← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 212

Sashe 34

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"WaÉ—annan sune Æ´an ukun Abusufyan É—in"modibbo ne yayi maganar yayin da idanunshi ke akan Su jahad dake zaune sunyi zuru zuru,'
  Har suna haɗa baki wurin cewa"Sune,"
Jinjina kai yayi tare da mayar da idanunshi kan Ammi yace"Ki kace yaran shaggu ne ko?Wata hujja gare ki na cewar bada aure ya haifesu ba?
  Fuskarta aɗaure tace"Ina da hujja,saboda nice mahaifiyarshi,kuma ni bansan an ɗaura mashi aure da kowa ba,"
  Girgiza kai modibbo yayi,sannan yace"hannunki ya taso ne?ko kuwa wurin ki kaɗae za'a iya ɗaura mashi aure ne"?
  Shiru tayi batace masa uffan ba,cigaba da magana yayi"don haka baki da wata hujja ta cewar abusufyan yayi aure ko baiyi aure ba,ya samu ƴa'ƴa,wlh Aisha kin ban mamaki!wai har yaushe ne zaki ajiye waɗannan makaman yaƙin naki ne?ke fa yanzu ba yarinya bace,kin tara ya'ya da jikoki amma har yau bazaki ajiye wannan zafin ran naki ba,sai yaushe ne ya'yanki da kuma jikokinki zasu ji daɗin zama dake ne?yanzu ni ba misali bane agareki?ko bakisan wanene modibbo ba?kinfi kowa sanina bani da wasa ko miskala zarratin,duk wani kangararre acikinku,keda ƴan uwanki nine nan nake tankwarashi,amma yanzu saboda na manyata,na tara ya'ya da jikoki,duk na ajiye waɗannan ɗabi'un,Na canza kaina ne ba don komai ba sai don saboda ya'yana da kuma jikokina suji daɗin zama dani,kuma suyi alfahari dani amatsayina na kakansu,bawai su dinga tsoro na ba,suna gudu na harma su dinga yi mun fatan mutuwa,kamar ke ɗin nan dai.....'yayi maganar yana nuna ta da sandar hannunshi,sunnar dakai Ammi tayi tana faman jinjina kai,

Canza harshe modibbo yayi izuwa harshen fulatanci,yayi hakan ne saboda kada faÉ—an da zaiyi mata ya zama tamkar tozarci ne agaban jikokinta,

  "Gaba ɗaya kin takurawa rayuwar ya'yanki,da ta jikokinki,kin hanasu sakat,ko irin wasan dake tsakanin kaka da jikan nan bakya yi masu,kullum burinki ki ƙuntata rayuwarsu,shin menene ribarki idan kinyi hakan? Ya ɗan dakata da maganar yana kallonta,kafin yaci gaba da cewa"Yanzu jibi yaran nan ƴan wurin fatima,hakanan kika ɗaura karan tsana kika ɗaura masu sai kace ba jininki ba!in ma saboda mahaifiyarsu ne,ke kin ta6a ganin inda laifin wani ke shafar wani ne?in kuwa haka ne ae da dukkanmu mun shiga uku,saboda wancan zaiyi sata ne a ɗaura maka laifin bayan bakai ne ka aikata ba,"
  Katse shi tayi cikin harshen fulatanci tace"Amma yaya modibbo ni meyasa ya'yana basu jin maganata ne?basu ɗaukeni mahaifiyarsu ba,suna yin abu gamon kansu batare da sun sanar mun ba,Hossein ya ƙetare ƙasar nan yaje yayi aure batare da sani na ba,sai dai kawai na ganshi da mata ya dawomin,matar kuma ma farar fata ba jinsun mu ba,sannan kuma Abusufyan shima yayi aure batare da sani na ba,saboda me zasuyi mun haka ne?
anzo dai dai wajen,acewar modibbo gyara zama yayi sannan yace"kin manta yadda akai kika auri salahuddeen ne?to idan kin manta bari na tuna maki,dama duk wanda ya bijire ma iyayensa ko ba daɗe ko ba jima sai shima yaga ba dai dai ba,na farko bada sa hannun iyayenmu ba,kika shiga aikin Soja,babu irin yadda ba'ayi dake ba don ana ganin bai dace dake ba,ba kaman daya kasance ke bafullatana ce,amma kika ƙeƙashe ƙasa kikace sai kinyi aikin soja,a ƙarshe da aka takura maki,shine kika tattara kayan ki kika dawo gidana da zama saboda kina tunanin cewar ni zan goya maki baya don ki samu abunda kikeso,da kika zo wurina a lokacin na nuna cewar nima bazansa hannu na ba acikin lamarin tunda har iyayenmu sun nuna basu so,a ƙarshe sai kika gudu batare da sanin kowa ba,kika shiga aikin Soja,sae dai kwatsam muka ganki da kakin Soja ajikinki,ko ba haka akayi ba"?

Wata irin zufa ce ta shiga wankowa a fuskar Ammi sam bata ta6a tsammanin cewa wannan ƙaramin kuskuren data aikata na bijirema iyayensu,zai dinga bibiyar rayuwarta bane,
"Akan wannan aikin sojan da kika shiga,babu wanda baiyi kuka dake ba,saboda kafiya,da taurin kai irin naki,ga jinkai dake gareki,iyayenmu basu isa su baki umarni kai tsaye kiyi abu ba,sai sun biyo ta wurina saboda shakkarki da suke ji,bayan wannan kuma,baki sanar ma kowa ba game da salahuddeen lokacin da kuka fara soyayya dashi ba,sai daga baya ne muka fahimci shi ya hure maki kunne har kika bijire mana kika shiga aikin sojan,hakan kuma yasa duk muka ki amincewa da farko ki aure shi,amman da yake Allah ya kaddaro aure tsakaninku ba yadda muka iya dole muka kyale ki ko don kafewar da kika yi da kuma rabon itama Ameena anan zata samu mijin, ko ba haka akayi ba"?
  Jinjina kai Ammi tashiga yi yayin da idanunta suka cicciko tab da kwalla amma bata bari sun zuba ba,
Gwaggon katsina kuwa,sae faman sakin murmushi takeyi,tana faÉ—in"kwarai kuwa,haka akayi,"Abban su junaid kuwa da hajiya azeema duk jikinsu yayi mugun sanyi,sae yanzu suka gane daga inda matsalar take,dama duk in mutun yaga rayuwarshi tana tafiya ba dai dai ba,kuma bai akaita wani zunubi,toWlh ya binciki kanshi!ya tuhumi kanshi ahankali zai gano dalili,

Su jahad dae suna nan tsugunne sun kasa kunne suna sauraronsu,sai dai subi bakin modibbo da kallo,daga bisani in Ammi na magana subi ta da kallo saboda basu iya fulatanci ba,haka Marshal Omar dasu ishaq duk basa jin fulatanci,haka zalika Sgr baya jin harshen nasu,dama shi ko hausa daƙyar ya koye ta,kuma har yau in yana magana da harshen hausa sai ka gane cewar ɗan koyo ne don sam hausarsa bata nuna ba shiyasa bai fiye yin magana da hausa zalla ba saiya haɗa da turanci ko spanish,amma kuma hausar tashi ba ƙaramin daɗi takeyi ma mutane ba,
Chapter 34 · 0% Book details