← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 212

Sashe 157

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarshi ya É—auko ya lalubo Layin Hafsat ya danna mata kira,Kamar jira takeyi ta É—aga kiran,
  "Daughter ina sauraronki!maganar menene kikeson Yi dani"?
"Daddy dan Allah ka taimaka,Nasan zaiyi wuya ka fahimceni,wlh Mommy tana cikin mawuyacin hali,Ta zama abun tausayi,ta kira ni da wani layi jiya tana kuka tana rokona cewa inyi maka magana ka yafe mata,Ta gane kuskurenta,Rayuwarta ta wulakanta Daddy a gefen bishiya take kwana zaune ba bacci,dare da rana a wurin nan take Yini......."
Tunkan Hafsat takai ƙarshen Maganarta,Ishaq ya katse ta"ke yanzu kin yarda da maganarta?Kodai kun haɗa baki ne da ita?
  Da sauri hafsat tace"Wlh daddy da gaske take,Ae nasa ta ɗauko mun video ɗinta,Wayarma fa aronta takeyi don ta kiramu,Zan tura maka video ɗin ta whatsapp yanzu,zaka shaida abunda nake faɗa maka,"
  Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da cewa"its okey,Am waiting for the video,"yana kai ƙarshen maganar ya katse kiran,Kafin Ya kunna wifi ɗinshi ya shiga whatsapp,Messages ne suka fara shigowa cikin wayar,can sai ga saƙon hafsat ya shigo,

Chat ɗinsu Ya shiga,Anan ya samu video ɗin data tura mashi,yatsanshi yasa ya ɗan ta6a video ɗin nan take Ya soma loading,ƙura ido Ishaq yayi akan Screen ɗin wayar yana kallon video ɗin,
   Bai ta6a tunanin zaiga laila a irin wannan ƙasƙantacciyar rayuwarba,a gefen bishiya take zaune,gefenta kwanon bara ne,ƙafarta ɗaya ta lalace babu kyan gani wani irin ruwa ke fita acikinta,Sae kuka takeyi tana magana
  "Don Allah Ishaq ka taimaki rayuwata,ba don halina ba,dan Allah da manzonsa zakayi,Nasan nina jefa kaina cikin wannan halin,Ku kalli irin wurin da nake rayuwa,kowa ƙyamar taimakona yake yi,babu mai son zuwa wurina saboda warin da nake yi,"_
  Saboda tsabar tashin hankali,Da sauri Ishaq ya kashe video ɗin tare da yin wurgi da wayar saman sofa ɗin,
Jingina bayanshi Yayi ajikin kujerar,tabbas Yaji tausayinta amma abunda ya ɗaure mashi kai shine taya akai taje Enugu!Uban me yakaita?don a iya saninshi bata da wata alaƙa da garin,Ya jima a haka kafin Ya ɗauki wayar Ya sake kiran Hafsat,
  Tana ɗaga kiran Yace"Naga video ɗin,wlh hafsat ba don zuciyar musulunci ba,babu abunda zaisa na taimaki Laila!ke bari in faɗa maki zan taimaketa ne kawai Saboda Allah!Taci albarkacinki hafsat!Zansa a ɗaukota akaita asibiti,Inyaso ko ƙafarce su cireta A maidata maiduguri,Amma ni bazan sake rayuwa da laila ba,"
  Fashewa hafsat Tayi da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,daƙyar ta samu ta tsagaita da yin kukan tace"Nagode sosai Daddy,koma miye laifinta ne,ita taja ma kanta,naji daɗi sosai Daddy Am really proud of u,"
  "Yaushe zaki dawo gida!kinsan cewa hutun aikin da kika ɗauka ya qare ko"?
  "Eh daddy,Ina nan ina shirin dawowa amma yanzu gidan bazaiyi mun daɗi ba,nafison na zauna a wurinsu Abba,tunda ga ƴan uwana acikin gidan inyaso sai ka nema mun transfer na dawo aiki a Abuja,"
  "Idan kika koma Abuja,ni kuma fa?nikaɗai akeso inyi ta zama a kaduna "?
  A ɗan shagwa6e hafsat tace"idan zaka ƙara aure,Sai in dawo nan,"
Murmushi ya saki anzo dai dai inda yafi so,
  "Calm down ur mind,just ki dawo gida kawai,Cikin ƴan kwanakin nan Nima zanyi aure,"
  Yana jiyo sautin dariyarta,alamar taji daɗin maganarshi,sun jima suna waya kafin suka Yi sallama,

*Boss Bature*

*AMANI*

Tana kwance saman gadonta,Amal ta faɗo cikin ɗakin Hannunta ruƙe da wayarta,hawa saman gadon tayi har zuwa inda Amani ke kwance tana sharar bacci,Hannu tasa tana bubbuga ƙafarta,
  "Aunty Amani!ki tashi ana kira,"
Daƙyar ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,sun ɗanyi jawur dasu,rai a6ace ta kalleta"Bana hanaki tashi na daga bacci ba in aka kira ni"?
  Sunnar dakai Amal tayi"Am sorry,dama Aunty hayaam ce ta kira tana kuka......"hankali aɗan tashe Amani ta yunƙura tare da mikewa zaune tana faɗin"kuka kuma!Allah yasa lafiya,"ta ƙarasa maganar tare da kar6ar wayarta da Amal ke miƙo mata,
  Call log ta shiga,Anan taga kiran da hayaam tayi mata,
  Calling ɗin layin tayi,bayan Hayaam ta ɗaga kiran Amani ta kara wayar a kunnanta,tun kafin tayi sallama taji shessheƙar kukan Hayaam
  "Subhanallahi!wai meke faruwa ne?hayaam ki buɗe baki kiyi magana mana,"a ɗan ruɗe tayi maganar,
    "Kodai Wani ya rasu ne"?
Sai lokacin Hayaam ta soma magana"Aunty amani muna cikin masifa!munga rayuwa,rayuwarmu ta wulaƙanta a idon jama'a......"anan hayaam ta kwashe dukkan abunda Ya faru bayan komawarsu maiduguri ta sanar da ita,
  Saukowa Amani tayi daga saman gadon tana ambaton"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,. 
  "Allah yajiƙan Mammy,Allah ya gafarta mata zunubbanta,Amma banji daɗin irin mutuwar da tayi ba,ƙaddara ta riga fata,da kunsani tun farko baku barota ba,
  Cikin shessheƙar kuka hayaam taci gaba da magana,
  "Munaji muna gani,zama gidanmu ya gagaremu,Mutane sun ɗaura mana karan tsana,Yanzu haka a gidan Malam limam muke,matanshi sun tsanemu,suyi ta tseguminmu suna zaginmu,Abinci basu bamu sai in liman yana acikin gidan,Abra ma sai addu'a domin kuwa ta fara samun ta6in hankali,sai sambatu takeyi tana faɗin duk ita taja,Itace tayi silar mutuwar Mammy...."kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da ya cuyota,
  Daƙyar Amani ta lallasheta"kuyi haƙuri ku rungumi ƙaddara,in sha Allah komai zai wuce,Yanzu nidai zanyi ƙoƙari wurin ganin na taimaka maku,Ko gidan ne a gyara maku shi,kafin Allah ya kawo maku mazajen aure,don kuwa yin auren shikaɗaine rufin asirinku,in ba haka ba mutane bazasu daina tsangwamarku ba,"
  (Wlh matsalar mutananmu kenan,idan mutun Ya aikata zunubi arayuwarshi yazo ya yi nadama ya shiryu,Sai su dinga tseguminshi suna ƙyamatarshi,Shi kanshi Allah daya halicce mu yana son bayinsa waɗanda suka Tuba daga aikata zunubi,Amma wasu mutanan da ruƙo,shiyasa wasu ko sun shiryun daga baya sai su koma ruwa saboda mutane,Wannan babban kuskure ne saboda mutane ka koma kana aikata barna,Makomarka zaka duba,In zaka tuba dan Allah zakayi,Dan kuma kanka,ba don mutun ba,a karshe ina mai jan hankalinmu da mu kiyaye harshenmu don zai iya jefamu a halaka,aduk lokacin da wata mummunar kaddara ta fada ma wani muyi Addu'a mu nemi tsarin Allah kada mu rinka zundenshi don muma bamu fi karfin Allah ya jarabemu ba,Allah ubangiji ya rabamu da mummunan kaddara yasa mufi karfin zukatanmu,Amin )

Sosai Hayaam ta shiga yi mata godiya,kafin daga bisani Su kayi sallama,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 6 na marece,Sehrish na kwance saman gadonsu abun duniya ya isheta,duk ta shiga damuwa saboda rashin samun kwakkwarar hujjar da zasu kama Azmee,tana cikin wannan zancen zucin taji an banko kopar ɗakin,A firgice takai idanuwanta kan mai shigowa,Jahad ce ta faɗo ɗakin fuskarta sharkaf da hawaye,a ruɗe Sehrish ta shiga tambayarta Lafiya,
  "Bakisan meke faruwa ba,Ga Abba can ya yanke jiki ya faɗi rai hannun Allah,"jin wannan maganar yasa Sehrish ta sauko daga saman gadon jikinta na kerma ta nufi hanyar fita ɗakin,atare da jahad suka fita,

Abunda ya faru,Alex na zaune gefen gado tana jiran fitowarshi daga toilet,tun da ya shiga shiru bai fito ba,tun tana sa ran fitowarshi harta fara tunanin ko lafiya kusan Awa ɗaya da rabi yana acikin toilet ɗin nan,Miƙewa tayi ta nufi toilet ɗin tasa hannu ta kwankwasa ƙopar"Abban Junaid!"ta kira sunanshi da ƙarfi,Shiru bai amsa mata ba,a ƙarshe dai ta yanke shawarar shiga ciki,tana tura ƙopa ta same shi kwance saman tiles,idanuwanshi sun jirkice,jikinshi sai kerma yake yi,Fasa ƙara Mommy tayi anan ta zube tana jijjigashi,Ganin cewa dagaske fa baya acikin hayyacinshi yasa ta miƙe da gudu ta fito daga ɗakin tana kuka,

A lokacin Abusufyan da abu suna zaune a main palour tare dasu Hosana da Jahad,Tun daga kan yarda ta faɗo falon Yasa su miƙewa suna tambayar lafiya,Kasa buɗe baki tayi sai dai nuna masu hanyar bedroom ɗinshi da tayi duk tabi ta ruɗe,da gudun gaske Abusufyan ya nufi ɗakin tare da abu,suna shiga ciki dama ƙopar toilet ɗin abuɗe Mommy tabarta,nan suka sameshi cikin mawuyacin hali,sunyi matuƙar girgiza,Cuccuboshi Abusufyan yayi ya fito dashi daga cikin toilet ɗin,Ya janyoshi zuwa saman gadon ya kwantar dashi,jiki na rawa Ya curo wayarshi saboda ruɗu daƙyar ya iya lalubo Layin Sgr ya danna mashi Kira,Sai daya bi kowannansu Ya sanar dashi halin da Mahaifinsu ke ciki,

A lokacin dasu Sehrish suka faÉ—o falon Ya yi dai dai da shigowar Omar da Sgr,da gudun gaske suka shigo kaitsaye suka nufi bedroom É—in Abbansu,wucewarsu keda wuya Kanal yousouf ya faÉ—o falon da gudu shima Ya wuce part É—in,gaba É—aya sai da matasan gidan suka hallara a É—akin,wasu tuni sun fara zubar da hawaye,tsoransu kada su rasa mahaifinsu a wannan halin da suke ciki,sae faman ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un suke yi,

Fawan dasu twins kuwa tuni sun fara kuka kamar wasu ƙananun yara,
  "Addu'a zakuyi mashi ba kuka ba,in sha Allah zai samu lafiya,"acewar Abusufyan shi kanshi dauriya kawai yake yi,don kada suga rauninshi,hakan zai ƙara tayar masu da hankali,
   yanke shawarar kaishi Asibiti suka yi,Sgr ne ya ɗauke shi asaman kafaɗarshi,Sauran suka bi bayanshi,
  Suna fitowa entry hall ɗin gidan,da gudun gaske armstrong ya buɗe mashi mota ya kwantar da Abbansu aciki,Sannan ya bude mashi front seat ya zauna,Jan motar yayi da gudun gaske motar Marshal tabi bayansu,Motocinsu Kanal yousouf suka rufa masu baya,hada Oummansu Sehrish aka tafi asibitin a motar fawan ta zauna tare da Jahad da Hosana,Mommynsu Junaid kuwa tana a motarsu Abusufyan sai lallashinta Yake yi,duk ta shiga damuwa alokacin motocinsu suka fita daga babban gate ɗin gidan,mutun uku aka bari a gidan Aunty Azmee dake kumshe a ɗakinta,Sae Haroon dake kulle a medical room dinsu,

Sehrish bata samu tabisu ba,daga komawa ta ɗauko mayafinta sai dai tajiyo tashin motocinsu,kamar tayi hauka lokacin da ta fito waje bata samu motar ɗaya daga cikinsu ba,anan ta zuƙunna gaban ƙopar palourn tana kuka,ga tsoron shiga gidan da takeyi,

Da wata irin jiniya motocinsu suka hau saman titi a jere,Lokacin da suka ƙaraso Katafaren Asibitin Sgr,Sai suka tsaida jiniyar,a hanzarce bayan sunyi parking ɗin motocin nasu,Sgr ya fito Ya ɗauki Abbansu,sauran ma suka fito gaba ɗaya suka wuce cikin asibitin,Zo kaga taron nurses da likitoci,Ai tunda suka ji isowar Sgr kuma suka ji cewa Mahaifinshi ne baida lafiya,nan fa sukayi dandazo domin duba lafiyarshi,

A wani katafaren É—aki suka kwantar dashi,kusan likitoci shida ne akanshi daga cikinsu hada Doctor Emran,
Chapter 157 · 0% Book details