← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 212

Sashe 178

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ba zato ba tsammani suka ji muryarshi ta bayansu,
  "Rafayet ya kashe mun ƴata,"firgigit sukayi gaba ɗaya suka miƙe atare suna kallonshi,Fuskarshi sharkaf da hawaye,
  Aruɗe Abba yace"Abusufyan tun yaushe kake tsaye awurin nan"?
  Muryarshi adisashe ya basu Amsa"tun lokacin da kuka fara magana nake tsaye ina sauraronku....."dakatawa ya ɗan yi da yin maganar,cikin sanyin murya ta wanda ya karaya yaci gaba da magana
"Dan Allah ku faÉ—amun gaskiya,Sehrish tana raye kota mutu?Ina Rafayet yakai mun ita?Ni ko gawarta ce dan Allah ya maido mun,"
  Wannan maganar da yayi ta ƙarshe ba ƙaramin Kashe masu jiki tayi ba....
  "In sha Allah,Sehrish tana raye Uncle,a duk inda suke yanzu nasan Sgr yana akan gyara 6arnar da yayi mata ne,dan Allah ina ba kowa hakuri amadadin ɗan uwana,wlh duk wani hali da zamu shiga ayanzu bamu kama ƙafarshi ba,Ya tsorata sosai,tunda nake a rayuwata ban ta6a ganin Sgr cikin matsanancin tashin hankali ba irin na yau,nasan ya cutar da ita,Amma duk yayi wannan ne saboda son da yake yi mata,Yana tsoran ku rabashi da ita ne........
  "Omar,Kana goyon bayanshi ne?Ni ƴata ba mutun bace!Allah kaɗai yasan irin muguntar da yayi mata,Rafayet baida Imani baida tausayi,Wlh nayi danasanin aura mashi Sehrish!Kuma duk inda ya shiga acikin garin nan saina nemoshi,Ya dawo mun da ƴata,koda gawarta ce" duk yadda Omar yaso ya fahimtar dashi,Amma yaƙi sauraronshi,a zafafe ya nufi hanyar fita daga falon,Da sauri Abba yabi bayanshi tare da ruƙo hannunshi,idanuwanshi sun rufe rai a6ace yake magana"Ya Hossein ka sake ni,Wlh bazan ƙyale rafayet ba,har ni zai wulaƙanta ma ƴa?Allah hukuma ce zata rabani dashi,"ranshi a matuƙar 6ace yake magana,
  "Kada ka yanke hukunci cikin fushi,muzo muna danasani....."tunkan Abba yakai ƙarshen maganarshi,Abusufyan ya fusge hannunshi,A fusace Ya fuce daga part ɗin,
  Bai ta6a tunanin Abusufyan zaiyi mashi haka ba,ya 6ata mashi rai sosai,
"Abba,ni ina ganin me zai hana A sanarwa Ammi halin da ake ciki,wata'ƙila ta dakatar dashi,
  Girgiza kai Abba yayi"kabarshi kawai,Yadda zuciya ta ɗebeshi ɗin nan bazai saurari kowa ba,Sam baya cikin hayyacinshi,Ni tsorona ma kada yace zai yi driving a irin wannan yanayin da yake ciki,"

Hannu Omar ya tura cikin trouser pocket dinsa Ya zaro wayarshi,Layin Abusufyan ya dinga kira,Wayar nata ringing amma yaƙi ɗagawa,
  "Dama kadaina wahalar kiranshi,don bazai saurareka ba,Ni yanzu babban tashin hankalina bansan a wani hali suke ciki ba,Omar ba yadda za'ae asan Location dinshi"?
  "Abba wayarfa tana a bedroom ɗinshi ya barta,Sannan nayi kokarin kiran Armstrong yaƙi picking,kuma ya toshe duk wata hanya da za'a yin tracking layinsa,'
  "Ina kake tunanin ya tafi da ita"?
  Shuru Omar ya ɗanyi yana kokarin yin tunani akan inda Sgr zai tafi da ita,
  "Da farko nayi tunanin asibitinshi ya tafi da ita don ya dubata,Amma munje har can nida Major bamu same shi ba,nidai inaji araina cewa Suna acikin garin nan,Sgr bai gudu da ita ba,nafi tunanin ya 6oyeta a wani wurine saboda gudun kada Abusufyan yaga 6arnar da yayi mata,Amma Ina da tabbacin cewa zaiyi ƙoƙarin Yi mata aikine da kanshi,"
  Jinjina kai Abba ya ɗan yi,tare da cewa"Dan Allah Omar,kuyi ƙoƙari wurin ganin kun gano mana inda yake,Zan cigaba da kiran Layin Abusufyan,har Allah yasa ya ɗaga,"

Amsa mashi yayi da toh Abba,A hanzarce Ya fuce daga part ɗin,Abba yajima zaune asaman sofa yana ta faman kiran Abusufyan Amma yaƙi ɗaga kiran,A ƙarshe ma sai ya kashe wayar gaba ɗaya,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,jiki asanyaye ya fito daga part ɗinshi,Ya sauko downstairs,bedroom ɗinshi Ya shiga,Mommy ya samu zaune gefen gadon,hannunta ruƙe da Cup,Tana ba Junaid magungunanshi yana sha,jin motsinshi yasa suka kai idanuwansu wurinshi,
  "Abba,"Junaid ne ya ambaci sunanshi,
Mommy tace"Ina ka shiga ne?Tunda kuka tafi masallaci ban ganka ba"
  Daƙyar ya iya buɗe baki yace"wani abune ya tsayar dani,"tunkafin ta ƙara tambayarshi,yayi saurin cewa"Junaid ya jikin naka"?
  "Alhamdulillah Abba,Am feeling better,Nayi missing dinka sosai,jiya kace zaka tashe ni mu tafi masallaci sallar Asuba atare,"
  "Am Sorry,Na manta ne,Amma gobe in sha Allah,Zamu fara zuwa masallaci dakai,tunda naga jikin naka ya murmure,"Ya ƙarasa maganar,yana kakaro murmushin dole,Mommy dai ta kafe shi da ido,Don ta lura akwai damuwa atattare dashi,Ga hawaye nan bushe kan fuskarshi,toilet ya shige yaja ƙopa ya rufe,a Gaban sink ya tsaya fuskarshi duk ta yamutse,Ya damu sosai akan son sanin Halin Da Sehrish take ciki,Allah yasa tana raye bata mutu ba,baisan ina zai tsoma ranshi ba,

"Abban Junaid"!mommy ce ta kira shi,daga cikin ɗakin,Da sauri Ya kunna fanfo ya wanke fuskarshi sosai,Kafin Ya nufi ƙopar ya fito daga cikin toilet ɗin,

A tsaye ya sameta,tana jiranshi,
"Inason magana dakai,"tayi maganar batare data jira amsarshi ba,Ta ruƙo hannunshi suka ja gefe guda,
"Wani abu ya faru ne?naga canji akan fuskarka,"
"Babu komai,bana jin daÉ—i ne kawai,ki tayani da Addu'a,"
"Ni banyarda ba,inaji araina wani abu ya faru,kawai ka sanar dani,"
Shiru yayi yana wasi wasi acikin ranshi,kodai ya faÉ—a mata gaskiyar abunda ya faru,wata'kil ta taimaka mashi,ta wani 6angaren kuma yana jin fargabar ya sanar da ita cewa,SGR yana da Aure,baisan ya zata É—auki abun ba,
"Ka tsareni da ido,Ka faÉ—amun mana,meke faruwa ne"
Juyawa ya É—an yi tare da kallon Junaid,Sam hankalinshi baya a wurinsu,Ya lullu6e kanshi cikin bargo,
Mayar da idanuwanshi yayi kanta"Zan faÉ—a maki,Amma ba yanzu ba,"
Ruƙo rigarshi tayi"kodai ka faɗamun abunda ke damunka ko kuma wlh duk inda zaka je saina bika,"
Gyaɗa kai yayi"shikenan zan faɗa maki,Amma dan Allah inaso ki fahimce ni........."natsuwa tayi tana sauraronshi,gaba ɗaya ya kwashe duk abunda ya faru tun daga kan auren Sgr da Sehrish da sukayi a 6oye har izuwa aika aikan da yayi mata yau,Don ance za'a rabashi da ita,Yayi tsammanin Mommy zata Balbaleshi da masifa,musamman da yaga ta kafe shi da blue eyes ɗinta,batare data ƙyafta ba,

"kiyi haƙuri dan Allah,nasan nayi maki laifi da ban sanar dake ba,na damune sosai akan halinshi,Shiyasa na ɗauki shawarar abokina akan inyi mashi aure ko zai canza,wannan dalilin ne yasa mukayi amfani da wannan damar muka shirya hakan tsakanina da Abusufyan"muryarshi asanyaye ya ƙarasa maganar,yana kallonta,

Jinjina kai ta É—an yi kafin tace"banji zafin auren da kayi mashi batare da sanina ba,Amma naji haushin Tursasa mashi da kuka yi akan ya saketa,Meyasa?Gashi yanzu kun jefa rayuwar yarinyar cikin hatsari,U made a mistake ku dukanku,U know him better than any other person, tunda ya nuna yana son tafiya da ita dat means yana sonta ne,tunda kasan yana da masu yi mashi aiki,,"ranta a6ace tayi maganar,

"Wlh nayi danasani sosai,laifin da rafayet yayi shine dabai miƙa wuya ba,Ya nuna cewa yana son ya tafi da ita don taci gaba da yi mashi aiki,maimakon Ya amince zai tafi da ita amatsayin matarshi,wannan maganar tashi ce ta harzuƙa Abusufyan harya tursasa mashi,Ni na goyi bayan Abusufyan ne,Saboda kafiyar da rafayet ya nuna,babu yarda banyi dashi ba akan Ya soke yarjejeniyar,amma yaƙiya,duk da dama bamu aura mashi ita da sunan yarjejiniya ba,tun tana yarinya Abusufyan ya bashi ita,........."dakatawa yayi da yin maganar yana sauke ajiyar zuciya,
Jinjina kai Mommy tayi kafin ta soma magana"Yanzu menene solution?Gashi babu wanda yasan inda ya tafi da ita,balle asan wani hali suke ciki,Babban tashin hankalinma idan Mahaifiyar yarinyar nan tasan cewa bata acikin gidan nan,Dole ta damu sosai,"_
"Ke zaki taimaka mun,kafin Allah yasa mu gano inda suke,kisan yarda zakiyi wurin kawar mata da tunaninta akanta,"
"Shikenan,Zanyi hakan,Amma pls kuyi kokari kafin rana ta faÉ—i asan inda suke,Sannan yakamata a bincika É—aya daga cikin guest house É—inmu,Zai iya zuwa can"_
Hugging ɗinta yayi don ba ƙaramin kwantar mashi da hankali tayi ba,
"Nagode sosai da shawarar da kika bani"ya ƙarasa maganar,tare da kama hanyar fita daga dakin,
"Allah yasa aje asa'a,"_
Ya amsa mata da Ameen kafin ya fuce,

Ta jima atsaye cike da zullumin abunda zai biyo baya,bata ji daÉ—in abunda Sgr yayi ba,tashiga damuwa sosai akan halin da Sehrish take ciki,fatanta Allah yasa yarinyar bata mutu ba,
Chapter 178 · 0% Book details