← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 212

Sashe 61

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Fitowa tayi daga part É—in nashi,ta wuce kitchen don ta shirya mashi dinner É—insa,a kitchen ta samu Azmee ita da Saude,sun kammala dinner suna gyara kitchen É—in,gaishe dasu ta fara yi,fuskokinsu a sake suka amsa mata,
"Aunty azmee a shirya mun dinner É—in babban yaya,inaso zan kai mashi ne,"
Murmushi Azmee tasaki tare da cewa"Masha Allah,ki ce Anyi welcome back kenan,"
Dariya sehrish tayi har fararen hakoranta suka bayyana,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"ae daddy,Ya amince na cigaba da zuwa part É—insa,inayi mashi aiki,"
"Amma naji daÉ—in jin hakan sosai,yanzu bari na shirya maki dinner É—in,"
Amsa mata tayi da toh,sannan ta tsaya tana jiranta,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta kammala shirya mata a warmers da sauran food stuffs asaman tray,ta miƙa mata,kar6a sehrish tayi tare da kama hanyar fita daga kitchen ɗin tana faɗin"nagode Aunty azmee,"

Babu kowa a main palour É—in,yawanci duk basu kaiga dawowa cikin gidan ba,wasu kuma suna acikin É—akunansu,tana cikin tafiya hannunta É—auke da tray,taji maganar mutun abayanta,
"Ƴar shila,"a ɗan firgice ta juya don taga kowanene,gabanta ne ya faɗi Rassss!cike da mamaki take bin shi da kallo yaushe rabon da ta sanyashi acikin idanunta harta manta,ita duk a tunaninta ma an tura shi aikine,ashe yana nan cikin gidan,
Fuskar nan tashi ɗauke da wannan shu'umin Murmushin nashi,ya ƙarasa tare da cin burki ya tsaya tagabanta,Face to face suka fuskanci juna,
Jikinshi na sanye da rigar ankara har guiwarsa,sae wandon jeans,sumar kan nan nashi yayi mata É—an iskan gyaran gashin nan daya saba yi,an saisaye gefe da gefe na kan,tsakiyar kuma anbar sumar a tsaye ba ladabi,
"Nayi kewarki sosai,abubuwa da yawa sun faru,bansamu isasshen lokacin da zamuyi magana ba,naso nazo na taya ki Murna na kasancewarki ƴar wurin Uncle ɗinmu Abusufyan,abun ya ƙayartar dani,"
Sakin baki sehrish tayi tana kallonshi,abun ya ɗaure mata kai,Yadda yake tsara kalami kamar ba wannan mashayin giyar ba,wata irin natsuwa wadda bata saba ganinshi da ita ba,har wani kyau ya ƙara,yayi haske abunshi,duk da ramar da ya ɗanyi,
"Naji kinyi shiru baki ce komai ba"
Jin muryarshi yasa ta dawo daga zurfin tunanin da tashiga,muryarta a É—an ruÉ—e tace"amma kaine dagaske?ko an yi musayarka ne,"
Wani ƙayataccen murmushi ya saki na gefen fuska,kafin yace"Ni ne mana HAROON ɗin da kika sani,koda yake na canza a yanzu,nayi ma kaina karatun ta natsu,saboda inaso in zama mutumin kirki,kamar kowa,inaso na shiryu,don na samu mace ta gari,a kwanakin baya kin ta6a yi mun nasiha akan cewa kinaso nazama tamkar ƴan uwana,naji daɗin maganar nan da kikayi mun,kuma nayi amfani da hakan gashi yanzu ni kaina inajin daɗin sauyawar da nayi,"

Zuba mashi ido sehrish tayi tana ƙare mashi kallo har yakai ƙarshen maganar tashi,tayi matuƙar mamakin jin abunda haroon ke faɗa mata,kokwanto ta shiga yi anya haroon ba wani plan yake shirya mata ba?
Ganin ta tsaya tana kallonshi yasa shi gane cewar kokwanto takeyi akanshi,Cikin sauri yace"nasan zaiyi wuya ki yadda dani,saboda sanin da kikayi mun ada,amma na canza ayanzu fiye da tunaninki,"
"Amma na daina ganinka acikin gidan nan"?
"Masallaci nake kwana,shiya sanya baki cika ganina ba,yanzu bana jin daÉ—in zama ko ina,in ba masallaci ba,acan nake rayuwata,in kinga na fita daga cikin masallaci to wani abu mai muhimmanci ne ya fidda ni,kinsan na tara zunubi sosai shiyasa nake kusanta kaina da ubangiji sosae,saboda in samu yafiyarshi...."

Yanayin yadda haroon yayi mata maganar ba ƙaramin tausayi ya bata ba,domin kuwa har hawaye sun taru acikin idanunshi,wata siririyar ƙwalla ce ta gangaro cikin idonshi,da sauri ya sanya hannu ya shareta,
"Yaya haroon,ka daina zubar da kwallarka,tunda dai har ka shiryu ka koma ga Allah,zai kar6i tubanka ne,fata na shine Allah yasa ka daina duk wani abu mara kyau da kake aikatawa,"
Tana kai ƙarshen maganarta,yace"In sha Allah nadaina,bazan ƙara ba,Ni dai yanzu babban burin da nake dashi arayuwata shine in samu mace tagari inyi aure,zan fi samun kwanciyar hankali,"
"Kada ka damu,in sha Allah zaka samu,"
Tana kai karshen maganar ta kama hanya da sauri ta nufi upstairs,
Bin bayanta da kallo haroon yayi har sai da ta 6ace ma ganinshi,fashewa yayi da dariya,a fili yace"Mata kenan!zuciyarku da rauni take,wannan alƙawari ne na ɗaukar ma kaina,Sai na cimma burina ko da ace shikaɗae ne abunda zan aikata kafin in bar duniya,"yana faɗin hakan ya wuce bedroom ɗinshi,

Sehrish kuwa,tun bayan da tabar wurin,zuciyarta ke cike tab da tausayin Haroon,bakomai take tunawa ba fa ce fuskarshi,yadda yayi mata magana yau ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba,sanya ƙafarta tayi acikin falon Sgr,sannan ta shiga da sallama abakinta,ganin bai fito falon ba,yasa ta wuce bedroom ɗin nashi,sanin cewa ya shiga wanka,yasa ta shiga cikin bedroom ɗin kaitsaye batare da yin sallama ba,
Gabanta ne ya fadi rass!!ganinshi tsaye gaban mirror daga shi sai short ajikinshi,hannunshi ruƙe da comb yana taje doguwar sumar kanshi,
Juyawa tayi da sauri zata koma falon,ta cikin mirror ya hangota,gyaran Muryar da yayi ne yasa ta ɗan dakata daga ƙoƙarin da takeyi na fita daga bedroom ɗin nashi,

"Where are u going?"
Muryarta na kerma tace"Falo,dama dinner ne na kawo maka,"
"Okey,idan kin kai abincin falo,kizo inason ganinki"
Da sauri ta amsa mashi da toh,fita daga cikin bedroom ɗin tayi,a saman table ta ajiye mashi tray din kayan abincin,sai da ta bada kusan minti 10 sannan ta koma bedroom ɗin nashi,A lokacin har ya kammala zura sleeping dress ɗinshi,Red colour sun fito da natural beauty dinshi,gefen gadonshi ya zauna,tare da aza ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya,yana karkaɗa ƙafarshi ta hannun dama wadda ya aza asaman ta hagun,yayin da hannunshi ke ruƙe da wayarshi yana daddanawa
Da yatsan hannunshi yayi mata nuni da tazo gabanshi,cike da fargaba ta ƙarasa tare da tsayawa a tsaye tana faman zare ido,
"Haka ya dace ki tsaya gabana?C'mon Kneel down"!
Hankali atashe ta zube saman guiwowinta,jikinta nata faman kerma,
Tun kafin ya kuma cewa wani abu,tayi saurin cewa"Am sorry babban yaya,daddy yace na baka haƙuri game da abunda ya faru jiya,dan Allah kayi haƙuri,"
Banza yayi da ita tamkar baiji abunda tace ba,gaba É—aya hankalinsa na akan wayar hannunshi,sae da ya mula yasha iska sannan yace"Wanene SA"?
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,hannu ta aza akai tana fadin"Innalillahi!nashiga uku,"ƙasa ƙasa tayi maganar tuni ido ya raina fata,
"Idan har kika bari na maimaita tambayar da nayi maki,jikinki ne zai gaya maki",
Wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Wlh babban yaya ba dakai nake ba,su6ul da baka ne nayi bansan nace ba,kuma Allah bakai nace ma sa ba,Ni kawai nasan dai nace kullum fuska a ɗaure kamar sa,Kuma fa waƙa ce nake rairawa..."
Bata ƙarasa maganar ba,ya katseta da cewa"Just one answer nakeso!ki faɗamun menene ma'anar kalmar SA da kika faɗi,if not u will be in serious trouble,"tashin hankali!
Nan fa sehrish tashiga mazurai,shin tayaya zatayi mashi bayanin cewa shanu take nufi da sa!tabÉ—ijancan,hauka ma takeyi da zata sanar dashi ainihin mai kalmar SA ke nufi,ta fahimci cewa baisan menene SA É—in ke nufi ba,shiyasa har ya tambayeta don yaji ma'anarta,yadda zaiji daÉ—in hukunta ta,
Shirun da tayi mashi ne ya 6ata mashi rai,tsawa ya daka mata wadda ta firgitar da ita,a ruÉ—e tace"SIR na Yalla6ai nake nufi,wani malamin mu ne na makaranta,muke kiranshi da SA,kuna kama dashi sosai,kyakkyawa ne shima,shiyasa nace fuskarka irin tashi,"
Guntun tsoki SGR yaja,kafin yace"Tashi kiban wuri,"da sauri ta miƙe,ta fito daga bedroom ɗin nashi,gaba daya ma tabar masa part ɗin,don ta lura yau kamar asama yake,

Bedroom ɗinsu ta koma hannu tasa tare da tura ƙopar ta shiga ciki,Jahad ta samu a zaune saman gadon nasu hannunta ruƙe da wayarta,ta ƙurama screen ɗin wayar ido da alama wani abu take karantawa wanda yaja hankalinta har bata ji shigowar Sehrish ɗin ba,hosana kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita,tana kwance naɗe cikin bargo,
Chapter 61 · 0% Book details