Sashe 135
Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wuri ta samu saman 2 seater ta zauna,Ishaq ya zauna saman 3 seater,
A tsanake ta soma magana bayan sun gaisa"Am Lailan tana ciki ne"?
 "A'a,bata nan fa,bata sanar dake bane"?
 "No Bata sanar dani komai ba,ai na faɗa maka ina ta trying layinta a kashe,"magana takeyi tamkar bata son motsa la66anta,dama hajjaju anji wayewa,ishaq kuwa sai ƙara kalleta yake yi,
  "bazan 6oye maki ba,Zancen gaskiya mun rabu da laila,Ni banma son inda take ba ayanzu ha...."bai ƙarasa maganar ba ganin yadda ta zabura ta miƙe tsaye tana faɗin"ka rabu da laila"?
Murmushi Ishaq ya É—an yi kafin yace"Calm down ur mind,koma ki zauna,"
 Muryarta tamkar zatayi kuka tace'haba Ishaq,taya zaka ce mun in zauna?zaman me zan yi kuma,bayan ka rabu da laila!amma gaskiya banji daɗin wannan maganar ba,"
 Zuba mata ido yayi yana kallonta,sai da ta kai ƙarshen maganarta,sannan yace"pls ki koma ki zauna,I will explain to you,"
 Fuskarta aɗaure ta koma ta zauna tare da cewa'wlh Ishaq ka bani mamaki,sam ni baka yi mun kama da irin mazan dake sakin matansu ba,meyasa zaka yiwa laila haka?idan ma laifi tayi maka,at least kodan saboda Hafsat ai bai kamata ka rabu da ita ba"
..shiru ya ɗan yi batare da yace komai ba,har sai da ta hasala,ta soma ƙoƙarin miƙewa"Ni zan wuce,dama saboda Laila nazo,tun da kayi mana tsiyar taku ta maza,banga amfanin zama na ba,"
 "Pls kada ki tafi,i will explain to u as i said,"Yanayin yadda ya furta maganar kamar akwai damuwa atattare dashi,hakan yasa ta gyara zamanta,tare da cewa"ina sauraronka,"
.."Ban cika son ina faɗin sirrikan matata ba,kuma bana ɗaya daga cikin mazajen da suke fallasa sirrin dake tsakaninsu da matayensu,so kamar yadda kika ce,banyi maki kama da mazajen da suke sakin matayensu ba,inaso ki ci gaba da yi mun wannan kyakkyawon zaton,Sam ni a tsari na babu sakin mace,kuma ke shaidace!kinsan wacece laila,kinsan halinta,bakowani namiji bane zai iya jure zama da mace irinta ba,amma haka ni na daure na rufe idona na zauna da ita,bayan duk irin Girman laifukan da take yi mun,Laila ta kaini maƙura ne,shiyasa har na zartar mata hukuncin saki........"Anan Ishaq ya kwashe dukkan Abunda ya faru tsakaninshi da laila game da irin Zaluncin da ta yiwa ƴa'ƴan Uncle ɗinshi ya sanar mata,
 Saboda tsabar tashin hankali,Hajjaju ta shiga zabga salati tana faɗi "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Dama su Sehrish ƴa'ƴan Abusufyan ne?"
 Cike da mamaki Ishaq yace"Dama kin sansu ne"?
 "Nasan su mana,Ae ni ce silar tura ita Sehrish din aikatau a anan gidanku,Ashe dama jininku ne su?Ya salaaam,"ta ƙarasa maganar tana dafe kanta da hannunta ɗaya,
 "Wlh Nayi danasanin rashin sanar dakai da ban yi ba,Nazo naga Hosana da Jahad,acikin gidan nan,tunda na kallesu dama nasan cewa suna cikin mawuyacin hali,bayin Allah,"
 "Dama kinsan da zamansu acikin gidan nan?kuma baki sanar damu ba?bayan kinsan halin ƙawartaki"?
 Idanuwanta cike tab da kwalla tace"Wlh banyi dabarar yin hakan ba,Amma ae komai ya wuce,kuma wlh nayi murna nayi farin ciki sosai da kasancewarsu ƴa'ƴan Abusufyan,in sha Allah idan na samu zuwa can abujan zanje na kai masu ziyara,"
Sun jima suna tattaunawa akan su Sehrish,bayan sun kammala firar tasu ne,Hajajju tace"Yanzu,mu dawo kan laila,"da sauri Ishaq ya katse ta da cewa"karfa kice zaki bani shawarar in mayar da ita,"
 Girgiza kai tayi"a'a ni na isa,kawai dai yakamata kayi zurfin tunani,banso ka yanke mata hukuncin saki ba,ka jima tare da laila,kodan albarkacin hafsat bai kamata ka rabu da ita,Ya kakeso rayuwar hafsat ta kasance babu uwa atare da ita"?tayi maganar tana kallonshi,
 "Hajjaju kenan!hafsat ba ƙaramar yarinya bace,ta mallaki hankalinta,ba zata yi maraicin uwa ba,zan iya sawa ayi mata transfer ta koma Abuja da aiki,in yaso sai ta zauna a wurinsu Abba,"
Â
"Kai kuma fa?ba zakayi maraicin rashin mace atare dakai ba?nasan dole ka buƙaci kulawa,gashi gidan ma ko mai aiki babu,"tayi maganar tana ƙarewa gidan kallo,
 Wani ƙayataccen murmushi Ishaq ya saki,anzo wurin da ya fi so,
  Jingina bayanshi yayi ajikin sofa ɗin tare da cewa"kin faɗi gaskiya,ina buƙatar mace atare dani,musamman wadda ta iya ɗaukar wankan lace,ta iya kashe ɗaurin kallabi,Sai dai ina jin tsoran na sake yin aure,saboda matan ne basu da tabbas,"
  "Ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,kada ka yanke hukunci akan abunda baka da masaniya akanshi,Dole akwai na gari kuma akwai na banza,shiyasa kafin mutun yayi aure yake da kyau ya tsananta bincike,Don ya sama ma ƴa'ƴanshi uwa ta gari,haka mu ma matan,"
 Sam bata kawo komai aranta ba,tana kai ƙarshen maganar ta ɗauki hand bag ɗinta tare da mikewa"Ni zan wuce,"bata jira amsarshi ba,ta nufi hanyar fita daga falon,
 Da sauri Ishaq ya miƙe tare da yin hazarin shan gabanta,ba arziki ta tsaya tana kallonshi,
  Marairaice mata fuska yayi"pls Kada kiyi mun haka mana,nasan kin fahimci abunda nake nufi,koda ban fito na bayyana maki ba,"ya ɗan daka da yin maganar yana jiran amsarta,
 "Sauri nake yi,dan Allah ka bani hanya na wuce,ae kasan alaƙata da laila,So bai kamata kayi mun wannan maganar ba,"
 "Ita laila ɗin ciki ɗaya kuka fito da ita ne"?yayi maganar tare da tamke fuskarshi,
 Girgiza kai tayi alamar a'a,
 "Ko akwai wani hadisi ko aya daya haramta wa namiji ya auri ƙawar matarshi"?
 Nan ma ta sake girgiza mashi kai"ko ɗaya babu,Amma ae ana barin halas ko dan kunya,Ishaq idan ma da wannan manufar kazo mun,Ni bazan iya aurenka ba gaskiya,ba wai don ka ta6a auren ƙawata bane,No kawai bana ra'ayin ƙara kasancewa da wani ɗa namiji ne,"
 "Koda ace ni ne"?yayi tambayar fuskarshi da alamun damuwa,shiru tayi bata tanka mashi ba,a qagare take ma daya bata hanya ta wuce,
   Cikin sanyin murya yaci gaba da cewa"Na jima da dakon sonki acikin zuciyata,Yanzu ne nasamu ƙwarin guiwar sanar dake,ko alokacin baya nayi kawaici ne kawai don saboda nasan bazaki amince da soyayyata ba,Saboda Ƙawanccan dake tsakaninki da laila,Amma yanzu babu Laila,meyasa zaki haramtawa kanki ƙara yin aure ne?nafa san komai agame da rayuwarki,lokacin da mijinki yayi hatsarin mota tare da ɗanki,hada ni cikin waɗanda suka halarci jana'izarsu,Nasan abun dole ya ta6a maki zuciya sosai,Amma Ya zakiyi?mutuwa ce kuma tana akan kowa...."
 Tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,cikin shessheƙar kuka tace"Dan Allah ka bani hanya na wuce"daƙyar sautin maganarta ke fita,
 "Zan baki hanya ki wuce,Amma kafin nan ki tsaya ki saurari maganata,kina buƙatar wanda zai maye maki gurbin mijinki,kuma ni ashirye nake dana zama madadinshi,zan baki kyakkyawar kulawa in har kika amince kika aure ni,ke kinsan wanene ni basai na faɗa maki ba,bazan yabi kaina ba,Amma nasan kinsan komai a wurin ƙawarki laila,kuma nima a wurinta nake jin labarinki,"
 Natsuwa tayi tana sauraran kalamanshi,yayin da take ta wasi wasi acikin zuciyarta,
 "Daga ni har ke,babu yaro acikinmu dukkanninmu mun mallaki hankalinmu,Ki amince kawai nasan ba zaki rasa manema ba,Ni late comer ne,Amma da shiri na nazo bada wasa ba,inaso na haɗa zuri'a dake,Yaronki da kika rasa,Zaki samu madadinshi atare dani....."bazata iya jure sauraron kalaman Ishaq ba,da sauri tabi ta gefenshi da gudu ta buɗe kopar falon ta fuce tana kuka,Ya fama mata tsohon ciwon daya daɗe acikin Zuciyarta,
Jiki asanyaye Ishaq ya koma saman sofa ya zauna tamkar ya fashe da kuka haka yake ji,bai yi tunanin zata ƙi amince mashi ba,gashi tunda yayi arba da ita ya rasa natsuwarshi,
  *Marshal Omar*
Abun ya ɗaure mashi kai!tunda ya shigo bedroom ɗinshi ya same shi kwance yana ta sharar bacci,Yaushe rabon daya ga Sgr yana bacci irin wannan,tun kafin mutuwar Junaid,wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana ƙare mashi kallo,Har cikin ranshi ba ƙaramin daɗi yaji ba daya samu Sgr yana bacci,da alama tun da yadawo daga sallar Asuba yake kwance yana bacci,don bai cire jallabiyar jikinshi ba,
Zuba mashi ido omar yayi yana kallonshi,yayi hugging ɗin pillow sosai a ƙirjinshi,kasa tashin shi daga baccin Omar yayi,don bazai so ya katse shi ba tunda an samu baccin ya ɗaukeshi,don yafi kowa shiga matsananciyar damuwa akan rashin Junaid,da kuma Alƙawarin da sukayi ma mahaifinsu,
Motsi ya soma yi da la66ansa da alama mafarki yake yi,matsawa Omar yayi kusa dashi ya kasa kunne don yaji me yake cewa,Sambatu ne yake yi yana ambaton sunan Reesh,abun ya ɗaure mashi kai,instead yaji yana sambatu akan Halin da suke ciki kaman yadda yai tunani amma sai yaji yana ambaton sunan reesh,Wai ma sunan menene reesh ɗin nan?ya tambayi kanshi tare da kallon sama yana ƙokarin tunano inda yasan sunan,
 Sai da yayi zurfin tunani sannan ya gane cewa sunan Sehrish ne ya maida reesh,
 Ƙayataccen murmushi Omar ya saki,aranshi yace"shegen bisa na,Allah ya toni asirinka,Allah kadai yasan me ya aikata ma ƴar mutane jiya da har yake sambatu akanta,Haba no wonder!ba banza ba yake ta sharar bacci,mutumin da saboda tsabar tashin hankalin da muke ciki ko runtsawa baiyi amma yau gashi ya baje yayi ɗai dai saman gado yana ta bacci,"