← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 212

Sashe 16

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Daughter"! ƙiris ya rage ta saki tray ɗin dake hannunta,don bata tsammaci jin muryar mutun a bayanta ba,bakowa bace wannan face Sehrish wadda ke tsaye a cikin kitchen tana shiryama Sgr fresh fruits tare da coffee,jikinta na sanye da doguwar riga ta bacci mara nauyi milk colour tayi rolling mayafi akanta launin baƙi,
Ganin daddynsu yasa ta sakin murmushi tare da cewa"daddy,dama idonka biyu bakayi bacci ba har wannan lokacin"?
  ƙarasa shiga kitchen ɗin yayi yana cewa"taya zan iya baccin?bayan ɗaya daga cikin ƴa'ƴana idonta biyu bata runtsa ba,raina ne ya bani cewar akwai wadda batayi bacci ba acikinku shiyasa na fito don inga wacece ashe kece...."
fashewa da dariya sehrish tayi jin abunda yace,shima dariyar ce É—auke a fuskarshi,
..tsayawa yayi dab da ita yana kallon kayan marmarin da ta kammala Jera ma sgr,ta gyare tsaf ta yayyanka mashi su,
  "Yanzu wannan kayan daɗin duk na wanene?ko ke zaki sha"?yayi tambayar a yayin da yakai hannunshi cikin ƙayataccen tray din wanda ke ɗauke da plate na kayan marmarin ya ɗauki yankin abarba ɗaya tare da turata abakinsa yana sha,
  "Bani zan sha ba,na babban yaya ne,"tunkan ta ƙarasa maganar taga ya dakata da taunar abarbar da yake yi yana kallonta fuskar shi ɗauke da mamaki yace"Kina nufin Rafayet kika shiryama wannan?shiya sanyaki ne"?
  Jinjina kai tayi tare da cewa"eh daddy,shine ya buƙaci na dinga kai mashi fruit tare da coffee adai dai irin wannan lokacin ƙarfe sha biyu na dare in sun dawo daga aiki....'daƙyar ta ƙarasa maganar ganin yadda fuskarshi ta canza,alamar wani abu baiyi mashi daɗi ba,
  "Daddy wani abu"?ta furta hakan tana kallonshi,
  shiru yayi jimmm kamar mai nazarin wani abu,kafin daga bisani yace"da sanin Abbanku"?
  girgiza kai tayi alamar a'a sannan ta ƙara da cewa"yasan cewa inayi mashi aiki daddy,amma banda tabbacin cewar ko yana da masaniya akan hakan,bansani ba ko babban yayanmu ya sanar dashi,'
  ta6e baki Uncle abusufyan yayi kafin yace"Abba bazai ta6a bari ba,bana tunanin cewar ya sani,taya mace kamarki zata dinga zuwa ɗakin namiji a irin wannan lokacin!!?
  Gabanta ne taji ya faɗi rass,sunnar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannnunta,
  "That's imposssible!!!Banaso gaskiya hakan bai kwantamin araina ba,duk da ɗan uwanki ne shi a yanzu,amma hakan bai dace ace kina zuwa ɗakinshi ba a irin wannan lokacin,in fact ba'a son mace da namiji suna ke6ewa,nasan kinsan da wannan!"
  Muryarta na kerma tace"Hakane daddy,
  Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Yawwa,ɗauki kayan marmarin ki kai masa,kada ki makara,"
  Hannunta na kerma ta ɗauki tray din da sauri da sauri ta nufi hanyar fita daga kitchen ɗin,har ta kusa fita daga cikinsa,muryarshi ta dakatar da ita,
  "Sehrish,"
"Na'am daddy,"ta amsa mashi tare da É—an juyawa ta baya tana kallonshi,
  "daga yau!banaso ki ƙara zuwa don kiyi mashi aiki,koda da safe ne ko da rana,Azmee itace mai aikin gidan nan,idan ma da buƙatar masu aikin zansa a ƙaro wasu,amma ba zakuyi aiki wa kowa ba,ina fata kin fahimce ni,'
  Tunda abusufyan ya fara maganar gabanta ya shiga faɗuwa,hankalinta yayi mugun tashi,tuni idanunta sun fara canza launi,
  Fuskarta ɗauke da damuwa tace"daddy,inajin tsoran shi sosai,bansan taya zan sanar dashi hakan ba,'
  Murmushi Abusufyan yayi tare da takawa kusa da ita suna fuskantar juna yace"Bance ki sanar mashi ba,kawai inaso daga yau ki ɗan ɗaga ƙafa daga zuwa part ɗinsa don kai mashi abinci ko yi masa gyara,nasan cewa bazai damu da hakan ba,tunda ga azmee,in ma yayi magana akan hakan ki sanar dashi cewa"NI NA HANAKI!"
  wani irin wahalallen yawu Sehrish ta haɗiye a bakinta,sam bazata iya yima daddyn nasu gardama ba,tasan cewa yayi hakan ne saboda tausayinsu da yake ji,baison suna aikin wahala,amma wannan hukuncin da ya yanke mata ba ƙaramin horo bane agareta,Na farko hakan zai nisanta tsakaninta da SGR,ganinshi zaiyi mata ƙaranci,in har ba downstair ya sauko ba,Allah ya haɗasu to bafa zata samu damar ganinshi ba,Abu na biyu kuma hayaam zata samu damar shige masa,don tasan cewar daga ta daina yin aiki a ƙarƙashinsa,hayaam zata kunno kai,na uku kuma batasan me zai biyo baya ba,in har yasan cewar ta daina yi mashi aiki,Shin zai damu ko bazai damu ba.....'
  "Zaki iya tafiya,kada ki jima a bedroom ɗin nashi,dare yana ƙara yi,da zarar kin kai mashi,kiyi hanzarin komawa cikin ƴan uwanki ki kwanta kiyi bacci ki huta,
  "Toh Abba,zanyi duk yadda kace,"
Murmushi abusufyan ya saki tare da cewa"ki kulamin da kanki daughter,sai da safe,"
murmushin tayi itama bayan ta amsa mashi,batare da 6ata lokaci ba,ta wuce sashen Sgr,kamar wadda aka zare ma lakar jikinta haka take tafiya,ba don komai ba sai don Hukuncin da Daddy É—insu ya yanke,Taya zata iya rayuwa batare da tana sanya babban yaya acikin idanunta ba akai akai!anya kuwa zata iya jurewa?wa zai kula mata dashi kamar yadda take kula dashi?tashin hankalin da ba'a sama shi date,

Wani irin farin cikine ya lullu6e hayaam dake la6e wurin kitchen ɗin tana sauraron abunda Uncle abusufyan ya tattauna tare da sehrish,kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha don tsabar farin ciki,ashe munafukar tana la6e ta kasa kunne tana sauraronsu,bakomai ya fito da ita ba daga ɗakinta face yunwar da taciyota,hakan yasa ta lalla6a ta fito don ta sama ma kanta abunda zata ci,anan ne fa tajiyo muryoyinsu suna magana acikin kitchen ɗin,shine tayi masu la6e,ta kwashe duk abunda suka tattauna acikin kunnanta,Lokaci guda ta manta ma da yunwar da take ji acikin cikinta,gudu gudu sauri sauri ta koma bedroom ɗinta,faɗawa tayi saman gadonta tana faman tiƙar dariya,bayan ta tsagaita da yin dariyar tashiga tufka da warwara acikin zuciyarta,
  "Idan har inaso in samu nasarar cigaba da zama acikin gidan nan,dole saina haɗa kai da wani!wanda zai taimaka mun,wurin ganin na cimma burika na!tabbas ina bukatar shi,"ta ambaci hakan ayayin da take ƙoƙarin miƙewa daga zaune,
  *WANENE SHI*!?

*Surgeon General Rafayet*

A ƙopar shiga bedroom ɗinshi ta tsaya,zuciyarta duk a ƙuntace take,don idanunta acike suke tab da hawaye ba don komai ba sai don hukuncin da daddynsu ya yanke agame da zuwanta part ɗin SGR,yanzu shikenan Yau zata kasance rana ta ƙarshe da zatayi aiki a sashen shi?shikenan bazata ƙara takowa ba da sunan ta kula dashi ba? 😥

Tamkar ta fashe da kuka haka ta dinga ji,dakyar ta daure ta cije tare da zuba sallama,shiru ba'a amsa mata ba hakan yasa ta ƙara daga muryarta,ta kuma zabga sallamar akaro na biyu,shima shiru bai amsa mata ba,hakan yasa ta fara tunanin cewa kodai yayi bacci ne ko kuma yana acikin toilet,don tasan shi akwai yin wankan dare duk in xai kwanta,

Tunani tayi ai shi muharraminta ne a yanzu hakan yasa ta kutsa kai tare da shigewa cikin bedroom ɗin nasa,wani irin daddaɗan kamshi ne ya daki hancinta,mai daɗin gaske,ga ratsa zuciya,lumshe idanunta tayi a hankali tare da sake buɗesu,tana ƙare ma shimfiɗeɗen gadon nashi kallo,kasa janye idanunta tayi daga kallon shi da takeyi,Yana a kwance saman gadon,yayi covering jikinshi da lallausan blanket ɗinsa,dai dai saitin stomach ɗinsa bargon ya tsaya,sumar kanshi ta rufe mashi fuskarshi da alama dae a gajiye suka dawo yau,baccin ma kamar bai shirya mashi ba ya ɗauke shi,duba da yadda yayi kwanciyar,right hand ɗinshi na asaman kanshi ya zagayo dashi ta dayan 6angaren,

A hankali sehrish ke nufar gadon nasa tana tafiya kamar wadda kwai ya fashe mawa akai,saboda rashin kwarin jikinta,ajiye mashi tray din tayi asaman side table ɗinsa,sannan tashiga tunanin,kodai ta tashe shi daga baccin kota ƙyale shi?ta jima tana nazari kafin zuciyarta ta bata shawarar cewa ta tashe shi kawai,ganin cewa ba kayan bacci ne ajikinsa ba,hakan na nufin baiyi night bath ɗin daya saba yi ba,tabbas bazaiji daɗin baccin shi ba,
  Zuba mashi ido tayi tana ƙare mashi kallo,anan taga zufa na tsattsafowa a saman dogon hancinsa,da kuma wuyansa,mamakine ya kamata,aranta tace"Zufa kuma?duk da sanyin A.c dake akwai?karfa ace babban yaya bashi da lafiya"?cike da damuwa tayi tambayar,can kuma tace"kodan baiyi wankan daren daya saba yi bane?zai iya yiyuwa hakane,amma fa ina tsoran tashin shi daga bacci,
  Bari dai kawai na haƙura kar in jama kaina,don na lura kwanan nan ɗaure mun fuska yake yi,kamar nayi masa wani laifi,'
Tana kai ƙarshen zancen zucin nata,tayi wani kwakkwaran juyi da nufin tabar wurin,cikin rashin sani tayi tuntu6e da doguwar ƙafarsa ɗaya data sauko ƙasan gadon,birkicewa tayi duk yadda taso ta ruƙe jikinta amma abun ya faskara,gaba ɗaya ta tafi ɗungurugum ta faɗa saman jikinshi,
Chapter 16 · 0% Book details