← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 168

Sashe 97

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kayan na shiga bayin, ban jimaba na fito gudun kar lokacin salla ya ƙwace min. Saida na farayin sallar magriba sannan. Saboda wutar dake akwai sai na jona hand dryer a soket kawai, nai zaman fara busar da gashina.
       Karatun Al-Qur'anin dana sakane yasa sam banji motsin shigowarsa ɗakin ba, sai da yay sallama, da sauri na juyo dan banyi tunanin ganinsa ba.
     Jay da tun ɗazun yaketa faman sallama ya ɗan tsura mata idanu, daya shigo baiga kowa a falo ba, har yay tunanin nufar nasa ɗakin sai kuma ya nufo nan saboda jiyo sautin karatu.
     Towel ɗin dana tsane kai na ɗauka na ɗaura a kafaɗa ta ya ɗan rufemin ƙirji, wanda na ɗaura ɗin kuma sai faman jansa nake ƙasa dan cinyoyina duk a waje suƙe. Ganin ya ɗauke kansa tamkar baiga abinda nakeyinba ya sakani saurin cemasa, “Sannu da zuwa”. “Yauwa sannunki kema”. Ya faɗa yana ƙarasowa cikin ɗakin sosai. Zama yay a bakin gadon yana sauke numfashi alamar gajiya. Daurewa nai na tashi, na raɓa ta gefensa na ɗauka kayana dake saman gadon zan nufi bayi dan na saka sannan na dawo ɗauka masa ruwa da zaman busar da kan.
          “Da miye na saurin yin wankan tunda kinsan bai tafiba?”. Maganarsa tazomin a bazata. Cak na tsaya tare dayin ƙasa da kaina dan ni bansan wace amsa zan bashi ba nikam, yaushe yasan nayi wankan to? Anya boss bai gani har hanji kuwa?.
       Ganin yanda ta wani tsume waje guda ya sakashi miƙewa yana girgiza kansa, zare rigarsa yayi ya raɓata ya wuce batare da ya sake cewa komai ba.
          Ganin ya shige bayi nai azamar saka kayan sauri-sauri sannan na fita na ɗaukko masa ruwa, zaman busar da kan na sakeyi yanzun kam hankalina kwance, saukar laimar ruwa da naji a kan hannuna ya sakani saurin ɗagowa na kalli mirror'n, shine tsaye a bayana, sakar masa hand dryern da yake ƙoƙarin amsa a hannuna nayi ina rumtse idanu, dan wani irin masifaffen harbawa zuciyata tayi, karan farko da naga namiji a tuɓe kamar haka a gabana bayan jazuga da baida wani fasalin kirki irin na zaratan maza. a raina rayawa nake, ‘Wai miyasa maza sam basu da kunya ne? Daga shi fa sai towel iya ƙugu zuwa gwiwa amma ya iya fitowa gabana ya tsaya’.
       Jay da duk yana kallon yanda ta rikice ta cikin mirror'n yay guntun murmushi kawai yana ƙarasa busar mata da kan, sai da ya gama tsaf ya ɗauki ribbon ɗin da yaga ta ajiye ya ɗaure matashi tsaf fiyema da yanda zatayi, harda su mata wani ɗan style da brush. Kujerar ya juya ya maido fuskarta inda yake kafin ya miƙar da ita tsaye ya ɗaura duka hannayenta saman ƙirjinsa daketa raɓar ruwan wanka. “Buɗe idonki” ya faɗa babu wasa.
          Hannunta dake ɗan rawa tai ƙoƙarin zamewa tana maƙe kafaɗa alamar “Ah-ah”. hannun nata ya maida da ƙyau, yana bin fuskarta da kallo. A bazata ya sumbaci inda batai zatoba duk da akwai riga a jikinta. A take ta waro idanu waje da masifar sauri tare da buɗe baki. Babu shiri Jay ya ƙyalƙyale da dariyar da bai niyyaba, dan yaga tsoron nata fiyye da yanda yake son gani.
       Bilkisu tai saurin duƙewa tana matse hannayenta duka biyu a ƙirjinta tare da cusa kanta duka a cikin cinyoyinta tana murmushi, dan ita kanta tabama kanta dariyar abinda tayin. Ga kunya mai tsanani akan abinda yayi ta lulluɓeta. Kafaɗunta ya kama ya ɗagota yana murmushi, duk yanda yaso su haɗa ido taƙi, daga ƙarshema saita ɗora kanta a ƙirjinsa ta ɓoye fuskar. Rungumeta yay da duka hannayensa yana murmushi tare da shaƙar ƙamshin da gashinta keyi da jikinma nata ya lumshe idanu. Kusan mintuna biyu suna a haka sannan ya zauna a bakin gadon ya ɗaurata saman cinyarsa. Fuskarta ya ɗago yanda zata kallesa duk da dai tanata faman yin ƙasa da idanu amma tana ganin fuskar tashi. Laɓɓansa ya nuna mata da ɗan yatsa yana wani ƙanƙance idanunsa. Kafaɗa ta maƙe da sake maida kanta a ƙirjinsa.
     “Ni ai sai nayi” yay maganar yana yin baya dasu a kan gadon ya birkiceta ta koma ƙasa. A take idanun bily sukayo waje, hanata dukkannin dama yay ya shiga yin yanda yaso da ita.
                Kiran sallar isha'i ne ya ƙwaci Bilkisu a hannun Boss, shima da ƙyar, dan daga kiss sai salon ya nema canjawa. Tunda ta samu ya barta ta cusa kanta cikin filos. Baice da i

ta komaiba shima ya fice yana murmushi. Ɗakinsa ya nufa ya sake ɗaura alwala da canja kayansa zuwa blue jeans da t-shirt itama Blue, ya saka turare kaɗan da ɗaukar wata ƴar ƙaramar bindiga ya saka a gefen ƙugunsa sannan ya fito. Ɗakin Bilkisu ya koma. isketa yay ta fito daga toilet fuska a jiƙe alamar alwala tayo. Ruwan data ajiye masa ɗazun ya ɗauka yana sha idonsa a kanta. Kofin ya ajiye yana kallon agogon hannunsa, “Bara naje za'a shiga salla, idan an idar zan ɗan ƙarasa wani waje insha ALLAH kafin goma zan dawo.
        Da sauri Bilkisu ta kallesa idanu cike da ƙwalla, “Dan ALLAH mu tafi tare, nidai tsoro nakeji”. Yanda ta kumbura baki taso bashi dariya, amma sai ya danne abinsa ya taka zuwa inda take tsaye, fuskarta data duƙar yasa hannu ya ɗago, acan ƙasan maƙoshi yace, “Kin taɓa ganin amaryar kwana ɗaya a gidan miji ta fita?”. “To ai babu wanda zaisan na fita tunda dare ne”. Fuskar tata ya saki yana ɗan ɗage kafaɗa, “Okey, ki shirya kafin na dawo salla saimu je”. Cike da murna ta amsa masa da to. Goshinta ya sumbata ya juya ya fice yana murmushi dan wayo kawai yay mata ba dawowa zaiyi ba.

        Ana idar da salla Jay ya fito daga massallaci, motarsa da dama ya bari a waje bai shiga da ita gida ba ya shiga ya bar anguwar, kai tsaye address ɗin da dattijon nan ya bashi ya nufa, anguwace irin sabuwar anguwarnan da uncompleted building sukama fi yawa, sai dai inda gidan drama'n yake anɗan gaggama wasu gidajen dan wajen harya fidda santa ɗoɗar, bakajin hayaniyar komai saina Genretor ɗin da suka kunna da ƴar hayaniyarsu alamar basu gama zuwa ba, akwai ƙwayayen wuta a waje da suka haska kusan rabin layin, sai mai Nama daketa faman haɗa wuta, gefensa mutum biyune ɗaya mai ruwa ɗa kayan drinks, sai saurayi da budurwa dake can gefe suna hira, sai kuma masu shiga da fita cikin gidan ɗai-ɗai dan yanzu suke kan zuwa. Waya ya ɗauka yay kiran wani abokinsa da ya kasance ainahin police, saida suka gaisa ya gama tsokanarsa da ango-ango, sannan Jay yace, “Auwal kuna garin nan amma tsageru har suke da lasisin buɗe wuraren iskanci irin haka?”. Daga can Auwal yace, “Haba dai Jay, kaima kasan hakan bazai kasanceba”. “Gashi kuwa na gani da idona, akwai wani gidan Drama a sabuwar anguwar nan data kusa haɗewa da jan-ɓauna, inason ƙarfe goma da rabi kuzo wajen kuyi kamen kan mai uwa da wabi”. Bai jira cewar Auwal ba yace, “Mu kwana lafiya” ya yanke wayar. facemask ya ɗauka ya saka tare da facing cap,  kallon kasan yayi a madubi ya tabbatar komai yayi kafin ya fito bayan ya kashe motar. Sai da ya tabbatar babu wanda yaga fitowarsa sannan ya nufi gidan.

★★★★★★

         Ina idar da salla na koma bakin gado nai zaman jiransa, ganin shiru-shiru sai kawai nahau yin game a waya, hamma na farayi ɗai-ɗai alamun inajin barci, nayi guntun tsaki da kallon agogon ɗakin, tara saura minti ashirin, zamewa nai na kwanta tare da jan filo na ɗaura kaina na cigaba da game ɗin, tun ina ƙoƙarin damƙe wayar dake neman suɓuce min harna yaddata batare dana saniba.
              A firgice na farka jikina na wani irin ƙyarma, ‘innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ na shiga ambata ganin ɗakin dunɗum da duhu bayan kuma nasan fitilar a kunne take, dariyar da aka tuntsure da ita ta sakani sake firgicewa nahau laluben gadon.....
        “Bilkisu! Kenan mai gadon zinari, wato ke amarya ko? Azatonki zaki iya tsere minne? Ke da kina tunanin na barki? Wannan gurɓataccen tunanine bilkisa, na rantse miki yau saina amshi abinda ya kasance cikar burina dan bazan rasa komai a dalilinki ba wannan gangan ne hhhhhhhhhh!!!!!!!!.................✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gama
[1/11, 10:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🥚Ƙwai Cikin Ƙaya🥚
.
Book Two
.
Bilyn Abdull 📚:
Page 42
Chapter 97 · 0% Book details