← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 212

Sashe 26

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ƙarasawa tayi tare da hayewa saman gadon a gefenta ta zauna,cike da mamaki take kallon jahad,ganin ko motsi ba tayi,bama tasan ta shigo ɗakin ba,ko menene yaja hankalinta haka?
  "Jahad!"Sehrish ce ta ambaci sunanta,a firgice ta juyo tana kallonta,ganin sehrish yasa ta sakin murmushi tare da cewa"Har kin dawo,ae nayi tunanin acan zaki kwana,"
  dariya sehrish tayi tare da dungurin goshinta tace"Abun hada tsokana,Nima nayi tunanin zanzo na same ki,kina bacci ashe idonki biyu,me kike yi da wayar ne"?don naga gaba ɗaya yaja hankalinki,"
  Ƙayataccen murmushi jahad ta saki tare da cewa"Hmmmm ba zaki gane bane,wani zazzafan hausa novel ne nake karantawa acikin wayarki,dama jira nakeyi kizo in tambayeki a ina zan samu cigaban littafin"?
  Cike da mamaki Sehrish tace"Novel kuma?ae ni bana karatun littafin hausa,banma san ya akai kika samu littafin a wayata ba,don gaskiya bana ajiye su,"
  Wani kallon rainin wayau jahad tayi mata tare da cewa"Kina nufin duk haɗuwar littafin nan baki ta6a karanta shi ba!hakanan kike ajiyar shi acikin wayarki?
  Yatsina fuska Sehrish tayi tare da cewa"nifa bansan dashi ba,may be cikin friends ɗina na makaranta ne wata wurin tura ma wasu ta turamun shi batare da sani na ba,"
  jinjina kai jahad tayi tace"gaskiya an barki a baya,tunda uwata ta haife ni ban ta6a karanta littafin me shegen daɗi irin wannan ba,tunda na fara karantashi bakina ke awashe,kamar anyi mun albishir da gidan aljanna,"ta karasa tana daria,
  Ta6e baki sehrish tayi tare da cewa"Wai ya sunan Littafin ne?naji sai faman zuzuta shi kike yi,inaso inji sunanshi ne saboda tun daga kan sunan littafi ake tantance in mai daɗi ne ko mara daɗi,"
  Ƙayataccen Murmushi jahad ta saki tare da Furta sunan Littafin*A SANADIN MAKWABTAKA*!
  Maimaita sunan Sehrish tayi"A sanadin makwabtaka"
  Jahad tace"kwarai kuwa,sunanshi kenan,"
  Gyara zama sehrish tayi tare da cewa"kawo wayar mu gani,zan jaraba karanta one page naji ya daɗinsa shin yakai Abban sojoji da nake jin friends dina nata faman cewa ya hadu"?
  Jahad tace"Ae ya zarce nan,"tayi maganar tare da miƙa mata wayar tace"one page kika ce zaki karanta,zan jira ki kammala don inci gaba daga inda na tsaya,"
   Hannu sehrish tasa tare da kar6ar wayar,ta buɗe page ɗin littafin asanadin makwabtaka,a natse ta fara karantashi,"
  Zuba mata ido jahad tayi tana jira taga reaction ɗinta,
  a hankali murmushi ya fara bayyana akan fuskar Sehrish,daga ƙarshe ma ta fashe da dariya,tunda tafara karanta littafin sae faman zabga murmushi takeyi,ita da tace zata karanta one page sai gashi ta zarce page biyar,ganin abun ya wuce gona da iri yasa jahad sanya hannu ta kar6e wayar tana cewa"Ya isa haka,je ki kwanta,gobe akwai shirye shiryen waleema,"
  ɗaure fuska sehrish tayi tare da cewa"wlh baki isa ba,sai da kika fara ɗanɗana mun zuma abakina na lasa daga baya kuma kizo kice zaki hana ni"?
    itama jahad ɗin ta tamke fuskarta tace"ae ni na fara karantawa tun farko,ke da bakisan ma da zaman littafin acikin wayarki ba sai da na faɗa maki"
wurga mata harara sehrish tayi tare da miƙa mata hannu tace"Bani wayata,"
  Jahad tace"wlh bazan bada ba,sai na kammala karanta littafin nan,"
  Abu kamar wasa suka shiga cece kuce,ran sehrish yayi mugun 6aci,aikuwa ta cakumi wuyan rigar jahad,nan fa suka shiga kokowa asaman gadon kamar ƴan wrestling,wani bugu da Sehrish takai ma jahad a kumatunta ne yasa ran jahad ya 6aci,a fusace tayi wurgi da wayar Sehrish,kai tsaye ta faɗi saman tiles,ta daku sosai ji kake taratssss!screen ɗin wayar ya tarwatse,
  Tashin hankali,
la66an sehrish har kerma sukeyi wurin cewa"kika fasa mun wayata"?
  Girgiza kai jahad tayi hankalinta a matuƙar tashe tace"dan Allah sehrish kiyi haƙuri,wlh bada sanina nayi hakan ba,raina ne ya 6aci saboda naji zafin bugun da kikai man"
  Hawaye ne suka cika idon Sehrish cikin murya kamar ta mai son yin kuka tace"Ni babban baƙin ciki na,ba wayar data fashe bane,nasan daddy zai iya canzamin wata,Amma littafin fa?a ina zan same shi,daga ji zai dauke ma mutum damuwa yasa shi nishadi"?
   Jahad tace"Am so sorry sehrish,na maki alƙawarin cewa,zan nemo maki shi,nasan baza a rasa me shi ba,akwai wata class mate ɗina sunanta hafsat bature,ta kware wurin karanta littattafan hausa,insha Allah idan muka koma school zan tambayar maki ita,nasan bazata rasa littafin a wayarta ba,idan ma babu littafin to ina da tabbacin cewar tasan marubuciyar shi,sae ta bamu numbar wayarta,"
  Jin haka yasa sehrish sakin murmushin jin daɗi,matsawa tayi tare da rungume jahad tace"yawwa jahad,kinyi tunani mai kyau,nagode sosai,yakamata mu kwanta yanzu,dare yayi fa sosai,"
  tayi maganar ayayin da ta gyara kwanciyarta,itama jahad ta kwanta,atare su kayi addu'ar bacci cikin ƙanƙanin lokaci baccin ya ɗaukesu,

"Nagode sosai da shawarwarin daka bani,kuma insha Allah ina da tabbacin cewar in muka biyo mashi ta wannan hanyar zamuci nasara akanshi,abun zai zama tamkar wasan kwaiwayo," Acewar Abbansu junaid dake tsaye a bakin ƙopar fita daga ɗakin Uncle abusufyan,Uncle ɗin na a bayanshi fuskar kowannansu ɗauke da murmushi,da alama sun kammala tattaunawar da sukeyi,

"Nike da godiya yaya Hossain,idan har wannan abun ya tabbata,zanfi kowa farin ciki,"

Juyowa Abba yayi cike da zolaya yace"kada ka manta,gobe ne fa sunan Æ´an ukun da aka haifa maka,me zaka yanka masu"?
..sunnar dakai ƙasa Abusufyan yayi yana dariya,yace"Sa za'a yanka masu guda uku,raguna uku,ɗawisu guda uku,ƴan shila guda ɗari uku,kaji guda ɗari uku suma,"
   Dariya Abba yayi yana bubbuga kafadarshi yace"Abun ya ƙayatar dani wato komai guda uku kenan za'a yanka masu,idan ma ba uku ba to ɗari uku,dole dae ukun ta fito kamar yadda suke ƴan uku,a ƙagare nake da goben nan tayi,bari na hanzarta zuwa na kwanta,"
  "Allah ya nuna mana ita lafiya,"acewar abusufyan daga haka Abba ya bude kopar tare da fucewa yana faɗin"mu kwana lfy,"
   Bayan fitarshi,Abusufyan ya koma tare da hayewa saman katafaren gadonshi,yayin da idanunshi ke fuskantar ceiling,bakomai ne ya faɗo mashi aranshi ba face ABU,a kullum cikin tunanin wani hali take ciki yake,haƙiƙa ya damu da ita sosai,kusan kullum ne sai yayi mafarkinta,dama da yawa idan ka sanya abu aranka,zaiyi wuya bakayi mafarki akansa ba,babban abunda yafi damunshi duk in zai ganta a mafarkin cikin wani irin mawuyacin hali,
  "Bakomai ne yasa na damu sosai akanta ba,face sanin cewa ita marainiya ce,bata da kowa a duniyar nan wanda zai damu da ita idan bani ba,da kuma ƴa'ƴan data haifa ba,Abu bata da kowa bata da wanda zai neme ta idan wani mummunan abu ya faru da ita,da ace ƙaddara bata haɗani da Abu ba harna aureta ba,a yau akace ta 6ace,nayi imanin cewa babu wanda zai damu akan hakan,mahaifinta ne kawai shi kuma Allah yayi mashi rasuwa,Allah yajiƙanka baba buzu,haka ya damƙa mun amanarta,duk da yasan halina bana jin magana ga ƙuruciya dake fusgata,yayi mun halaccin da bazan ta6a mantawa ba,kuma Insha Allah zan ruƙe mashi amanar daya bani,bazan ta6a mantawa dashi ba,saboda shine silar komai,gashi har nasamu ƙaruwar ƴan uku tare da ƴarsa,naso ace yana raye nasan zaifi kowa farin cikin ganin jikokinsa,'
  Hawaye ne suka soma gangarowa daga cikin idanuwansa masu ɗumin gaske,murmushin takaici ya saki tare da gyara kwanciyarshi,ya runtse idanunshi daƙyar bacci ya ɗauke shi,

A 6angaren Abba kuwa,bayan sun rabu da Uncle abusufyan,yana shiga bedroom ɗinshi,ya tsaya turus ganin junaid kwance yana sharar bacci,ga mommynshi agefe tana bacci itama,girgiza kai yayi tare da cewa"bansan meyasa junaid keyi mun haka ba,ya raina ni wlh,"juyawa kawai yayi tare da fucewa daga bedroom ɗin ya koma upstairs bedroom ɗin junaid ya nufa ya kwanta,ya ƙyale shi ne saboda yana cikin farin cikin gobe walima,baison abunda zai 6ata ranshi,
Chapter 26 · 0% Book details