← Book details Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 212

Sashe 1

Abban Sojoji Takun Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

Zagayeta su kayi gaba ɗayansu,su jahad na ambatar sunanta,fawan ne ya ɗauko masu ruwa a fridge ya dawo ya miƙa ma uncle ɗinsu,kar6a yayi tare da buɗe murfin ya ɗebo ruwan hannunshi nata kerma ya watsa mata shi a fuskarta,nan take ta farka tana faman yin atishawa,Alhamdulillah suka shiga faɗi suna kallonta,yunkurawa tayi ta tashi daga zaune tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ta mayar da idanunta akan Su hosana da jahad da suka zuba mata ido,
   Muryarta na rawa tace"jaj..jahad hos...sana...ku ne?ko dae idona ne ke nuna mun ba dai dai ba?
  Ba ƙaramin farin ciki ne ya lullu6esu ba sehrish ta dawo cikin hayyacinta ta gane su,atare suka faɗa jikinta suka rungume juna suna kuka,
  Murmushi kawai Abusufyan ke saki bashi kaɗae ba ma fuskar kowannansu na ɗauke da murmushi,musamman Abbansu junaid farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,haka hajiya azeemarsu har cewa take yi"yanzu nan waɗannan ƴan ukun duka namu ne?ƴa'ƴan mu ne?Allah abun godiya,yau dole in yi nafilar dare don miƙa godiyata ga Allah S.W.A daya nuna mun ƴa'ƴan abusufyan ɗinmu da ranmu kuma da lafiyarmu,Ashe dae da rabon yara suga danginsu,bayin Allah sun sha wahalar rayuwa,amma bakomai har yanzu lokaci bai ƙure mana ba,zamu nuna maku soyayyar da baku samu ba arayuwarku,Zamu baku duk wani jin daɗi na duniya da kuka rasa,zamu gatanta ku,sai mun cika ku da farin cikin da zaisa ku manta duk wani ƙunci da kuka ta6a fuskanta arayuwarku,waɗanda kuma sukayi silar jefa rayuwarku cikin hatsari tabbas sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sunji dama ba'a halicce su cikin duniyar nan ba,

Abbansu junaid ya kar6e da cewa"Ae daga rana irin ta yau su fara ƙirgen kwanakin mutuwarsu,saboda ƙarshen su yazo,sun tabka babban kuskuren ta6a jinin SALAHUDDEEEN HUSSEIN!Wallahi thumma tallahi ɗaya daga cikinsu bazai sha ba!' ranshi amatuƙar 6ace yayi maganar,
   Abbas yace"Abba ina ganin yakamata yaran nan suje su kwanta dare yayi sosai,suna buƙatar hutu,in yaso koma menene gobe zamu ida tattauna akai,'
   Jinjina kai Abbansu yayi tare da mayar da idanunshi kansu sehrish dake manne da juna suna kuka,
   Gyaran murya ya ɗan yi masu,atare suka ɗago suna kallonshi da idanunsu dake zubar da hawaye,
  "Kuyi kuka yara bazan hanaku ba,dole kuyi kuka domin kuwa an cuci rayuwarku,an zalunce ku,an ƙuntata maku,an rabaku da mahaifinku na asali kuma an rabaku da danginku,duk akan laifin da baku kuka aikata ba,saboda son zuciya irin na mutanan nan su rasa akan wa zasu ɗauki fansar su sae akan waɗannan bayin Allahn....  'Shiru ya ɗanyi yana faman sauke ajiyar zuciya,
  abusufyan na zuƙunne akusa dasu ya sunnar da kanshi ƙasa,hakanan ya dinga jin kunyar yaran yana ji aranshi tamkar duk shi ne silar jefa su cikin halin da suka shiga,
  Su fawan kuwa dasu twins irfan jabeer da sauransu duk suna atsaye kowannansu jikinshi asanyaye kamar waɗanda aka zare ma lakka,lokaci guda sukaji tsananin Son yaran ya kamasu,
  duk wannan abun dake faruwa gwaggon katsina,na zaune saman kujera tana ta faman matsar kwalla,har lokacin bata daina tsinar dangin Sayyadi ba,haris sai faman lallashinta yake yi tana buge mashi hannu tana faɗin"ka rabu dani Harisu!abun da ciwo wlh,Zuciyata tafarfasa takeyi,ƴa'ƴan abusufyan ɗina aka wulaƙanta kamar dabbobi?wlh bazan ta6a daina tsinewa Sayyadi ba,munafuki algungumi ɗan wuta,Ya Allah ka tsine ma sayyadi da duk zuriyarshi harda unguwar zomar da ta yanke mashi cibinshi, Ya Allah kayi mana maganinsu,Sayyadi ko ɗan iska,uwarshi ta haifa mana masifa....munafuki lokacin da yake zuwa wurin abu har ƙasa yake zukunnawa ya gaishe Ni,da wata guntuwar jallabiyarshi ta gado,ƙafafun nan nashi kaman shebur sanye cikin silifar ɗan ta shegiya...Muna yi mashi kallon Biri yana yi mana kallon ayaba.....'
  sai faman sambatu takeyi abun ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,can kuma tace"Allah sarki abu,nasan yanzu ta gane cewa Allah ɗaya ne,yarinyar nan akwai taurin kai kamar kwallon goruba ga kafiya,kunnuwan nan nata kamar na Zoman daji falo falo dasu,ba irin jan kunnan da banyi mata ba,amma taƙi ji na,Ae ga irinta nan yanzu majnun ya koya mata hankali yanzu tana can Saman bola tana sambatu baiwar Allah,wama yasan uwa duniyar data shiga.......'
  "Sehrish ku tashi ku tafi ɗaki ku kwanta,gobe zamu ƙarasa magana daku," Abbansu ne yayi maganar,
  Miƙewa sukayi tsaye tare da yi masu sallama sannan suka wuce ɗakin nata,gaba ɗaya sehrish ta ɗan shiga ruɗu,batasan meya faru ba,amma bakomai yafi ɗaure mata kai ba face ganinsu hosana da jahad,taya akai suka San inda take har suka zo wurinta?abun kamar a mafarki take ganinshi,
  Atare suka shiga cikin ɗakin,anan fa suka tsaya suna kallon juna fuskar kowaccen su ɗauke da tsantsar farin ciki mara misaltuwa,
"Sehrish Ashe da rabon zamu sake ganinki a duniyar nan"?jahad ce tayi maganar yayin da hawaye ke sauka a fuskarta,
ta ɗaura da cewa "Sehrish munyi kewarki sosai,munyi kukan rashinki atare damu,munsha wahala sosai,abubuwa marasa daɗi sun faru damu bayan rabuwar mu dake,amma duk wani hali da muka shiga hakan baisa mun manta dake ba sehrish kullum kina aranmu,koda yaushe muna cikin zullumin a wane hali kike?kina raye kuwa?kina jin daɗin rayuwarki?kina da ƙoshin lpy ko akasin hakan ....'
  jin wannan maganar ta Jahad yasa ta fashe da kuka mai cin rai,janyota jahad tayi jikinta sosai ta rungumeta,itama hosana ta matsa tare da sanya hannayenta ta bayansu,suka haɗe su ukun,sun jima a wannan yanayin kafin daga bisani suka haye saman gadon su duka ukun suka zagaye junansu suna fuskantar juna a zaune
  Sai lokacin sehrish ta buɗe bakinta tare da cewa"inaso ku faɗamun meya faru na daina samun wayar tsohuwa,sannan kuma inason jin yadda akai har ku ka san inda nake,nayi mamakin yadda na manta daku gaba ɗaya acikin rayuwata,nasan ban kyauta maku ba,Amma kuyi haƙuri ku yafe mun........'
  ta ƙarasa maganar tare da kai hannunta ta shafo gefen fuskar hosana tana kallonta da idanunta waɗanda suka canza launi sosai,sai lokacin ta gane cewa ashe sune yaran da Marshal Omar ke ruƙo a wurinshi,rashin sani yafi dare duhu,har waya suka yi dasu jahad amma bata ganesu ba,saboda bata acikin hayyacinta,
  Jahad ce ta kwashe dukkan abunda ya faru tun daga kan Jefa wayar tsohuwa da hosana tayi acikin Masai da kuma mutuwar tsohuwa,da kuma zamansu acikin cell,haɗuwarsu da Marshal Omar,zamansu a wurin gwaggon katsina da kuma rayuwarsu agidan Aunty babba,komai ta sanar mata,
Sosai sehrish tayi kuka tamkar ranta zai fita,har zazza6i saida ya lullu6eta nan take,bakomai yafi girgiza ta ba face mutuwar tsohuwa,da kuma zamansu hosana a gidan Aunty babba,abun ba ƙaramin ta6a zuciyarta yayi ba,wani irin ciwon kai ne ya rufar mata mai raɗaɗin gaske,rarrafawa tayi ta koma gefe guda saman bed mattress ɗin ta kwanta tare da janyo pillow ta rufe fuskarta dashi,Wurinta su jahad suka koma tare da kwantawa kusa da ita,kowanannsu na acikin yanayi,tabbas sunga rayuwa......

Daƙyar bacci 6arawo ya sace su,amma fa dukkansu babu wanda babu zazza6i ajikinshi,

Kowa fa ya manta da cikinshi saboda lamarin su hosana,a gidan babu wanda yaci abincin daren shi,saboda ƙunci da takaicin yadda rayuwar ƴa'ƴan uncle ɗinsu ta kasance,

Lokacin da Azmee ta turo ƙopar ɗakin nasu samun su tayi kwance suna bacci kowacce fuskarta ɗauke da hawaye,bacci sukeyi amma hawayen basu daina zuba daga idanunsu ba,ba ƙaramin tausayinsu taji ba,ta jima tana kallonsu kafin ta rufe masu ƙopar ta koma bedroom ɗinta,

Kwance yake asaman katafaren gadonshi,tunda ya dawo bedroom ɗinshi,ya shiga toilet yayi wanka,ya dawo ya kwanta yana tunanin duniya,juyi kawai yake yi asaman gadon bacci yaƙi ɗaukarshi,har lokacin zuciyarshi bata sauka ba,abun ya dame shi sosae,ya tsani zalunci arayuwarshi,ya tsani mugun mutun mai hali irin na dabbobi,tabbas idan har sayyadi ya bari ya shigo hannunshi sai ya ɗanɗani kuɗarshi,daga baya kuma ya dawo yana tunanin wai yanzu ƴar yarinyar nan da take yi mashi aiki,ashe ƴar uwarshi ce?jinin shi?ɗiyar Uncle ɗinsu?hakan na nufin cewa ita ƙanwarshi ce...?
"Wonders shall neva end'ya furta hakan tare da lumshe idanunshi,nan take kuma ya tuna da hoton da Uncle abusufyan ya basu lokacin da suke a U.s,hakan na nufin cewa Hoton yaran ne ya basu lokacin da suke ƙanana,zan tambayi uncle hoton wacece nai selecting acikinsu,as I promised then zan taimaketa da kuɗi ta sayi duk abunda takeso bazan fasa ba...... '

Wasu dae sunyi bacci a wannan daren yayin da wasu kuma Baccin ya ƙaurace ma idanunsu,a tsaye Abusufyan ya kwana idanunshi sun ƙanƙance saboda raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi,bawan Allah,wlh abunda ciwo,taya ma zai iya bacci?yasha kuka dae,ga wani irin Matsanancin ciwon kai da yake fama dashi,yawo yake ta yi acikin dakin yama rasa tunanin da zai yi yayin da tafin hannunshi na dama ke dafe da saitin zuciyarshi,wani irin bugawa takeyi mashi mara daɗi,
Chapter 1 · 0% Book details