Sashe 110
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
After few minutes da shigarshi palourn,Sae ga wani Soja ya shigo hannunshi ruke da manya manyan ledoji na restaurant,A bayanshi kuma wani sojan ne hannunshi ruke da Katan katan na lemunsha,Saboda tsabar farin ciki,bakin Abusufyan yaƙi rufuwa,dama tunanin da yake yi kenan,gashi sun shigo da baƙi kowa ya kwaso yunwa gidan kuma ba wani abunsha,Balle abinci,
  Ƙarasowa ciki sukayi tare da ajiye kayan a tsakiyar palourn,
  Atare suka haɗa baki wurin cewa"Sgr ne,yace a shigo maku dashi,zaizo anjima,"
 Murmushi Abusufyan ya ɗan saki tare da cewa"Okey,mun gode sosai,Allah ya kawo shi lafiya,"
Juyawa su kayi atare suka bar É—akin,
 Sehrish ya kira,ta ɗauki ledojin takaisu kitchen,acan ta haɗo masu kayan abincin A cikin warmers ta jerasu a saman tray,Saman dining table ta jera masu su tare da drinks,Gaba ɗaya nan suka harhadu,dama kowa ya kwaso yunwa,don sun jima a asibitin nan,Nan fa kowa ya shiga ɗurama cikinshi abinci,bayan sun ci sun ƙoshi,daga bisani,wuraren sallar magrib,Nurse ɗin tare da doctor su kayi masu sallama,
Abusufyan ne ya É—auko su acikin motarshi tare da Baban sadeeq saboda zasu wuce masallaci daga nan,'
Tun bayan da ta kammala sallar magrib,ta koma saman gadon Oummasu ta zauna tana kallonta,a ƙagare take da ta farka duk da tasan cewa,ba a hayyacinta take ba,batasan wacece ita ba ayanzu,
 "Yakamata in sanarwa su Jahad da hosana,"tayi maganar cike da zumuɗi ta dauki wayarta dake ajiye gefenta,
 Contacts ta shiga,tare da lalubo numbar jahad ta danna mata kira,Kusan sau uku tana ringing ba'a ɗaga ba,hakan yasa ta tura mata text message,
  Layin hosana,ta kira itama wayar bata a kusa da ita,tayi ringing harta katse ba'a ɗaga ba,
 Yanke shawarar kiran junaid tayi,cikin rashin sa'a ta samu wayarshi a kashe,
 Tur6une fuska tayi ranta a 6ace,taso ace itace zata fara yi masu albishirin ganin Oummansu,Amma duk sun ƙi ɗaga kiran wayarta,
 Yunƙurawa ta ɗan yi saitin fuskar Oummansu,ta ɗauketa photo da camera ɗin wayarta,kusan hoto uku tayi mata,
ta whatsapp ta tura masu hotunanta,'
Motsin mutane taji acikin palourn,ranta ya bata cewa Su Baban sadeeq ne suka dawo,bata leƙa ba,kwanciya tayi a gefen oummantasu,
Su biyu suka shigo cikin palourn,zama sukayi saman sofas ɗin suna fuskantar juna,Abusufyan yace"Bamu da wasu kalmomi da zamu iya amfani dasu wurin gode maku,kunyi matuƙar yin ƙoƙari,kun kula da rayuwar abu,tamkar ƴar cikinku,kun damu da ita sosai,Allah ne kaɗai zai iya sakamaku,"
 Baban sadeeq yace"duk yiwa kaine,idan ka taimaki rayuwar wani kaima Allah sai ya taimaki ta ka,Naji daɗi sosai,kuma nayi matuƙar farin ciki,daya kasance kaine Mijin Zainab duk da an shiga tsakaninku,kuma mahaifinsu sehrish!hankalina ya kwanta sosai,Abu zata rayu atare da mijinta ga kuma ƴa'ƴanta,uwa uba kuma ga dangin mijinta,Allahu Akhbar,najiye mata daɗi,ƙarshen wahalarta yazo da yardar Allah,"
 Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa"Amma malam,Ya maganar sayyadi ne!?ko kuna da labarinshi"?
 Shiru Malam nura ya ɗanyi na wani lokaci yana tunani kafin yace"Ae Sayyadi tun ranar da aka nemi abu aka rasa,tun daga ranar bamu ƙara sanyashi a idanuwanmu ba,gidan ma a garƙame muka same shi da ƙaton ƙwaɗo,".
 dakatawa yayi da yin maganar,
Hakan yasa Abusufyan cewa"dama nasan bazai tsaya ba,guduwa zai yi,"
 Girgiza kai Baban sadeeq ya ɗan yi tare da cewa"A'a,bana tunanin ya gudu,Munafukin duk inda yake yana acikin garin nan!yanzu haka ba mamaki yasan da zuwanku!ae ba ƙaramin shu'umin mutun bane,"
 "Amma taya akai kasan cewa,yana acikin garin nan?ko kun ƙara haɗuwa dashi ne"?acewar Abusufyan,
 Baban sadeeq yace"ƙwarai kuwa!Kama tuna min!ae can shekarun baya lokacin da aka nemi abu aka rasata,fitsararran ya tako da waɗannan ƙafafuwan nashi masu kama dana zabbi har ƙopar gidana,
 Lokacin na dawo daga sallar asuba,na shiga da mashin cikin gida,nadawo zan rufe ƙopa kenan ina ƙokarin rufewa,Naji an banko mun ƙopar,A firgice na kai idanuwana wurin don inga wani taƙadirinne!aikuwa sai nayi tozali dashi,A tsaye ruƙe da qugu,nan fa nashiga faɗin A'uzubillahi minasshaiɗanir rajim,"sai cewa yayi"Ni ne shaiɗanin"?nace mashi "to ae baku da bambanci da shaiɗan,ƙahonne kawai ke babu!shin me ma yakawo ka ƙopar gidana?ko kazo ne kayi mun futsarar taka daka saba ne?sai yace mun saƙo ne yazo dashi,nace saƙo kuma?yace mun eh,yasa hannu cikin aljihun jallabiyarshi ya zaro wata ƴar doguwar takarda,ya miƙo mun tare da cewa"Saƙon Abu ne,idan mun sameta,A bata wasiƙar," jin cewa sakon na abu ne yasa na amsa,to tun daga wannan lokacin da ya haura ƙafa,ban ƙara sanya sayyadi acikin idanuwana ba,hatta makarantar islamiyyar da muke koyawa atare dashi,ya daina zuwa...."
 Lokacin da ya kai ƙarshen labarinshi,Abusufyan yace"Amma kun karanta wasiƙar"?
 Baban sadeeq yace"A'a,babu wanda ya ta6a ta,Ae amana ce,yace wasiƙar ta abu ce shiyasa bamu karantata ba,"
 A ƙagare Abusufyan yake daya ga wannan wasiƙar,
  "Yanzu wasiƙar tana ina ne"?
"Tun lokacin dai,bayan tafiyar sayyadi,dana shigo cikin gida,kaitsaye wurin Maman Sadeeq na wuce,ita nabawa ajiyar wasiƙar,"
 Ajiyar zuciya Abusufyan ya sauke,
 "Gobe,in Allah ya kaimu,sai muje gidan a ɗauko wasikar,yau dai anan zaku kwanan mana,"acewar Abusufyan,
  "Akwai yaronmu fa,mun barshi a gida,"Baban Sadeeq ne yayi maganar,
"idan mun fita yin sallah,sae mu dawo tare dashi," acewar Abusufyan
 Suna cikin tattaunawar nan aka kira sallar isha'e,atare suka fita yin salla daga can zasu wuce gidan,Su ɗaukko Sadeeq,
Fitowa Sehrish tayi daga Bedroom ɗin Oummansu,wuraren ƙarfe 8:30 na dare,a palour ta samu Maman sadeeq zaune,jikinta sanye da hijabi,
 Tana ganin Sehrish ta mike,tare da tunkararta,
 "Rishi,zonan mana,baki bani labarin ya kuka ƙare ba,bayan kun bar nan"tayi maganar tare da ruƙo hannunta,saman 3 seater suka zauna,
 Nan fa Sehrish ta shiga bata labarin rayuwarsu,tun daga lokacin da suka koma katsina har Æ™arshe,jikin Maman Sadeeq ba Æ™aramin sanyi yayi ba,jin irin wahalar da suka sha,ta wani 6angaren kuma ba Æ™aramin farin ciki tayi ba,Â
sun jima suna firar yaushe rabo,kafin suyi sallama kowa ya wuce ɗaki,don ba ƙaramar gajiya suka kwaso ba,
Koda Sehrish ta koma É—aya daga cikin bedrooms É—insu da aka gyara masu,wanda ke a upstairs,toilet ta shiga don ta watsa ruwa ajikinta,kafin ta kwanta,Maman sadeeq kuma a downstairs ta zauna,É—akunan su Dr haris a lokacin baya,
  fitowa tayi daga cikin toilet,jikinta sanye da undi ta ja shi har saman kirjinta,ƙarasawa tayi gaban gadon,inda ta ajiye kayan baccin da ta dauko don ta sa,tare da phone ɗinta,
 Tana ƙoƙarin kai hannu ta ɗauki wayar,Ta jiyo sautin dirar mota acikin gidan,
 "Su Daddy sun dawo kenan"tayi maganar tare da ɗaukar wayar,Har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi,bakinta fa ya ƙi rufuwa tunda aka samu Oummansu,babban burinta yanzu bai wuci Oummansu ta dawo cikin hayyacinta ba,waƙa ta kunna ta ƙure Volume,Nan fa ta shiga yin rawa,kamar wata zautacciya,juyi ta dinga yi,iska na kaɗa gashin kanta,duk cikin farin cikin ne,yaushe rabon da tayi dancing irin haka harta manta,dama can ita ba ma'abociyar yin rawa bace,duk da tana son yin rawar,yanayin rayuwane yasa bata samu wannan damar ba,a hankali ta soma bin wakar abakinta,
_rawa da girgiza zanyi gabanka,in jujjuya,zanyi maka albishir kayi dace da mai tarbiyya,sannan zan zame maka farin ciki na nan gidan duniya,Nafi kowa saninka acikin abunsha kafi son coffee_
Bata ƙarasa baitin ba,ta tsaya cak sakamakon mutun da ta hango tsaye ta cikin mirror,ya goya hannayensa asaman wide chest ɗinshi,gabanta ne ya faɗi rass,lokaci guda ta shiga taitayinta,duk tabi ta kame kanta kamar wata mara gaskiya,
Bakowa bane fa ce Sgr,still dress É—in É—azu ne ajikinshi,tun lokacin da ta fara rawar yazo É—akin,kuma ta hanyar kiÉ—an wakar da ta kunna ne yasa ya gane cewa akwai mutun a É—akin,dama kuma ita yake nema saboda ya tayata Murnar ganin mahaifiyarta,
tsayawa su kayi suna kallon juna ta cikin mirror,kunya duk ta rufe ta,saboda É—an undi É—in dake ajikinta sharara yake,gashi ko bra bata sanya ba,