Sashe 117
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Daga waje suka koma,Saman waiting seats suka zauna suna jiran tsammani,É—age kanshi yayi jikin seat din yasa Hanky ya rufe fuskarshi,Allah kaÉ—ai yasan irin raÉ—aÉ—in da yake ji acikin Zuciyarshi,bakowa yafi ji ma tausayi ba,Fa ce Abbansu,don muddin yaji irin Mummunar mutuwar da Junaid yayi tofa Zuciyarshi zata buga ne,A rasa duka biyun,Sojojin dake a kewaye dasu,sai tausarshi sukeyi ganin yadda kamanninshi suka sauya saboda damuwa,
 "Haƙuri zamuyi yalla6ai,nasan abun da ciwo,raɗaɗinshi yafi ƙunar wuta,Amma ya zamuyi?mutuwa ce tana akan kowa,Junaid addu'armu yake bukata a yanzu,Allah ya jiƙanshi,ya gafarta mashi zunubbanshi,Yasa can yafi mashi nan,Su kuma waɗanda suka shirya mutuwarshi,Allah ya tonu asirinsu,don bazamu ƙyalesu ba,sai sun ɗanɗani kuɗarsu,"sosai Major ya shiga tausarshi yana ƙara ƙarfafa mashi guiwa,
 a hankali Omar ya zame hanky ɗin dake akan fuskarshi,ta kumbura sosai la66ansa sunyi suntum,idanuwanshi sunyi jawur dasu luhu luhu,daƙyar ya iya buɗe baki yace"Nagode sosai Major,naji daɗi sosai,kalamanka sun dan sanyaya mun zuciyata,Amma inaso ka sani rashin Junaid atare damu babban gi6i ne,wanda babu wanda zai iya cike sa,he's our weakness!maƙiyanmu sunci galaba akanmu!Sun kashe mana duk wani ƙwarin guiwa da muke dashi!laifin me junaid ya aikata da ya cancanci wannan ɗanyen hukuncin?Yaron da baison komai ba,Soyayyar ƴan uwansa kawai ya sani,burinshi koda yaushe ya sanya kowa farin ciki,amma yau an samu wasu marasa imani,Marasa tausayi,sun yi silar mutuwarshi!wlh ɗaya daga cikinsu bazai shaba,Sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin duniyar nan,"yana magana hawaye na wanke mashi fuskarshi,
Major na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,Suka jiyo hayaniya daga can cikin asibitin,Sautin kuka suka jiyo mai sautin gaske,Gaban Omar ne ya faɗi rasss jin Muryar jahad wadda tun a jiyan su major suka sa aka maido ta nan,A hanzarce suka miƙe tsaye suna kallon wurin da sautin ke fitowa,da gudun gaske take tunkarosu nurses sun biyota da gudu,sae ihu takeyi tana faɗin"wuta!wuta!Junaid yana acikin wuta,ataimaka a fito mun da ɗan uwana,kada ta ƙona shi,"wannan shine sambatun da takeyi,tashin hankali!
 Duk da jikinshi ba ƙwari haka ya nufeta,tare da ruƙota jikinshi,idanuwanta sun juye kwata kwata bata iya gane wanene agabanta,ita dai kawai sunan junaid take ambato acikin bakinta,hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kar ace ta samu ta6in hankali,don da alama abunda ke shirin faruwa kenan,
  "Jahad!ki natsu ki kalleni,Ya Omar ne fa"
 Kuka takeyi sosai,jijiyoyin wuyanta duk sun firfito waje,don bala'e Allurar kashe jiki akayi mata,Amma babu abunda allurar tayi mata,tamkar an ƙara mata ƙarfin jikinta,baiwar Allah taga tashin hankalin da bata ta6a gani ba,kuma akan Masoyinta da take tsananin so,
 Jijjigata ya shiga yi yana ambaton sunanta"Jahad!Ina zaki je?
  Firgita tayi agigice ta dinga faɗin"Gashi can!yana kuka wuta!wuta!ke ci ajikinshi!Yana kuka,Ya Omar a fiddo shi kada ya mutu ya barni,"da ƙarfi take yin maganar tamkar maƙoshinta zai 6allo,ƙoƙarin ƙwacewa take yi daga hannunshi don taje wurin abunda idanuwanta ke hango mata,Ko ina ta kalla,sai taga motar junaid tana ci da wuta,shine abunda idanuwanta ke nuna mata,
 Hawaye ne suka kuma wanke mashi fuskarshi,tsananin tausayin jahad ne ya kamashi,gaba ɗaya babu natsuwa atare da ita,ta haukace ta gigice ta firgice,kamar wadda tayi shekara ɗaya tana hauka,
  Hannu yasa tare da sa6arta saman kafaɗarshi,saboda rashin ƙwarin jikinshi,har tangal tangal yayi kamar zai faɗi daƙyar ya samu ya tsayar da kanshi,wuce wa nurses ɗin sukayi gaba yabi bayansu,yana jin yadda jahad keta bugun bayanshi,ta dunƙule hannayenta sae ɗumarshi take yi don ya saketa,Allah sarki innocent girl kamar jahad,yau ta zauce har tana bugun Ya Omar ɗinsu,
 Er nurses ɗin suka wuce har zuwa room ɗin da aka kwantar da ita,Shiga yayi da ita ciki,a lokacin har jikinta ya fara saki,alluran da aka ɗurka mata sun fara aiki,a hankali ya kwantar da ita saman gadon,kamar matacciya haka ta koma,ko yatsanta bata iya ɗagawa,la66anta sun bushe sosai,sun farfashe sakamakon ciccijesun da tayi,tsayawa yayi daga tsaye yana kallonta,idanuwanta suna a rufe,tunda yake a rayuwarshi bai ta6a fuskantar tashin hankali irin na jiya da kuma yau ba,bai ta6a cin karo da mummunar rana ba,irin ta yau,ta ko'ina babu sauƙi,zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi saboda ƙunar da takeyi mashi,
 Shigowa cikin ɗakin Major yayi tare da wani baturen Likita,jin sallamarsu yasa Omar juyawa yana kallonsu,da sauri ya tunkari Doctor ɗin yana tambayarshi dangane da jahad,
 "She is having a panic attack as a result of the incident"acewar Dr Antony,
  Dafe kai Omar yayi da hannu ɗaya ya ɗan runtse idanuwanshi tare da buɗesu,Muryarshi a kasalance yace"Yanzu Doctor babu yadda za'ae yarinyar ta dawo cikin hayyacinta!"
 Dr Antony yace"It will be very difficult for us to overcome her now,but we will do our best to see her regain consciousness,"
 "Pls Dr,try as much as u can"
Jinjina kai Dr antony yayi,tare da dafa kafaÉ—ar Marshal don ya lura baya acikin hayyacinsa
  "Calm down ur mind,she will be ok,zamu yi iyakar bakin ƙoƙarinmu wurin ganin mun shawo kanta,"
  Daga haka Major ya ruƙo hannunshi suka fito daga waje,zama fa bai gansu ba,Zarya ya shiga yi tsakanin room ɗin da Jahad take ciki dakuma room ɗin Sgr,sam ya kasa samun natsuwarshi tuni ya mance da shima mara lafiya ne,ana cikin wannan tashin hankalin,Tsautsayi yasa Omar ya kar6i wayarshi daga hannun Major,Yana kunnata kwatsam!sai ga kiran Abbansu ya shigo cikin wayar kamar jira yake yi,!
 Zubawa screen ɗin wayar ido yayi,tare da ɗagowa ya kalli Major,tun kafin ma yayi magana,major ya riga shi cewa"Abba ne ko"?ɗaga mashi kai yayi alamar eh,
  "Seriously I can't pick his calls,saboda bansan amsar da zan bashi ba,if he asks about junaid,"ba don yaso ba haka ya katse kiran Abbansu,Abunda bai ta6a yi ba arayuwarshi,
yana ƙoƙarin kashe wayar gaba ɗaya sai ga message ya shigo ta sama,hannunshi na kerma ya buɗe message ɗin,fearfully ya soma karantawa,
 _Omar kun kyauta ku dukanku,kowa yaƙi ɗaga kiran wayata,dama inaso in sanar dakai cewa,Yau zamu dawo gida_
 Saboda tsabar kiɗima,Omar baisan lokacin daya saki wayarshi ba,ta faɗi ƙasa sosai ta daki tiles ɗin,
 "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!Allahumma ajirni fil masibati wa'aklifni khairan Minha"wannan shine abunda yake ambato acikin bakinshi,
  "Major menene mafita?Ka taimaka min!abubuwa sunyi mun yawa,Ya zanyi da rayuwata!Babu Junaid,Jahad ta zauce!Ga Sgr ma a kwance gadon asibiti,Na shiga uku ni yau!wannan wace irin baƙar rana ce!?
 Wani irin tausayinshi ne ya lullu6e major,janyoshi yayi ajikinshi ya rungumeshi sosai,dama a buƙace yake da ya samu kafaɗar da zai aza kanshi,Ya zubar da hawayenshi sosai,ko ya rage raɗaɗin dake acikin zuciyarshi,
 Cikin shessheƙar kuka yace"Major menene mafita yanzu?Ya zanyi da Abbansu?
 Hannu major yasa yana ɗan bubbuga bayanshi yace"Sir,in sha Allah komai zai tafi dai dai,bazamu rasa abunyi ba bi'iznillahi,"
  Ruƙo hannun Omar yayi suka koma saman waiting seat ɗin suka zauna,kwantar da kanshi ya kumayi asaman kafadar major,sai faman sauke ajiyar zuciya yakeyi,bakomai yake faɗo mashi arai ba,fa ce Fuskar Baby Junaid ɗinsu,mai ɗauke da wannan kyakkyawan Murmushin,
  *Boss Bature*
*Sehrish*