← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 212

Sashe 100

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,hankalinta har ya kwanta da ta tabbatar cewa shine,Tayi tunanin wani mugunne yazo don ya cutar da ita,tayi farin cikin ganinshi sosai kamar tayi ihu,Amma ta wani 6angaren tsoran hukuncin da zai yanke mata take yi,duk a tunaninta yazo ne don ya hukuntata,tunda ya bata Command taƙi bi,
   Ganin irin kallon da yake yi mata ne yasa tayi saurin sunnar da kanta ƙasa,tana wasa da yatsun hannunta,
    Hanky ya zaro daga cikin trouser pocket ɗinsa,Ya miƙa mata tare da cewa"Take it,"hannu tasa ta kar6a,ta shiga goge fuskarta sosai,
   "In kawo maka ruwa kasha"?cikin sanyin murya ta ambaci hakan,
   Girgiza mata kai yayi alamar a'a,kafin ya wuce cikin falon,Ya zura hannayenshi biyu acikin aljihun wandonshi,
  juyowa tayi tana kallonshi,A dai dai lokacin suka jiyo sallamar Abusufyan"Assalamu Alaikum",
   Amsa mashi su kayi da"Wa'alaikum salaam,"
  Shigowa cikin falon yayi,hannunshi ruƙe da key ɗin Motarshi,
  Koda yayi arba da Sgr,cike da mamaki yace"Rafayet!Ashe dagaske ne,Abban ku ya sanar dani cewa,zai yi wa Omar magana ko shi ko kai wani yabiyo bayanmu don yaso yana nan muzo dashi,Banyi tsammanin cewa kaine zaka zo ba,Yanzu kawai ina karyo kwana da motata naga sojoji zagaye da gidan nayi ta mamaki cikin raina,Gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba," ya karasa maganar a yayin da yake ƙoƙarin rungumarshi,da alama Abusufyan ba ƙaramin daɗi yaji ba,Sai murmushi yake yi,
   "Na same ku lafiya,"?
"Lafiya lou Alhmdllh,Naje masallaci ne,na biya naga wani Abokina daga can kuma na wuce wani store zanyi mana siyayyar kayan abinci,Inata fargabar nabar yarinya ita kaÉ—ai acikin gida",
  Sgr yace"nayi mamakin ganinta ita kaɗai zaune acikin gidan,time ɗin dana shigo kuma bansan meya faru ba,duhu ko'ina,so sai daga bayane hasken ya dawo,"
  Abusufyan yace"Ae ɗaukewa su kayi da wutar ne,yanzu nima ina kan hanyar dawowa naga sun dawo da ita,"
  wurga idonshi yayi kan Sehrish dake tsaye hannunta ruƙe da hanky dinsa,ta kammala goge hawayen,
  "Daughter,zonan mana,"ya kirata da hannunshi,wurinsu tazo ta tsaya tana facing din Abusufyan,
   "Faɗamun meya faru?bayan na tafi"?
murmushi ta É—an yi,batare da tace komai ba,
   Mayar da idanuwanshi yayi kan Sgr yace"Amma dai ba nan zaka kwana ba ko"?
   "I will spend the night here,"
Abusufyan yace"ba ka ga yadda gidan yake ba ne?Ni nasan bazaka iya bacci acikinsa ba,Yakamata ka wuce hotel kawai,ina ganin zaifi maka daÉ—in zama,"
  Girgiza mashi kai yayi"No,i wanna stay here," gyaɗa kai abusufyan yayi tare da kallon sehrish yace
  "Sehrish ki kaishi bedroom ɗin da kika gyara,ya zauna acan,Amma dai banso ba wlh,Don nasan cewa zaka takura sosai,Ga zafi ga sauro duk da na siyo maganin sauron,Amma bana tunanin zai iya dakatar da saurayen dake acikin gidan nan,"
  Amsa mashi tayi da toh,Sannan ta juya tare da kallon Sgr tace"Mu shiga ciki,"
  Gaba tayi yabi bayanta,daƙyar yake iya taka kasan palourn,saboda daudar dake a wurin duk da sun gyara shi,
  Shiga cikin bedroom ɗin su kayi atare,Wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana ƙarewa ɗakin kallo,
  "Kana bukatar wani abu,in kawo maka,"
   "No need"ya ambaci hakan a yayin da yake zaro wayarshi daga cikin aljihun wandonshi,
"Sehrish!"Abusufyan ne ya kwala mata kira,da sauri ta juya ta fita daga É—akin,
  Komawa tayi cikin palourn A tsaye ta same shi,Ga kayan da yayi masu siyayya hada gass cylinder saboda yin girki,Sojoji ne suka shigo dasu,A cikin buhu guda biyu,sae cylinder ɗin da suka ajiye nan,
  Ƙarasawa tayi wurinshi,"Gani Daddy,"
   "Kunyi magana dashi ya fada maki ko yana buƙatar wani abu?"
"a'a bai bukaci komai ba,"
Shiru Abusufyan ya dan yi,ganin damuwa akan fuskarshi yasa tace"Meya faru daddy," hannu yasa ya ɗan shafa sumar kanshi kafin yace"Daughter,bazai iya kwana acikin gidan nan ba,Ni nasan waye rafayet,Wlh nayi mamakin ganinshi banyi tsammanin cewa shi zaizo ba,Kalli fa gidan nan ki gani,babu wani shiri da mukayi,yanzu da zarar an ɗauke da wutar nepa,Shikenan zafi zai rufe mu,kuma ko kaɗan baison zafi,Gashi da ƙyankyami toilet idan bana bedroom ɗinshi ba,baya shiga na kowa,Kuma dole ya buƙaci yin wanka,Ni bansan ya zamu ƙare dashi ba,"
  Murmushi Sehrish tayi,ita kanta ta jinjina ma ƙarfin hali irin na Sgr,yadda yake da ƙyanƙyamin nan,Amma a haka yace zai kwana acikin gidan,Koya zasu ƙare,?
  "Daddy,kada ka damu,tunda yaji ya gani,zai kwana anan ɗin ka ƙyaleshi kawai,"
  Gyaɗa kai Abusufyan yayi tare da cewa"Shikenan kawai,Yanzu dai bari na shiga da kayan abincin nan kitchen,"
  Yayi maganar tare da sa hannu ya dauki buhu ɗaya,hannu tasa itama ta kama ɗayan buhun,taja shi izuwa cikin kitchen,bayan sun kammala kwashe kayan sunkai kitchen,
  Ta dube shi tare da cewa"Zan iya dafa mana ko taliya ce?
  Abusufyan yace"Kina jin yunwa ne"?
  "A'a,bana ji,saboda kai dama zan dafa,naga bamu ci Dinner ba,
  "Ki barshi kawai,akwai kayan tea dana siyo da bread,idan kina jin yunwa ki haɗa ki sha,Yanzu dae bacci nake ji,"
  Yayi maganar yana hamma,
"A ina zamu kwana"tayi tambayar tana kallonshi,
"Ki wuce inda mijinki yake mana,Ni zan kwana a palour ne,Ki dauko mun bargon da zan É—an shimfiÉ—a in akwai"
  "Toh" ta amsa mashi tare da
  Kama hanya ta fuce daga cikin kitchen ɗin,Shima fitowa falon yayi ya tsaya a tsaye yana jiranta,

Lokacin da ta shiga bedroom ɗin,A kwance ta samu Sgr yana bacci ya ƙure fankar ɗakin har ƙarshe,iska ta ko'ina,hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba,wurin wardrobe ta wuce ta sanya hannu ta buɗeta,daga gida na kasa blanket din suke tare da bedsheet,hada mosquito net,
   Bargo ta dauko mashi,Sannan ta koma falon,har lokacin Abusufyan na atsaye,yana jiranta,
   Ƙoƙarin shimfiɗa mashi tayi,da sauri yasa hannu ya kar6i bargon tare da cewa"Yawwa My Own Daughter,nagode sosai,"
"Sae Allah yakaimu Daddy,"fuskarta asake tayi maganar,
  "Allah ya kaimu lafiya,take care of my son,don't allow even one mosquito to bite his skin,If not ranki zai 6aci,"cike da zolaya yayi maganar,
  Fashewa tayi da dariya,tare da juyawa tana faɗin"don't worry daddy,In sha Allah i will look after him,very well,"
  Gyara kwanciyarshi yayi saman sofa ɗin,cikin lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dashi,
  Komawa cikin bedroom ɗin tayi,bedsheet ta dauko acikin wadrobe ta shimfiɗa a kasa,sannan ta matsa wurin gadon,ta ɗauko pillow guda ɗaya ta ajiye shi saman zanin gadon,
   Wurin switch taje,ta kashe light ɗin ɗakin,Nan take duhu ya gauraye ɗakin amma ba sosai ba,akwai hasken ƙwan dake a falo guda daya da aka bari akunne,ya ɗan haska ɗakin nasu,
    Moving tayi izuwa wurin gadon inda Sgr ke kwance yana bacci,addu'o'i ta shiga karantowa tana ɗan tattofa mashi,bayan ta kammala ta koma saman shimfiɗar da tayi,ta gyara kwanciyarta,sai da itama ta karanta addu'o'in tabi ta shafe jikinta kafin ta rufe idanuwanta,bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,

Around 1:30 na dare,Ƴan nepa suka yi tsiyar tasu da suka saba,Tashin hankali,Ƴan sakanni da ɗauke wutar fanka ta tsaya cak,Wani irin zafi ya fara ziyarta ɗakin,Sai ga mutanen da gudun gaske sun fara kwararowa cikin ɗakin,Buuuuuuuuuu da wani irin kuka mai sautin gaske,tun yana juyi saman gadon yana kai hannu yana buge sauron dake ƙokarin attacking ɗinshi,har ya fara ƙokarin farkawa,Wata irin zuface ta soma tsastsafo mashi ajikinshi,Sharkaf ya jiƙe,tuni numfashinshi ya soma kokawar fitowa daga hancinshi,kamar an toshe shi,A firgice Sgr ya farka yana faman zazzare blue eyes ɗinshi,Hankalinshi yayi mugun tashi,arayuwarshi ya tsani sauro ko miskala zarratin baisan halittar nan,bai taso a inda ke akwai taba,Amma yasanta sarai a matsayinshi na Dr yasan irin cututtukan da take haifarwa,Gashi ya tsani duk wani abu da zai naƙasa lafiyar jikinshi,tuni jikinshi ya soma kerma,hannu yasa ya ɗebe rigarshi gaba daya,ya shiga kokawar korarsu daga kusa dashi bayan ya kunna fitilar wayarshi dakin yayi haske,ji kake fass fass!kaff kaff!!haka ya dinga bubbugesu,duk yabi ya ruɗe,

Cikin bacci Sehrish ta dinga jin muryarshi yana faɗa da sauraye yana fadin"Don't come close to me!Am gonna shoot you"tashin hankali Sgr fa ya zauce da alama,duk sun rikitashi sun mayar dashi ƙaramin mahaukaci,Idan ya sanya riga bala'e biyu,ga zafi ga sauro,idan ya cire rigar kuma Sauraye zasu sha jini,bai da choice,
  A firgice ta farka,hankalinta a matukar tashe ta mike daga kwancen da take saman bedsheet ɗin,Wurin shi ta ƙarasa,yanayin da ta ganshi gaba ɗaya ya rikice ba ƙaramin tausayi ya bata ba,gaba daya yabi ya susuce ya hargitsa sumar kanshi,
   "Ya Rafayet,"ta ambaci sunan shi da wata irin kasalalliyar murya ta mai bacci,ƙoƙarin hawa saman gadon tayi don ta taimaka mashi ta kore mashi su,kafin su san abunyi,ae tana hawa saman gadon,ya ƙanƙameta ya rungumeta sosai,A faɗace yake ce mata ta kori saurayen su fita su bar ɗakin,ko ya harbesu da bindiga,tuni taji hawaye sun cicciko mata acikin idanuwanta,tsananin tausayinshi ne ya kamata,dama sai da Uncle yace bazai iya kwana a cikin gidan ba,Amma yace zai iya,wani iko na Allah,babu halittar da Sgr ke jin shakkarta irin sauro,Gashi Yau Allah ya haɗasu,ƙananun ƙwari sun firgita babban kwaro,Shaggu sun ga Farar fata,burinsu kawai su tsotsi jininshi,Dama abu tubarkalla masha Allah,
  gaba daya hannayenta na asaman bayanshi,ya cusa kanshi a kirjinta,numfashin shi da wani irin huci yake fita,
   Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Ya rafayet,dan Allah ka natsu,zanje wurin daddy na kar6o mana maganin sauron,"tayi maganar tana ƙoƙarin janye jikinta daga nashi,ƙin barinta yayi,yaƙi yarda ta motsa daga jikinshi,gani yake kamar in tabar wurin Saurayen zasu shanye mashi jinin jikinshi ne,
  Ganin yaƙi sakinta yasa takai hannu ta ɗauki rigarshi da yayi wurgi da ita gefe saman bedmattress ɗin,Ruƙo rigar tayi a hannunta,ta shiga kore mashi saurayen dake akewaye dasu,

Duk wannan budurin da akeyi,Abusufyan na kwance saman doguwar kujerar,Shi kanshi zafi ya ishe shi ga saurayen a kewaye dashi,Amma hakan baisa ya farka ba,sae faman juyi yake yi,
   (Allah sarki,haka talaka ke fama,da zarar an ɗauke da wutar nepa lokacin zafi,Ya rasa inda zaisa kanshi,ga sauro ga zafi,yayin da masu kuɗi ke can suna shan sanyin A.c,a lokacin zafi,idan kuma na sanyi ne su kunna room heater,Talaka kuma Ya hura garwashin wuta😥)
Chapter 100 · 0% Book details