunty Azmee wannan itace Oummanmu,mahaifiyarmu,"
  Sannan ta nuna Azmee"Oumma ga Aunty azmeen da muke baki labarinta jiya,ba iya girki kaɗai ta iya ba,tana da kyakkyawar zuciya,mutuniyar kirki ce ita,"
  Murmushi abu ta saki tare da miƙa ma azmee hannu suka gaisa da juna,kowa fuskarshi ɗauke da murmushi,

Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke,ganin hankalin kowa ya koma kansu yasa tayi saurin lalla6awa ta wuce kitchen,shaf shaf ta shiga haÉ—a mashi breakfast É—inshi,

"Sehrish ta faÉ—amun irin halarcin da kikayi mata,bansan da wasu kalmomi zanyi amfani dasu ba wurin gode maki,Allah ne kaÉ—ai zai iya saka maki"
  Murmushi Azmee tayi"Ae duk yiwa kaine,na dauki sehrish tamkar ƴar cikina,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar,ta mayar da idonta kan Abusufyan"ina tayaka murna sosai,Allah ya ƙara haɗa kan zuri'arku,"addu'o'i ta shiga yi masu suna amsa mata da Ameen,kafin daga bisani Abba yace"Samu wuri ki zauna,Ke ma Azmee daga yanzu bana so kina wannan tsayuwar,don yanzu kinfi ƙarfin ƴar aiki a wurinmu,pls kada kiyi mun musu kamar yadda kika saba,"
Murmushi Azmee tayi tare da samun wuri a table ɗinsu Abusufyan ta zauna,Abu ma ta zauna,a tsanake kowa yake cin abincinshi,Abunda zai ɗaure maka kai,ya baka mamaki shine duk bayan ƴan mintina sai abu ta saci kallon Azmee,da alama dai tasanta ne,kuma tana ƙoƙarin tuna wurin da suka ta6a haɗuwa,itama Azmeen satar kallon nata take yi,kowa da abunda yake sakawa aranshi,
Fitowa tayi daga cikin kitchen ɗin hannunta ruƙe da ƙayataccen tray,hannu bibbiyu ta ruƙo shi,cikin sanɗa ta wuce upstairs,direct ta nufi part ɗin Sgr,a bakin ƙopar shiga falon ta tsaya sallama tayi jin shiru ba'a amsa mata ba,yasa ta wuce ciki izuwa bedroom ɗinshi,tana ƙoƙarin shiga,tajiyo maganganunsu shi da Omar,kasa kunne tayi tana sauraronsu,
  "Yanzu ya zamuyi?duk mun jefa kanmu cikin haɗari,idan har Abba yasan cewa ƙaryane ba kidnapping ɗin su Junaid akayi ba daga ranar zai ƙullace mu aranshi,kuma girmanmu zai faɗi agaban ƙannenmu ne,nayi regretting wlh,"Omar ne yayi maganar,a yayin da yake zaune gefen gadon,
  "Omar,nima ina danasanin yin hakan,na shiga damuwa sosai,bansan ya zamu yi ba,remain just one week and some days,daddy tare dasu fawan jiranmu kawai suke yi mu kawo masu Junaid"yayi maganar ne yayin da yake tsaye gaban mirror yana gyara jikinshi dake sanye da Bathrobe,ga danshi danshin ruwa da alama bai jima da fitowa wanka ba,
  Kowanne fuskarshi akwai tarin damuwa,abun ya tsaya masu aransu,
  Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,
  "Assalamu alaikum,"jin muryarta yasa suka tsagaita da yin firartasu,
   "Who's there"Sgr ne yayi tambayar
  "Sehrish ce,breakfast ne na kawo maka"
  Murmushi Omar ya fara saki,yana kallonshi,harara Sgr ya ɗan wurga mashi,
  Miƙewa Omar din yayi"kar na takura maka,bari na baka wuri,idan Mun haɗu zamuyi magana,"bai tanka mashi ba,Ya nufi hanyar fita daga ɗakin,
  Sehrish na ganinshi tayi saurin gaisar dashi"Ina kwana ya Omar,"
  Fuskarshi ɗauka da fara'a ya amsa mata"Lafiya lou,ina fata kema haka". 
  "Ina lafiya,"daga haka ya matsa mata hanya ta wuce ciki,Shi kuma ya fuce daga ɗakin,

A hankali take tafiya ta cikin mirror yake ƙare mata kallo,A saman table ta ajiye mashi tray ɗin,sannan ta ɗan juya tare da kallon bayanshi,gaisar dashi tayi"Gm ya Rafayet,ka tashi lafiya,"shiru bai amsa mata ba,kamar bashi bane ya gama magana yanzu tare da Omar,

Juyawa tayi saÉ—af saÉ—af zata bar bedroom É—in nashi,
  "Where are u going?kin kammala aikin ki ne?"
   "A'a,naga kamar kana shiri ne,Zan jira a falo,idan ka kammala zan shigo daga ciki in yi aikin,"
  A wani slow ya juyo tare da kallonta,adai dai lokacin itama ta waiwayo shi,
   Har sai da gabanta ya faɗi lokacin da idanuwansu suka haɗu cikin na juna,
  Da hannu yayi mata alamar ta dawo,kamar wadda aka zarewa laka,haka ta dawo daga ciki duk tasha jinin jikinta,ƙoƙarin gyara Mashi bedroom ɗin ta shiga yi,kamar daga sama taji ya cire mata mayafin jikinta,da sauri ta juya tana kallonshi
   "Taya zaki ji daɗin yi mun aiki da wannan abun a jikinki"?
  Shiru tayi batace komai ba,Sae ƴan kame kame takeyi,
   Jefa mata shi yayi asaman bayanta,"ki san inda zaki ajiye shi,"
  Ruƙo mayafin tayi tare da ɗaure ɗamararta dashi kamar yadda ta saba yi,mayar da hankalinta tayi wurin gyara mashi gadon,
  Cike da tsantsan sha'awarta yake bin jikinta da kallo,bai ta6a sanin kyawun launin ja ba sai da yayi arba da rigar jikin Sehrish wadda ta kasance Red colour,ga shi hannu ɗaya gareta,Soft skin ɗin bayanta mai matukar jan hankali sai fisgarshi takeyi izuwa gare ta,
Chapter 137 · 0% Book details