← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 212

Sashe 112

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tracking layin Jahad su kayi har suka ƙaraso inda Motar junaid take,tunkan su fito daga cikin motar jikin kowannansu,yayi mugun sanyi,

A wani irin sukwane marshal Omar ya fito daga cikin Motar,da sauri mutane suka dinga darewa suna basu hanya don su wuce,Lokacin daya ƙarasa wurin da motar junaid take a ƙarmashe,ta lanƙwashe ta dagargaje,Jikinshi a mace ya zube saman guiwowinshi,komai ya tsaya mashi cak!tsit kake ji,
  Girgiza kai ya shiga yi da wata irin razananniyar murya ya shiga faɗin"innallillahi wa'inna ilaihirraji'un"!hannu yasa ya damƙi tokar dake a ƙasan wurin,Nan take ya fashe da wani irin matsanancin kuka,hawaye ne suka soma gangarowa asaman fuskarshi Major dake tsaye akansa,haka zalika sauran Soldiers ɗin dake a wurin kowannansu,idanuwansu cike taf da hawaye,tunda suke a rayuwarsu basu ta6a ganin hawayen Marshal ba sai yau,
   Cikin shessheƙar kuka ya furta"ku faɗamun meya faru dasu?ina ƙanina yake?Ina jahad"?
  Daƙyar ɗan sandar nan ya iya buɗe baki yace"Yalla6ai,A bayanan da muka samu a wurin mai siyar da ice cream ɗin da yarinyar taje,Sun tsayar da motarsu a bakin titin ne,ita yarinyar itace ta fito daga cikin Motarsu,tabar shi Yaron acikin Motar,ta tsallaka titi,kafin ta dawo ne,babbar mota tabi takan Motar,nan take kuma ta kama da wuta,koda muka iso bamu samu komai daga sassan jikinshi ba,
   Hannu Marshal Yasa ya tallabe kanshi,saboda wani irin jiri dake ɗibarshi,sai faman ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yakeyi,Yanke jiki yayi ya faɗi ƙasa a sume,
"yalla6ai!"major ne ya ambaci sunanshi da ƙarfi,tare da zuƙunnawa agabanshi,
  Suna cikin wannan alhinin saiga Motar journalists ta ƙaraso wurin,aikuwa tun kafin ma su sauko daga cikin motar,sojojin nan suka koresu daga wurin,a hanzarce suka ja motarsu suka koma,

  Sau uku suna yayyafa mashi ruwa,yana sake sumewa,hakan yasa suka cuccu6eshi izuwa cikin Motarsu,don su wuce dashi asibiti,

Jami'an ƴan sandar nan,sunyi ƙoƙari wurin ganin sun gano yadda abun ya faru,har street Cctv aka bincika,amma kash Camera ɗin ta jima da samun matsala,
  *Allah yajiƙan junaid,ya gafarta mashi,mutun mai kyakkywar zuciya irinta junaid,munayi mashi fatan dacewa don yayi mutuwar shahada,bawan Allah naji mutuwarshi sosai,don har hawaye saida na zubar,akan laifin da bashi ya aikata ba,Anyi silar mutuwarshi,saboda Soyayyar da akeyi mashi itace taja mashi,babu komai,wanda sukayi silar mutuwar tashi kowa zai ɗanɗani kuɗarshi ne,masu cewa junaid yayi azkhar da addu'a before ya fita,kada ku manta,idan lokacin mutun yayi koda sallah yake cikin yi ko agaban ka'aba ne hakan bazai hanashi mutuwa ba,yakamata mu tuna da wannan,bawa bai isa ya gujewa ƙaddararsa ba,ko da yayi addu'a in dae anan ajalinsa yake dole ya mutu ba makawa😭*

  *Boss Bature*

Rishraf,

Gabanshi ne yaji yayi wani irin bugu,ba arziƙi ya zame hannunshi daga saman ƙirjin sehrish,ja da baya yayi,yayin da hannunshi ke dafe da saitin zuciyarshi,hankalin shi yayi mugun tashi,lokaci guda ya rasa natsuwarshi,da sauri ya fuce daga ɗakin,hakan yaba Sehrish damar motsawa,ta ɗauki undi ɗinta dake ajiye a ƙasa,ta sanya ajikinta,wata irin kasalace ta baibayeta ga wani irin faɗuwar gaba da take ji,daƙyar ta lalla6a ta haye saman gadon ta kwanta,hannunta rungume da pillow,

Saukowa downstairs,yayi hannunshi na kerma ya zaro wayarshi,yama rasa wa zai kira gida,yaji kowa yana lafiya,ko wani abu ya faru ne?don yanaji aranshi cewa,Something is wrong,that's why yake jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa,
  Layin Marshal Ya kira,a lokacin wayar na a hannun Major,koda yaga kiran Sgr,ƙin ɗaga wayar yayi saboda baisan taya zai fara sanar dashi ba,game da mutuwar junaid,

Almost 3 times,wayar na ringing ba'ayi picking ba,layin junaid ya lalubo ya danna mashi kira,lokacin da aka sanar dashi cewa layin daya kira a kashe yake,nan fa hankalinshi ya ƙara tashi sosai,saboda tunda yake a rayuwarshi bai ta6a samun layin junaid a kashe ba sai yau,a ruɗe ya danna ma Abbansu kira,tana fara ringing,Abbansu ya ɗaga tun kafin ma yayi mashi sallama,muryar Abbansu ta katse shi da cewa"Rafayet!wai meke faruwa ne?ina ta kiran Layin junaid akashe!hankalina yaƙi kwanciya,"
  Muryar Sgr,a kasalance yace"Daddy,i don't know why nima na kira layinshi,switched off,Na kira layin Omar ma,tayi ringing ba'ayi picking ba"
  "Dan Allah rafayet,ka bincikamun meke faruwa a gidan nan,Hankalina bazai kwanta ba,in har banji muryar baby junaid ɗina ba,wlh har bacci ya fara ɗaukata amma na farka,saboda nasama raina zai kirani ne kamar yadda ya saba kirana,duk in dare yayi kafin ya kwanta,"acewar Abbansu,
  Jikin Sgr ba ƙaramin sanyi yayi ba,daƙyar ya iya cewa"In sha Allah daddy,zan yi ƙoƙari na haɗa ka dashi,"
  Daga haka sukayi sallama,zarya ya shiga yi acikin falon gidan,tunanin zuwa Abuja yake yi,don ji yake in har bai sanya junaid a idonshi ba,to hankalinshi bazai kwanta ba,

Ranshi ne ya bashi cewar,ya jaraba kiran layin Haroon may be,yana a gidan,can kuma ya soma tunani Anya ma yana da numbar haroon?tabbas baida ita,layin Major ya kira kaitsaye don ya samu ya haÉ—a shi da Omar,tunda na hannun daman shi ne,
  Lokacin da kiran ya shiga wayar major,suna tsaitsaye cirko cirko a cikin asibitin Sgr,Yana ganin sunan Sgr ya bayyana akan screen ɗin wayarshi,jiki na rawa ya kashe wayar gaba ɗaya,
  Abun ba ƙaramin ɗaurewa Sgr kai yai ba,kowa ya kira ba'a picking,shi Major ma kiran ya shiga,daga baya kuma aka kashe wayar,hakan ya ƙarasa shi zargin cewa wani mummunan abunne ya faru,
  Komawa Upstairs yayi da sauri bedroom ɗin da Sehrish take ciki,tura kopar yayi ya shiga,a kwance ya sameta rungume da pillow,

   "I know u are awake,inaso ki kiramin layin wani daga cikin sisters ɗinki,i wanna talk with them "
  Yunƙurawa sehrish tayi tare da kai hannu ta ɗauki wayarta da ta aje gefenta bayan ta kashe wakar,layin jahad ta lalubo ta danna mata kira,A lokacin wayar na a hannun Major ya kar6eta daga hannun police men ɗin,koda yaga kiran My Own sis ya shigo,ta layin jahad,kin daga kiran yayi har ya yanke,hakan yasa sehrish sake kira,sai ya kashe wayar gaba ɗaya,
  ɗagowa tayi tare da kallon Sgr,tun kafin tayi magana,ya riga ta cewa"Switch off ko"?ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tare da cewa"Bari na kira layin Hosana,"
  Numbar hosana ta lalubo,tare da danna mata kira,tana fara ringing hosana ta ɗaga kiran,muryarta da alamun bacci atare da ita,
   "Wai wanene ke kira na"?
Sehrish tace"ke nice,Ina jahad ne na kira layinta a kashe"?
   Hosana tace"tun ɗazu da suka fita da junaid shan ice cream basu dawo ba,inata jiransu har bacci ya ɗauke ni,"kafin Sehrish ta ƙara cewa wani abu,da sauri Sgr ya sanya hannu ya kar6e wayar,
  tare da karata a kunnansa"Ina Omar yake"?rass taji gabanta ya faɗi,daga kwance take,amma jin maganar babban yayansu yasa ta miƙe zaune,anatse tace"Wlh bansan inda yake ba,ko yana gida ko yana waje oho,ni dai ina ɗakinmu,"
   "Go to his bedroom right now,and see if he's around,"
Mikewa hosana tayi tare da saukowa daga saman gadon,gudu gudu sauri sauri ta wuce upstairs bedroom ɗin Omar,a buɗe ta samu ƙopar,turawa tayi ta shiga daga ciki,ko'ina ta duba,hada leƙa toilet ɗinsa,ganin babu kowa yasa ta sanya wayar a kunnanta,
  "Ya Rafayet,na duba ko'ina,amma banga ya Omar ba,"
  "Its okey,ki koma ɗaki,"yana faɗin hakan ya katse kiran,
  ɗagowa yayi da lumsassun idanuwanshi masu ɗauke da bacci ya kalli Sehrish itama kallon nashi takeyi,duk jikinsu yayi sanyi mika mata wayar yayi"take ur phone,"hannu tasa ta kar6a,
  Da sauri ya juya,jikinshi duk babu ƙwari a lokacin idonshi ya sauka kan belt din shi dake akasa,hannu yakai ya dauka ya fara kokarin maida shi jikinsa tare da fucewa ya nufi downstairs,a dai dai lokacin Abusufyan na fitowa daga ɗakin da suka kwantar da Abu,jikinshi sanye da jallabiya,
  Yana jin takun takalmi,yakai idanuwanshi wurin,yana ganin Sgr ya tunkareshi da sauri,
  "Rafayet!wai kunyi waya da Junaid ne?i ave been trying his phone number,Amma akashe!nayi traying har nagaji,since evening ya sanar dani cewa,zasu fita tare da jahad shan ice cream,inaso naji ko sun koma gida,itama kuma phone dinta akashe"
  Ƙarasa saukkowa daga saman benen Sgr yayi tare da kallon Uncle ɗin nasu yace"Uncle nima bansan meke faruwa ba,kowa na kira layinshi switched off,babu mai picking call ɗina,That's why na yanke shawarar zuwa Abuja yanzun nan zan bi jirgi naje can," ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin wucewa ta gefen Abusufyan,da sauri ya ruƙo damtsen hannunshi tare da cewa"A'a Rafayet!ka haƙura sai gobe mana ka wuce can ɗin,"acewar Abusufyan
Girgiza kai ya shiga yi tare da cewa"Bazan iya jurewa ba,inaso nasan meke faruwa ne acan É—in,na damu akan rashin jin muryar Junaid,daddy ma ya kira ni yanzu,yana cikin damuwa,ko don saboda shi inaso naje can na haÉ—ashi da junaid,if not ko bacci bazai iya yi ba,tunda ya sama ranshi son jin muryar junaid,"
  "Zanyi magana da yaya hossein ɗin,ka ajiye tafiyar nan dare yayi,sai zuwa gobe da asuba,"
  Ba don ya so ba,a dolenshi ya haƙura,komawa sukayi saman sofa suka zauna jigum jigum,Suna jiran tsammani,kowa da abunda yake saƙawa acikin ranshi,
 
*HAROON*
Chapter 112 · 0% Book details