← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 212

Sashe 206

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sam ta kasa runtsawa saboda rashin dawowarsu Sgr,kusan ƙarfe 1:30 na dare,tana a tsaye agaban Glass window mai girman gaske,Ta jikin glass ɗin tana kallon yadda ruwan sama ke sauka gwanin ban sha'awa kamar ta faɗa cikin ruwan tayi wanka,ta jima tana sha'awar hakan amma tafiso suyi atare da Sgr sai ya fi daɗi,Babydoll ce ajikinta me matukar jan hankali,Pink colour sharara daƙyar ta wuce ass ɗinta,da rigar da babu duk ɗaya ne zallar net ne ajikinta,Gyaran gashin da akayi mata ba ƙaramin kyau ya ƙara mata ba,har wani lumshe ido take yi saboda iskar dake kaɗawa,ba ƙaramin daɗin yanayin take ji ba,bakowa take gani acikin idanuwanta ba face Sgr,komai nashi burgeta yake yi,miskilancinshi,murmushinshi,iya ɗaukar wankanshi,Jan ajinshi,kyakkyawar surar jikinshi da komai nashi,ta mutu akanshi sai kace ba mallakinta ba,Gayen ne ya iya Loving and Caring,kullum ƙara nutsar da ita yake yi cikin soyayyarshi,ta yadda bazata iya rayuwa batare dashi ba,aduk Lokacin da ya shirya zai tafi headquater sai taji tamkar ta fashe da kuka,daƙyar suke rabuwa dashi da hawaye akan fuskarta,Sam basa gajiya da juna,
  tana cikin wannan tunanin,ta fara jiyo jiniyar motocinsu,Wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,A hanzarce ta zuge glass door ɗin,Nan take iska ta soma busowa saman fuskarta Gashinta ya dinga reto ruwa na fallatsar mata,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,Duk ta ƙagara ta ganshi,ba halin yin hakan saboda akwai tazara sosai,Slowly motocinsu suka shararo da matsakaicin gudu ta babban gate ɗin gidan suka shigo a jere,Motar Sgr da Motar Omar,gaba da baya motocin Security ne,uku gaba, uku baya,masu ɗauke da fusatattun Sojoji,

  Ƙura ido Sehrish tayi tana son ta leƙoshi ruwa ya hanata buɗe idanuwanta dakyau,bayan sunyi parking ɗin motocin,A hanzarce Security soldiers ɗinnan suka diro daga saman motocinsu suka ƙarasa tare da buɗe masu tasu,A hankali ya zuro ƙafarshi me sanye da army shoe,saukowa yayi daga cikin motan Jikinshi sanye da kaki,Daga sama ya ɗaura military Coat wadda takai mashi har ƙasan guiwarshi,kanshi ya sanya Hula ta kakinsu,Yayin da sumar kanshi ke ɗaure ya saketa har tsakiyar bayanshi,Fitowa Omar yayi daga cikin motarshi,shima yana acikin kakinsa,Biyu daga cikin Soldiers ɗin hannunsu na ruƙe da Lema sunyi masu rumfa asaman kansu don kada ruwa ya jiƙasu,sallama suka yi da Major da Amstrong kafin Omar ya ruƙo hannun Sgr acikin nashi kamar yadda suka saba,A haka suka nufi cikin gidan,A bakin Main palour ɗin Soldiers ɗin suka Juya,Suna shiga palourn da gudun gaske Hosana ta miƙe ta nufo su har tana tuntu6e zata faɗi,da sauri Omar ya ruƙota a jikinshi,Shafa Curly hair ɗinta yayi"My Hosana,me kike yi bakiyi bacci ba?
Ashagwa6e ta soma magana"kai nake jira Ya omar,"
Murmushi yasaki tare da kallon Sgr wanda tuni yayi gaba a hanzarce yake tafiya don yayi missing É—inta Over,
Hannu yasa tare da tallabo fuskarta ya manna mata kiss asaman forehead É—inta"Nayi missing É—inki sosai hosanata,Ina fata kin ci abincinki"?
  "Ni banci komai ba,kai nake jira muci atare,"sarai yasan cewa ƙarya take yi mashi saboda bata da Jumurin yunwa,Duk da haka yaji daɗin maganarta,its Okey,Mu je ki tayani cire kaya,in yi wanka in na fito sai muci atare ko"?ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ruƙo hannunta yayi tare da janta suka nufi part ɗinsu,sae murna takeyi Ya omar ɗinta ya dawo,

Lokacin da ya shiga part ɗinsu tun abakin door din palour yayi sallama ya soma ƙwala mata kira"Reesh!My baby....'dama jiran shigowarshi take yi,yana shigowa bedroom ɗin ta faɗa mashi asaman wide chest ɗinshi,wani irin sanyine ya ratsa zuciyarshi,a hankali ya shiga furta"Alhamdulillah Ya Allah,"ba ƙaramin daɗi yake ji ba aduk lokacin da ya dawo agajiye daga wurin aiki,Sehrish ta faɗa mashi a jikinshi,tamkar maƙoshine dake bushe a yanayi na buƙatar ruwa,yafi buƙatarta fiye da komai,a hankali ya sanya hannunshi asaman sumar kanta yana shafa lallausar gashin kanta,
  kashe murya tayi tare da cewa"Welcome back,My own husband,nagode ma Allah daya dawo mun dakai Lafiya,I really missed you,na yini acikin duhu,amma yanzu haske ya haskaka idanuwana da zuciyata,"
  daɗaɗan kalamanta ba ƙaramin tasiri suke yi akanshi ba,
    Duƙar da kanshi yayi zuwa saitin fuskarta,bayan ya dago da ita,irin gaisuwar da suka saba ma junansu,haɗe bakinsu yayi wuri guda a hankali yake kissing ɗinta,yayin da idanuwansu ke kallon cikin na juna,tamkar su haɗiye juna haka suke ji,ya jima before ya zare tongue ɗinsa daga cikin bakinta,ɗaukarta yayi kamar ƴar baby,Ya ƙarasa da ita gaban dressing mirror,ya juyo da front chair ɗin mirrorn tukunna ya ɗaura sehrish asaman kujerar yadda tsayinsu zaizo ɗaya,haka kullum sukeyi saboda ta taimaka mashi wurin cire kayanshi,Wannan ma wani sabon salon soyayyarne,Sae faman sakin murmushi sukeyi,
  "Ya gajiyar aiki,"tayi maganar tare dakai hannu ta zame coat ɗin dake ajikinshi,
   "Babu gajiya atare dani idan har ina tunaninki acikin zuciyata,Reesh kece ƙwarin guiwar da nake dashi,"
Murmushi tasaki har dimple É—inta ya lotsa,
  "Yaushe zamuje Honeymoon"?
"Na baki za6i,kiyi choosing countries É—in da kikeso muje,cos ur choice is mine,"
  Wani irin daɗi take ji kamar kamar me,zame vest ɗin jikinshi tayi ya rage saura army trouser dinshi,saukowa tayi daga saman kujerar ta zuƙunna ƙasa,ta sanya dukkan hannayenta tare da zare igiyoyin takalmin ƙafarshi ta ciresu,tare da safar,kafin ta miƙe ta zame belt ɗin wandonshi,daga shi sai short fari ta bari ajikinshi,tana kammalawa ta tattara kayan da ta cire mashi ta kaisu laundry,tana dawowa ya ɗauketa asaman kafadarshi ya wuce toilet da ita,kamar yadda suka saba,

Tun acikin bathtub suka fara having sex,almost more than 30 mins suna acikin toilet din,kafin ya fito ɗauke da ita a hannunshi,suna sanye da towel,komai atare suke yin shi,agaban dressing mirror ya sauketa saman kujerar,Sai daya bi ko'ina na jikinta ya shafe shi da cream dinsu,itama ta shafa mashi ajikinshi,hand dryer suka dauko suka fara busar ma junansu gashi,afterward suka bar wurin mirror din suka koma can cikin ɗakin da yake yana da faɗi sosai,wurin closet ɗinsu tanƙamemen gaske mai ɗauke da sliding door,ta cikin glass din kana iya hango jerin kayansu kamar a company,shaf shaf suka shirya junansu cikin pyjamas blue colour,yadda kasan tagwaye,hatta kayan sawarsu iri ɗayane,

"Me kake son ci in kawo maka"tayi maganar tana kallonshi,
  "Bana jin yunwa,"
Bubbuga ƙafarta tayi ashagwa6e tace"ni ban yadda ba Ya rafayet,wlh bakasan cin abinci,kana so kaga angry face ɗina ko,"
  Natsuwa yayi yana kallonta,idan tayi shagwa6a gaba ɗaya kashe mashi jiki takeyi,
   Tamkar zatayi kuka taci gaba da cewa"banfa ci komai ba Saboda kai,saboda nafi so muci atare,ina baka abaki kana baniii"ta ɗan ja maganar daga ƙarshe cikin shagwa6a,
  Murmushi kawai yake saki yana kallonta,
  Ruƙo hannunshi tayi"pls mijina nakaina,kafaɗamun me kakeso insa akawo mana,idan ma kanaso ni in girka maka zan shiga kitchen ne,"tana magana tana wasa da yatsun hannunshi,
Allah kaɗai yasan yadda yake jinta acikin zuciyarshi,ta iya soyayya,tasan takan miji,tunda ya kafeta da sexy blue eyes ɗinsa bai ko ƙyaftasu ba,
  Bubbuga ƙafafuwanta ta ƙara yi tare da faɗawa saman ƙirjinshi,tana cigaba da yi mashi shagwa6a,
Cikin sanyin murya ya furta"its okey,zanci,"ajiyar zuciya ta sauke,ta É—ago daga jikinshi,juyawa tayi da sauri ta É—auko wayarta dake ajiye saman pillow,Call log ta shiga É—aya daga cikin layin masu aikin gidan ta kira,ta basu umarnin su kawo masu dinner a part É—insu,bayan ta ajiye wayar ta É—an juya tare da kallonshi har ya kishingiÉ—a saman gadon,
    "Am sorry,naso ace ni na girka maka abinci dakaina kamar yadda nasaba,don banason kana cin abincin masu aiki,"
  "I don't want u to Cook for me,duk wani aikin wahala banaso kinayi,ɗawainiya ma da kike yi dani ya isa basai kin ƙara da wani abu ba,duk kin shagwa6ani,ko Office nake kamar zautacce haka nake yini ina murmushi,kowa mamaki yake yi,wai Sgr ne da murmushi,"
  Natsuwa tayi tana sauraronshi har yakai ƙarshen maganar,kafin ta bashi amsa wayarta ta soma ringing,da sauri tayi picking,Amsawa tayi da "okey u can leave,"daga haka ta ajiye wayar,
   Moving tayi zuwa saitin fuskarshi"food is ready,in kawo maka anan ko a palour zamu ci,"
  Saukowa yayi daga saman gadon ya ruko hannunta suka nufi palourn,Dining area suka tunkara hannunsu acikin na juna,sai da suka isa sannan ta saki hannunshi,suka zauna suna fuskantar juna,
Chapter 206 · 0% Book details